11
by @nanadiso10
Manyan directors da investors suna zaune cikin nutsuwa, wasu suna duba documents, wasu suna rubutu, yanayin ya cika da professionalism da hankali, a tsakiyar wannan meeting ne aka ba Hanan damar gabatar da sabon import-export expansion proposal wanda ya shafi shigo da kayan luxury textile daga Turkey zuwa France da kuma rarrabawa a kasuwannin Turai, ta miƙe tsaye cikin confidence, tana sanye da kaya masu kyau amma kalamanta ba su da zurfi, “Based on our projections… I think this deal will generate high revenue…” ta fara magana, tana nuna slides amma ba tare da cikakken bayani ba, ta ci gaba da faɗin kalmomi masu sauƙi kamar “growth”, “opportunity”, “market expansion” amma babu figures masu ƙarfi, babu risk analysis, babu detailed breakdown, wasu daga cikin directors suka fara kallon juna cikin nutsuwa, wasu suka ɗan murmusa a ɓoye, Rayyan na zaune a ƙarshen table yana kallonta cikin nutsuwa, ba tare da ya katse ta ba, amma a cikin idanunsa ana ganin cewa yana nazari sosai, ya lura da yadda take skipping important data, yadda bata yi mention na logistics cost, taxation impact, supply chain risk, currency fluctuation, and ROI margin ba, hakan ya nuna a sarari cewa ba ta shiga cikin document ɗin da gaske ba, amma duk da haka ya bar ta ta gama, saboda yana son ya ji yadda za ta kare kanta.
Ta gama magana tana ɗan ɗaga kai cikin confidence kamar ta yi abin kirki, shiru ya sauka na ɗan lokaci, Rayyan ya sauke idanunsa a kanta a hankali, sannan ya ɗaga kai yana kallon sauran members, ya ce cikin murya mai sanyi amma mai nauyi, “Interesting…” kalmar guda ɗaya ta sa wasu suka gyara zama, ya juya ya kalleta kai tsaye, “Ms. Hanan… how exactly do you expect us to make profit from this deal?” kalmar ta fito da nutsuwa amma cike da tambaya mai zurfi, Hanan ta ɗan tsaya, ta yi ƙoƙarin murmushi, “Well… I think…” ta fara magana amma kalamanta suka rikice, ba ta da cikakken amsa, ta yi ƙoƙarin ƙara wasu kalmomi amma hakan ya ƙara bayyana rashin shiryawa, Rayyan ya ɗan jingina da kujera yana kallonta cikin nutsuwa, “You think?” ya maimaita cikin sanyi, “This is not about thinking… this is about numbers, strategy, and risk management,” wasu daga cikin board members suka ɗan sunkuyar da kai, wasu kuma suka ɓoye murmushi, Hanan ta ji kunya amma ta yi ƙoƙarin kare kanta, “The market demand is high and” kafin ta gama, ya ɗaga hannu a hankali ya katse ta, “Market demand alone doesn’t guarantee profit,” ya ɗan matsa gaba, yana kallon screen, “Where is your cost analysis? Where is your risk assessment? What about import duties? Logistics? Currency volatility?” ya jera tambayoyi cikin nutsuwa amma da ƙarfi, shiru ya sake sauka, Hanan ta kasa amsa, wannan karon kowa ya fahimci abin da yake faruwa.
Rayyan ya miƙe tsaye a hankali, presence dinsa ya cika ɗakin, “Based on this presentation… this deal will most likely lead to loss, not profit,” kalmar ta fito da tabbaci, ya juya ya kalli board members, “Please inform the stakeholders… we need professionals handling this project,” ya ɗan tsaya, “Let’s set a new review session next week… with a proper strategy and complete documentation,” ya ɗauki file ɗinsa ya rufe, ya kalli Hanan na ƙarshe cikin nutsuwa, ba tare da ƙara magana ba ya juya ya fita daga ɗakin.
Shiru ya cika wurin Hanan ta tsaya a wuri guda. Idonta ya cika da hawaye amma ta riƙe kanta. Directors suka fara miƙewa ɗaya bayan ɗaya, babu wanda ya yi jayayya, babu wanda ya yi magana, saboda kowa ya san gaskiya idan Rayyan ya yanke hukunci a business, babu wanda ke musanta shi, suna girmama shi ba saboda shi ɗan Haroon bane kawai ba… sai saboda shi kansa ya tabbatar da ƙwarewarsa.
Kunya ce ta rufe Hanan gaba ɗaya kamar wani nauyi da aka ɗora mata, zuciyarta na bugawa da sauri yayin da take tattara files ɗinta cikin gaggawa, ba ta iya kallon kowa ba, ta miƙe daga kujera cikin rashin nutsuwa ta fita daga Executive Boardroom ɗin RH Global Holdings, takunta ba su da tsari kamar yadda ta saba, zuciyarta cike da kunya da ɓacin rai, tana shiga elevator hannunta na rawa, tana riƙe da wayarta kamar wani abu da zai ba ta kariya, da zarar ta isa parking lot ta shiga cikin motarta Range Rover Velar, ta rufe ƙofar da ƙarfi, ta jingina da kujera tana sauke ajiyar zuciya mai nauyi, “This is embarrassing…” ta furta a hankali, kafin ta iya haɗa tunaninta wayarta ta fara ringing, sunan da ya bayyana a screen ya sa jikinta ya ɗan yi sanyi
Abiey. Ta ɗan tsaya na ɗan lokaci kafin ta ɗaga.“As-salamu alaikum, Abiey…”
Muryarsa ta fito kai tsaye ba tare da wani ɓoye ba “Baby… me kika je kika aikata?”
Kalmar ta sauka da nauyi. Hanan ta ɗan daidaita kanta, tana ƙoƙarin ɓoye abin da ke zuciyarta, “Abiey… na yi yadda ka ce… I followed the document…” Ya ja numfashi mai nauyi daga ɗayan ɓangaren, “Hanan… I gave you a full business proposal… did you even read it properly?” Shiru tayi Ba ta da amsa.
Ya ci gaba, muryarsa na nuna takaici, “What you did in that meeting… babu kwarewa… no structure… no analysis… nothing… wannan kadai ya isa ya lalata duk wani deal da muke so mu samu.” Hanan ta haɗiye wani abu a makogwaronta, kunya ta ƙara rufe ta.
“Abiey…”
Ya katse ta cikin sanyi amma mai nauyi, “Do you even know who you were standing in front of? Rayyan Haroon is not like other boys… he’s trained… he’s built for this… mentor dinsa shi ne Haroon Kareem himself… idan maganar kasuwanci ce… we don’t have anyone above them in Paris.”
Kalmar ta tsaya a zuciyarta. Wannan karon ba kunya kaɗai ba… tsoro ne ya shigeta.
Ya ɗan sauke murya, “Hanan… this deal is important… very important… akwai kudin da ba za mu bari ya kuɓuce mana ba… and you just walked in there unprepared.”
Jikinta ya yi sanyi gaba ɗaya. “Sorry Abiey…” ta faɗa cikin rauni, wannan karon babu iko a muryarta, “What do I do now?”
Shiru na ɗan lokaci. Sai ya yi magana cikin nutsuwa mai haɗe da dabara “Good girl…”
Ta ɗan ɗaga kai kaɗan. “I’ll send you his number…” Zuciyarta ta ɗan buga. “Call him… talk to him… ask for a second chance… tell him you’ll correct the proposal… understand the numbers this time… you need to fix this mistake.” Hanan ta lumshe idanunta. Rayyan
Mutumin da ya tsayar da ita a gaban kowa.
Mutumin da ya karya confidence ɗinta. Yanzu…ita za ta kira shi? Ta haɗiye wani abu.
“Okay… Abiey…” Ya ƙara da murya mai tsauri kaɗan, “And listen carefully… I want that deal… do whatever it takes… but don’t lose it.” Kalmar do whatever it takes ta ɗan tsaya a zuciyarta. Ba ta fahimta gaba ɗaya ba… amma ta ji nauyinta. “Alright…” Ya katse wayar.Shiru ya mamaye motar Hanan ta jingina da kujera. Idonta ya cika da hawaye amma ba ta zubar ba Ba saboda zafi ba…
saboda kunya,Saboda nauyi,Saboda pressure. Ta ɗaga wayarta a hankali.
Ta ga message ɗin ya shigo Rayyan Haroon’s number. Ta kalle shi na ɗan lokaci. Zuciyarta na bugawa. “Do I really have to do this…?”
Ta furta a hankali Amma ta san gaskiya Ba ta da zaɓi ta riƙe wayar da ƙarfi.
*****
Daga fitowarsa daga meeting ɗin, Rayyan bai tsaya ko’ina ba, kai tsaye ya nufi Executive Office Suite dinsa da ke saman ginin RH Global Holdings, tafiyarsa cikin nutsuwa amma cike da iko, ma’aikata suna jere a corridor suna gaishe shi cikin ladabi “Good afternoon sir” yana amsawa da ɗan ɗaga kai kaɗan kawai, presence dinsa kaɗai ya isa ya sanya kowa ya gyara zama, a gefe kuwa Noor na tsaye tana kallonsa da wani irin nutsuwa da zuciya, numfashi ta ja a hankali tana furta a zuciyarta “Ya Allah…” ba ta taɓa ganin irin wannan mutum ba, ba wai kawai saboda kyawun da Allah ya yi masa ba, ba wai saboda kuɗi da matsayi ba, sai saboda yadda yake rayuwa discipline, distance, focus ba ya hulɗa da kowa barkatai, ba ya yin abokai marasa amfani, balle harkar mata, alhali duk wanda ya kalle shi zai rantse cewa yana da duk abin da mace zata nema, amma shi… ya zaɓi natsuwa, ya zaɓi tsari, ya zaɓi mutunci.
Noor ta daure zuciyarta, ta ɗauki file ɗin da take riƙe da shi, ta nufi ƙofar office dinsa, ta yi knocking cikin ladabi knock… knock… “Come in” ya amsa cikin sanyi, ta shigo a hankali tana ɗan sunkuyar da kai “Good afternoon sir” ya amsa ba tare da ya ɗago kai sosai ba “Afternoon” ta miƙa masa file ɗin, “This requires your signature,” ya karɓa ya buɗe, ya duba cikin sauri amma da fahimta, ya sa hannu cikin neat signature dinsa, ya mayar mata, “Thank you sir,” ta faɗa, ta juya ta fita cikin nutsuwa, zuciyarta na bugawa amma fuskarta ta riƙe professionalism.
Bayan wasu mintuna kaɗan, wani ma’aikaci ya shigo da ƙaramin mini gourmet basket mai kyau da aka kawata da ribbon, “Sir… this was delivered for you,” Rayyan ya ɗaga kai ya kalle shi, “From who?” “From your mom, sir,” murmushi mai laushi ya bayyana a fuskarsa nan take, wani irin smile da ba kowa ke gani ba, ya karɓa a hankali, ya buɗe abinci mai kyau, fruits, snacks komai cike da kulawa, ba tare da ɓata lokaci ba ya ɗauki wayarsa ya kira Mom. “Hello my sweetheart…” ya faɗa da dariya Fatima ta yi dariya a ɗayan ɓangaren, “Son… did you get it?” “Yes Mom… Allah ya ƙara miki lafiya… Allah ya kula min dake…”
Ta amsa da farin ciki, “Ameen… keep doing what you’re doing… but please eat something, my love… don’t skip meals.”
Ya yi murmushi yana kallon basket ɗin, “I will… I promise.” Ta yi masa addu’a cikin nutsuwa “Allah ya sa albarka a aikinka… ya tsare ka…” “Ameen Mom…”Suka yi sallama.
A hankali ya fara cin abincin, ba da gaggawa ba, yana jin wani irin natsuwa da ba ya samu a ko’ina sai daga gare ta, wannan ƙauna ce da ba a saye da kuɗi, wannan alaƙa ce da ba a gina ta da jini kaɗai ba, ya gama cikin nutsuwa, ya miƙe tsaye ya ɗauki keys dinsa.
“Prepare the car.” ya faɗa. Driver ya amsa “Yes sir.” Ba tare da ɓata lokaci ba suka fita, wannan karon bai tuƙa ba, ya bar driver saboda yana son yin tunani, motar ta nufi farmland estate dinsa da ke wajen Paris wuri mai faɗi, gonaki masu kyau, tractors na aiki, workers suna motsi, iska mai ɗan sanyi na kadawa, da zarar suka isa, ya sauka daga mota yana kallon gonar da idanunsa, wannan ba kawai kasuwanci bane a gare shi, wannan legacy ne, wannan wani ɓangare ne na rayuwarsa da Fatima ta fara, shi kuma ya bunƙasa, manager ɗin gonar ya zo da sauri “Sir, the last harvest was very successful…” ya fara bayani, “We exceeded expectations… almost double profit,” Rayyan ya ɗan yi murmushi, “Good… increase production next season… and invest in better equipment,” ya faɗa cikin nutsuwa, amma kalamansa na ɗauke da umarni. Saboda wannan nasara…
ya riga ya yanke shawara siyan Sabbin gonaki Sabbin investments,Sabuwar expansion, Kuɗi ba matsala bane,Strategy ne komai.Yana tsaye a cikin gonar…
iska na bugun fuskarsa… ya ɗaga kai yana kallon sararin sama.