Muradin zuci
by @bintuuu
Bayan tafiyar Papa da kwana biyu, Maimuna ta kira Momma. "Anti Binta kiyi hakuri, alamarin dai beyi dadi ba. Yarinyar kamar wanda aka jefemu da ita, daga wannan sai wannan" Momma tace "Ni dai haka kuma za'a ganni a barni, ana zaton mutuwa zanyi dan ya fara neman wani auren kome?" Maimuna tace "Kai Anti Binta, ni ai kinsan duk abunda ya shafeki kamar ni ya shafa. Muma ba dadin wannan lamari mukeji ba. Kuma naji zafin wannan maganar auren nima. Amma kuma kema kinyi sanyi sosai akai Anti" tace "Kamar ya nayi sanyi akai" Maimuna ta danyi qasa da murya "Yar sarkin Borno fa yake nema yanzu haka, shekaran jiya ma Baban Sajida ya fadamin suna shirin zuwa da manya neman auren, Mai martaba yayi reaching out to Masarautar, kuma ga dukkan alamu ana daf da shirin basa auren" Wani irin buguwa zuciyar Momma tayi, 'Yar sarkin borno' bama common mace za'a kawo mata cikin gidan ba, Yar wata Masarautar me qarfi. Gumi ne ya yanko mata batasan lokacin da ta miqe daga zaunen da take akan kujera ba, tace "Yaushe za suje?" Maimuna tace "kamar dai yace cikin satin da zamu shigan nan dan basaso adau lokaci. Anti ki fitar da yarinyar nan daga gidanki, zamanta ba alkhairi bane kwata kwata. Tun ba'a je ko Ina ba kinga abunda ta fara jawowa, wallahi ni kwata kwata ma banason yarinyar nima" jikin Momma na rawa tace "Bari zan kiraki Maman Sajida" da haka ta kashe wayan. Kira ta dannawa Madina har ya katse bata dauka ba, ta sake bugawa a na biyun ta dauka tareda sallama, Momma bata ma tsaya amsa sallaman ba tace "Madina kishiya za'a min dai saboda yar tsintuwarcan" ta qarasa maganan muryarta na rawa, Sai Madina tace "Hasbunallahu, Adda kishiya akanta kuma. Toh saboda me?" tace "Saboda zai kawo mai kula masa da yarsa da kyau. Madina wai ni yau Abdulaziz yake nunawa duniya wata tsintacciya ta fini a gurinsa, wai ni ya tozarta saboda yarinyar da shima kansa baisan asalinta ba. Shikenan yanzu kam sai maqiyana su zuba ruwa a qasa su sha son ransu dan dadi" Madina tace "Wallahi tallahi bazata sabu ba, Yar Ina ce?" cikin rawar murya Momma tace "Yar Shettiman Borno" sai da Madina tayi shiru na wasu daqiqu tukunna, can tace "Me Adda Aina'u tace? Kin fada mata?" Tace "Na fada mata tace in karbi kaddarata, inyi hakuri" a zafafe Madina tace "Shi hakurin mun bi kansa mun taka da kafarmu. Wallahi baza kiyi hakuri ba Adda, bazata sabu ba, bamuga ta zama ba. Yar sarkin Borno fa!" "Kuma fa ki tuna wannan karon choice dinsa ce, shi ya ganta yake son aurenta, in baki manta ba zan tuna miki Adda. Auren hadi aka muku da juna" Kukan da Momma take riqewan ne ya kubuce mata, tana yinsa tace "Amma Abdulaziz yana Sona" Madina tace "Nasan hakan Adda, amma dole ki tashi tsaye wannan karon, dan yana sonki ai ba zama zakiyi ki tankwashe kafarki ba, ni mijina na biyun nan da zan aura Kinsan fafutukar da nayi akansa ne?" Momma ta danyi shiru tana digesting maganar na dan wasu sakanni sannan tace "Madina bazan je gurin malami ba, Wallahi akan tatsitsiyar yarinyar nan bazan je gurin malami b..." Madina ta katseta "Ai ita wannan zan baki shawaran yanda zakiyi da ita, ita ai qaramar alhaki ce. Akan wadda za'a kawo miki zaki dau mataki. Mutanen Maiduguri yawancin su basa zama hakanan Adda, wasunsu guma guman 'yan bin malamai ne, ba ga qawayena nan muna ta fafutukar tare ba. In baki sani ba wanda yamin aiki akan mijin nan nawa har can Maidugurin na bisa ya gama min komai, Wallahi ba'a zama hakanan Adda. Itama da shirinta zata shigo miki kinaji kina gani kin zama 'yar kallo a wajen Babban jidda" cikin firgici Momma tace "Na shiga uku na ni Fatima!! Madina nidai ko jifana akayi da yarinyar nan ne? Kamar wadda tazo ganin bayana. Daga wannan sai wannan duk a dalilin 'yar tsintuwaaa" Madina tace "Toh kin ma san yadda zakiyi a samu maslaha....kawai ki hallaka yarinyar sai muga ta inda za'a bullo da auren, ai me renon ta za'a auro miki ko? To ki kashe ta kowa ma ya huta Adda" Dif Momma tayi shiru tukunna, maganar na samun waje a kwakwalwarta, Madina ta sake cewa "Kiyi tunani ki gani Adda, wallahi in ba haka ba kin rinqa qunsan bakin ciki ta dalilinta, ai wasu haka Allah yayisu, da ibtila'i suke yawo a jikinsu, wannan mafari ma kenan tun tana wata biyu a duniya, Ina ga ta girma?" sai sannan Momma tayi magana cikin wani irin sanyin jiki "Kina ga hakan ne mafita Madina?" da sauri ta amsa da "Tabbas. Adda ki dau mataki yanzu kafin gaba kizo kina danasani" "Zaman yarinyar nan a gidanku ba alheri acikinsa. Uwarta ma ta jefar da ita ko ta mutu ko tayi rai balle ke. Masifa ce mai zaman kanta inkin ga hakan" har sannan Momma jikinta bai dawo daidai ba, sai kawai tace "Bari zanyi shawara, zan kiraki zuwa gobe" tace "Toh Adda. In kuma bazaki iya ba ai kinada amintacciyar hadimarki. In bakyayi da Habiba yanzu ai akwai Laure, wannan idonta a bude suke zata iyayin komai dan kudi" Momma ta sake cewa "Zan dai kirakin" da haka sukayi sallama ta kashe wayan cikin sanyin jiki. Tunani ta fada wanda batasan lokacin da Lauren ta shigo falonta na biyun tana sanar da ita tayi baqi a falon farko ba, firgit ta dago kai tana kallon Lauren, sai ta sake cewa "Kinyi baqi ranki shi dade suna Babban Falo" ta gyada kai kawai batace komai ba.
Da wannan maganar Momma ta kwana arai tana tishi akan tishi. Ita dai tasan batason yarinyar ko na misqala zarratan, amma kuma anya kisan beyi tsauri ba kuwa. What if Abdulaziz ya gane, what if asirinta ya tonu kowa ya gane ita ta kashe yarinyar? tasan Abdulaziz bazai taba yafe mata ba. Toh amma inta bar yarinyar tun yanzu ga abunda ta jawo mata, then what if nan da wasu shekaru in ta girma, wani irin masifa zata rinqa janyo mata? What if Abdulaziz ya fifitata akan su Jidda da Khadija, kai har dasu Imam ma. Inaaaa abunda bazata taba zuba ido ta gani ba kenan, 'ya'yanta sune gaba akan komai a gidan nan, 'yan asali, tsatson mulki gaba da baya. Da wannan shedan ya kanainaye zuciyar Momma a wannan daren. Takai ta kawo ma babu abunda take hasaso wa sai jana'izar Fadwa da za'a yi nan da kwanaki qalilan.
Washegari haka ta tashi da wannan tunanin. Da wata Hadimarta mai suna Yalli ta zo yi mata hidima sai tace "Kice da Laure Ina buqatar ganinta" ta amsa da "Toh ranki shi dade" da haka ta miqe daga tsugunnen da take sannan ta fice.
Bata dade da fita ba Laure ta shigo falon, bayan ta gaisheta cikin girmamawa sai Momman ta miqe ta nufi dakinta tareda fadin "Biyoni". A kan resting sofan dakinta ta zauna sannan ta umurci Lauren da ta rufe kofa, da hanzarinta tayi abunda aka sata sannan ta zauna a qasan carpet tana sunkuyar da kai. Saida Momma ta nausa sannan cikin nutsuwa tace "Magana nakeson muyi, amma Inason ya kasance daga ni sai ke, kuma har duniya ta nade banason jin na ukun mu a cikin wannan maganar" cikin hanzari Laure tace "Allah ya qara miki girma, wane ni...har in mutu baza kiji ba, wannan alqawarine" Momma ta gyada kai cikin amincewa, dan ba tun yau suke tare da Laure ba, ta mata sani tun da kuma tana ji ajikinta bazata bata matsala ba, sai taji Lauren tace "Amma kafin nan ranki shi dade Inason ki amincemin in leqo ko Ina, dan tabbatar da babu na ukun a boye" tace "Na amince" nan Laure ta miqe tareda leqa manyan windunan dake dakin ta tabbatar babu alamu kowa a gurin sannan ta jasu ta rufe gaba daya, da haka ta dawo ta zauna tana maida dukkan hankalinta kan uwar dakin nasu. Saida ta Jira Momma tace mata akan Fadwa ne batun sannan tace "Ranki shi dade. Nidai tun dawowar ku na qissima abubuwa dayawa game da yarinyar nan. Shegu irin su ba sa kawo alkhairi a duk gidan da suka shiga daman" Momma ta gyada kai cikin gamsuwa tace "Inason mu hada kai wajen kai qarshen yarinyar kowa ya huta, ko nawa kikeso zan biyaki in har aikin ya tafi daidai" cikin gamsuwa Laure tace "Ko baki biyani ba zan iya miki wannan aikin, kuma hakan shine daidai ranki shi dade. Ai qaramar alhakice, ba wahala zeyi ba. Ta hakan ne hankalin mai girma Yarima zai dawo jikinsa. Yara irinsu ba abun riqo bane. Hakan da zamuyi taimako ne" Mamma ta sake gyada kai tace "Kije sai na nemeki, kuma kinji dai abunda na fada miki ko? Kar na uku ya shigo cikin maganar nan dan ke zan sako a gaba" da sauri tace "Nayi rantsuwa kuma nayi alkawari ranki shi dade, babu mai ji har tashin qiyama" da wannan ta fice daga dakin tabar Momma a zaune tana qissima abubuwa a rai.
Washegari Momma taje sashen Uwah dan gaisheta kamar yadda ta saba. Laure na riqe da Khadijah tana biye da ita a baya suka yi sallama a babban falon. Basu samu kowa anan ba sai suka zauna zaman jiran fitowarta. Hadimarta laraba ce ta isa ciki dan sanar da ita isowarsu, Jim kadan Uwah ta fito daga dayan falon nata tare da wasu mata guda biyu wanda daga gani mutum zai shaida 'yan'uwanta ne. A ladabce Momma ta gaisheta tana sunkuyar da kai, ta amsa a tsanake kamar ko da yaushe. Saida Momma ta gaisa da sauran matan sannan daya daga cikin su tace da Laure ta miqo musu Khadija su ganta. Suna riqe da itan sai Uwah ta miqa hannu zata karbeta su Momma suka jiyo kukan jinjira daga can falon da Uwah suka fito din, da hanzari Uwah tace da Laure "Maza jeki daukomin Fadwa ta tashi" da haka ta fasa karban Khadijan duk Momma na kallonta. Kawo Fadwa dakin sai Momma ta rinqa binta da kallo, nan da nan Laraba ta kawo ruwanta da madaranta Uwah ta karba da kanta ta hau bata ruwan a nutse. Daya daga cikin matan ne ta kalli Fadwan tace "Ina abun qi ga d'a irin wannan, yarinya ma mai hakuri. Inajin tun zuwanmu bata budi baki ba sai yanzu" dayar tace "Ko daya, ai irin wa'innan in dai ka riqesu tsakani da Allah kaine da riba, kuma aljanna na nan tana jiranka" daya ta sake cewa "Wallahi kuwa, Allah dai ya kawo mata uwarta ta gari itama" Uwah dai zuwa sannan ta koma bawa Fadwan madara kuma batace uffan ba hankalinta na kanta.
Momma takai qololuwar cika da maganganunsu da tasan jifanta suke a kaikaice, amma har ta baro sashen itama batace uffan ba. Haka ta kade zaninta ta musu sallama sannan ta fice Laure na biye da ita riqe da Khadijan. Saida suka isa sashenta sannan tace da Laure "Zan nemeki gobe da dare" ta amsa da "Toh ranki shi dade".. Tsabar bacin rai ma koda Papa ya kirata a wannan daren bata dauka ba, ta cika tayi maqil da zancen kishiyar da matan nan suka jefeta dashi.
Washegari da safe ta aika a mata kiran Habiba. Da Fadwan goye a bayanta ta shigo har cikin dakin Momma da tace ta shigo. Sai da Momma ta dauki minti biyar batace komai ba tana feeding Khadija sannan ta dago kai "Bandakin nan zaki shiga ki qara wankemin towels dinnan, sannan ki wankemin shi" ta amsa da Toh tana kokarin miqewa tareda Fadwa a bayanta sai Momma tace "Da itan zaki shiga kenan?" nan da nan ta sauqo da Fadwan, ganin yanda ta riqetan tana kokarin kwantar da ita akan carpet yasa Momma cewa "D'orata kan kujera". Saida ta jira shigan Habiban bandakin sannan ta kwantar da Khadija a tsanake ta miqe tareda nufan gun Fadwan. Sunkuyawa tayi a hankali tana kallonta sosai, tana bin kowanne features na fuskar yarinyar da kallo a tsanake tanajin zuciyar ta na qara bushewa akanta. Har a wannan lokacin batajin nadaman decision dinta akan yarinyar. Ita kuwa Fadwa sai kallonta take da manyan idanunta, hasken dakin na qara fito da color na kwayar idanunta da suka kasance Grey. Baiwar Allah sai wasa take da hannunta a baki tana damalmala yawu kamar yanda jirajirai sukeyi. Momma takai tsahon minti uku a duqen tana kallonta, sai taji ance "Momma". Da wani mugun firgici ta miqe daga duqen abunka da mara gaskiya, idonta wuri wuri ta kalli Imam dake tsaye a bakin kofar yana kallonta shima, a dan zafafe tace "Meye haka? Ba sallama zaka shigo har nan, Meya faru?" a nutse yace "Imran bai shigo nan ba?" tace "Imran din abokin yawo na ne da zaka min tambayar nan, ba tare kuke ko yaushe ba?" sai yayi shiru yana kallonta, can kuma ya maida idanunsa kan Fadwa dake kwance, har sannan idonta na kan Momma tana wasanta da hannunta, sai kuma ya sake kallon mahaifiyar tasa. Ganin yanda yake binsu da kallo yasa Momma cewa "Meye kake kallona?" "Kaje sashen Uwah ka dubosa" a hankali ya juya daga bakin kofar ya tafi. Da sauri ta koma bakin gadonta ta zauna dan har sannan razanar da tayi yasa bugun zuciyarta bai dawo daidai ba. Habiba ce ta fito daga bandakin tace "Ranki shi dade na kammala komai, akwai wani abun da kikeda buqatar ayi?" fuska a hade Momma tace "Dauketa ku tafi" da haka Habiba ta dauki Fadwan suka fita tana binsu da kallo.
Da yammaci ta sake kiran Madina. Sun dauki lokaci mai tsayi tana sake qarfafa mata gwiwa akan alamarin, ta kuma ce zata kirata da daddare kar ma tace zata canja shawara, sai tace "Madina a yanda nakejin zuciyata a yanzu ba sai kin qara bani wani qwarin gwiwa ba, I'm a goner now. na gaba yayi gaba sai dai Abdulaziz ya samo gawarta in yanada halin isowa da wuri kenan" Madina tace "Ai na sanki ne Adda, wani zubin kema komawa kike kamar Adda Aina'u. May be ma a binne ta kafin ya dawo, Kinga ya huta ta baqin ciki" "Zan kiraki dai anjiman duk da haka" Momma ta amsa tareda kashe wayan. Dare nayi kafin ta kira Laure sai gata tazo da kanta. Daki suka shige Momma tayi qasa da murya "Menene shawararki akai? Ta wacce hanya zaki yi batareda an dau lokaci ba?" ahankali Laure tace "A cikin dakin zan gama komai ranki shi dade, ki bar komai a hannuna" ta gyada kai sannan tace "Kiramin Habiban". Da Habiba tazo sai Momman ta gyara zamanta a bakin gadon kamar ba wani abu, tace "Kin gama kula da yarinyar zan saki aiki ne" a ladabce tace "Nagama ranki shi dade, tana bacci ma" tace "Toh kije babban kitchen, ki dafomin tuwo acan. Miyan kubewa zakimin, na nan din banji dadinsa ba yau" Habiba tace "Toh, yanzu zanje inyi" da haka ta miqe ta fice. Jim kadan Laure ta shigo sai Momma ta miqe tayi qasa da murya "Ta tafin?" tace "Eh ta tafi can sashen, tabar yarinyar a daki" sai Momma tace "Toh ki fadamin ya zakiyi tukun" tace "Jinjira ce fa, da pillow ma bazai dauki lokaci ba" Momma ta gyada kai gumi na hade mata a goshi tace "Toh Ina jiranki" da haka Laure ta fice, sai kuma Momma ta kasa zama ta fara pacing a dakin tana zuwa da dawowa ta harde hannuwanta a qirjin tareda cizan yatsa daya cikin tsumayen abunda zai faru. Batayi pace hudu ba Laure ta dawo dakin ad'an gigice tace "Bata dakin" cak Momma ta tsaya zuciyarta na bugawa tace "Kamar ya..Kamar ya bata dakin?" Laure ta dan qara yin qasa da murya hankali a tashe tace "Wallahi bata dakin kuma banga Habiba ta fita da ita ba" da hanzari Momma ta fita daga dakin suka nufi can dakin Fadwan, amma sai suka samu babu kowa acikinsa, a firgice tace "Nemomin Habiban?" "Dubomin ita yanzunnan" da haka suka fice tare Laure tayi waje. Da farko tsayuwan jira Momma tayi a falon sai kuma ta nufi dakinta ta samu Madina na kiranta, tana dauka tace "Madina na shiga uku, kar wani ya san abunda muka qulla, an dauke yarinyar" itama adan firgice tace "Kuma kin tabbatar ba Habiba bace ta dauketa" tace "Laure ta tabbatar min ta fita babu yarinyar, ita Habiban da kanta tace min tayi bacci ma" a zafafe Madina tace "Qarya take, ku nemota tun kafin ta muku tonan silili. Inada tabbacin tasan komai" ai a rikice Momma ta jefar da wayar a gado zata fita suka ci karo da Laure da ta shigo tana haki, tace "Wallahi batacan din ma, har sashen Uwah sai da naje, mun shiga uku. Tasani wallahi, ta gudu da yarinyar" Momma ta dora hannuwanta duka biyu akai tace "Na shiga Uku ni Fatima" .......
----------------------------
Eighteen Years Later......
--------------------
End of free pages.
Bintu Musa.