SIRRIN ZUCIYA

Chapter seven

by @aysharano22

Ganin kallon da yake jifanta da shi yasa tayi saurin cewa “kofa brush banyi ba baby, and you are kissing me”, bai bari ta ƙarasa ba cikin wani irin yanayi yace “baby i don’t care okay…all i want is you plss”…

Kama hannunshi tayi tana daga kai ta kalleshi don ya fita tsayi sosai tace “no baby you need to rest first…nasan direct daga airport nan kazo bakaje gida ba so u need rest”…

Kai ya gyada mata yana janyota jikinshi yace “not just from the airport baby i came directly from Nigerian Army headquarters Abuja…ko gida banje na cire uniform ba kawai from headquarters na wuce airport, from Abuja airport to Lagos airport then to Victoria Island to see my baby”…

Ya ƙarasa mgn yana sake hugging ɗinta a jikinshi…bai bata damar yin mgn ba yace “baby i have a surprise for you”…

Dagowa tayi tana kallonshi har snn bata daina murmushi ba tace “really babe?..what type of surprise tell me”…

Jan hancinta yayi yana cewa “idan na fada miki ya tashi daga suprise”…

Tsuke baki tayi zata fara mishi shagwaɓa ya dauko cap dinshi dake ajiye ya saka mata a kanta, snn ya kama hannunta suka fita daga ɗakin yana cewa “come let me show you”…

Ba musu ta bishi suka fita daga ɗakin…basu tsaya a parlor ba taga ya fita har compound da ita nan take ta ware eyes ɗinta sbd ganin soldiers dinshi guda uku suma duk sanye da uniforms dinsu kowa ya riƙe wani decorative abu kmr board da akayi rubutu a jiki aka kuma ƙawatashi da all sort of flowers…

Juyawa tayi ta kalleshi full of excitement before ta maida kallonta ga boards din ta fara karanta na farko wanda aka rubuta happy anniversary baby, i wouldn’t want to do this thing called life without you.

Na biyun kuma aka rubuta loving you is my biggest achievement in life, i love you dearly.

Sai na uku wanda ya kasance na ƙarshe aka rubuta happy birthday in advance my love..you are my whole world.

Wani ihu data saki har su nanny da Abigail cook dinsu saida suka fito compound din don duk a tunaninsu wani abu ne ya faru da ita, can saiga daddynta shima ya fito nan duk suka samu gefe suka tsaya suna kallon soyayya…lol😜

Da wani irin gudu ta sake fadawa kanshi shima ya dagata cak ya shiga juyi da ita a wurin kmr ’yar baby yana pecking ko ina yaci karo da shi a jikinta kafin ya dakata da hajijiyan da yake har snn kuma tana makale a jikinshi kmr zata fashe da kukan farin ciki tace “baby you do all these for me?”…

Kai ya gyada tareda pecking lips ɗinta yace “anything for my baby girl”…

Sake hugging nashi tayi tana cewa “thank you so much baby i really appreciate..and i love you”…

Sake pecking lips ɗinta yayi bayan ya ajiyeta ƙasa har snn kuma cap dinshi na sanye a kanta yace “there’s one more surprise baby”…

Ido ta wara mishi tana cewa “again?”…

Yace “yes”, daga haka ya juya yana kallon soldiers dinshi yayi musu signal, nan take kuwa suka gane abinda yake nufi shi kuma ya juyo da ita yanda bazata ga abinda sukeyi ba har saida ya tabbata sun gama snn ya juyar da ita garesu yana cewa “look”…

Ba musu ta kai dubanta kan abinda yake nuna mata aikuwa a take taji kmr numfashinta zai dauke tsabar mamaki wanda bata gama shanyeshi ba ta juyo gareshi sai ya sake tafka mata wani abun mamakin…

Durƙushe yake a gabanta kan guiwa guda daya ya fiddo wani box ɗan ƙarami daga pocket dinshi ya bude tareda ciro ring din dake ciki sai talli yake yana walwali, ya shiga miƙa mata ring din yana dubanta da dukkan seriousness yace “Miss Suhana..Abraham..Montana..will you plss do me the honor of being my wife?..will you marry me Suhana?”…

Ya ƙarasa mgn yana wani lankwasa mata wuya kmr ba soja ba, haba wa nan da nan wurin ya dauki sowa da tafi su nanny da soldiers dinshi dama sauran ma’aikatan gidan da abun ke faruwa a gabansu sai ihu suke suna hailing dinsu, banda daddy da yayi crossing hands dinshi a ƙirji yanata kallonsu da murmushi kai da gani kasan shima abin ba ƙaramin burgeshi yake ba…

Suhana da har ƙwallar farin ciki saida tayi na ganin wnn tsantsar so da Desmond ke mata batasan time data miƙa hannun tana gyada kanta ba tace mashi “yes yes yes I’ll marry you baby”…

Saka mata ring din yayi a hannunta tareda miƙewa ya sake kankameta a jikinshi bai ko jin nauyin mahaifinta dake wurin to abunka da arna shi dadi ma yakeji ’yarshi tayi finding true love😂

Cikin kunne Suhana ke sake jaddada mashi cewa zata aureshi shi kuma yana sake jin kanshi tamkar a aljannah don farin ciki…nan kuma daddy ya nufo inda suke yayi hugging nasu duka yana congratulating dinsu hakama nanny dama sauran wanda abun ya faru a gabansu sai tayata murna suke, daga nan kuma daddy yace ya kamata su shiga ciki suyi celebrating…

Abinda Suhana bata sani ba shine duk wnn budurin da sukayi Desmond yasa daya daga cikin soldiers dinshi ya musu video don haka ana gamawa ya mashi transferring videon shima nan take ya tura mata yana cewa tayi sharing wnn good news da fans dinta, aikuwa kmr ya shiga zuciyarta don dama tunanin yanda sam bata tunada yin videon ba take sai kuma gashi ashe yasa anyi musu.

Wanka daddy yace taje tayi ta shirya sai tazo suyi popping champagne, aikuwa ba musu ta wuce bedroom dinta tayi yanda yace faka faka sai gata ta dawo sanye da wasu arnan riga da wando da sukayi mata kyau sosai face dinta ba make up da yawa haka sukayi popping champagne dinsu suka sha hadda su nanny aka sake yin hotuna snn ta tafi raka Desmond gidanshi don ya samu yaje shima ya huta kuma tayi mashi su girki da sauran abinda yake buƙata kafin ta dawo.

Abinka da arna babu wanda yayi yunkurin hanata don su ko cewa tayi zata koma gidanshi da zama gaba daya ba wani abu bane indai suna son junansu…bayan tafiyarsu ne daddy ya kira event planner daya bama order organizing mata biggest birthday party a gobe don jin yanda preps din ke kasancewa.

Captain Desmond saurayin Suhana ne da suka hadu last year ana gobe birthday dinta na 21 so yau suka cika 1 year daidai da haduwa, dukda cewa ba daga haduwarsu suka fara dating ba.

Soja ne shi da yake aiki a Warri sometimes kuma Abuja amma asalinshi ɗan Cross River ne…son da yakema Suhana kowa mamaki yake tunda ba iya boyewa yake ba, dukda itama tana sonshi amma nata son bai kama ƙafar wanda yake mata ba…har yanzu kuma bala’in sonta yake dukda ba ko wani responsibilty dinta ta dauka na girlfriend dinshi ba don su a wajensu girlfriend din mutum na iya zama kamar matarshi, so duk wani abu da mata zatayima miji girlfriends dinsu na musu amma in Suhana’s case da akwai difference.

Tun kafin su fara dating dama ta sanar dashi policy dinta na no sex till after marriage. Haka nan she consider it dirty kuma duk rainon mahaifiyarta ne, domin akwai wata mgn da take yawan fada musu itada sister dinta tun suna ƙanana wanda shine take riƙe da shi har yanzu.

Tace babban abinda mace zata bama mijinta tukuici da shi bayan aurensu shine virginity, sbd hakan na ƙarawa mace ƙima da daraja a idon mijinta kmr yanda loosing wnn virginity ke ƙaskantar da mace ya kuma zubar da duk wata ƙima da darajarta a idon namiji.

Wnn shine dalilin da yasa kwata kwata ma bata taba yin saurayi ba sai akan D, shima kuma bata fara sonshi ba saida ya amince da kudurinta, wanda hakan ya tabbatar mata cewa lallai ita din yakeso ba jikinta ba.

Da farko kmr bazai yadda da wnn policy nata ba sbd yanaga kmr bazai iya jurewa ba tunda su sun saba rayuwarsu da mata, wani ko sati bazai iyayi ba tareda mace ba koda kuwa bashida aure, amma sai son da yake mata yafi ƙarfinshi don haka dole ya amince da buƙatarta dukda cewa yasan bai zama lallai ya iya jurewa hakan ba.

(note:ga duk wanda yasan christians din kudu yasan haka lifestyle dinsu yake..basu dauki sex before marriage a bakin komai ba matuƙar its consensual, so kar aga na rubuta wani abun ace ai suna yin abu kaza ba da aure ba su haka lifestyle dinsu yake shiyasa zaki dade baki samu mace data haura 20 virgin ba a kudu, wasu ma tun a teenage age dinsu ake rabasu da shi ko kuma ince suke bawa samarinsu da kansu, Allah yasa mu dace Ameen).

Ranar yini tayi a gidanshi suna shan soyayya duk yabi ya ƙanainayeta ya hanata sakat ko video da takeso tayi editing tayi posting bai barta tayiba, haka ta yini a gidan da an fara hirar arziki zai fara tabebeniya sai da ƙyar take samu ta dakatar dashi duk yasa taji tayi regretting biyoshi, sbd ta tsani wnn habit din nashi sam, shi kuma har yana wani ce mata shi bazai iya haƙuri har sai sunyi aure ba, cikin zuciyarta tace “aiko saidai mu rabu”.

Haka dai ta samu ta lallaba ta rabu dashi lfy sai wajen 7pm ya maidata gida, shima don tace mashi zatayi karatu ne sbd tanada test gobe amma da bazai bari ta tafi ba shi ko bazaiyi komai da ita ba at least yayita kallonta yana samun sauƙi.

Sai bayan tafiyarshi ne ta samu tayi posting videon da taketa son posting ya hanata, ta tsaya ta tsara caption din daya dace ta kuma yima fans alƙawarin amsa duk tambayoyinsu zuwa gobe don bata taba posting abinda ya shafi love life dinta ba sai yanzu tasan kuma zatasha tambayoyi daga wurinsu…

Bayan ta gama ta kira Esther da Lilly tace duk suje Whatsapp group dinsu tana son mgn dasu nan suma ta fada masu duk abinda ya faru tareda tura musu videon…Esther sarkin ihu saida tayi ƙyanta cikin voice note suma sunata congratulating dinta sun jima suna hira kafin su sauka sbd kowa taje ta karanta abinda ya sawwaƙa kafin bacci ya dauketa.

The next morning ƙarfe 8 ta gama shirin tafiya school nanny tayi mata packaging breakfast dinta as usual, nan daddy ke fada mata yasa anyi organizing mata mini celebration a school, yayi reserving cafeteria dinsu so idan ta gama lectures dinta sai ta yanka Cake tareda course mates da school fans dinta da bazasu samu damar zuwa the real birthday partyn nata ba.

Sbd tsabar farin ciki rasa ma wane irin godiya zata mishi tayi kawai tayi hugging dinshi tana ce mishi she loves him…saida ya rakata har mota yaga fitarta daga gidan kafin ya koma ciki yana jin kanshi cikin farin ciki sbd wnn excitement daya gani tattareda ita.




Rano✨