12
by @nanadiso10
PAGE 12.
Cikin ɗakin babu wani sanyi zafi ne na zuciya da hassada ya mamaye wurin, Zeynab na tsaye a tsakiyar falon tana kai kawo kamar wadda aka tsokano, hannunta na rawa yayin da take magana cikin fushi, “Yaya Usman… wallahi wannan shi ne ƙarshen haƙurina Ba zan ƙara jurewa ba… idan ban tarwatsa rayuwar Fatima ba, hankalina ba zai taɓa kwanciya ba ” muryarta ta cika ɗakin, idonta ya yi ja saboda zafin zuciya, “Tun ranar da ta shigo gidan nan… komai ya sauya…haroon sai da izininta yake komai.. ya daina ganin kowa” Uncle Usman na zaune a kan kujera mai faɗi yana sauraron ta, fuskarsa ba ta nuna komai sosai ba amma a cikin zuciyarsa akwai wani irin abu mai duhu da ke motsi, ya ja numfashi a hankali ya ce cikin nutsuwa, “Zeynab… ki rage zafi… kin san halin yaron nan… idan kuka yi masa abu kai tsaye, zai iya juya muku baya gaba ɗaya,” ya ɗan tsaya yana kallonta cikin ido, “Kuma kar ki manta… matar nan ta yi masa wani abu… wannan ba soyayya kawai ba ce…”
Zeynab ta yi dariya mai ɗauke da raini, “Black magic? Ko white magic? Wallahi duk abin da ta yi… sai na tarwatsa shi” ta faɗa cikin ƙarfi, zuciyarta na cike da ƙiyayya, “Ba zan bar ta ta zauna cikin wannan jin daɗin ba… ni ma ina nan” A cikin zuciyar Uncle Usman kuwa… wani tunani ya zo masa, “Da zan samu dama… har Haroon ɗin ma zan girgiza…” amma bai furta ba, ya ɓoye a ransa, a fili kuwa sai ya ce cikin nutsuwa, “Ki yi haƙuri… akwai hanya… akwai lokacin da za a motsa… ba komai ake yi da gaggawa ba…” kalamansa sun fito da dabara, kamar wanda ya riga ya fara tunanin wani abu. A gefe kuwa Didi tsohuwar da ke zaune a kan kujera ta ɗan yi tsaki tana girgiza kai, “Yaron nan… tunda ya samo kuɗi fa… baya ganin kowa da daraja Ka ga kwanakin baya nace masa ina buƙatar kuɗi… sai da ya tambaye ni me zan yi da su…” ta ɗan ɗaga murya cikin ɓacin rai, “1 million fa ya bani…”
Zeynab ta juya ta kalleta cikin mamaki, “1 million?” Didi ta girgiza kai, “Eh duk arzukinsa kuma na tabbatar matar ta zugashi …”
Uncle Usman ya yi ɗan dariya mai sanyi, amma dariyar ba ta da daɗi, “Ai ya hau kai ne… dukiyar Umar ce ya gada… shi ya sa yake ganin kamar komai nasa ne,” ya ɗan karkata yana magana cikin ƙasa, “Da kuɗinsa ne kawai… da bai kai haka ba…”
Zeynab ta ɗaga kai cikin fahimta, “Shiyasa nace… akwai wani abu a ciki… ba haka kawai suka bar rayyan ba saboda sun cinye dukiyarsa ne.Uncle Usman ya ƙara da “Suka raba shi da kowa… suka mai da shi na su kaɗai…” Kalmar ta tsaya a sarari. Shiru na ɗan lokaci ya mamaye ɗakin. Sai numfashin su kaɗai ke tashi.
Zeynab ta zauna a hankali, idanunta sun yi ja, “Ba zan bar wannan abu ya wuce haka ba…” ta furta a hankali. Didi ta girgiza kai, “Ku dai ku sani… wannan ba ƙaramin abu bane ko zaku janyo rayyan saifa kun karya asirin nan tukunna…” Uncle Usman ya ɗan jingina baya yana kallon su, “Ku bar komai a hannuna…”
****
Hanan na komawa gida cikin dare, gidan su mai alfarma da ke Avenue Montaigne ya cika da shiru mai laushi, fitilu masu kyau suna haskaka corridor ɗin cikin nutsuwa, amma a zuciyarta babu wannan natsuwar, kanta na mata ciwo sosai, zuciyarta na cike da gajiya da kunya da kuma wani abu da ba ta saba ji ba pressure, ita fa tun tana ƙarama ba ta son wahala, ba ta son aiki mai nauyi, rayuwa a gare ta ta saba da sauƙi, da kulawa, da samun abin da take so ba tare da ƙoƙari mai yawa ba, burinta ɗaya ne kawai ta samu miji mai kuɗi, ta yi rayuwa cikin nutsuwa, amma yau… an ɗora mata wani abu daban, wani abu da ya sa ta ji kamar ana gwada ta, ta shiga ɗakinta kai tsaye, ta cire kayanta cikin gajiya, ta shiga shower, ruwan ɗumi ya sauka a jikinta amma bai iya cire damuwar da ke zuciyarta ba, bayan ta fito ta sa kayan barci masu laushi, ta zauna a gaban mirror tana kallon kanta, “This is not me…” ta furta a hankali, ta shafa fuskarta tana jin wani abu yana canzawa a ciki.
Ta fita ta ce wa mahaifiyarta “Good night Mom” cikin sauƙi, ba ta tsaya hira ba, saboda zuciyarta na can wani wuri, ta koma ɗakinta ta rufe ƙofa, ta ɗauki wayarta, ta duba number ɗin da aka turo mata Rayyan Haroon, ta ɗan tsaya na wasu seconds kafin ta kira, wayar ta shiga ringing… amma ba a ɗaga ba, ta sake kira… shiru, har sau biyar, babu amsa, haushi ya fara shiga zuciyarta, “Seriously?” ta faɗa cikin ɗan tsaki, ta jefa wayar a kan gado, amma ba ta dade ba sai ta tuna kalaman Abiey “I want that deal…” ta ja numfashi, ta sake ɗaukar wayar. Ta kira Wannan karon…aka ɗaga. Shiru Ba sallama,Ba magana. Sai numfashi a ɗayan ɓangaren.
Ta ɗan haɗiye wani abu kafin ta ce cikin ladabi, “Assalamu alaikum…” Shiru “Mr. Rayyan…” ta ƙara. Sai ya amsa cikin sanyi, “Yes.” Kalma guda. Hanan ta daidaita kanta, “I’m sorry… about earlier…” Ta ɗan tsaya.
“Ina roƙon ka kayi haƙuri… this was my first time… ban yi proper review na document ɗin ba… but I want to fix it.” Rayyan bai yi magana ba. Kamar yana sauraron yadda take faɗa.Kamar yana tantance gaskiyarta.
Hanan ta ci gaba cikin gaskiya wannan karon, ba da girman kai ba, “I need another chance… zan gyara duk abin da na yi kuskure…” A ɗayan ɓangaren…
Rayyan ya jingina da kujera a cikin ɗakinsa, wayar a hannunsa, yana kallon pop, muryarta ta fito masa daban wannan karon, ba kamar a meeting ba, ba kamar yarinya mai nuna iko ba, sai wani laushi… wani irin sauƙin kai da ladabi Sai ya ce a hankali “Hmm…”
Ya ɗan gyara murya. “Okay.”
Kalmar ta sauka. Hanan ta ji zuciyarta ta ɗan sauke. “Thank you…” ta faɗa cikin sauri.
Sai ta ƙara da sauri kamar tana jin tsoron ya katse, “Please… if you’re free… can I come tomorrow? I want to learn… properly…”
Rayyan ya ɗan yi tsaki kaɗan, “Is this a school?” Kalmar ta fito da ɗan tsauri.
Hanan ta yi saurin cewa, “No… please… I just need guidance…” Ta ɗan yi shiru kafin ta ƙara cikin ladabi, “Please…” Rayyan ya yi shiru na ɗan lokaci. Sai ya ce cikin sanyi “10 AM.” Ya ɗan tsaya. “If you’re late… don’t come.” “Okay… I’ll be there…” Ta faɗa cikin sauri.
Sai ya katse wayar. Hanan ta zauna a kn gadonta. Wayar a hannunta Shiru ya mamaye ɗakin Sai ta ɗan yi murmushi kaɗan.
****
Da sassafe hasken rana mai laushi yana shigowa ta labulen ɗakin Nayla yana haskaka fuskarta mai kyau da ke kwance cikin bacci mai nauyi, shiru ne ya mamaye ɗakin sai ƙarar AC mai sanyi, ƙofar ɗakin ta buɗe a hankali Fatima ta shigo cikin nutsuwa amma fuskarta ɗauke da ɗan tsanani na uwa mai son tarbiyya, ta tsaya a gefen gadon tana kallonta na ɗan lokaci kafin ta girgiza kai, “Nayla…” ta kira cikin murya mai cike da faɗakarwa, babu amsa, ta matsa kusa ta ɗan taɓa kafadarta, “Nayla… sau nawa zan gaya miki ki daina wasa da azkar?” Nayla ta motsa a hankali tana buɗe idanu cikin bacci, “Mom…” ta furta da muryar da ta cika da kasala, Fatima ta ɗan ɗaga murya kaɗan, “Wannan rayuwar fa sai da addu’a ake tafiya, ke ba ƙarama bace yanzu, ki tashi kiyi abin da ya dace, ko sai na dawo?” Nayla ta yi saurin miƙewa tana jan duvet ɗin gefe, “Mom kiyi haƙuri please… zan yi yanzu…” ta sauko daga gadon cikin sauri, kafin ta juya ta kalli Fatima, “Mom… yaya yana nan?” Fatima ta ɗan kalleta, “Ya fita yanzu yanzu… lafiya?” Nayla ta ɗan yi murmushi kaɗan tana ɓoye wani abu a zuciyarta, “Ina da wani abu da nake son ya duba min… may be lesson teacher… kinga ƙaramin lokaci ya rage mu gama school…” ta ɗan ja numfashi, “Jiya na ga su Amnah suna da teacher ɗinsu… na gaya wa Dad ya ce na sanar da yaya…” Fatima ta ɗan yi murmushi cikin nutsuwa, “Okay Nayla… Allah ya baku sa’a, ki hanzarta kada ki makara,” Nayla ta ɗaga kai, “Thank you Mom…”
Da sauri ta shiga bathroom, ruwan sanyi ya sauka a jikinta yana kawar da ragowar bacci, ta fito cikin nutsuwa ta sa kaya masu kyau, ta shimfiɗa sallaya ta tsaya cikin nutsuwa tayi sallah, daga nan ta zauna tana karanta azkar ɗinta da nutsuwa, lips ɗinta na motsi a hankali, zuciyarta na samun natsuwa a hankali, bayan ta gama ta ɗauki bag ɗinta mai kyau ta tsaya a gaban mirror tana kallon kanta na ɗan lokaci, fuskarta ta nuna wani abu da ba kowa zai gane ba wani irin tunani, wani irin shiru, wani irin abu da ke motsi a zuciya.
Tana saukowa ƙasa ta fita zuwa mota, driver ya buɗe mata ƙofa, ta shiga cikin nutsuwa, motar ta nufi Université de Paris, amma a zuciyarta ba karatu kaɗai bane, tunanin jiya yana dawowa mata, fuskar sa… yadda yake magana… yadda yake kallon ta, ta ɗan lumshe idanunta tana murmushi kaɗan ba tare da ta sani ba, “What is this…” ta furta a hankali, zuciyarta na bugawa da wani irin yanayi da ba ta saba ba.
A cikin lecture hall tana zaune amma ba cikakkiyar nutsuwa, lecturer na magana amma rabin hankalinta baya wurin, lips ɗinta na ɗan motsi da murmushi lokaci zuwa lokaci, kawarta Amina ta karkata tana kallonta, “Hmm… Nayla…” ta faɗa cikin wasa, “Me ke faruwa ne? You’ve been smiling since morning…” Nayla ta ɗan gigice kaɗan, “Nothing…” ta faɗa cikin sauri, Amina ta yi dariya kaɗan, “Don’t lie… akwai wani abu…” Nayla ta juya idonta kaɗan tana ɓoye murmushi, amma a zuciyarta…
*****
Ganin lokaci ya kure yasanya Hanan tashi da sauri daga gadonta, agogon dake bango ya nuna 9:30am zuciyarta ta buga da karfi “Ya Allah…” ta furta a hankali tana sauri shiga bathroom, wanka tayi cikin gaggawa ruwan sanyi na sauka a jikinta amma hankalinta na kan lokaci, bata ma samu nutsuwar shiryawa yadda take so ba, ta fito da gaggawa ta sa kaya masu kyau abaya mai launin ja mai matukar dacewa da siririn jikinta, ta ɗan tsaya a gaban mirror ta kalli kanta na dan lokaci, “You can do this…” ta furta tana ɗaukar bag dinta, ta sauko kasa tana cewa “Mom I’ll eat later” ba tare da ta tsaya ba ta ɗauki key na motarta Range Rover Velar ta fita cikin gaggawa, engine ya yi ƙara mai sanyi motar ta tashi cikin gudu tana yanke titunan Paris cikin hanzari, zuciyarta na bugawa saboda lokaci yana tafiya, 9:52… 9:57… 10:05.
Ta isa gaban RH Global Holdings, ginin mai hawa da gilashi mai kyalli ya tsaya a gabanta kamar wani al’amari mai girma, ta sauko cikin sauri, guards suka kalleta cikin tsari suka tambayeta, “Do you have an appointment?” ta gyara murya, “Yes…come in with Mr. Rayyan,” bayan an tabbatar aka bata damar shiga, tana tafiya cikin corridor mai sanyi da kamshi mai dadi, heels dinta na bada karamin sauti a kasa, amma zuciyarta ba ta nutsu ba, ta isa reception area inda Noor ke zaune, Noor ta ɗaga kai ta kalleta da wani irin kallon da ba ya boye komai kallon raini da kuma wani abu daban, “You’re late,” ta faɗa cikin sanyi, Hanan ta tsaya tana dan jin nauyin kalmar amma bata amsa ba, Noor ta nuna mata kujera, “Sit. He’s in a meeting.”
Hanan ta zauna cikin nutsuwa amma a ranta tana jin wani abu mai nauyi, mintuna suka fara tafiya… 30 minutes… 1 hour… 2 hours… har kusan 3 hours, lokaci ya zama kamar yana tafiya a hankali, ta kalli agogo sau da yawa, hannunta na dan rawa, wannan ba rayuwarta ba ce, ita ba ta saba zama tana jira haka ba, amma yau… ta zauna, ta daure, ta haɗiye girman kai, ta ji a zuciyarta “Tabbas… ba kowa bane…” Noor ta sake kallonta tana cewa cikin ɗan tsaki, “Madam… idan soyayya kika kawo… oga baya irin wannan,” Hanan ta ɗan kalleta cikin rashin fahimta, bata gane ba, amma bata ma damu ba, zuciyarta na wani wuri dabam. A ƙarshe…“Noor… let her in.”
Muryarsa ta fito daga ciki. Hanan ta miƙe da sauri, ta gyara abayar jikinta, ta shiga. Da zarar ta shiga… wani irin sanyin iska mai ɗauke da kamshi mai tsada ya bugeta, office ɗin ya wuce tunaninta glass walls, leather finishing, desk mai tsari, view na Paris daga sama, komai cike da nutsuwa da alfarma, “Ya Allah…” ta furta a ranta, amma ta daure ta gyara nutsuwarta, “Good morning sir,” ta faɗa cikin ladabi. Rayyan ya ɗaga kai ya kalleta.
“Sorry for keeping you waiting.”Ta ɗan tsaya.
Mamaki ya bayyana a fuskarta.Wannan ba irin amsar da take tsammani ba ce.
“It’s okay…” ta faɗa cikin nutsuwa.
Ya nuna mata kujera.“Have a seat.”Ta zauna cikin ladabi, ta fitar da documents dinsa, tana shirin fara bayani, amma kafin ta fara ya ɗaga hannu a hankali.“Listen first.” Kalmar ta fito cikin nutsuwa amma da iko.Sai ya fara.
“Business is not about assumptions… it’s about data.”Ya ɗauki file ɗin ya buɗe.
“In your proposal… you ignored cost structure… that’s your first mistake.” Ya ɗan juya screen yana nuna mata. “Import duties… logistics… warehousing… currency fluctuation… these determine profit, not just demand.” Hanan ta yi shiru.Idonta na kansa.
Ba wai tana jin kalamansa kawai ba… tana kallon yadda yake magana. Yadda yake bayani. Yadda yake da iko Ya ci gaba.
“Second… risk management… what happens if supply chain delays? What’s your backup plan?”vYa ɗan kalleta. “Business needs foresight… not guesswork.”