10
by @nanadiso10
PAGE 10.
Nayla basu dawo ba sai after magrib Rayyan yaje da kansa ya dauko su, dama yayi waya da ita yace su jirasa zai zo ya ɗauke su, tafe suke Suhayla sai labari take zuba masa kamar yadda suka saba yi masa aduk lokacin da suke tare, sai dai wannan karon banda Nayla bata ce komai ba tunda ya ɗauko su, ba tare daya kalleta ba yana driving “Nayla what's happening?" Juyowa tayi ta kallesa jiki a sanyaya, a yau kaɗai, acikin awannin da basu gaza biyar zuwa shida ba ta faɗa soyayyar wanda bata taɓa gani ba sai yau, soyayya mai zafi da tunda tayi ido biyu dashi sai nukurkusar zuciyarta take yi, gashi takasa fadawa ko da Amnah ce balle ta samu sassauci abinda take ji, ji take yi kamar tai karfin halin sanar da yayan nata sai dai bata san taya zata fara yi masa bayani ba, ɗauke kanta tayi tana kallon gefen fito jin ya sake jefo mata tambayar "nothing Yaya.” "Are you sure?" “Up course." Jin ta tabbatar masa da haka sai kawai ya share zancen, a wani mall ya tsaya ya shiga dasu, abubuwan duk da yasan suna bukata a matsayinsu na mata yasa suka ɗauko Mom kuma ya siyo mata turarukka sanin yadda take masifar son ƙamshi, dama duk wata yakan ɗaukesu ya kai, ko kuma yaje da kansa ya siyo masu, tun suna yara shi ke maye masu gurbin Dad idan baya ƙasar har ma idan yana nan wajen kula dasu ga duk abubuwan daya san zasu buƙata ba tare da gajiyawa ba saboda yana kallon hakan a matsayin dolensa, a ransa yana ji bai da kamarsu kamar yadda basu da kamarsa, shiyasa ya dauki alwashin zame masu Yaya mahaifi wajen basu kariya da kuma kulawa ga dukkanin abinda zasu buƙata.
Bayan sun gama suka nufi gida Nayla jiki tamkar an yimata duka kai tsaye ta wuce ɗakinta, Allah ne sheda matsuwa tayi su iso gida dan duk wanda ta gani sai taga yana mata gizo da wanda ta gani gidan su Amnah, hatta Ya Rayyan ɗin da suna magana da Suhayla taga yayi dariya sai taga tamkar shi ɗinne lokacin da yake yiwa Ikramah dariya “Ya Allah! Wanene shi?" Nayla ta faɗa kan gadonta tana faɗa tare da rufe idanuwa.
_(Tofah! Nayla ta ɗebo mai zafi zafi💃)_
MONDAY MORNING
Kamar yadda Dady ya faɗa haka ta kasance, tun kafin ya sanar da Alhaji Nuhu Shattima ƙudurinsa na don haɗa yar wajensa da tsaronsa Rayyan yana kiransa akan zancen taron yake sanar dashi bazai samu damar halarta wajen taron ba saboda tafiya Egypt ta kamasa zai kai mahaifiyarsa a dubi idanuwanta da take fama dasu suna yimata ciwo, amma ya sanar dashi zai sa Hanan ta wakilcesa wajen ya tabbatar duk abinda ake buƙata daga ta ɓangarensa zata bayar yadda Yakamata, murmushi Dady yai, a zuciyarsa yana cewa faɗuwa tazo dai-dai da zama, a zahiri kuwa cewa yai babu Matsala bayan ya jajanta masa tare da cewa ya bayar masa da Hajiya idan sun dawo zasu zo dubata shi da iyalinsa, a cikin daren ya kira Rayyan ya sheda masa yana da wani taro da zai halarta yana so shima yake ya wakilcesa a wajen wannan taron, ya bashi duk wasu documents daya kamata, ya yi masa bayanin duk wani abu da za'a gabatar saboda kusan shine jagoran taron, sosai Rayyan ya fahimci bayani sa har yana sake bashi shawarwarin abunda ya dace a wasu wuraren, Dady ya ji daɗi hakan dan haka yace yaje duk abinda ya kamata a gabatar, idan ya dawo daga baya zasu tatfauna matsayar da aka cimma wajen taron da manyan yan kasuwan.
Karfe 8:30am
Rayyan ne ya sauko a gurguje saboda karfe tara za'a gudanar da taron ya ɗan so ya makara, MOMY na kitchen ya saketa acikin yai hugging ɗinta ta baya yana gaisheta, gefen fuskarsa ta shafa “Masha Allah" tana miƙa masa mug din dake hannunta data gama juya tea, yasan bazai tsaya yin kari ba saboda makarar da yai, hakan yasa yana kuran tea ɗin tana saka masa yankin sandwich a baki, bai ci ci uku yai ba da yake team ɗin ba zafi ya karasa shanyewa ya ajiye cup ɗin " Bye Mom.” " Bye my son kayi tuƙi a hankali kaji? ALLAH ya taimaka ya baka nasara." Ta dan ɗaga murya dan tuni ya fita, hannaye ta daga sama “Ya Allah ka haɗa hankalinsu idan ita din alkhairinsa ce kuma matarsa ce." “Amin" ta ji Dady ya faɗa shima daya fito cikin shirin sa, dining suka nufa ya karya sannan ya fice ita kuma Mom takoma ɗaki bayan ta dawo wajen yi masa rakiya tana mai addu'ar Allah ya dawo mata dasu duka lafiya.
Ɗakin taro mai fadi a wani katafaren gini a Paris. Hasken rana mai laushi na shigowa ta manyan tagogi, yana bugawa kan tebur mai sheƙi da matuƙar ɗaukar hankali saboda tsaruwarsa, kana gani kasan wajen tattaunawa ne na manyan mutane akan wani kasuwanci ko wata mafita da ake son samowa ko kuma cimma matsaya akan wani abu, cike yake da manyan yan kasuwa na ƙasar dake neman hadin guiwa da kamfanin kasuwanci na Alhaji Haroon Kareem, kowa ya samu waje ya zauna kujera biyu kacal ce babu mazauna a wajen sai tattaunawa suke yi a tsakaninsu, a dai-dai lokacin ƙofa ta buɗe a hankali, Rayyan ya shigo cikin nutsuwa amma da iko a tafiyarsa. Sanye yake da dark tailored suit deep navy colour mai kyau, Farar riga ce aciki sai tie mai launin dark wine da takalmi baƙi mai sheki (classic Oxford shoes), Agogo ne mai tsada ɗaure a tsintsiyar hannunsa, gashin kansa gyararre sai sheƙi yake yi, ƙamshinsa ne mai sanyi da jan hankali yasa mutanen dake cikin ɗakin juyowa, a hankali ya ƙaraso ciki takalmansa na bada sauti mai karfi kaɗan ya nufi kujerar da yake da tabbacin wajen zamansa ne, cike da mamaki da al'ajabin ganinsa don bashi sukai tsammanin gani ba mutanen dake dakin suka shiga gaishesa.
“Good morning, Mr.” Sai sukai shiru kuma, a hankali bayan ya isa jikin kujerar ya lalle su duka yace "Rayyan." Yana ɗan sauke kai kasa kaɗan alamun girmamawa tare da ƙawata fuskarsa da murmushi sannan ya zauna. Idonsa ya zagaya ɗakin ya hango kujerar ɗaya daba mutum, agogon hannunsa ya duba karfe tara dai-dai, ɗago kai yai zai yi magana ƙofar ta sake budewa a karo na biyu, Kyakkyawar matashiyar yarinya ce ta shigo, takalmin heels ɗinta na bada sauti mai laushi, Sanye take da tailored suit na mata launin soft grey (Paris classy tones) jikinta ya fito da tsari mai kyau amma cikin mutunci. Hannunta na rike da takardu ta yane kanta da mayafi idanuwanta saye da glass da yai matuƙar yimata kyau, takalminta heels ne masu tsayi amma simple nude, Karamin handbag mai kyau luxury but subtle, fuskarta ta ɗanyi Make-up light, natural glow, cikin nutsuwa da kima take takowa kana kallon ta kasan akwai tsantsar ilimi da wayewa tare da ita, Ba ta kallo kowa ba ta nufi kujerar da ita kaɗai ta hango babu kowa akai tana passing ɗin ta Rayyan ta ja ta zauna, a kallo daya zaka fahimci she's Intelligent, calm, amma akwai hidden fire atare da ita, wani irin yanayi mai nauyi ya cika ɗakin, Rayyan ya ɗan ƙanƙance ido kamar mai nazarinta yana haɗe fuska ganin bata cewa kowa komai ba bayan ita kadai ya rage da ake jira, ta ɗago kai kaɗan ta gaida mutanen wajen cikin girmamawa, dan janye idanuwansa Rayyan yai da tana juyowa suka hadu da nasa, kirjinsa ne ya buga lokacin da idanuwansu suka haɗu yana ji kamar ya taɓa ganinta amma ya sani ba su taba haduwa ba da ita ko sau daya idan ba yau ba, me ke shirin faruwa ne akan yanahin da yaji nan take kanta? Saurin bayarwa yai jin wurin yai shiru. Kokarin fara Meeting ɗin akai, nan take aka gabatar da proposals tare da tattaunawa mai zafi akan yadda abun zai kasance daya shafi kasuwancin, bayan an kammala Hanan dake zaune, idan ta kalli wannan yana magana ta kalli wanca, ta mike cikin nutsuwa, ta fara magana da kwarjini tana gabatar da nasu proposal dini, bayan ta gama tace “Wannan tsarin zai kawo sauyi a kasuwa matuka idan aka tsaya aka duba abin da kyau.” Mutane suna sauraronta tare da jinjina kai. Rayyan kuwa dake kallonta
Ba wai proposal ba ne ya dauke hankalinsa akanta ba, Ita ɗin ce da kanta. Bayan ta gama sai ya ɗan jingina baya cike da sanyi “Interesting… amma ba practical bane.” Dakin ya yi shiru. Hanan ta kalle shi kai tsaye, yadda yai maganar daga ƙarshe ya balain ɓata mata dai “Ko kuma kai ne ba ka son ganin wani ya fi ka?” Karamin hayaniya ta kare wajen jin yadda tai maganar itama, Rayyan ya dan murmusa na raini kaɗan. “Ki tabbatar kina fahimtar abinda kike fada kafin ki kalubalance ni saboda muna amfani da hujja mai ƙarfi ne” ya jingina da kujera, hannunsa a hade, idanunsa suna kallon Hanan da wani irin zafi, Hanan kuma ta kauda kai cikin nutsuwa amma fuskarta na nuna karfin hali. Ta dora takardu a gaban ta, tana kallon Rayyan kai tsaye.
Rayyan yasa hannu ga janyo takardun ya duba abinda ke ciki sannan ya mayar ya rufe ya sake tura mata “Wannan proposal din naku ba shi da tushe. Ba zai yi anfani ga kasuwa ba, balle kamfaninmu.” Hanan ta ɗan yi murmushi kaɗan, irin wanda ke nuna ba ta ji tsoro ba sannan tace “Ko kuma dai kai ne ba ka so kuyi rashin nasara ba saboda proposal ɗin nan zai iya zarce naku sau uku.”
Wani daga cikin mahalarta ya yi kokarin shiga tsakani, amma Rayyan ya ɗaga masa hannu saboda game ɗin tasu nishadi take bashi musamman yadda take haɗe rai, Rayyan yana kallonta sosai yace
“Kin tabbata haka? Wannan fa ba wasan yara bane.” Hanan ta matsa gaba kaɗan, idanunta suna haskawa da jarumta
“Ni ba yarinya bace da zaka raina, Rayyan or what?. Kuma bana magana sai da hujja.” Shiru ya ratsa ɗakin. Kowa ya tsaya kallon su.
Rayyan ya dan sunkuyar da kai, yana murmushi kada, amma wannan karon ba raini bane, wani sabon abu ne yake ji a ƙasan zuciyarsa akanta, Ya ɗaga ido ya sake kallon ta a karo na ba adadi…
_Ana wata ga wata, me ke shirin faruwa ne? Aryan ya faɗa soyayya shima a kallo ɗaya, ata ɗaya ɓangaren ya bawa iyayensu zavin su aura masa wacce suke so ba tare da sanin itace wadda zuciyarsa ke so, shin Hannan zata bar abinda ya faru a office tsakaninsu idan aka haɗasu ta karbi soyayyarsa ko kuwa zata ki amincewa ta karɓi soyayyarsa? Ku biyo mu muje_🏃♀️
ZK2026
***
***