MURADIN ZUCI

Muradin zuci

by @bintuuu

Har garin Allah ya waye Momma bata rintsa ba, wani irin zafi da nauyi ta rinqa ji a zuciyarta kamar ana diga mata wuta. Babu abunda ke mata dadi a wannan lokacin, kuka kuwa ta yisa har ta gaji, ta kuma tsinewa jinjirar da duk ahalinta da suka ja mata wannan fitinar a gidan aurenta. Ita babu abunda yafi ci mata ranta irin wai akan yar tsintuwa za'a mata kishiya, akan yarinyar da ba'a san asalinta bama balle susan wacece ita. Indai haka ne toh tana jin har duniya ta nade babu ranar da zatazo Fadwa da abunda ya shafeta, bazata taba manta baqin cikin data qunsa ta dalilinta ba. Tun gari bai gama wayewa ba ta danna kira a Aina'u, a bugu na uku ta dauki kiran sai ta fashe da kuka me cin rai, hankalin Aina'un a tashe tace "Subhanallahi, Binta meya faru?" Momma bata bar kukan ba tace "Adda in nace banason yarinyar nan ko a gaba kar kowa ya kamani da laifi. Wallahi na tsani komai game da ita, ji nake kamar in kasheta in huta" da sauri Aina'u tace "Innalillahi, meya haka wai. Kanki daya kuwa, ki nutsu ki fadamin meya faru?" Cikin gunjin kuka tace "Wai akanta Abdulaziz yake ikirarin qaromin abokiyar zama, kishiya fa Adda, kuma wai akan yar tsintuwa" ta qarasa maganan wani kukan na zuwa mata da karfi. Shiru Aina'u tayi dan wannan batu ya daketa sosai itama, amma cikin dakewa tace "Binta kowa da irin kaddararsa a rayuwa, taki tazo a hakane sai ki zamo me karba ki godewa Allah, bawai kuma Ina bin bayan Abdulaziz bane, haqiqa dan kyautawa bai kyauta ba. Hakan da yayi kuma sake tabarbare lamuran yayi, duk da kema kinada naki kamashon kusan kashi saba'in acikin alamarin nan, na fada miki ki danne komai ki riqe yarinyar nan, ta hakan ne zaku samu maslaha tunda kin fahimci yanason yarinyar sosai, da ta hakan ne zaki qara janyo mijinki a jiki amma kikayi biris da maganata Binta, kika nuna ke kin isa kiyi yanda kike so babu mai tanqwaraki, Kinga irin kofar da kika bude yanzu ko, kinga irin matsalan da nake guje miki ko? Yanzu wa gari ya waya?" Momma ta share hawayenta cikin qunan zuci tace "Nida Yarana mun zamo abun banza agurinsa kenan? Kinason kicemin yar tsintuwar ta fimu a gurinsa kenan?" Aina'u tace "Ko daya, ni nasan bata fiku a gurinsa ba, amma laifinki anan shine. Tunda kikaga a karo na farko Abdulaziz bai bi ra'ayinki akan yarinyar nan ba sai ki sauqo ki karbeta, da shine zaman lafiyan naku, amma kika nuna naki taurin kan. Ta Ina kikaji ance Maza suna son macen da kullum tanason nuna ra'ayin ta ne abun fifiko akan nasu, Namiji ba'a masa haka duk sanyinsa Binta, amma baki fahimceni ba, sai da nace miki kota salon kissa ki karbi yarinyar da yanzu wata maganar mukeyi" Momma tayi shiru tana dafa kanta, ji take komai na duniyar ya fita kanta a wannan lokacin, wani kukan ne yana qara zuwa mata, sai kawai ta sakeshi a hankali wannan karon, shiru Aina'u tayi tana sauraron ta, dan itama bawai bataji zafin lamarin bane, amma tasani Binta tana aure a gidan sarauta ne kuma ko ba yanzu ba, there are high chances sai Mijinta ya qaro mata abokan zama, amma cewar ta dalilin Fadwan ne kwata kwata yasa itama taji ta fara qin yarinyar a zuciya. Tunda yarinyar ta shigo picture din abubuwa suke ta lalacewa a gidan auren qanwar tata. 
Hakuri ta hau bawa Momman, ta qara da fadin "Kiyi hakuri, kuma a yanzu ma lokaci bai qure ba. Ki samesa kuyi magana ta fahimta, mijinki yanada sanyin hali ta wani wajen. Nasan ko yau kika karbi yarinyar zai ajiye wannan batun agefe. Try that Binta, in sha Allah komai zai wuce" sai sannan Momma tace "Bazai taba wucewa ba, wannan baqin cikin da nake ji ayanzu bazai taba wucewa ba wallahi" Aina'u ta sake cewa "I said try that Binta, I'll be traveling later. It's a morning flight, 10 o'clock" Momma tace "Yau ne tafiyar?" tace "Eh in sha Allah, we decided Bristol was okay" tace "Allah ya sauqeki lafiya Adda, sai nan da two months din kenan?" Aina'u ta dan ja numfashi "I wish I'll be there for you, amma in sha Allah zan rinqa kira, ni dai dan Allah ki sauqo da kanki kibi lamarin nan ta hankali. Sannan ki kama bakinki, ba kowacce magana zaki rinqa fadi ba yanzu, nasan halinki in kina cikin bacin rai, akan gab'a mijinki yake yanzu komai zai iya faruwa. Ki sauqo ku fahimci juna, sannan banda wannan banzan dabi'ar taki na rufe daki. Kun dawo cikin jama'a ne yanzu. Ki bashi girman sa sosai. Mutumin nan is in line for the next ruler of that Emirate Binta, yanda kike mu'amalantarsa kwata kwata bai dace ba. A Gidan mulki respect yana zuwa fiye da komai, kin taso cikinsa amma sai in kasa gane ta inda halinki ya banbanta" shiru Momma tayi tareda dago kai ta kalli kofar ta data rufe tun jiyan, sai Aina'un ta cigaba da magana "I'll call you in muka isa" tace "Toh Adda Allah ya kaiku lafiya" ta amsa da Amin sukayi sallama. 

Saida Momma ta ajiye wayan kuma taji abubuwan na dawo mata da daddaya, maganganun da Papan ya fada mata suna amsa kuwwa a kanta da daddaya, ta duqar da kanta tareda dafawa da hannunta duka biyu. Tananan zaune aka kwankwasa kofan nata, shiru tayi da farko sai taji Laure tace "Ranki shi dade kiyi hakuri ki bude" sai kuma kukan Khadija ya karade dakin, da dan hanzari Momma ta yaye duvet dinta ta sauqa daga gadon ta nufi crib din da Khadijan ke kwance, a hankali ta dauke ta sannan ta nufi kofan ta bude. Da Jidda ta fara cin karo an shiryata cikin blouse dinta na yara me kyau a jikinta tana tsaye a bakin kofa ta fara kuka itama. sai ta miqa mata spare hannunta alamun ta iso gareta, da sauri yarinyar ta taho gurinta, sai ta nufi makeken gadonta hannuwanta riqe dasu. Zaman ta bakin gadon sai da ta fara feeding Khadijan sannan ta riqo Jiddan a jikinta tanajin sonsu na shiga lungu da saqon zuciyarta. Sun fi minti biyar a haka sannan  Laure tayi sallama. Momman ta dago kai tareda bata izinin shigowa, nan ta shigo ta gaisheta cikin girmamawa, ta gyada mata kai tana maida hankalinta kan Khadija, fita Laure tayi bata dade ba ta kawo mata breakfast dinta in different dishes har kala uku, ta jera mata su a kan ottoman din dake tsakiyan babban dakin sannan ta sake fita. Batafi 30 minutes da fita ba su Imam suka shigo dakin suma, kasancewar weekend suna gida ranar. Ganinsu yasa Momma ta musu murmushi tace "My boys, kun tashi kuma?" dan ta quduri niyyan bazata sake fushi da 'ya'yanta ba akan wani dalilin bacin ran da mahaifinsu zai saka mata. Ganin fara'arta yasa su Imran suka iso wajenta da murmushi suna gaisheta, tana kallonsu ta amsa sai ta kai hannu ta shafa kan kowannensu aranta tana karanto musu addu'a. Ita sai yanzu take ganin kuskurenta na dora fushinta ga 'ya'yanta, to me sukayi su?. Hira suka fara mata Imran harda kwanciya da miqewa a gadonta duk tana kallonsu. Tana gama feeding Khadijan sai Imam ya miqo hannu zai karbeta, a nutse ta dago ta daga jikinta tace "Oya! go to your big brother" tana murmushi ta miqa masa ita ya riqeta yana kallonta, bayan shudewan sakanni kuma ahankali tace "Imam" sai ya dago kai yana kallonta, sannan ta kalli Imran ta kira sunansa shima, sai duk suka bata hankalinsu suna saurarenta, tace "These are your sisters, kunji? Bakuda wasu qannen sai su biyun nan, Inason ko me zakuyi ku jasu a jiki kunji" Imran ne ya fara amsawa da "Toh" while Imam yayi shiru yana kallon uwar tasu, sai ta cigaba da maganan "Duk inda za'a je a dawo bakuda kamar qannenku biyun nan, ku hada kanku kunji" Kafin su amsa Papa yayi sallama a bakin kofan, Jidda ta tafi da gudunta tana kiran sunansa. A nutse ya shigo dakin yana kallonsu da murmushi a fuskarsa, saida ya zauna a dayan bangaren gadon sannan Momman ta gaishesa, ya amsa yana kallonta sai kuma ya miqa hannunsa gurin Imam ya basa Khadija. Sai da Papa ya jira yaran suka fita ya miqe tareda dawowa kusa da Momma har sannan hannunsa riqe da Khadijahn, a nutse yace "Meyasa kike son rufemin kofa ne Fatima?, banason sabuwar dabi'ar nan taki" bata kallesa ba tace "Ai na bude, yanzu ma ai ba a kulle ka samota ba" sai ya kawar da zancen da fadin "Inason zuwa Abuja gobe, and maybe it'll take me one week or so" rass Momma taji zuciyarta ta tsinke tuna yanzu yanada wata a waje da har maganar aure ta fara shiga tsakaninsu, sai ta dago ta kallesa tace "Ka bani yarinyar a qarqashin kulawata zan riqeta" dan stiff yayi yana kallonta, ta sake cewa "Naji zan riqeta a gurina, sai mu bar zancen auren naka" nan ma bai amsa ba ya dauke kansa, ganin haka tace "Dama akanta zaka qaro min abokiyar zaman kuma yanzu na yarda zan riqetan. Shikenan ai ko?" sai sannan ya dan dubeta yace "A'a... Kiyi hakuri jiyan ma nayi kuskure wajen yin maganar cikin bacin rai, amma tun asali inada niyyan qarin auren ko ba dan zuwan Fadwa ba. I'm sorry i made you think it's because of her" ya juyo gaba daya, ahankali ya nusar da murya "I'm sorry Fatima" cikin bacin rai Momman tace "Wallahi saboda ita ne, ai babu abunda zaka fadamin in yarda dakai yanzu Abdulaziz" sai ya juya ya kwantar da Khadija da tayi bacci akan gadon sannan yace "In Allah ya kaimu gobe zan tafi, akwai abunda kukeda buqata?" muryarta na rawa tace "Gurinta zakaje ko, baka dade da dawowa ba amma har zaka koma, in ba gurin ta ba Ina zakaje?" cikin gajiyawa yace  "Gurin aiki na zanje Fatima, I'm the leader in this family co-operation, and basically! They need me there everytime to analyze most of the work. Sannan ita wadda kike fadin zanje gurinta ba'a Abuja take ba, A Maiduguri take. Ina Abuja Ina Maiduguri?. Sannan wannan magana taje gaban iyayena, sun kuma bani ammana akan hakan. Yanzu maganarki kike so in bi kenan ko me?" Kawai sai ta fashe da matsanancin kuka, nan ya hau lallabinta amma bata fasa ba, daga qarshe tace "Dan Allah ka fita, banason ganinka. Kaje can ka qaro mata dubu ma Abdulaziz, ka auri duk matan duniyar nan sai ka gutsittsira Yar tsintuwar taka ka raba musu kowa ta riqe nata sashen". Da bacin rai Papa ya bar dakin a wannan karon ma.


Free page 

Bintu Musa ✍️