GADAR TSAUTSAYI 22
by @nusybee143
Page 23
Kamar wadda ake controlling da remote ta fara girgiza kai cikin sauri hawaye yana zubo mata,da ƙyar cikin in ina ta fara faɗin "a'a!
A'a yaya!yaya don Allah ka daina, yaya ta yaya za kace kana so na?yaya ka tuna,nice fa kanwarka wadda kake ji da ita,ka yi min alƙawarin za ka tsaya min a komai,yaya idan ka ce za ka aure ni ai ba za ka samu damar tsaya min ba,don Allah yaya kar ka yi min haka,yaya let's change this topic please,don Allah yaya!"
Muyassar ya ƙarasa inda take da sauri, cikin tashin hankali ya riƙo hannunta,muryarsa tana rarrabewa ya ce "Please Shaheeda!
Please!!don Allah kar ki yi min haka,ban san yadda zan yi ba idan kika rabu da ni"ta runtse idanu ta ce "ka tanadi yadda za kayi yaya,don wallahi bana sonka!bana son aurenka!! Mubarak shine abin da zuciyata take so kuma take muradi,yaya don Allah kar ka yi abin da zan tsane ka,yaya ina sonka,kai ɗin best friend ɗina ne,kar ka zama rival a gare ni, Please yaya!!!"tana kai wa nan ta fizge hannayenta daga na Muyassar ta ruga zuwa hostel ɗin su, wani irin tashin hankali da ɓacin rai kawai take ji,da gaske take jin sam abin babu tsari wai Muyassar yana sonta da aure, mutumin da ta ɗauke shi tamkar wanda suka fito ciki ɗaya
Arnold da yake zaune a gefe yana kallonsu,yana jin abin da suke cewa,amma kasancewar da Hausa suke magana ba ya fahimta,sai dai kuma ya fahimci cewa ko ma akan me suke magana ba mai daɗi bane
Muyassar ya bi Shaheeda da kallo cikin tashin hankali, kafin ya ɗauke kai,ya nufi inda Arnold yake zaune yana kallonsa, Arnold duk da ya fahimci Muyassar ba ya sonsa,amma ganin ya zo sai ya saki fara'a yana miƙewa don su gaisa,amma Muyassar yana zuwa ya nuna shi da yatsa, cikin harshen turanci ya fara magana
"Bana son na ji dalilin da ya sa kake tare da ƙanwata,amma bana son na sake yi maka kashedi akan ka rabu da ita,idan ka kuskura ka lalata min ƙanwata za ka gane bani da kyau, muddin ka yaudare ta sai na yi maka abin da za kayi nadamar zuwa duniya, ka je ka nemi daidai kai,amma ƙanwata ta fi ƙarfinka!"ya karasa faɗa yana hankaɗa shi
Hankalin Arnold ya tashi sosai,har Muyassar ya yi gaba ya zo ya sha gabansa kamar zai yi kuka yana faɗin "don Allah ka saurare ni,da gaske so nake na auri ƙanwarka,na musulunta ma ko ba ta gaya maka ba?"
Muyassar ya tsaya ya kalle shi cikin idanu ya ce"ka musulunta saboda ka auri ƙanwata ko?
To ka koma addininka na baya,amma ƙanwata ba zata taɓa aurenka ba"ya bangaje shi ya wuce, Arnold ya bi shi da kallo cikin tashin hankali
Abu Kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba,don Muyassar kai tsaye da ya koma Nigeria ya sanar da Abba abin da yake faruwa, hankalin Abba da Ummeey ya tashi sosai, Hajiya Ruƙayya da labarin ya yi matuƙar yi mata daɗi tana murmushi ta ce
"Ai dama matsalar da ake samu kenan idan mace ta ce zata tafi ƙasar waje ba wani nata don ta yi karatu,to Allah ya sa ma ba su yi watsewarsu ba"
Abba ya kalle ta fuska a ɗaure ya ce"in sha Allah watsewa sai dai ki ganta akanki,ba akan Shaheeda ba"Hajiya Ruƙayya ta taɓe baki ba tare da ta sake magana ba
Washe gari Abba da kanshi ya je Belgium,a lokacin har Shaheeda ta yi kukan ta gama,sun sake komawa da Arnold wanda ya koma Mubarak, tare suke karatu,su yi hira tare,sai dai bai taɓa zuwa inda take ba,itama haka
Hankalin Daddy ya tashi sosai, saboda ya fuskanci soyayyar da take tsananinsu ta yi nisa sosai,kuma ta nuna masa kiri-kiri so take ta auri Arnold, wanda ya koma Mubarak yanzu
Tana kuka take faɗin "Abba saboda ni ya musulunta,ina sonshi sosai Abba,don Allah Abba kar ka raba mu"
Abba ya ja numfashi cikin damuwa ya ce "Fatima!na farko dai yaron nan ban yarda da tabbacin Musuluncinsa ba,don ya musulunta ne saboda ya aure ki,ba saboda Allah ba,na biyu ko da ace ya musulunta saboda Allah sai dai ya yi haƙuri, don na riga na yi alƙawarin aurenki ga Muyassar,don haka zan same shi mu yi magana,ba zan aura masa ke ba"
Ihun kuka sosai Shaheeda take yi tana roƙon Abba kar ya hana ta auren Mubarak, Alhaji Yusuf da Alhaji Aliyu da suka tafi tare hankalinsu ya tashi sosai,a ranar suka tattara Shaheeda suka mayar da ita gida, Alhaji Yusuf ya yi rantsuwa akan ta gama karatun
Kamar taɓaɓɓiya haka suka dawo da ita, Abba ya wuce da ita sashensa,tana kuka tana kiran don Allah a bar ta ta auri Mubarak
Duk yadda ya so ya yi mata bayani ya yi,amma hakan ya ƙi aiki,dama Shaheeda akwai kafiya,akwai ta da gardama da tsayuwa akan ra'ayinta,hakan ne ya fusata Alhaji Yusuf,ya sa aka ƙwace wayarta,aka rufe ta a sashen Ummeey
Duk abin da yake faruwa Ummeey tana kallo,amma bata magana,sai dai can ƙasan ranta ita kaɗai ta san me take ji saboda tashin hankali,amma ta miƙa lamuranta ga Allah kawai,kuma ta ja bakinta ta yi shiru
Tsawon sati biyu babu wani canji,gaba ɗaya Shaheeda ta lalace ta fige ta fita hayyacinta,ba damuwarta karatun da Abba ya hana ta ba, damuwarta raba ta da Mubarak ɗinta da ya yi, wanda ya zama wani sashe na rayuwarta
Sai da ta yi watanni uku da dawowa sannan ta koma hayyacinta,shima ta zama silent bata yawan magana, Muyassar kuwa tuni suka yi uwar watsi saboda haushinsa da take ji saboda shine silar rabuwarta da abin da take so,a cewarta
Shima bai damu ba,ya koma don cigaban karatunsa ya ba ta waje don ta sake hutawa
A lokacin ne Abba ya ba ta Sabuwar waya da sabon layi, sannan ya shaida mata zai mayar da ita makarantar BUK don ta cigaba da karatunta,amma ya yi mata gargaɗi akan kule-kulen maza,da kuma focusing akan karatunta
Sannan ya ƙara da faɗin "maganar mijin aure kuma na riga na zaɓar miki, Muyassar shine mijinki,bana son na sake jin kin kula wani,tashi ki je, Allah ya yi miki albarka"ta miƙe jiki babu ƙwari ta tafi bayan ta yi masa godiya
Tana komawa ɗaki ta yi murmushi tana kallon wayar hannunta, ba tare da ɓata lokaci ba ta hau jera numbern da take ta ajiya a ƙwaƙwalwarta tsawon watanni, lokaci guda kuma ta wuce zuwa banɗakinta da yake cikin ɗakin
Tana rufe ƙofar daidai da fara ringing da wayar da ta kira ta yi,ƙirjinta ya tsananta bugu,duk da cewa banɗakin babu zafi amma haka take sharce gumi, lokaci guda kuma kamar an tsayar da jinin jikinta ta ji ya ɗaga wayar
"Hello!"
"Mubarak!"ta faɗa muryarta tana rawa,kuka yana kubce mata
Sai da ya yi shiru na wasu sakwanni, kafin a hankali ya ce "Shaheeda!
Shaheeda ke ce?"ya furta cikin harshen dutch
Ƴar dariya ta yi tana goge hawaye ta ce"Mubarak a ina ka san sunana Shaheeda?"
Murmushi ya yi sosai,ya ce"a wajen yayanki, yanzu dai ba wannan ba, kina ina ne?
Me yasa kwana biyu na ji ki shiru?"
Tana kuka ta tsara masa abin da ya faru, shiru ya yi na ɗan lokaci,a hankali ta ce"ba zan iya rayuwa babu kai ba Mubarak,ina sonka,kai ne rayuwata,kai ne farin cikina,kai ne komai nawa,ka taimake ni na same ka kar na rasa ka, Please Mubarak"
Mubarak ya ja ajiyar zuciya mai nauyi ya ce "to yanzu menene abin yi?
Ya kamata na zo na samu Daddy na yi masa magana,ya ba ni aurenki "
Girgiza kai Shaheeda ta yi ta ce"ba zai yarda ba, Abbana ya ce ya ba wa yayana Muyassar ni,ya yanke ba zai taɓa komawa baya ba, in dai aka tafi a haka na tabbatar ba zan same ka ba"
Mubarak ya ce"to yanzu ya ake ciki?"
Shaheeda ta ce"ban sani ba nima, makaranta ma an dawo da ni Nigeria "
Mubarak ya ce"zan zo Nigeria,zan zo har makarantar taku,za mu tattauna mu samo mafita "
Shaheeda ta jinjina kai ta ce"ina jiranka, Allah ya kawo min kai lafiya "
Ya jinjina kai yana faɗin"very soon "
Daga lokacin kuma Shaheeda da Mubarak suka ɗinke suka koma zuba soyayya sosai,amma a ɓoye, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ta mayar da jikinta,walwalarta ta dawo kamar baya
Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci aka gama yi mata komai na komawa makaranta,inda zata cigaba da karatunta daga level two a maimakon level three,Sam hakan bai dame ta ba, musamman da ya kasance akwai wani gagarumin shiri da suka yi ita da Mubarak,duk da cewa duk sanda ta tuna da hakan jikinta yana yin sanyi
Allah ya taimake ta ta cigaba da zuwa makaranta,sai dai a ɓoye duk ranar da ta je makaranta sai sun haɗu da Mubarak,kuma da yake a Nigeria ne babu wanda ya damu da ya saka mata idanu
Game da Muyassar ma sun cigaba da zumunci,sai dai ba kamar baya ba,don da ya watsar da ita ma,daga baya ya dawo, kuma da ya ga ta sauko sai suka cigaba da zumunci, sai dai ya karance ta tsaf bata son batun aure ko soyayya ya gifta a tsakaninsu
Yau ma tana makaranta,tun sassafe da ta je bata shiga lecture ba,suna tare da Mubarak,ya dube ta ya ce"ina fatan kin gama shirya komai Fatima"
Ta girgiza kai, cikin sanyin jiki ta ce"ina sonka sosai Mubarak,amma ba zan ɓoye maka ba,ina son iyayena, mahaifiyata ni kaɗai ta haifa,ina tausayin ranar da zata buɗe idanu ta ga bana kusa da ita, kuma bata san inda na je ba,ji nake yi tamkar ban kyauta mata ba"
Mubarak ya dube ta sosai ya ce "to yanzu ya kike so a yi?ko aikinmu kike son ki dawo mana da shi baya?"
Da sauri ta girgiza kai ta ce "a'a ba ka fahimci me nake nufi ba,game da...."
"Relax Fatima!
Nima kar ki manta mahaifiyata ni kaɗai gare ta,kuma ba ta amince ba kamar dai mahaifanki,amma na bijire mata na taho nan,duk da so da kewata da take yi,kuma hakan ba yana nufin bana sonta bane,amma kuma ina sonki
Ni ba zan raba ki da iyayenki ba,a madadin haka ma bayan auren za mu zo mu gaishe su mu nemi gafararsu,amma ya kika ce?"
A sanyaye ta jinjina kai,ya yi murmushi yana kallonta,suka cigaba da tsare-tsaren yadda za su yi aurensu su rayu cikin farin ciki da juna
A wannan halin ne Mubarak ya yi mata visa ta hanyar wani abokinsa Solomon ɗan ƙasar Nigeria,ya yi mata komai na ƙasar da suka zaɓa don tafiya,su cigaba da rayuwar su a can,wato ƙasar Spain
A ranar da suka shirya auren tun da safe ta sauka a makaranta,sai dai babu alamu na niyyar shiga lecture a tare da ita,tana zaune hankalinta baya jikinta tana jiran shigowar Mubarak
Can ta hango shi,ta miƙe cike da farin ciki,ya ƙaraso inda take yana kallonta yana murmushi,ya ce"ki zo mu tafi babu lokaci, Imam yana can yana jiranmu "babu musu ta bi shi,suka fice daga cikin makarantar
Kai tsaye wajen wani limami suka nufa,anan aka ɗaura musu aure,bisa sadakin wani zobe na diamond da ya ba ta
Ta yi tsananin murna sosai na samun mallakin zuciyarta Mubarak,shima dai farin ciki kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha,ya ɗauke ta ya ya mayar da ita makaranta
Sai dai kuma yana dire ta karaf! idanunta suka faɗa cikin na Muyassar! tashin hankali ba'a saka maka rana, tuni jikinta ya kama karkarwa,sai dai kafin Muyassar ya ƙaraso wajen Mubarak ya ja motarshi ya tafi, Muyassar ya bi motar da kallo ranshi a tsananin ɓace
Ƙarasowa ta yi tana murmushin yaƙe,ya watsa mata wani kallo ya ce"ke da wanene a cikin motar nan?"
"Am....dama....um.. wani course mate ɗina ne......"
"Karya kike yi Shaheeda!"ya faɗa cikin ɓacin rai yana ɗaga murya
Shiru ta yi tana haɗe rai, ranshi a ɓace ya ce "last question, Shaheeda da wa kike tare a cikin motar can?"
"Yaya na faɗa maka kuma ka ƙi yarda,na ce maka course mate ɗina ne fa,kuma...."
"Ƙarya kike yi Shaheeda!kar ki sake yi min ƙarya!!
A bar shi ma gaskiya kika faɗa, me ya haɗa ki da course mate ɗin ki har haka?ana yi muku lecture amma ke kina cikin motarshi?"ya sauke numfashi cikin ɓacin rai,ya dube ta fuska a ɗaure ya ce
"Bari na yi miki gwari-gwari don ki san cewa ni ba shashasha bane
Wannan kafirin saurayin naki ne Arnold,na san yana shigowa makarantar nan lokaci zuwa lokaci,kuma don ke ya zo ƙasar nan, to zan gayawa Abba gaskiya,tunda a nan ɗin ma ba ki fasa ba,gwara ya ɗauki duk matakin da ya so akanki sakarya! wadda bata san ciwon kanta ba!!!"
#Nusy_bee