Chapter eight
by @aysharano22
Koda ta isa school saida suka gama first lecture dinsu before su fara test din farko wanda suka gama bayan one hour...bayan break na 30 minutes suka sake yin dayar itama sukayi one hour so a takaice dai kafin one sun gama tests dinsu lecture daya ya musu saura kuma malamin bazai samu zuwa ba sai next week don haka kai tsaye Esther da Lilly sukayi announcing cewa cafeteria is reserved for Su's birthday don haka duk wanda is interested yana iya zuwa ayi shagali dashi.
Aikuwa kafin ma su tafi mutane da dama suna can suna jiransu...ita kuwa dukda ba make up tayi applying ba saida ta sake gyara face dinta cikin mota kafin su nufi cafeterian tareda Esther da Lilly.
Suna shigowa wajen ya dauki tafi da sowa sai wishing nata happy birthday ake tana amsawa da murmushi kan face dinta cox batasan tanada fans cikin Uni Lag har haka ba(ina ruwan cele🤣).
Karasawa sukayi ciki suka zauna Esther yau ta zama mcn karfi da yaji don daukan mike tayi tana welcoming wanda zukazo at the same time kuma waiters na raba different type of cuisines suna ajiyewa each table har wani silent music ke tashi a wurin...bayan kammala rabe rabe kowa ya hau cin kayayyakin dake gabanshi bayan an gama akazo yanka cake nan suka hada baki suna chanting mata"Happy birthday to you...happy birthday to you...happy birthday dear butter...happy birthday to youuu"..gama chanting din yayi daidai da lokacin da tayi cutting cake din nan aka shiga tafa mata, ta dauki cake din ta bama Esther da Lilly a baki suma suka bata sauran kuma ta bama waiters tace duk a rabama jama'ar dake wurin...hakan kuwa akayi don yayyanka qatoton cake din nata akayi aka ajiye kowane table daga nan kuma Esther ta hau kan table ta mike tsaye rikeda champagne bottle a hannunta tana jijjigawa itama Suhana ta dauka Lilly ma haka, nan kuma sauran mutane kowa ya dauko tumbler ya taho suka zagayesu kowa ya daga tumbler yana jira ayi popping ya samu rabonshi.
Meanwhile in one corner of the cafeteria Ayaan ne zaune yana rubutun proposal dinshi sai tsaki yake saki sbd hayaniyar da suka dameshi dashi...he wonder wane irin hauka ne wnn kawai mutane kuzo ku cikama mutane kunne da ihu sai kace wayanda suke a club ko gidan gala...hayaniyar ce yaji ba karewa zatayi ba ya kara sakin wani tsakin ya mike ya tattara takaddunshi ya bar wurin, shi baisan ma tsautsayin da ya shigo dashi cafeterian ba in the first place...kuma ai tunda ya shigo wurin tsitt yake shiyasa ma ya shigo din amma lokaci daya ya koma kmr market place.
Lilly ce ta shiga musu count down"one...two...three"...tana gama fadin three din suka bude champagne din a tare, nan da nan drink din dake ciki yayi tsalle yana fitowa daga cikin bottles din daidai lokacinda Ayaan ke kokarin kutsawa ya wuce ta tsakaninsu kawai saijin abu yayi kmr ruwa ya zubar mashi a kirji...kallon kirjin nashi yayi yaga yanda drink din yayi staining white shirt dake jikinshi nan take yaji ranshi yayi mugun baci...a hankali ya dago blue eyes dinshi fuskar nan a tamke kmr bai taba dariya ba yabi inda drink din ya fito da kallo nan kuma idanuwan nashi suka sauka cikin na Suhana Montana da itama ta gama waresu tsaf a kanshi tana dan cije lower lip dinta ganin aika aikar da tayi...sauke ido Ayaan yayi suna hada ido da ita ya sake tamke fuska don haka nan yaji ko hada ido bai sonyi da ita tsabar haushin da ta bashi...ita kam Suhana murya can kasa take furta"shit shit shit"...sai kuma tayi saurin ajiye bottle dake hannunta ta zaro tissue cikin tissue box dake kan table din ta nufeshi da sauri ta shiga goge mashi drink din daya bata gaba daya chest dinshi tana cewa"am so sorry plea......", ai ko karasawa batayi ba sukaga yayi wani irin zabura ya turata da iyakar karfinshi yace"get your fucking hands off me"....ya karasa mgn with full rage yana muzurai kmr wanda akama wani gagarumin abun...kiris ya rage Suhana ta fadi sbd force din da yayi applying wajen pushing nata Esther tayi saurin riqeta a jikinta...ba Suhana ba kadai kusan kowa dake wajen yasha mamakin abinda yayi mata gashi wuri a cike maqil har an samu wanda suka firfito da waya suka fara video don a samu na trending tunda sunsan she's a social media influencer...wani irin qululu Suhana taji ya tokare mata a makoshinta, ta wani kafeshi da ido kmr zata cinyeshi shi kuma bai sake tsayawa wasting time ba ya juya kmr walqiya ya fita daga wurin har yana tuntube don saurinda yake, Lilly tabi bayanshi da saurin itama tana surfa mashi bala'i kmr an aikota...sai a snn mutanen dake wurin suka fara processing yanda abin ya faru don da farko duk qamewa sukayi tsabar mamaki kmr wanda aka kafesu...wasu hawaye masu zafi Suhana taji sun ciko idanunta lokacinda ta daga kai ta kalli yanda wurin ke cikeda jama'a kuma wai duk sunga wnn cin mutuncin da yayi mata tasan kila da yawa daga cikinsu ma dadi sukeji...tunanin hakan yasa taji kmr zata hadiye zuciya ta mutu, wnn wane irin humiliation ne?...wane irin mara mutuncin mutumi ne wnn da baisan alkhairi ba?...mikewa tayi da sauri zata bar wurin Esther tabi bayanta tana riko hannunta suka bar cafeteria din.
Kai tsaye parking space suka nufa Esther ta amsa key din motar a hannunta ta bude suka shiga Suhana kmr jira take tana ganinta cikin motar ta fashe da wani matsanancin kuka dake cin zuciyarta...rungumeta Esther tayi tana cewa"butter take it eazy nauu...haba!, it's not that deep"...a fusace ta dago tana kallonta fuska shabe shabe da hawaye tace"seriously Esther is this all you could say?...i was humiliated right in front of you and all you could say to me is that is not that deep?...are you even my friend?"...da sauri Esther ta riko hannunta tana sake cewa"kinsan i didnt mean that...am sorry but plss kibar wnn kukan, its not worth it"...kwace hannunta Suhana tayi daga rikon da tayi mata ta wani hade rai tareda kauda kanta gefe...Esther ta sake matsawa kmr zata shige jikinta tace"i said am sorry Su, ni ba haka nake nufi ba, pls ki daina kukan nan you are a birthday girl, crying doesn't suit you"...sake kauda kai tayi bata ce mata komai ba daida lokacinda Lilly ta dawo daga bin Ayaan da tayi saida ta gama barbada masa rashin kunya snn ta dawo dukda ko kallon inda take ma baiyi ba balle ya nuna yasan me take fada...shigowa cikin motar itama tayi ganin yanda Suhana ke kuka itama tayi hugging nata tana dan patting bayanta tace "it's ok butter stop crying...shima naje na fada mashi abinda nasan har ya mutu bazai manta ba"...lafewa Suhana tayi a jikinta cikin ranta ta danji sanyin binshi da Lilly tayi har shima ta fada masa ba dadi, tasan dai duk tsiya yanzu ba ita kadai ce cikin bacin rai ba hadda shi...shiyasa dai takeji da Lilly sosai don tafi Esther hankali sometimes, kuma itama tana sonta sosai.
Ko driving ranar kasayi tayi sai Esther ce ta tuqasu har gida ita kuma suna baya tareda Lilly da har snn bata gaji da lallabata tana bata baki ba...kawai duk ta tuno abinda yayi mata sai taji kmr zata hadiye zuciya ta mutu...gashi ita Kuma ba iya wani masifa tayi ba balle itama ta sameshi watarana ta zazzaga masa rasshin mutunci a bainar jama'a kmr yanda yayi mata.
Koda sukaje gida ma saida nanny ta tambayi abinda ke damunta Lilly ta bata labarin duk yanda akayi, itama sam abin bai mata dadi ba dole ta shiga cikinsu aka dinga bata baki ana lallabata kan ta fara shirin birthday party dinta da ya rage few minutes a fara...haka nan dai aka fara mata make up duk bata cikin walwala kmr ba birthday girl ba and most importantly kmr ba Suhana da kusan koda yaushe zaka ganta cikin farin ciki ba...she’s a very happy person, zaiyi wahala kaga fushi ko masifarta don batama dasu at all sam bata iya fada ba, sanyi ne da ita sosai hade da rauni da hakuri shiyasa ko dan yaya abu yake sai ya daga mata hankali.
Haka dai sukaje akayi wnn birthday party sam babu walwala a tareda ita...daddy kanshi da yaga yanayinta saida yayi mamaki sbd yasan yanda ta kwallafa rai kan birthdayn nan nata...daya tambayi abinda ke damunta kin fada mashi tayi tace head dinta ne kawai ke ciwo, hakama babynta Desmond daya tambaya bata fada mashi ba as tasan shi sai yafi kowa ma daukan zafi kuma gashi soja dama ba imani ke garesu ba, tsaf zai iya cewa zai dau mataki akai, ita kuma ko matakin zaa dauka zatafi so a barta ta dauka da kanta yanda yaiji ciwon abin sosai kmr yanda taji ciwom wanda yayi mata.
Haka dai aka gama taro birthday girl ta samu gifts sosai ta yanka zabgegen Cake dinta su kuma mutane kowa yaci yasha kafin aka watse.
Masu buqatar siya zasu tura 500 zuwa 0013569116 Aisha Ahmad Tijjani Jaiz Bank. Sai a turamin evidence ta ***.
Rano✨