BARRISTER SUHAIL

45

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️-----45 

A ɗakin Ammi ta iske Yaya Mubarak yana sauke kayan sa 

Bakin kofa ta tsaya tana kallon sa 

Shi Ma kallon ta yayı na dan lokaci ganin yadda ta tsaya taƙi shigowa kuma taƙi magana 

"ke lafiya kika tsayawa mutane bakin kofa,mi kuma ya kawo Suhail gidan nan shi ko kunyar zuwa gidan nan ma bayayi bayan Abinda yayi maki"

sai lokacin ta gane fushin da yaya Mubarak yake ashe na ganin suhail ne 

Ammi da ke fitowa daga daki duk taji abinda ke faruwa ta ce "Mubarak minene haka kake yi ina ruwanka da mijin ta"

juyawa yayi ya kalli Ammi 

"Ammi bansan miyasa ba,na tsane shi bansan miyasa kuke daukar abinda yayi ba komai ba"

kalmar tsanar daya furta akan Suhail ba iman ba hatta Ammi sai da taji babu dad'i ta rasa wata kalar zuciya Mubarak ke da ita mai riƙo ba ya yafiya duk abinda aka masa sai ya nuna kullum tana rokon Allah ya yaye wa Mubarak Wannan halin nasa

Iman ta sunkuyar da kanta

Hawaye suka cika idanun Iman amma ta hana su zubowa

Bata taɓa tunanin wata rana za ta ji zafin jin ana magana a kan Suhail haka ba

cikin Rashin jin dadin maganganun da Mubarak yake ko kunyar idanunun ta bai ji ba yake zagin Suhail a gabanta 

Ammi ta ce “komai da minene bai kamata ka fadi wannan kalmar a kansa ba ko ba komai mijin ƙanwar kane"

"Ammi idan kinga na dena tsanar sa ya daina cutar da iman"

A karo na farko ta kalli Yaya Mubarak kai tsaye

"yaya ni bai cutar dani ba"

"Dama taya zaki ga ya cutar dake"

Shiru ya mamaye ɗakin.

Ammi ma ta zuba mata ido

Iman ta ci gaba da cewa,

“Yaya, idan akwai wanda ya yi ƙoƙarin faranta min rai a wannan rayuwar, Yaya Suhail yana cikin mutanen"

Mubarak ya bude baki yana kallon iman yaushe tayi baki haka har take sa'in'sa dashi akan Suhail 


tashi tayi rai bace ta koma daki 

Ammi ta kalli Mubarak ta ce"kaga Abinda nake fada maka,idan zaka cire hannun ka a lamarin auren Iman"

Mubarak kuwa ya fahimci abin da ya gani to kodai Hafsat karya ta masa akan Abinda ta ce ta gani a gidan iman

Amman yasan halin Hafsat bazata taɓa masa karya akan abinda bata gani ba

Anan Ammi ta tashi ta barsa ya jingina da kujera dakin yana kallon kofar da iman tabi 

tabbas akwai wani abu da bai sani ba game da auren Suhail da Iman,yayi wa kansa Alƙawarin bazai  ƙara ɗaukar Abunda da bai gani ba 

a daren ranar iman ko Abincin dare bata ciba duk yadda Ammi ta lallaɓata ƙin ci tayi har ta hakura ta gyale ta 

Allah Allah take gari ya waye Suhail yazo ya dauke ta daga gidan 

washe gari

zeenah ce zaune a bedroom mami sanye da rigar bacci iya gwiwa marar hannu 

mai aiki ta shigo da breakfast ta ajiye a gabanta

ta juya zata fita ta ce"heey"

jummai ta juyowa tana kallon ta "mi kika kawo ne"

"Hajiya doya ce da kwai dai tea mami ta ce a kawo maki"


tsaki taja tare da cewa "come and park You local good zeenah bata saba cin irin su ba"

duk abinda ta faɗa jummai taji dan tana jin turanci 
batayi wata wata ba ta kwashe kayan ta fita dasu

Allah ya sani tun shigowar zeeenah gidan taji bata yi mata ba ta cika girman kai da gadara haka jiya da tare ta saka girki ya kai kala hudu duk abinda ta kawo sai ta ce bai mata ba daga ƙarshen ta kawo mata indomie da kwai shima bai wuci cokali biyar taci ta ajiye wai ta koshi

Jummai ta jima tana aiki a gidan, amma ba ta taɓa ganin baƙuwar da ta raina komai kamar Zeenah ba

a falo ta iske Mami ganin ta fito da kayan ta ce"bata ci bane"

"hajiya ta ce Abincin yayi local ba irin sa ra saba ci ba"

mami sai taji ranta ya bacci da zeenah minene laifin breakfast din nan ta lura da zeenah duk abinda zatayi mara bazata burge taba hakan yasa ta ce ki maida su Kitchen idan mijin ta yazo sai ya kawo mata Abinda zata ci nayi bakin kokarina"

Jummai na fita zeenah ta kira Suhail cikin Sa'a ko ta same shi 

"hello babe yunwa nake ji"

da mamaki ya ce"zeenah yunwa kuma mami bata baki Abinci bane"

fuska ta taɓe "ta bani babe amman bansan da irin saba it's just yam and tea kai ma kasan bana cin irin su"

jinjina kai yayi ya ce"Wannan da kika rena su naci na girma har kika gani kika ce kina so"

katse wayar sa yayi 

zeenah tabi wayar da kallo cike da haushin abinda Suhail ya ce mata 

gaba daya nadamar zuwa kaduna take da tasan Wannan halin zata kasance data biyo Suhail ba taje gidan su Abba ya tare ta da faɗa gashi nan din ma abinda zata ci ya gagare ta 

Zeenah ta jefar da wayar kan gadon tana cije baki.

Maganar da Suhail ya gaya mata ta kasa fita daga ranta

cikin ta banda kukan yunwa ba Abinda yake  amma girman kai ya hana ta sauko ta nemi abincin da Mami ta aiko mata 

A can falo kuwa Mami na zaune tana duba wasu takardun 

Suhail part din mami ya nufa 
na sanye da jallabiya  

a ƙasa ya zauna ya gaishe da Mami ta amsa masa 

har ya tashi zai fita ta ce"Ka shiga ka duba matar ka gata chan taƙi breakfast fa"


Mami, idan ta ji yunwa zata ci Ba komai ake biye wa mutum ba”

kan ya rufe baki Zeenah ta fara saukowa daga kan step din 

har Yanzu sanye take da rigar baccin nan 

suhail ya kalleta cikin mamaki lokaci guda kuma kunya ta kamasa zeenah bata da kunya Yanzu ko kunyar ma bata ji ta sauko a haka 
Karon farko Suhail ya ji kunyar halin Zeenah a gaban Mami

gaban Suhail ta tsaya tana hade rai "babe abincin ka kawo min"

wata kalar harara ya watsa mata yayi ficewar 

mami ko mamaki ya hanata cewa komai tunda take bata taɓa ganin mace marar kunya kamar zeenah ko ta manta gidan surukan take 

amman so mai hana ganin laifi,duk abinda zeenah take bata taɓa Ganin laifin ta ba



Kuyi manage da Wannan 

Kuyi like  share and comment