ALIYU HAYDAR

Chapter 11

by @nieemartullah

Yau takasance litinin,duk wanda ka gani cikin shiri yake,wasu na shirin makaranta wasu na shirin fita aiki wasu kuma na shirin zuwa wajen kasuwancin su,  yau suke shirin komawa Lagos shiyasa yana tashi a bacci wuraren qarfe tara na safiya ya fada toilet agurguje yayi wanka ya fito da towel daure a qugunshi sai qarami a hannun shi yana tsane sumar kanshi,bayan ya gama goge jikin shi ya dakko face and neck lotion din shi na Glowbiotics ya shafa sannan ya qara dakko subtle Energies Rasayana hand and body lotion shima ya shafa bayan ya gama shafe shafen shi ya qarasa closet din shi sanin cewa office zasu tsaya kafin su wuce gida ya sa shi fiddo da suit grey color na company TORM FORD,dress shirt ya fara sakawa wacce ta kasance fara kafin ya saka suit din yana dai daita zaman necktie a wuyan shi,safa ya saka kalar baqi a qafar shi yana dakko Santiago black mix patent milano leather loafers takalmin min shi ya saka,gaban madubi ya wuce inda ya bude wata drawer dake jikin madubin ya dakko agogon Rolex ya daura a tsintsiyar hannunshi kafin ya shiga fesa turarukan shi na Gucci Intense Oud,Pur Oud Louis Vuitton,Creed Aventus da Gris Dior bayan ya gama feshe jikin shi da turarukan shi masu masifar qamshi da zama a jiki ya dauki wayoyin shi ya saka cikin aljihun suit din shi ya nufi hanyar fita,yau ma dai kamar jiya ne yana fitowa ya tarar da safiyyah ta jera mashi breakfast a kan dining din dake part din shi tunda ya kalli wurin sau daya basu samu arziqin ya qara kallon wurin ba ya fita daga part din shi cikin takunsa na qasaita ya qaraso compound din iro me gadi ya kira yace ya kira mashi baba tanimu iro ya sunkuyar da kai alamar girmamawa yace ranka ya dade shekaranjiya ya tafi qauyen su anyi mashi rasuwa gyada kai kawai yayi yace Allah ya jiqan musulmi yace ameen juyawa yayi ya koma cikin gida saboda dama yaso ne ya kaishi gidan mamy saboda ya dawo da motar a parlor dinshi ya zauna yayi ordering bolt yana jira babu dadewa bolt din da yayi order ya qaraso miqewa yayi ya fita ya hau suka wuce gidan mamy........................
Hakan ya zama kamar al'adarta ne a kullum bayan tayi sallar asuba zata je ta gaishe dasu yau ma hakan ce takasance bayan ta idar da sallah part din papi ta wuce a parlor ta tsaya tayi sallama,jin shirun yayi yawa yasa tayi tunanin bai ji sallamar ta bane bedroom din shi ta nufa tayi knocking jin shiru yasa hankalinta ya tashi ta bude dakin ta shiga tana tunanin ko wani abu ne ya samu papi amma sai dai me tana shiga ta tarar babu kowa a dakin kuma daga dukkan alamu bama a kwanta akan gadon ba,turo baki tayi tana qunquni kenen papi tafiya yayi bai fada masu ba,bayan ta fito dakin Meemarh ta shiga inda ta same ta akan daddumar da tayi sallah tana azkhar,kan daddumar ta zauna tare da dora kanta akan cinyar Meemarh tana fadin good morning Meemarh,morning sweetie how was your night?tace Alhamdulillah,where is papi?I can't find him in his room ta fada tana tura baki gaba,tana shafa kanta tace he traveled yesterday night sweetie but he won't stay long,jin baze dade ba yasa ta saki ranta sun dan taba hira har bata san lokacin da bacci ya dauke ta ba,sai da ta bari baccin ta yayi nisa kafin ta dora ta akan gado tana da nauyin bacci shiyasa har ta dora ta bata farka ba sai qara gyara kwanciya da tayi da ta kwantar da ita sai ta sauka qasa don ta bawa amsu aiki umarnin abinda zasu dafa..................................
Tana isa asibiti tayi parking sabuwar motar ta company infinity,fitowa tayi ta shiga cikin asibitin tsirarun ma'aikatan dake kai kawo suna gaishe da ita har ta shiga lifter da zai kaita office dinta dake last floor,tana shiga office din ta aje handbag dinta sannan ta zauna,ko minti biyu bata yi da zama ba akayi knocking izinin shigowa ta bada ba tare da ta damu da tambayar waye ba,qamshin da taji ne yasata dago kanta don if she's not mistaken qamshin turaren sadeeq ne kamar yadda hancin ta ya jiyo mata shi din ne ba wani ba dauke kanta tayi sannan ta furta good morning sadeeq dan murmushin sa me kyau yayi mata kafin yace morning love yana nuna mata kujera da hannunshi kafin yace may I kallon shi tayi tare da kau da kai tace you will never change sai da ya daidaita zaman shi kafin yace me dokar bacci ne ya bige da gyangyadi, this is so unusual of you sanin inda zancen nashi ya nufa ne yasa ta rasa abinda zata ce masa saboda baxa ta ita fada masa maganar Ayaanah ba don ba hurumin sa bane sanin hakan,dan murmushi tayi masa beauty point din ta na lotsawa ciki tace jiya banyi bacci da wuri ba na tsaya yin wasu ayyuka shiyasa yau da na tashi na tashi da ciwon kai that's why kaga na makara ta qarasa maganar tana sauke ajiyar zuciya sosai hankalin shi ya tashi ya shiga tambayar ta if she's okay ganin yadda ya daga hankalin shine yasa ta cewa hey I'm okay,and I'm sure you can attest to that ta fada tana kallon yadda ya tashi hankalin shi lokaci daya sai da ya tabbatar da she's okay din da ta ce kafin ya sauke ajiyar zuciya yace you scare the hell out of me,don't fall sick plsss ya fada kamar wani qaramin yaro har yana pouting lips din shi sosai abinda yayi ya bata dariya har bata san lokacin da ta fara dariya ba bai san lokacin da ya tsaya yana kallon ta ba ganin how cute she looks while laughing sai da ta lura da irin kallon da yake mata yasa tayi keeping serious face tace wait,what brings you to my office ma at the first place miqewa yayi ba tare da yace komai ba saida yaje bakin qofa ya murda handle din sannan ya juyo yace mata just checking up on you love,take care of yourself for me ya bude qofar ya fita ba tare da ya jira jin mai zata ce ba,sai da taga fitar shi kafin ta girgiza kai a cikin zuciyar ta tace this man will never change,ta shiga duba files din dake gabanta,bayan wani lokaci ta aje files din gabanta ta dauki farin lab coat dinta ta saka don zuwa duba marasa lafiya,ba qaramin kyau lab coat din tayi mata ba dan qaramin siririn glass fari ta saka tare da yin waje......................
Bayan HAYDAR ya bar gidan da kamar awa daya akayi knocking qofar gate din gidan,iro me gadi da yake zaune yana jin radio yayi saurin miqewa don ya duba yana budewa yaga baba Tanimu riqe da ledar kayan shi haqora ya washe yana fadin mallam Tanimu barka da dawowa yawwa mallam iro ya aiki Alhamdulillah ya kuma qarin haquri,haquri mun godewa Allah toh masha Allah,Allah ya baku haqurin rashi ya kuma yi mata rahama ameen ya fada yana cewa da alama yau kana cikin farin ciki naga sai washe haqora kake yi dariya mallam iro mai gadi yayi yace kaga ranar da ka bar gidan nan alhaji ya dawo yau kuma da ya fito yace man zai koma kuma ai kasan baze tafi bai cika mana aljihu ba cizon yatsa yayi bawai don bai samu kudin ba,shi dama mutum ne da baya da son abin duniya kawai yayi takaici ne da bai samu damar hada shi da litakar da ta duba Ayaanah ba a zuciyar shi yace in shaa Allah wani zuwan da zai yi zai mashi bayanin abinda ya faru ya kuma hada su dai wannan tunanin yayi wa mallam iro sallama akan zai shiga ya huta ya dakko hanya kafin ya dawo bakin aiki....................................
Bolt din shi na tsayawa ya fito jikin gate din ya qarasa yayi knocking,gefe ya koma yana jira a bude daga can kuma lawwali me gadi ne ya bude qaramar qofa yana tambayar waye ganin HAYDAR tsaye yasa shi bashi hanya yana mashi sannu da zuwa amsa masa yayi kafin ya wuce cikin gida,ganin babu kowa a parlour qasa yasa shi yin hanyar stairs,tun kafin ya qarasa hawa saman yake jiyo maganganun su,yana shigowa parlour suka juya gaba dayan su suna kallon hanyar shigowa ganin shine ya sasu dauke kai suka cigaba da hirar su kamar ma basu san da shigowar shi ba,gefen qafar Mamy ya qarasa ya duqa kafin yace good morning Mamy,morning waleed (Mamy ce kadai ke kiranshi da Waleed saboda a ganinta har gobe shi din yaro ne,kallon da kowace uwa kewa yi ma abinda ta haifa ko da kuwa furfura akan shi)kana Lafiya? Alhamdulillah Mamy, har ka shirya?ta tambaya tana shafa gashin kanshi amsa mata yayi da eh mamy toh masha Allah sai ku tashi ku tafi saboda kar kuyi missing flight din ku,Allah yayi maku albarka,gaba daya suka hada baki wurin fadin ameen kallon zannur tayi tace usman tashi ka dakko man wannan saqon kafin ku wuce,da toh ya amsa yayi hanyar dakinta bayan dan lokaci kadan ya dawo riqe da wata babbar Leda wacce take dauke da manyan jarkokin zam-zam guda biyu ya aje su inda mamy take a zaune HAYDAR ta kalla kafin yaji ta kira sunan sa ALIYU hankalin shi ya bata baki daya jin ta kira shi da asalin sunan shi yana sauraron abinda take fada wannan ledar da ka gani zam-zam a ciki magani ne na tsari nasa aka karbo maku kai da Usman saboda duniya babu gaskiya kana zaune zuciya daya da mutum amma shi ba haka yake a nashi bangaren ba zannur ne yayi saurin karban zance da cewa hakane kam Mamy don akwai wani abokin mu da yana zaune lafiya da mutane ashe babban aminin shi yana jin haushin shi saboda ya fishi samun kudi haka ya nemi salwantar da rayuwarshi sai da aka dage mashi da addu'a kafin Allah ya bashi lafiya wani banxan kallo HAYDAR ke bin zannur dashi jin abinda yake cewa don shi fa he don't believe in all kinds of such things Mamy da ta gama jin abinda zannur yace,tace shiyasa nima na karba maku zam zam akayi maku addu'a a ciki,wallahi idan har bakayi amfani da zam zam din nan ba wallahi kaji ma har sai da na rantse sai nayi mugun batar maka rai,tun wuri ma idan kasan baza kayi amfani da shi ba don't even carry it,a hankali yace zanyi in shaa Allah Mamy tace toh Allah yayi maku albarka ku tashi john ya kaiku airport din bari na kira jiddarh sai ta maku rakiya kamar wanda suka hada baki miqewa sukayi suka ce toh Mamy mun gode Allah ya qara girma tace ameen,wayarta ta dauka ta shiga kiran jiddarh dake dakinta tana dagawa tace ki saka hijabi ki fito ki raka yayyin ki airport sannan ta kashe wayar,hijab kawai ta dora akan sleeping dress dinta ta dauki wayar ta ta fito a zaune ta tarar da mamy tana kallon sunnah TV dugawa tayi ta gaida mamy kafin tayi mata sallama a cikin mota ta tarar dasu suna jiranta zannur ya zauna a front seat shi kuma ranshi ya dade ya kame a baya tare da hade rai saboda haushin zannur yake ji,dayan side din da HAYDAR ya zauna ta zagaya ta bude sai da ta dai daita zaman ta kafin john ya tada motar suka bar gidan lokacin qarfe sha daya da rabi....................................
Yau tunda yaje office hankalin shi baya jikin shi,duk motsi kadan zai duba time,gani yake kamar ma lokacin baya tafiya sai tsaki kawai yake yi,qarfe biyar yake komawa gida amma yau gani yake bazai iya ba gani yake kwata kwata lokacin baya tafiya yau baki daya qarfe uku da minti goma sha biyar ya dauki makulli ya fita daga cikin building din yana yin hanyar motar shi don komawa gida,baze iya cigaba da zama ba gani yake kaman agogon wayan shi ne ya sami problem so is better ya kuma gida don baya son zuwa da dare,yafi yaje da yamma..............................
Sai da ta shiga ko wani ward na asibitin kafin ta koma office dinta a gajiye,dan madaidaicin dakin dake cikin office dinta ta shiga ta kwanta don tana da buqatar hutawa kafin ta cigaba da aiki,bacci tayi sosai kafin ta bude idanun ta jin ana kiran sallar azahar a masallacin dake cikin asibitin,sai da ta dan ji qarfi kafin ta zuro farar qafarta wadda idan ka kalla zaka yi tunanin bata taba taka qasa da ita ba,toilet din cikin dakin ta shiga tayi alwala ta fito dadduma ta shinfida ta saka hijab kasancewar tana kaiwa yamma yasa ta aje dadduma da kuma hijab saboda sallah,bayan ta idar da sallah ta linke komai ta maida shi ma'ajiyar sa ta fito daga dakin tana zama akan office chair din ta,kamar hadin baki tana zama akayi knocking izinin shigowa ta bada,bude qofar akayi Nurse Habeebah ta shigo murmushi ne kwance akan fuskar ta tace da alama doctor bacci kika yi?itama murmushin tayi tace aikam dai Nurse Habeebah fitowa ta kenan kika yi knocking gurin zama ta nuna mata alamun ta zauna,thank you ta furta kafin ta zauna,doctor dama an kawo wasu mutane ne su uku sunyi accident suna emergency and your attention is needed tun kafin ta qarasa magana ta miqe ganin ta miqe yasa ta biyo ta tana fadin su matan ana kan basu temakon gaggawa amma shi namijin gaskiya da alamun sai anyi masa theatre saboda wani glass da ya shiga cikin sa tana dora hannunta zata bude aka riga ta daga waje sadeeq ne ya bude qofar ganin itama fitowa zata yi yasa ya wuce ba tare da yayi magana ba,theatre room din suka nufa su duka ukun babu wanda ya qara cewa qala,sai da suka shiga ciki sannan Nurse Habeebah ta taimakawa JAY ta saka gown din da ta dakko mata tana miqo mata gloves da face mask.......................................
A hanya jiddarh ta rinqa musu surutu a mota ganin yadda shi gogan yake amsawa tasan bata masa rai akai hakan yasa tayi shiru da dan bakin ta kar laifin ya dawo kanta,basu wani dade ba suka iso airport din don basu wani samu hold up ba a hanya,babu mai kaya a cikin su,kowannen su wayar sa ce kawai riqe a hannun shi bayan sun sauka suka qara yin sallama da jiddarh wadda take jin ina ma ta bisu,ta san ma hakan ba mai yiwuwa bane shiyasa ta kalli zannur tace yaya zannur ka fadama aunty lateefah idan muka samu hutu zan zo,murmushi yayi mata yace dama kuwa tana ta jajen ki murmushi kawai tayi tace toh shikenan yaya ka gaishe man da yara na kafin ta juya wurin HAYDAR tace safe trip bro dan murmushin yaqe yayi kaman wanda akayi ma dole yace thank you kafin ya juya ya bar wurin  dan tabe baki Zannur yayi don yasan shi yake ma duk wannan cin maganin a ranshi yace kayi ka gama in dai nine don banxa zan bawa ajiyar ka har ka gama rashin mutuncin ka har ya juya ya tina da zam zam din da mamy ta basu john ya sa ya bude mashi booth din motar ya dauka kafin yabi bayan HAYDAR...............
Yau ko school Laylah qin zuwa tayi,don tunda Sooraj ya fita aiki take ta zagaye gidan hankalin ta yaqi kwanciya so take kawai ya dawo ta tabbatar da ko dagaske ne asirin ya kamashi,tana zaune a parlour taji horn da sauri ta tashi daga inda take zaune tana bude curtains din parlour don taga ko shine, agogo ta kalla taga yanxun ba lokacin dawowar shi bane hakan yasa ta koma ta zauna,bayan ya shigo kallonta yayi ba tare da yace mata qala ba yayi hanyar dakin shi,hakan da yayi ne yasa hankalinta ya tashi gumi ne ya shiga jiqa mata jiki duk da uban AC dake aiki tunda ya shige ta kasa koda motsi,tana nan zaune har bayan shudewar mintuna talatin ta ganshi ya fito cikin wani tsadadden cashmere blue black wanda yayi matuqar yi masa kyau kasancewar yana da hasken fata,tunda ya fito take kallon shi gabanta na faduwa har ya qaraso inda take bata sani ba,ganin ta shagala da kallon shi yasa shi hade hannayen shi guri daya suka dan yi qara,hakan da yayi ne ya dawo da ita daga tunanin da ta fada,duqawa yayi daidai saitin fuskar ta ya hura mata iska a idon,dan far far tayi da idon wanda yasa shi qara kawo fuskar shi daidai tata fuskar yayi kissing idon kafin ya dago yace mata I'm going out wife take care of yourself,ya wuce ta ba tare da ya jira jin me zata ce ba,ji tayi kaman kawai ta qwala ihu ko zata ji ta dan samu nutsuwa,a haukace ta fara neman wayar ta har wani dishi dishi take gani,can ta hango ta kan kujerar da ta fara zama kafin ya shigo gidan number Hafsat ta kira da itama zaman jiran kiran Laylan take yi tana dagawa tace na shiga uku Hafsat,shi kadai take ta maimaitawa,tun tana tambayar ta cikin laluma har sai da ta gaji tace kinga malama idan baza ki bude baki kiyiman bayani ba zan kashe don ina da abinyi bazan tsaya sauraren koke koken ki ba sanin halin Hafsat yanxu sai ta kashe wayar yasa ta tsaida kukan da take yi ta kwashe labarin kaf abinda ya faru ta fada mata,tsuka tayi tace ke matsala ta dake gajen haquri ki bari ya dawo gidan zuwa dare kiga,ni nasan tunda malamin nan ya bamu assurance to an gama komai kawai ki sa ido kiyi kallo,ba wai donta yadda ba suka yi sallama akan zasu qara magana zuwa gobe don susan matakin da zasu dauka...............................
Sai qarfe hudu da rabi suka fito daga theatre,office dinta ta wuce don yin sallar la'asar da bata yi ba,bayan tayi sallar ko zama bata yi ba ta sakko don zuwa taga jikin sauran mutanen da suka yi accident din tare,Nurse Habeebah ce ta mata rakiya har bakin dakin da suke,tura qofar dakin tayi ta shiga tare da yin sallama a saman labbanta,gaban godon ta qaraso da niyyar duba marasa lafiyan amma wacce ta gani kwance akan gadon ne yasata ja baya qafafunta na rawa kamar wacce ake wa kidan gangi,sai da ta kama gadon ta riqe kafun ta iya tsayuwa da kafafunta fuskar da baza ta taba mantawa da ita ba har lokacin da zata yi numfashin qarshe a duniya,fuskar da ta dade da fidda qara ganinta a duniya,fuskar da har gobe baza ta iya mantawa da ita ba,bata san lokacin da hawaye suka fara fita daga cikin idanunta ba sai saukar su taji akan kyakyawar fuskarta,cikin sauri ta kai duban ta kan fuskar ta jin alamun motsi,idon ta ne ya sauka akan fuskar ta idanun ta na dan motsawa alamun ta fara dawowa hayyacinta,akan fuskar JAY da tayi tsuru ta sauke ganin ta,qura mata idanu tayi tana son tabbatar da abinda idanun ta suka gani,bata yarda da abinda ta gani din bane yasa ta saka hannunta ta riqo na JAY ganin bata bace ba yasa ta bude bakinta tace dagaske ke ce nake gani a gaba na JAY ko kuwa irin mafarkin da na saba yi ne?hannun ta data riqe ta qara riqewa gam kamar za'a kwace mata tace ba mafarki kike yi ba ni din ce a gaban ki Munarh ba wata ba,kuka ta fara itama tana miqo mata hannun ta alamun tayi hugging dinta bakin gadon ta zauna suka qanqame juna suka cigaba da koke koken su,kukan da suke yi ne ya farkar da dattijuwar matar da take kan dayan gadon,sai a lokacin ta tsaida kukanta tace mata bari ta duba ta gani take da ta saki hannun ta zata farka daga baccin da take hakan yasa ta qara qanqame hannun JAY sanin abinda take nufi da qara qanqame hannun ta yasa tayi dan murmushi tace mata baza ta bace ba tana nuna mata dayan gadon tace zata duba tane sai a lokacin hankalinta ya kwanta ta saki hannun,yan tambayoyi tayi ma matar tana bata amsa ganin babu wata matsala sai ciwon da tace qugunta nayi yasa tace ma Nurse Habeebah dake tsaye a bakin qofa kaman gunkin da aka dasa a wurin tunda suka shiga ta samu ruwan zafi adan gasa mata qugun dan buguwa ne tayi,aljihun lab coat dinta ta duba tana neman wayan ta don ta yi ma mom albishir amma wayam bata gani ba,tunawa da tayi ta barta cikin handbag dinta a office yasa ta yin tsuka a can qasan wuyanta,tana son zuwa ta dakko wayarta amma bata son motsawa gadon Munarh ta koma ta zauna tana mata murmushi,ita ma martanin murmushin ta mayar mata kafin tace JAY ina Besty na,gabanta ne ya fadi amma sai ta maze tayi kaman bata ji me tace ba ta fara tambayar ta bata jin ciwo a jikinta,amsa mata tayi da eh bata jin ko wani irin ciwo kafin ta qara maimaita mata abinda ta fada dazu pretending tayi kaman bata ji me tace ba ta miqe tace Munarh bari na dakko waya na a office gyada mata kai tayi kawai tana tunanin maybe bata ji tambayar da ta mata ba,amma idan ta dawo zata qara tambayan ta,bayan fitar JAY ya kasance su biyu ne kawai a dakin sai kawai tayi disconnecting drip din da aka saka mata ta sakko daga nata gadon ta je dayan gadon ta zauna,murya can qasa irin ta marasa lafiya tace sannu Ummi ya jikin?murmushin qarfin hali tayi tace da sauqi Maimunatu ya naki jikin?da sauqi ummi toh masha Allah,ta san Ummi baza ta taba tambayar ta wacece JAY ba idan har ba itace ta fada mata ba,Allah yayi ta mace mai sanyi hali babu ruwanta da sa ido irin na wasu iyayen miji hakan yasa tayi murmushi tace Ummi baki tambaye ni wacece wannan ba murmushin itama tayi mata don har cikin zuciyar ta take mata kallon yar da ta haifa ba suruka ba tace ke da baki da lafiya Maimunatu ai nasan zaki fada man wacece ki bari idan muka koma gida kika ji sauqin jikin ki sai ki bani labarinta ko?tayi maganar a sigar tambaya,tohm shikenan Ummi amma da alama ita ce kullum kike cika mana kunne da labarinta,ta fadi hakan murmushi kwance akan fuskar,gyada kai tayi tana murmushin itama ta koma nata gadon ta kwanta.............................................
Shi kanshi ya rasa irin zumudin da yake ciki yau,so yake kawai ya ganshi a qofar gidan su,tafiya yake yi yana dan qara gyara zaman hular dake kanshi,sai da ya shigo layin gidan su JAY ya fara dube duben inda yake,tunani ya fara yi na me ya kawo shi nan don kamar anyi ruwa ya dauke ya ma manta da ya taba haduwa da wata halitta mai kama da JAY,ganin yana batawa kanshi lokaci kuma shi ya tabbatar babu abinda zai yi a nan din yasa shi yin reverse ya nufi hanyar gidan shi,ji yayi duk duniya babu abinda yake son gani da kuma kasancewa dashi kamar Laylah,sai da ya tsaya ya siya mata ice-cream da chocolate don yasan tana matuqar qaunar su shi kuma ya siya ma kanshi fruit kafin ya dauki hanyar da zata maida shi gidan shi..........................................