MUTUWAR AURE...! BOOK 1

16

by @aishatouuu

_Aishatou_
          ***


Da safe shiya shigo ya tashe ta, lokacin da ta buɗe idanun ta akan Babanta ta ɗora su, ya tsare fuskar ta da ido yana bin bushashun hawayen da suka kwanta akan kumatun ta da kallo a ranshi yaji babu daɗi amma saiya dake yace.
"Husnah kuka kikayi? Meya saki kuka?" Ya tambaye ta. Budar bakin ta sai cewa tayi 
"Baba dan Allah ka kaini wajen Yayana tunda kace Mama bata nan." Husna ta yi maganar da yanayi na roƙon da mai Kano har sai da yaji wani abu mara daɗi a ransa.
"In sha Allah zan kaiki amma ba yauba kinji?"

Kasan cewar ta yarinyar da aka rena cikin sanyin hali rashin gaddama kulawa da soyayya saita ɗaga masa kai ba tare da ta sake cewa komai ba.

"To tashi kiyi Sallah." Ya faɗa yana kama hanyar barin ɗakin, yana so ya gyara inda dabbobin suka ɓata kanya fita tunda dama kwana kawai suke yi a ciki, yasa kafarshi zai fita a ɗakin tace "Baba yaushe zaka samu a makaranta?"
"In sha Allah ranar Lahadi ina gida zan kaiku Islamiyya keda yar Iya, Boko kuma yanzu ana hutu sai an koma zan saku."
"To." Ta faɗi tana tashi ta fito waje.

Tana fitowa tsakar gidan da idanun Nana ta fara cin karo, ta watso mata uwar harara.

Kanta ta ɗauke ta wuce banɗaki, zata shiga Abba na fitowa yana gyara ɗaurin wando baya ta koma ta tsaya ya wuce yana binta da kallo.

Kanta gama alwala Baban ta harya gama sharo ɗakin inda ragunan suka ɓata Kuma ya wanke sa tas kamar basu kwana a ciki ba.

Bayan tayi Sallah ta gaida Nana kamar yadda ta saba amma ko kallan inda take bata yi ba, haka ta tashi ta koma ɗaki, saida taji Baban ta ya fito zai tafi sannan ta fito tayi masa a dawo lafiya.

            Mai Kano a ƙofar gida suka haɗu da Sale anan yake sanar da shi yau zai yi tafiya ƙyauye duba noman da ake masa.
"Kaga naso mu tafi da waccan Yaron amma yaƙi, hmmm Allah dai ya shirye shi, zan yi kamar sati ɗaya."
Mai Kano yace "Abba sai addu'a komai zai wuce, anya nima ba noman nan zan fara ba kuwa? Kafa yi mana wayo."
Sale yayi dariya yace "ai kai ka  daɗe da zama Bakano saidai a noma ka siya kaci."
"Au haka ne? Zan baka mamaki kuwa, kawai saidai kaji nace ma zo ka rakani girbi."
"Hhhhh ai kuwa daka kyauta noma ai da daɗi." Sale ya faɗa suna tafawa.

Bayan an gama karin safe Husna ta haɗa kwanukan wanke wanke zata wanke, saida tazo ɗiban ruwa Nana tace "ke rufe min ruwan nan na gaji da wannan lalacin naki maza ɗauki botiki ki ɗebo na wanke wanken a famfon masallacin mai unguwa." 

Husna tayi sororo tana kallon Nana, Ni'ima dake kusa da ita a zaune tana cin nata tuwon sai ta dubi Nana tana taɓe baki tace "kema dai Nana da jawa kai magana kike, banda haka tsakani da Allah a ina Ma'u zata iya buga tuka-tuka? Kuma ma naga nan shekaran jiya da aka yi wahalar ruwa naje dibo na wanka   Baba ya ganni kina jin faɗan da yayi tamin yace karna sake zuwa ɗiban ruwa, shi ne kuma yanzu zaki turata?"
"Na tura tan, nace na tura tan uwata, ke babu dama ayi magana sai kin samu abin faɗa, sallamammiyar yarinya yadda kika san bani na haife kiba duk wani halin ubanki kin kwashe, to saita ɗebo ɗin in yaso in uban naku ya dawo saiki faɗa masa nasa uwarki Ma'u ɗiban ruwa." Nana tayi maganar da masifa  kamar zata rufe Ni'ima da duka. 
"A'a ni meye nawa a ciki kuma Nana? Daga faɗar gaskiya." 
"Ba'a son gaskiya taki." Sai kuma ta juya wajen Husna dake tsaye tana kallon su tace "ke kuma kin ɗau botikin kin tafi ɗebo min ruwan ko saina taso kanki? Munafuka kika tsaya kina kallon mutane." 
Jiki a sanyaye ta dau botikin ta tafi ɗiban ruwan.

Nana kuma taci gaba da zazzagawa Ni'ima faɗa "ke babu dama nayi magana saiki sani a gaba kina min tsari kuma saboda rashin sanin daraja ta a gaban wannan munafukar yarinyar kike yi salon ta raina ni, kema kinyi min bare ita? Aikin banza aikin wofi." Nana keta zuba ruwan masifa Ni'ima kuwa ko a jikin ta taci gaba da uzurin gaban ta kamar bata san da ita Nana ke faɗan ba.

.......layi ake a famfun sosai wanda yafi ƙarfin ka ya ture ka ya diba, duk wanda Husna ta riga su zuwa tana kallo suke ɗiba su tafi, tana tsaye a gefe riƙe da botikin ta a hannu. Babu wanda ya damu da tsayuwar ta a wajen bare yace layin ta yazo bari ta ɗiba, to famfo ne da kowa ƙarfin shi ke ɗiba masa ruwa.

Tana nan tana zaman jiran gawon shanu Abba da Jaku nan su suka zo shan ruwa, cikin ƴan sakwanni suka tarwatsa mutanen kan famfon suka fara bawa Jakunan su ruwa, har suka gama ban ruwan babu wanda ya zo wajen da sunan zai ɗebi ruwa, dan sun san halin su basu da kirki yanzu in ka musu wasa zasu fasa maka bokiti kuma sun fasa banza, sanin wannan halin nasu yasa kowa ke matsawa ya basu waje saisun gama sun tafi sai kowa yaci gaba da ɗiban ruwan sa, har sun gama zasu juya Abba yaga Husna tsaye da bokiti a hannu.
"Ke zo nan." Abba ya kirata da gwarjin muryar shi ta masara ji.
Husna bata zoba dan ko kaɗan bata ɗauka da ita yake ba, saida ya sake kiranta sannan ta zo inda yake, yace "Waya turo ki nan?"
"Nana ce." 
"Nana." Ya sake maimaita sunan sai kuma ya karɓi botikin ta ya jefa wa wani acikin su yace "kai Maɗi zuba mata ruwa tabar wajen nan." Yana faɗin haka ya ɗane kan jakin sa yayi gaba.

Wanda Abba yasa ya zuba mata ruwan saida ya cika mata botikin ya ɗora mata sannan ya kada nashi Jakunan yabi bayan su Abba.
Duk da babu nisa tsakanin gidan da Famfon amma da ƙyar ta kawo ruwan gida saboda bokitin yafi ƙarfin ta.

            "Ni'ima kama mata ta sauke ruwan nan dan wallahi in kika fasa min botiki ubanki saiya biyani."
"Kema uban wa ya saki cikowa." Ni'ima ta fada tana sauke wa Husna ruwan tana hararar ta.

Washegari ma haka ce ta faru, sannu a hankali zuwa ɗiban ruwan wanke wanke ya shiga cikin jerin ayyukan da Husna keyi a gidan.

        yauma kamar kullum ta ɗebo ruwa tana tafiya ta wuce ta gaban su Abba a zaune a dabar su suna busa wiwi tazo ta wuce su, Maɗi ya bita da kallo sai kuma ya juya yana duban Abba dake murza wiwi yace "wai yarinyar nan dama a gidan ku take?"
Abba ya dubi Husna data ɗanyi nesa dasu sai kuma yace "eh ƴar gidan Baba Abdullahi ce."
"Shege Abba naga kana kula ta kodai kana ciki ne?" Wani a cikin su ya faɗi haka yana dariya. Abba ya harare sa sai kuma yace "kai fa banza ne mezan samu anan inna bita, kawai dai." Sai kuma yayi shiru.
"Maɗi yayi dariyar ƴan iska yace "wallahi ban yarda da kai ba Abba munfa san baka abu dan Allah, amma kuma tayi ƙarama fa dan naga ko eah abun nan bata fara ba babu abin da zaka samu."
Saida Abba ya zuki wiwin shi ya busa hayakin ta sama ta bade masa fuska sannan yace "zasu fito in sukaji wannan." Ya ware yatsun shi guda biyar sauran abokan iskancin sa suka kwashe da dariya.
Maɗi na dariyar mugunta yace "shege Abba kasan takan tsiya gashi kuma yarinya ta tara mazaunai duk da ƙarancin shekarun ta."
"Ina faɗa ma wannan in taji Maza za'a yi mace fa." 
Haka suka rinƙa maganganun banzan su akan Husna da duk wacce ta zo wucewa ta gaban su.


*****Yawan kukan da Husna keyi in taje kwanciya bacci yasa ta kamu da ciwon ido mai zafi, amma duk da haka Nana bata ɗaga mata Kafa, Baban ta ya kaita Cemist aka bata magani nasha dana digawa, kullum in zata kwanta da kanshi yake sa mata, yanzu harta fara sabawa da kwana tare da ragunan. 
Har maganin ya ƙare aka kuma siyo mata wani idon bai warke ba saboda yawon aiki da take yi da shi a rana, ido kuma baya son wahala duk lokacin da tayi aken rana ta tawo gida haka idon zai cakwale ya sake yin ja. 

Babu wanda ya damu koya kula da halin da take ciki, Baban tane kawai ya damu da lafiyar ta shi kuma sai Magarba yake dawowa gidan wannan yasa bai san mai yake faruwa ba.
            
Yau Nana ta sata shara, tana sharar tana share ido tsabar ƙura ko ganin gaban ta batayi sosai.
"Kina min ba daidai ba saikin sake gwanda ma ki maida hankali kiyi mai kyau." Nana ta faɗi haka lokacin da ta fito taga yadda take sharar sama sama, dan da gaske bata iya share gida mai rairayi ba.
Kanta gama sharar tayi jargaf da gumi ga ruwa nabin idan ta, da dabara ta ɗebi ruwa a buta ta fara wanke idonta amma ina yau jin ciwon idon take har cikin kanta. 

Tana tsugunne a bakin makwarara Nana ta fito ta dube ta, sai kuma ta kalli cikin gidan kwata kwata bai sharu ba saboda rashin iyawa da batayi ba ga idan ta da bata ganin inda take sharewar da kyau saida dabara.

"Lallai ma wannan ita ce sharar dana saki? To ai saiki tashi ki maimaita."
"Ba zata maimaita ba." Abba da shigowar shi gidan ke nan ya faɗa yana cogewa a ƙofar gidan yana kallon Nana a ɗage.
"To uban mutane kai asu wa da har zaka sawa mutane baki?" Nana na rufe bakin ta Abba yace "ni a wanda na isa, ke kallon kifa kawai nake dama kin kular dani jiya nayi shanya kin haɗa mini kaya, to wallahi in kika sake shiga sabga ta sai nayi maganin ki, bani da kyau fa, bar ganin ina ɗaga miki kafa." Abba yayi maganar yana wani ciccijewa.
Nana tace "An tattare ɗin ai ba kaika ɗaura min igiyar ba da zaka zo ka baza Kayan dattin ka akai kaki kwashe wa."
"Ke ni kike faɗawa haka?" Abba yayo cikin gidan yana ɗan layin da kana gani kasan a buge yake.
"Daga ciki Ni'ima tace "wallahi Nana in kika kula wannan komai yayi miki yawa banza babu abinda za'a masa, hmmm bashi da mutumci dan baki sani bane."
"Hhhhh faɗa mata dai yarinya, ita bata fita ke kuma mun haɗe dake a waje dole ki fita sanin karatun." Abba ya faɗa yana dariya.
Nana tayi cikin ɗakin ta da sauri tana zagin shi.
"Debabbe wanda bashi da albarka, yo iyayen kama baka bari ba bare ni, ɗan isaka."

Husna dai tuni ta zare jikin ta ta shige ɗaki da ƙyar ta iya diga maganin ciwon idonta ta kwanta, kuma sai Allah ya taimake ta har bacci ya ɗauke ta Nana bata neme taba kodan Abba na gidan yana zuba rashin mutumcin ne oho! Ita dai gaba ta kaita koba komai ta samu ta huta yau.

          Bayan kwana biyu idan ta ya ɗanyi sauki saidai har yanzu da sauran ciwon.
Kamar kullum yauma saida Baban ta ya tabbatar ta kwanta yasa kuba ya rufe ɗakin ta waje sannan ya koma ɗaki ya kwanta.
Wajen ƙarfe biyu na dare Husna taji kamar ana taɓata ta sake juyawa ɗaya barin tana ɗan kunkuni irin na mai bacci. 
Abba da yayi likimo a gefan katifar da take kwance ya zare hannun shi daga kan mazaunan ta da yake shafawa, saida yaga ta koma baccin sosai sannan ya sake maida hannun sa jikin ta yana matsa mata ɗuwawo yana wani lumshe idon iskanci.

Hannun shi ya fara ƙoƙarin turawa cikin wandon jikin ta, Husna kuma jin abu na taɓa mata jiki yasa ta buɗe idon ta da sauri tana zare su a cikin duhun ɗakin dan bata son haske kwana biyu saboda idon ta shi yasa Babanta kanya fita yake kashe mata fitila.
Jikinta taja kefe tana ƙanƙame wa, Abba daya zare hannun sa daga jikin ta tun lokacin data tashi yayi luf kamar baya ɗakin.

Bayan wucewar wasu yan mintuna Abba ya ɗauka Husna ta koma bacci ya sake matsowa zai taɓa ta, ta cikin hasken window taga mutum na matsowa kusa da ita duk da bata gane waye ba amma tabbas taga mutum wannan yasa tana gani yana miko hannun zai taba ta buɗe baki zata kurma ihu ya rufe mata baki yana zare mata ido acikin duhun ɗakin yace.
"Shishiiiiiii!" ya faɗi yana hanata ihun da zatayi, ai tuni jiki ta ya fara rawa saboda tsoro.

A hankali kamar ɓarawon dake gudun a kama shi yace "kiyi shuri kar kiyi kuka babu abinda zan miki kinji." Ya faɗa yana sake matsowa kusa da ita.
Kar...kar..kar Husna ta ɗaga masa kai ta na rawar jiki.

Hannun shi ya zare daga bakin ta, yana binta da kallon jaraba ta cikin duhun ya fara hilatar ta da cewa.
"Ki saki jikin ki kinji? Wani abu zan nuna miki in kika yarda zan baki Naira Ashirin gobe da safe, kuma zan siya miki duk abinda kike so kinji?"

Husna daba gane abinda yake cewa take ba tsabar firgici da tsoro kawai sai ta sake daga masa kai kamar ƙadangaruwa.

Wandon jikin shi yaja ƙasa daiga jikin shi ya fito waje ya miƙa hannun zai jayowa hannun ta ya ɗora akai ta kurma uban ihun da saida ya rufe kunne saboda ƙara.

            Kamar a cikin bacci Mai Kano yaji ihun Husna firgigit ya farka yana sake kasa kunne yaji ko itan ce.

"Dan ubanki ba nace karkiyi min ihu ba? Abba ya faɗa yana hawowa kan gadon gaba ɗaya ta sake ƙwala kiran.
"Babaaaaaaaa! Babaaaaa!! Babaaaaaaaa!!!" Ta kira sunan Baban ta ajere har sau uku, Mai Kano da kiran suka sauka akan kunnen sa radau zumbur ya miƙe tsaye ya fara laluman rigar shi, kan ya kai ga saka rigar ya kuma jiyo kamar muryar Husna nata cewa 
"Ni dai ka kyale ni, nace maka bana so, wayyo Allah Babana, Yayaaaaa! Mamaaaaa" Ta ƙwala wa Baffa kira tana rusa kuka, ai Mai Kano saiya yarda rigar ya fito da gudu.
Abba takaicin abinda Husna tayi masa yasa ya kifa mata mari yana huci zai kuma yin kanta yaji kamar an buɗe kofar daki za'a fito wannan yasa ya fasa kai mata cafka ya dira ta windo yayi ɗakin sa da gudu dama kuma ta nan ya shigo, Mai Kano yaji dirar mutum amma baiga Abba ba lokacin da ya fito, saida ya zo ƙofar dakin ya tuna bai ɗakko kubar ɗakin ba Husna na kuka ragunan ɗakin na kuka dan suma sun tsorata da dirar da Abba yayi.

Jikin Mai Kano na rawa ya buɗe ɗakin yana haske ciki da fitila, can karshen katifar ya hango Husna a cure jikin ta na rawa.
"Husnah meya same ki? Ke Husnah keda waye?" Muryar Baban ta da taji ya sake sata kuka, da sauri ya riƙo ta yana girgiza ta dan gaba ɗaya ta tsorata, Nana da tun ihun ta na farko ta tashi tayi kamar tana bacci jin suturun Mai Kano yasa ta fito tayi ɗakin tana faɗin.
"To lafiya kuma cikin daran nan?"

Bai bata amsa ba sai lallaɓa Husna da yake tayi magana amma ta kasa saboda ta riga ta tsorata da ƙyar ta buɗe baki tace 
"Baba Ab....ab...ab...ba ne ya shigo kum.... kum.....kuma yace sa...sas....saiya.....ya...yank..." ta kasa ƙarasa maganar kawai sai gani yayi ta sume masa.

Nan da nan ran Mai Kano yayi mugun ɓaci kanshi yaji ya sara lokaci ɗaya tsabar ɓacin rai yama manta data suma ya tashi ya tafi ƙofar ɗakin Abba yana kiran sunan shi.
"Abba kai Abba! Abba kai fito nan kai Abba kana jina." 

Abba najin Mai Kano yana kiran sa yayi masa banza dama yana shiga ɗakin yasa sakata kai daga karshe ma saiya saka kiɗa a cikin daren yadda duk abinda Mai Kano zai faɗa ba zai jishi ba.

             Mai Kano ya dawo ɗakin ya tadda Nana ta zuba wa Husna ruwa ta farka tana mata magana amma taki sauraren ta, sai kuka take kamar ranta zai fita. 

A ranar dole Mai Kano a ɗakin ya ƙarasa kwanan shi dan Husna ta riga ta firgice. 

A zaune ya ƙarasa ganin wayewar gari, yana zaune yana lissafa yadda zasu kwashe da Abba da safe aka kira sallar farko, lokacin kuma ya samu Husna ta koma bacci amma ta riƙe hannunsa ƙam Nana ta leƙo ɗakin taga yana zaune har yanzu yadda ta fita ta barshi haka yake.

Saida aka fara kiran Sallah sannan ya zame hannun shi da dabara ya fito yayi Alwala yana duban ɗakin Abba dake  buɗe da alama baya ciki.

Abinda Mai Kano bai sani ba kuma shi ne Abba tun komawar sa wajen Husna ba daɗe wa ya fito ya kama katanga ya haure yayi nasa waje.

Bayan an fito daga Masallaci Mai Kano ya samu Malam Malam yake faɗa masa abinda ya faru.
"Subhanallah wannan yaron na Sale baya jin magana Abdullahi, yadda kasan ba Sale ne ya haife shi ba." Malam Malam ya faɗi maganar bayan ya gama jin bayanin Mai Kano, sai kuma ya sake cewa.
"Karka damu bari a jima saimu sashi a gaba muyi masa faɗa in sha Allahu ba zai sake ba."
"To malam Allah ya kaimu jimawar nagode sosai Allah ya ƙara lafiya." 
Mai Kano ya faɗa yana juyawa gida, Malam Malam kuma ya shige gidan sa yana sake juya rashin jin Abba a ransa.

Da safe sama da ƙasa a ka nemi Abba a unguwar nan aka sara duk inda akasan yana zama anje amma baya nan, wannan tasa dole Mai Kano ya shirya ya fita kasuwa suka barwa dare inya dawo sayi masa magana.

Husna kuwa ranar duk rashin tausayin Nana saida ta kyale ta da jarababban aiken ta dan sosai ta tashi da zazzaɓi da ciwon kai, danma saida Baban ta ya bata magani kanya fita yace inya dawo sai ya kaita Cemist.
Ranar a kwance ta wuni a ɗaki abinci ma Ni'ima ce ta miƙa mata, da ƙyar ta samu taci kaɗan shima tana gamawa tayi aman shi.
Ni'ima ta dubi Nana tana zama a gefan ta bayan ta gama kwashe aman da Husna tayi tace "wallahi Ma'u tausayi take bani Nana dubi duk yadda ta koma daga daren jiya zuwa yau? Allah bakiji jikin taba har yanzu zazzaɓin bai sauka ba."
Nana ta taɓe baki tana ci gaba da yin aikin gaban ta tace "shi yasa yau kika taɓe a wajen ta sai kace uwarki ce ta kwanta ciwo? To ai ba uban wani ne ya ɗora mata cutar ba." 
"Hmmm Nana ke nan dan bakiga yadda take jin jiki bane?" 
"Inna gani ma zan yaye mata cuwon ne? Ke dan Allah ni kin ishe ni da zancen banza, duk waya ja mata hakan inba jarababbiyar Kakar kuba, data barta wajen uwarta ai da kowa ya huta."

Ni'ima sai tayi shiru bata sake cewa komai ba saboda takaicin maganganun Nana....