15
by @aishatouuu
_Aishatou_
***
_________________
A karo na biyu zama ya sake mai da Mai Kano da iyalinsa gidan Aminin sa Sale, tunda suka shigo farkon layin Mai Kano ya hangi sale tsaye a ƙofar gidan shi yana jiran iso war su.
"Maraba da Abokina lalle da dawowa kusa dani ɗan uwa." Bakin Sale a buɗe da fara'a yake faɗin kalaman lokacin da motar ta gama tsayawa suka yi hannu biyu da juna.
"Hhhhh yau dai ƙorafi ya ƙare gamu kusa ko?" Mai Kano ya faɗa yana dariyar jin daɗi.
Kanya bashi amsa Nana data ƙaraso wajen tace "ina wuni Baban Abba?"
"Sannun ku da zuwa uwargida, a'a wai Ni'ima ce ta sake girma haka kai masha Allah, Husnan Baba yada maƙale wa daga baya? zo nan mu gaisa, ko rigimar ce ta motsa?" Sale ya ƙarasa maganar yana kamo hannun Husna data tsaya a bayan Ni'ima, Nana ta kalle ta ta gefan ido, a ranta tace "Munafuka in batayi haka ba tasa a zage ni." Sai kuma tayin gaba.
"Ina wuni Baba Sale?" Ni'ima ta gaisheshi, ya amsa mata da fara'a, Husna ma tace "ina kwana Baba."
"A'a ina wuni dai Husnan Baba, ko kuma nace Ekaro dan nasan Safiya bata wasa da yarenta tun kina ƙarama ake miki Yarabanci zuwa yanzu kuwa ai tuni ya nuna a bakin ki." Sale yayi maganar cikin wasa da sakewa da yara kamar yadda yake a dabi'ar shi, ta wani bangaren kuma yana tuna zaman su na baya tare da Safiyar mace mai karamci da sanin ya kamata.
"Ai yadda kasanta haka ta rene su da Yarabanci da Turanci sosai suka nuna a bakin Husnah." Mai Kano ya faɗa yana ɗan jin wani abu na taso masa, Sale yayi murmushi zuciyar sa fal da tausayin Abokin nasa.
Cikin gidan suka shiga a tare, ginin gidan fuloti guda ne awun igiya babba, ɗakuna huɗu ne a gere uku manya sai ɗan ƙarami daga karshe wanda shi ne cikon na huɗun, banɗakin gidan babba ne ɗaki kuda sai Kitchen da Turken awakin shi daga tacan karshen gidan, tsakar gidan kanta katuwa ce, duka ɗakunan a gyare suke a sumince tsakar gidan ce dai babu suminti da alama za'a sha shara.
"Ku ɗauki wancan ɗakin na karshen gabas nasa an sake gyara shi, ga ɗakin su Khairiyya can (yaran shi) sai su Husna su ɗauka, ni kuma ina kusa da yarana, wannan ɗayan kuma na tsakanin mu raguna nake kulle wa a ciki da daddare saboda mutanen namu kasan Sallah ta matso yanzu sun matsa mana da sata, babu dama dabbar ka ta fita sai wani ikon Allah zata dawo gida, yanzu kuma abun nasu har gida suke haurowa cikin dare su kunce maka dabba, abun kuma kamar da tambaya (asiri ) suke zuwa har suzo su sace su fita baza ka sani ba kai ko motsin su bazaka jiba sai gari ya waye kaga wayam sun yashe ka." Sale ya faɗa da alhini.
Mai Kano yace "Subhanallah yanzu kuma haka suka zama a gidan ma kayan mutum bai tsira ba?"
"Ai kaidai bari lamarin mutanen nan namu sai dai Allah ya saka mana, kasan shekaran jiya aka shiga gidan Mamuda na nan gaban mu kaɗan wallahi raguna biyu suka kunce masa, kuma abinda zai baka mamaki gana ƴan gargajiyar unguwar nan a waje duk a titi suke kwana amma ko da wasa bazaka taɓa jin ance an sace musu dabba ba."
"Eh to ai kasan ba'a raba su da ƴan kange kange, gaskiya kayi dabara gwanda ka rinƙa kullewar, Allah ya sake shiga tsakanin mu dasu."
"Amin ya Allah." Sale ya faɗi.
Cikin ƙanƙanin lokaci aka gama shirya komai ɗakin su Husna Mai Kano da kansa ya shiga yasa musu katifa ya buga musu net (gidan sauro) saida suka tabbatar da komai yayi daidai sannan suka fice daga gidan zuwa masallaci dan gab ake da kiran sallar Magarba.
Suna tafe suna hira wanda kallo ɗaya zaka musu ka sheda cikakkun abokai ne.
"A'a Malam Abdullahi yau kaine a anguwar tamu?" Malam Malam ya faɗa yana duban su dai dai lokacin da suka iso ƙofar gidan shi.
Sale ne ya karɓe zance da cewa "wallahi shi ne gashi nan na sake nemo mana shi."
Mai Kano suka gaisa da Malam Malam ya tambaye shi almajirai yace "Alhamdulillah"
"To Allah ya taimaka." Mai Kano ya faɗa sunayin gaba.
Bayan sun dawo daga masallaci suna tsaye a ƙofar gida suna sake tattauna wa Mai Kano ya dubi Sale yace "wai ni kuwa ya wajen Abba? Yanzu komai yayi daidai ko?"
Sale ya girgiza kai fuskar shi har ta canja yanayi "lamarin Abba ai sai addu'a, Yaron nan ya zame min jarrabawa, ko kasan ya sake guduwa daga makarantar dana cema na canja masa?"
Mai Kano ya zare ido yace "ya sake guduwa kuma?"
"Eh, kwanan shi huɗu acan Malamin su ya kirani yace min basu ganshi ba, ban tashi hankali na wajen neman saba dan kasan wannan ba shi ne karon sa na farko yana gudun makaranta ba." Sale yayi furucin cikin rashin jin daɗi.
"Kayya amma ai daka neme sa a ƙalla dai kasan inda yake ko?"
"Mai Kano bazan neme saba, kaga in nayi wasa baƙin cikin Abba ne zai kashe ni nabi uwar shi kabari lokacina baiyi ba, dan haka duk ma inda yake yaje can ya karata daɗin abin Namiji ne shi ba mace ba, kuma rashin zaman Abba a kusa dani shi ne kwanciyar hankali na, kasan halin Abba bajin magana yake ba tunda uwarsu ta rasu komai ya sake kwaɓe wa, kullum cikin kawo min ƙarar sa ake, a unguwar nan ya hana yara sake wa, yaƙi Boko yaƙi Islamiyya yaƙi neman kuɗi to ya yake so nayi masa? Allah ya sani nayi iya nawa yaje duniya ce t......"
"Kai Sale."
Da sauri Mai Kano ya hana shi ƙarasa maganar ta hanyar kiran sunan sa da yayi.
"In rai ya ɓaci hankali fa baya tafiya kada ɓacin rai yasa kayi masa baki ya sake lalacewa, nasan komai akan Abba nasan kuma shi ne matsalar ka, amma kayi hakuri muci gaba dayi masa addu'a Allah ya dawo da shi kan hanya ya gane dai-dai, sannan dole ka kira yan uwa kaji koya je wani wajen."
Babu karsashi a zancen Sale yace "hmmm! Amin."
........Sannu a hankali rayuwa ta fara tafiya gashi yau har su Husna sun cika kwanaki biyar da dawowa, Sale da Mai Kano tare suke cin abincin dare.
Husna har yanzu Babanta na kula da ita Nana tayi makircin tayi kwantar dakan amma Mai Kano yaƙi sake yarda da ita.
Wannan abun nashi kuma shi ke mata ciwo, kullum da baƙin cikin su take kwana take tashi babu in taga ya saka ta gaba yana jero mata tambayoyin "me kike so? Babu abinda ke damun ki ko?" Duk lokacin da ta gansu haka wani ƙullutun baƙin ciki ne yake ƙume mata zuciya.
Karma inta ganshi yana mata wanki ita kuma ta sashi a gaba tana masa surutu.
Kamar yadda ya saba yau ma da kansa ya shiga ɗakin su ya fara ware kayan dattin Husna yana fitowa dasu waje, tunda Nana taga haka tasan wanki zai yi mata.
"Ke Ni'ima kema ɗebo naki kayan Baban ku ya wanke miki ai ba ita kaɗai bace ƴar sa kema fa haihuwar ki akayi, yarinya ta zame mini kishiya dan masifa." Nana ta faɗa tana huci dan yau ji take komai za ayi saidai ayi wallahi amma ta gaji da wannan iskancin.
"Kema dai Nana nice Baban mu zaimim wanki saboda jin daɗi? Ita mafa kinsan dan ba zata iya bane yake mata ke kuma kince ba zakiyi mata wanki ba." Ni'ima ta faɗa mata haka kanta tsaye.
Nana tace "Allah ya tsare ni da yiwa ƴar kishiya wahala."
Sai kuma fuuuu tayi ɗakin ta, sai gata ta fito da zanin gado daidai Mai Kano da baisan me ake ba ya kwaso kayan wankin Husna ita kuma ta ɗebo wasu tana cewa "yawwa Baba kace zaka fara koya mini wanki ko?"
"Eh amma saikin ƙara girma." Ya bata amsa yana zube kayan a hanyar banɗaki.
"Ga wannan saika haɗa da shi ka wanke mana dan Wallahi bazan iya wanke wa ba." Nana ta fadi a gadarance tana aje zanin gadon a kusa da shi.
Bawai bazai iya wanke mata bane amma yadda tayi masa maganar ne baiyi masa ba dan shi ba danta bane, har ya buɗe baki zai yi mata magana sai kuma ya fasa saboda yara na wajen bai kamata yana kulata sunayin magana irin wannan a gaban suba, maimakon haka saiya kalli Husna yace "ɗakko wancan ƙaramin botikin kizo."
"To." Ta juya da sauri inda botin yake ta dakko.
Kujera yasa mata a gaban shi yace ta zauna, ruwa ya zuba da omo a botikin ya ware pant da bes ɗin ta ya bata.
"Ki fara wanke waƴan nan in naga sun fita saina sake baki ɗan kwali ki wanke in kuma basu fita ba shike nan Husnan Baba bazata iya wanki ba."
Ai kuwa cikin murna dajin daɗin itama yau zatayi wanki ta fara wanke kayan tana ta zuba masa surutu, yayin da hakan ya sake kona ran Nana dan duk abinda suke tana kallo kuma tana jinsu.
"Wai kai da Mijin ka baza kuyi hira ba, inya dawo hankalin shi nakan yarinya ƙara ma dan jaraba." Nana ta fadi a zuciyar ta tana sake sake.
"Baba na gama wanke wa kuma duba ka gani ai sun fita ko?" Husna ta faɗa tana nuna masa cikin botikin.
Ga mamakin shi sai yaga kayan sun wanku sai ɗan abinda baza'a rasa ba.
"Gaskiya Husnan Baba tayi ƙoƙari, inye shi ke nan ta fara iya wanki."
Ai kuwa daɗin maganar shi yasa ta kyalkyale da dariya sai kuma tace
"Yawwa Baba yaushe zaka kaini wajen Mama da Yaya?"
Shiru ya ɗanyi yana haɗa abinda zai ce mata dan tambaya ce da bata gajiya dayi masa ita.
"Kin tuna nace miki Mama bata nan tayi tafiya?"
"Eh." ta ɗaga kai.
"To bata dawo ba amma inta dawo zan kaiki."
"To wajen Yaya fa?"
Kanya bata amsa Allah ya cece shi Sale ya shigo gidan hakan kuma shiya ɗauke hankalin ta akan maganar amma yasan ba mantawa tayi ba.
Dama ɗazu a kasuwa Abdussamad yazo yace masa yaje gidan shi ance masa basa nan sun tashi. Shi wallahi gaba ɗaya ya manta bai faɗa musu ya tashi ba sai lokacin yake sanar da shi tashin sa daga gidan.
Abdussamad yace "Allah yasa Albarka in sha Allah zan shigo duba Husnah." Ya faɗa yana miƙe wa suka yi sallama ya tafi.
WASHEGARI
ɗan Malam yazo yiwa Nana cefane tace wa Husna "ke ƴar hutu wacce ba yar wahala ba tashi ki bishi kiga inda yake siyo komai nagaji da cida ke a banza niba wata uwar kike tsinana min ba."
Babu musu Husna ta saka hijabin ta tabi ɗan malam cefane.
Ranar cefanan gidan tare suka yishi, shi ke nan kuma tun daga ranar Nana ta sallamin ɗan malam Husna ke zuwa cefane, gashi dan baƙar mugunta Nana bata tashi aken ta sai taga rana ta take. Haka zata aike ta tayi ta gallafiri a unguwa ga wajen aiken ba daya ba ba biyu ba.
Kanta gama mata aiken duk tayi firgai firgai da ita.
In taje ta tadda layi ta dade kuma inta dawo saita zage ta tsaf, duk wannan abun da ake kuma Ni'ima na zaune tana kallon su Nana bata isa ta sata abu ba saita gadama zatayi inta matsa mata kuma tace "Nifa Nana saina kwashe kayana na koma wajen Dije haka kawai bazaki hanani hutawa ba."
Wannan yasa ko aikin cikin gidan Nana bata saka Ni'ima sai wanda taga dama zata taya ta.
Husna ke tafe tana ta duba hanya, daga gidan su zuwa gidan Malam Malam taje ta dawo yafi a irga tana neman kuɗin da Ni'ima ta aike ta ta siyo mata riɗi a gidan Malam Malam, saida taje siyan riɗin ta rasa kuɗin ta sake biyo hanya kuma bata gani ba.
Jikin ta asaɓule ta shigo gidan tana raɓe wa, Ni'ima ta zuba mata harara tace "Wato ke indai aka aike ki saikin shanya mutane kanki dawo ko?" Ni'ima ta faɗa a zafafe Husna ta sake komawa baya. Nana tace "Au yau da yake naki ne aiken ai kin magantu dani na aike ta ta daɗe haka nayi mata magana da tuni kince nina fiya masifa." Nana tayi maganar tana taɓe baki.
"Wai aiken ne bazaki kawo min ba ko me kike nufi? Dama kin raina ni tunda kinga kanmu ɗaya ko Ma'u?"
Husna dai tana tsaye a bakin kofa ita bata shigo ba ita bata fita ba.
Saida Ni'ima ta shammace ta sannan ta danƙi rigar ta batayi wata wata ba ji kake "kauuuuu." Ta wanke ta da mari tace "Dan uwarki ina aiken dana miki?"
"Ku....Ku....Kuɗin ne ya faɗi." ta faɗa tana fashewa da kuka dan sosai marin ya shige ta.
"Kan bala'i ke kin isa ki yarmin da kuɗi, baki taɓa yarda kuɗin kowa ba sai nawa saboda kinga ina raga miki?"
"Tass.....tass." Ni'ima ta sake wanke mata fuska da wasu marinkan guda biyu a jere sai kuma taci kwalar rigar ta kamar wata sa'ar ta.
Nana dake kallon su daɗi ya cika zuciyar ta tace "da kyau dama ai lefin kine Ni'ima da kika bari ta rena ki."
Ta ɗaga hannu zata sake marinta Abba ya shigo cikin gidan kanshi yayi wani irin aski tsakiyar kan anyi masa wani abu cibiri cibiri kamar kitso, wandon jikin shi kuwa irin crezy Jens ɗin nan ne da kaɗan ya wuce gwiwar sa singlet ce kawai a jikin sa baƙa kana ganin shi kaga irin yaran nan da basa jin magana cikin maganar sa ta marasa ji yace "Ke daga ina kike kin maƙale yarinya zaki more ta?" ya faɗa yana shigowa cikin gidan gaba ɗaya, Ni'ima ta bishi da kallon rashin sani, sai lokacin kuma Nana dake kwashe shanya ta ɗago kai ta ganshi, itama da ɗan Mamaki take duban sa dan bata sanshi ba.
"To kai kuma daga ina zaka shigowa mutane gida babu sallama." Nana ta faɗa tana ƙare masa kallo.
Baibi takan maganar Nana ba ya cewa Ni'ima "ke dalla sake ta, kibar nan."
"A'a kai asuwa to? Kasan me tamin ne da zaka ce na sake ta? Haka kawai ka shigo gidan mutane kace zaka baza mata iko." Ni'ima ta faɗi maganar cike da fitsara.
Abba yayi wata dariyar rashin mutumci yace "tab amma yarinyar nan yau kinci bulus kinyi sa'a yanzu na dawo bana son daga zuwana tsohon can yazo ya fara min faɗa amma bamda haka da kinci uwarki yau."
Sai kuma ya haɗe rai yace "sake ta tayi gaba ko naci kazar ubanki." Abba ya luƙa mata ashar ɗin da Ni'ima da Nana basu taɓa jin irin taba, Husna kuwa saida ta tsorata da tsawar daya yiwa Ni'ima.
"Ke sake ta karya buge ki daga ganin wannan ba ɗan arziki bane." Nana ta faɗa tana janyo Ni'ima baya.
Abba yabi su da kallo yace "ke tsohuwar banza zanzo kanki." Sai kuma ya juya wajen da Husna ke tsaye tana share hawaye yace "dalla kema bar nan."
Ga mamakin sa sai yaga itama tayi cikin gidan yabi bayan ta da kallo.
Kamar ya shiga cikin gidan sai kuma ya juya ya fice, dan yaga alamar Baban sa yan haya yasa a gidan su.
Da daddare su Mai Kano suna zaune suna cin tuwo Sale ya dubi Mai Kano yace "wai kasan Abba ya dawo kuwa?"
"Alhamdulillah ya baro wajen Nasurun ke nan?" Mai Kano ya faɗa.
Sale yayi murmushin da kana gani kasan bai kai zuciya ba yace "wazai iya zama da Abba ai sai iyayen shi suma danya zame musu dole ne, kasan Allah kaga nina haifi Abba ko? To wallahi dazan samu inda zan kaishi ya zauna da kaisa zanyi nima kona huta da tashin hankalin da yake sani."
"Kayya nace ka daina faɗin haka a kansa amma baka ɗauka kaifa ubane ya kamata kana sanin mai zaka rinƙa faɗi akan sa." Mai Kano ya kwabi Sale.
"Kayya a rashin ji wanne irin ne Abba bayayi? To inka cire sata wallahi ko wanne iskanci daka sani Abba yasan yadda ake yin sa, ni ƙarin damuwa ta ma yaƙi neman kuɗin arziki sai korar jakai, yaƙi karatu da ƙyar fa ya kammala aji ukun Sakandire, ."
Mai Kano yayi shiru yana tunanin abinda Nana ta faɗa masa ɗazu "oh shiya shigo gidan ke nan, tabbas shi ne Nana bata sanshi ba shi yasa tace wani." Ya ayya maganar a ranshi sai kuma yaja numfashi, ya fara dannar Sale dan tabbas Abba jarrabawa ne a gare sa.
Washegari Mai Kano yayi wa Nana bayanin waye Abba sai dai bai faɗa mata halayen saba.
"Shi dai yanzu wannan mai zubin marasa mafadan kana nufin ɗan Sale ne na cikin sa Baban Ma'u?" Nana ta maimaita zancen tana kama baki.
"Eh ɗan sane shine babba sai ƙannen shi biyu mata suna hannun yayar Sale, saiki kama kanki, yawwa maganar da kika min shekaran jiya nace a'a." Ya danyi shiru yana juya zancen dan harga Allah ba'a son ranshi zaibar Ni'ima zuwa makota tayin kwana ba, amma babu yadda ya iya hakan ya kamata yayi yasan Sale bazai ce su bawa Abba ɗaki ba saidai shi a matsayin sa na wanda yasan daidai dole hakan za'ayi.
"Wai maganar taya Amarya kwana kake nufi?"
"Eh ita, kince ita da yar Malam Malam ne zasu rinƙa taya ta kwanan ko?" Ya faɗi yana duban ta.
Nana tace "Eh haka tace, yarinyar nada kirki dan tunda aka kawo ta garin nan tana yawan shigowa mu gaisa, Mijin nata ne wai inya tafi sai yayi wata uku huɗu bai dawo ba kuma ita ba yar nan bace daga Jalungo aka kawo ta."
"Ni duk ban tambaye ki wannan ba, ke kinsan badan dawowar yaron nan ba da babu inda Ni'ima zata wani tayin kwana makota to dole ce tasa, na yarda taje su kwana gari na wayewa kuma ta dawo gidan nan, in sha Allahu zuwa karshen watan nan za'a fara ɗora min gini, kuma ki kula da itafa banda gantali iya kwana zatayi ta dawo in lokacin kwanciya yayi ta tafi da safe ta dawo gida."
"To shike nan." Nana ta amsa tana tunanin yadda zai yi da Husna, kamar ta tambaye shi sai kuma tayi shiru tana addu'ar Allah yasa ya maida ita can dangin uwarta ita ma ta huta da baƙin cikin da suke ƙunsa mata.
Saida ya kira Ni'ima da kansa ya sake ja mata kunne sosai sannan ya shiga ɗakin su ya fara fito da kayan su.
Kayan sawar Husna ne kawai a cikin ɗakin sai katifar su dan kayan Ni'ima suna ɗakin Nana.
Abun ya bawa Nana mamaki ganin Mai Kano na kafa bululluka a ƙarshen ɗakin dake tsakanin su wanda ragunan Sale suke kwana.
Saida ya gama jera bulon sannan ya ɗakko ƙyauran daya fara siya na gidansa yana ajiyewa ya ɗora akan bulon wajen sai yayi kamar gado, Nana bata sake tsinkewa da lamarin Mai Kano ba sai da taga ya ɗakko katifar Husna ya ɗora akai, ya sake sharo ɗakin tas dama ya wanke shi kan ya fara aikin, kayan sawar Husna yasa a saman katifar yabar gefe ɗaya inda zai ishi mutum kwanciya.
Saida ya gama aikin yana wanke hannu sannan Nana ta ce "wai wa kayiwa makwanci haka?"
Bai dube taba yace "Husna ce zata rinƙa kwana a ciki kafin muga abinda Allah zai yi, in sha Allah ginin nan ba zai cini wata biyu ba, inna samu nayi mana ko ɗaki biyu ne kawai saimu koma na ƙarasa sauran muna ciki."
Nana tayi sororo tana kallon shi kamar ta sake cewa wani abu sai kuma tayi gum da bakin ta.
"Meye nawa a ciki yarka ce can ta matse muku."
Ta faɗi a ranta, sai kuma ta tafi kai masa ruwan wanka.
Kanya fita saida ya kama hannun Husna ya nuna mata komai tare dayi mata bayanin da zata gane a nutse.
Ta ɗaga kai ta kalli Baban nata bayan ya gama yi mata bayanin a nan zata dawo da kwana tace "Baba kuma da ragunan Baba Sale zan dinga kwana?"
Saida ya tsuguna a gaban ta dai-dai tsayin ta sannan yace "kiyi hakuri kinji babu abinda zasu miki kuma kinga ai ina kusa ko? komai kikaji ki kirani zanzo kinji, in kika yi Sallah kiyi tamin addu'a na samu kuɗi na gina mana namu gidan da wuri kinji ko?" Husna baiwar Allah babu musu ta ɗaga masa kai.
Sale baisan mai yake faruwa ba saida ya dawo yaga abinda Mai Kano yayi ai kuwa nan yace sam bazata yiwu ba.
"Haba Abdullahi ya zaka min haka? Shiba namiji bane yaje can cikin abokan shi ya kwana." Sale ya faɗa. Mai Kano ya tari numfashin sa da cewa
"Muda muke addu'ar Allah ya shirya mana shi sai kuma mu sake tura shi ciki su? Kaga karka damu duka kwana nawa ne? Asiri ma ai ya rufu tunda da wajen kwanciyar."
"A'a wallahi, a ina asiri ya rufe kasa yarinya kwana da dabbobi, to kuwa sai dai na fito dasu waje in rabone a samu."
"Wallahi bazaka fito dasu ba inka fito dasu kuma to ka nuna min iyaka ta Sale." Mai Kano ya fadi maganar cikin tabbatar wa.
Wannan abu baiwa Sale daɗi ba amma babu yadda ya iya da Mai Kano dan yayi kicin-kicin da fuska.
A ranar farko da Husna fara kwana da raguna a ɗakin suna ganin mutum a ɗakin su suka rinƙa kuka, ita ma kusan kwana tayi tana kukan da babu wanda ya sani, kuka tare irin kukan nan da ake kira da kukan rashin madafa, kukan maraicin uwa, kukan da babu mai baka haƙuri ka daina, duk da ƙananun shekarunta amma wani irin ciwo take ji aranta, nan da nan ciwon kai mai zafin da har cikin Idanunta take jinshi ya rufe ta bata samu bacci ba sai can cikin dare bacci yayi awon gaba da ita Idanun ta sharkaf da hawaye....