MUTUWAR AURE...! BOOK 1

17

by @aishatouuu

_Aishatou_

***
_________________


Wajen ƙarfe biyar na yamma gumi ya karyo wa Husna alamun zazzaɓin jikin ta ya sauka, a hankali ta yunƙura ta fito tsakar gidan, Nana kaɗai ta tarar a murhu, ruwa ta ɗiba a buta ta shiga ban ɗaki bata jima ba ta fito sai kuma ta samu waje a gefe ta zauna, wanka take so tayi amma tana tsoron ɗiban ruwa Nana ta balbale ta da masifa, daga karshe dai ta yanke shawarar zuwa ta ɗebo kamar yadda ta saba, ɗaki ta koma ta sako hijabin ta da wuyan ma ya ɗan buɗe kanta babu hula a haka ta ɗauki botiki ta fice daga gidan.

Duk abinda take Nana na kallon ta ta gefen ido amma tayi kamar bata san da tsuron ta a wajen ba harta fice daga gidan sannan ta raka bayanta da harara tana sakin tsaki tace "Aikin banza an barwa mutane wahala."

Husna na tafe tana gyara wuyan hijabin ta dake faduwa harta isa Famfo. Allah ya taimake ta babu layi, da yake yamma ce mutum biyu kawai ta tarar suna ɗiba tasa nata buga ruwan ma da dabara tayisa tana yi tana hutawa harta samu ta zuba rabin bokitin sai kuma ta tsaya jiran wanda zai taimaka ya ɗora mata.

          Tun fitowar Husna daga gida Abba ya ganta akan indan shi ta wuce saidai ita kwata kwata bata kula da shiba harta ɗakko ruwan ta kamo hanyar gida.

Da ƙyar take takawa bokitin na yawo a kanta saboda rashin kwarin jiki, tadan gota digan Malam Malam kaɗan taji.
"Shuuuuuuu." 
An zuba mata bulalar da saida ta zagaye cikin ta, tsabar gigicewa bata san tayi fatali da botikin kanta ba, tana juyowa suka haɗa ido da Abba dake tsaye a bayan ta riƙe da murtikekiyar igiyar dabai bainbayin Jaki yana huci Idanun nan nasa a juye kana gani kasan yasha wani abu, yace "Ke dan kut*****mar ubanki ni zaki yiwa ihu?"
"Tsuuuuuuuu" ya sake zubawa Husna duka da ƙarfi jikin ta na rawa ta fasa ihu ta kwasa da gudu, ya rufa mata baya, tana gudu nata kukan neman taimako shi kuma yana binta a baya yana duka kamar bawa da Ubangidan sa, haka Husna ta rinƙa gudun tsira tana kuka Abba yana binta a baya yana jibga suna zagaye layin, duk wanda yayi masa maganar ya daina dukan ta baya sauraren sa inka sake masa magana kuma ya dannama zagi, har ƙarfin Husna ya fara ƙare wa Abba bai dena binta yana duka ba, da taimakon Allah ta samu ta shige gida ya rufa mata baya Nana na zaune taga Husna ta shigo tana ihu rigar ta ta yage hijabin ta yayi nasa waje, kan tayi magana Abba ya shigo da gudu shima Allah ya taimaketa ta shige ɗakin Nana, zai rufa mata baya Nana ta tsaya a gaban sa, tace "Ina zaka kuma mara mutumci wallahi karka sake ka shigar min ɗaki." Nana ta faɗa tana babbake hanya.

Abba ya wani juya kai yana kallon Nana da jajayen idanun sa, yace "Ke wallahi in baki matsamin a hanya ba saina haɗa dake."
"Inka fasa haɗawa dani baka haifu ba, kai nace maka inka fasa dukana shege kake ba ɗan halak ba. Kuma wallahi inka sake ka shigar min ɗaki saina sheka maka tafasasshen ruwan can nakan wuta inka isa kuma ka ture ni ka shiga ka gani."

Zuciyar Abba da abinda yasha suna faɗa masa ya ture Nana kawai ya shige Malam Malam ya shigo gidan yana kwala masa kira dawowar sa ke nan almajiran shi da ƴan unguwa suke faɗa masa abinda ke faruwa.
"Kai Abba kai Abba wannan wanne irin dabban cine? Kanada hankali kuwa?" Malam Malam ya faɗi a faɗace.
Duk iskancin Abba yana dagawa Malam Malam ƙafa saboda ba shiga harkar shi yake ba kuma Abokin Baban sa ne, amma da yake ƙwayace a kansa sai cewa Malam Malam.
"Wai harni wannan yarinyar zata yiwa ihu danna shiga ɗakin ta? To wallahi kinyi sa'a yau kin tsira amma da saina kusa turaki ƙiyama yadda ko kuɗi aka baki bazaki sake mun musu ba." Abba ya jero maganganun yana yin gaba da baya kamar zai kifa.
"Innalillahi wa inna ilaihirraju'un kai Abba babu kunya babu tsoron Allah kake faɗin wannan maganar? To zoka fita kabar gidan nan, in kuma kaƙi wallahi yanzu nan zansa garada su danne min kai na saka a mari." Malam Malam ya faɗa yana tattara malum malum ɗin sa. Abba yace "Eh.....ai zan fita, amma ke duk randa kika kuma yimin ihu wallahi saina..." Sai kuma bai ƙarasa maganar ba ya juya yana tangaɗi yayi waje.
Nana tace "Salamamme mara amfani haihuwar asara."

Ni'ima data ɓoye a bayan Malam Malam saboda tsoro da sauri ta matsa ya wuce, Malam Malam kuma ya rufa masa baya.

Ƴan unguwa kuwa abin nema ya samu tuni suka fara kus kus kowa da abunda yake faɗa, wanda abun ya faru a gaban idan su sai mai da zance suke.

..........Mai Kano na dawowa Malam Malam ya tare shi da zancen, faɗin ɓacin ran da ya shiga dajin wannan mugun zance ma bata baki ne, a zuciyarsa yace "dole abinda banaso shi zanyi."
Bai tsaya dogon zance da Malam Malam ba ya shige gida yana ayyana halin da zai iya samun Husna aciki.

                Da sallama ya shiga gidan, Nana da Ni'ima suka amsa tare da yi masa sannu da zuwa.
"Yawwa Sannun ku." Ya faɗa yana rarraba ido a tsakar gidan, can kusa da ƙofar ɗakin Nana ya hango mutum kwance akan taburma yana rawar sanyi, ko ba'a faɗa masa ba yasan Husna ce dan ya hangi zanin atamfar ta data rufa dashi.
"Subhanallahi." yayi maganar yana ƙarasa wa kanta da sauri, ya yaye zanin yaga ta dunƙule waje ɗaya tana rawar sanyi haƙoran ta har haɗuwa suke saboda mugun bugun da zazzaɓi ya sake mata bayan dukan da tasha a hannun Abba.
"Husnah sannu kinji? Yi haƙuri tashi zauna mu gani, bari muyi Sallar Magarba saina kaiki ko nan Sir Sunusi ne, kai amma jikin naki yayi zafi da yawa." Mai Kano ke jero maganganun yana tashin ta zaune, amma saita kasa zama saboda zazzaɓi sai a jikin shi ya jingina ta.
"Ai zazzaɓin ma ɗazu ne ya sake rufe ta bayan wancan sallamammen ya jibgeta amma ai bata wuni dashi ba, inka karɓo mata magani anan Cemist ɗin bakin hanya ma zata ji sauki, ba sai kayi wahalar zuwa asibiti ba dan ciwon nata ba mai yawa bane tsamin jikine kawai yasa ta sake narke wa, wannan kuwa dama ai dole tayi shi tunda ta daku." Nana ta faɗi maganar tana aje masa ruwan shan data kawo.

Caraf Ni'ima dake saurarensu tace "taɓ wallahi Baba Ma'u yau a kwance ta wuni da zazzaɓin nan."
"To ƙarya nayi ke nan? Ƴar me bakin maganar tsiya." Nana ta faɗa tana bankawa Ni'ima harara.

Takaicin Nana ya kama Mai Kano dama gashi ranshi a ɓace yake, ya fita da ɓacin ran abinda ya faru ya dawo ya tadda wani maimakon ta tayashi jimanta abinda ya faru shi ne zata sashi a gaba tana masa soki burutsu.
"Eh soki burutsu mana inba haka ba wani mara hankalin ne zai ga jikin Husnah yace wai ciwon ba wani mai zafi bane." Yayi maganar a ranshi, a fili kuma sai ya dubi Ni'ima yace "ƴar Iya zoki zauna kusa da ita naje masallaci na dawo." 
"To." 
Ni'ima ta amsa tana tasowa daga inda take zaune ta dawo kan taburmar da Husna ke kwance.

Idanun ta biyu amma zafin zazzaɓi ya hanata magana kukan ma saboda tsabar ciwon da kanta ke mata baya fitowa sai hawaye kawai kebin gefan fuskar ta.

Jingina ta yayi da jikin katanga amma ta kasa zama dole ya sake kwantar da ita ya tashi, hular shi da wayar sama anan ya bar su yayi Alwala ya fice dan har an tada Sallah.

Ana idar da sallar yayo gida ya samu Ni'ima na bata ruwa fuskar shi a sake ya kama Husna yasa Ni'ima ta dakko mata riga da hijabi yasa mata, Ni'ima tace "Baba zan biku." Sai da ya riƙo Husna zasu fita daga gidan sannan yace "A'a ƴar Iya kinga yanzu dare ne muma yanzu zamu dawo kinji?"
"To Baba Allah ya sawake."
Ta faɗi da tausaya wa, sai kuma sannan Nana tayi magana.
"Allah ya bata lafiya."
"Amin." 
Ya amsa suna ficewa waje inda mai Adaidaita sahu ke jiran su dan daga masallaci ya taho dashi saboda yasan Husna bazata iya hawa bayan mashin ba.
          Suna fita Nana tace wa ni'ima "Yar me shishshigin jaraba, banza mara kishin kanta kina zaune kina kallo ubanki na nunawa wata so amma kina tayashi dan asara." 
Ni'ima tana jinta tayi mata banza sai baki data tura gaba.


_Sir Muhammadu Sunusi Hospital_
Mai Kano ya sha faɗa a wajen likitoci kansu karɓi Husna, yara ƙananan da ya haifi wasun su haka suka rinƙa yi masa faɗa amma haka ya rinƙa basu hakuri.

To ya ya iya da Ƙaddara yasan komai ya faru Allah ne ya jarrabe shi kuma Iya taja masa dan ita ce sila. Badan ƙaddara da bawa baya wuce ta da mai zai kawo faruwan hakan ma bare har yazo nan yara na shimfiɗa masa wulaƙanci.

"Malam ga wannan kaje ciki ka siyo mana wannan alluran yanzu, dan Allah karka ɓata lokaci." Wata Nurse ta faɗawa Mai Kano haka tana miƙo masa takardar da aka yi rubutu akai.

Bai ce mata komai ba ya karɓi takardar yabar wajen, Allah ya taimake shi bai samu layi a wajen siyan Allurar ba.
Cikin lokaci ƙanƙani suka yiwa Husna Allurai suka saka mata ƙarin ruwa tun ba'a daɗe da ɗaura mata ruwan ba bacci yayi awun gaba da ita, yana zaune a kusa da ita ledar farko ta ƙare aka saka mata ta biyu. 

Gumi yaga ta fara yi alamun zazzaɓin ya sauka, hannu yasa yana share mata gumin sai kuma ya cire mata hijabin jikin ta da dabara yadda zata sha iska.
            Sha biyu na dare baifi saura ƴan mintuna ba suka baro asibitin, lokacin kuma Husna da ƙafafun ta take takawa yana riƙe da hannun ta, Alhamdulillah jikin nata yayi sauki sosai dan yanzu bata jin ciwon kan haka babu zazzaɓi, sai sauran tsamin jiki da sai a hankali zata dena ji.

Suna fitowa ya samu mashin sai dai yasha tsada dan dare ya fara yi.Yana riƙe da ledar magungunan ta ita kuma tana zaune a gefan shi.

Tunda ta tashi daga bacci bata yi masa magana ba, har yanzu da suke hanyar komawa gida batace masa komai ba, duk abinda yace mata kuma saidai ta ɗaga masa kai alamar "eh." Ko "a'a 

Shi bai san Husna da miskilanci ba amma ya fuskanci sauyin rayuwa yasa ta fara canjawa, abubuwa da yawa daya santa dasu duk yanzu babu.

Ya juyo ya kalli yadda ta kwantar da kanta ajikin mashin ɗin tana kallon hanya duk sai yaga ta canja masa kamar ba Husnan shi daya sani mai yawan cika shi da surutu da karaɗiba. Yarinyar da ko faɗa suka yi da yayanta yana zuwa shi take fara faɗawa amma dubi yadda yanayi yasa tayi masa shiru ko zancen dukan da Abba yayi mata bata yi masa ba.
Sosai yaji wani abu mara daɗi ya tsaya masa a wuya, har mai mashin ɗin ya kawo su kofar gida Mai Kano na lissafi da tunanin yadda zai inganta rayuwar ƴar shi dan ranshi baya masa daɗi inya ganta cikin damuwa da kaɗai ci. 
"Anya banci amanar Safiya ba?" Ya tambayi kanshi yana sake duban Husna....!

.........Nana najin shigowar su ta fito tsakar gidan.
"Kun dawo?" Ta faɗi tana duban shi, kai ya gyaɗa mata, ta mele baki gefe sai kuma ta sake cewa.
"Allah ya sawaƙe."
"Amin." Ya amsa yana yin hanyar ɗaki da Husna.

Wajen kwanciyar ya sake gyara mata tana tsaye tana kallon shi tausayin kanta da mugun tsoron Abba zai sake dawowa ya kamata jikin ta har sai da ya ɗan fara rawa kuka na son kwace mata.
"Zoki kwanta kafin Allah ya kaimu gobe." Babanta ya faɗa yana kamo hannun ta tazo ta kwantan amma sai taɗan tirje taƙi zuwa ta kwanta, kanshi ya ɗaga ya kalle ta sai kuma yayi murmushi ya ja mata hanci yace "Babu fa inda zani yau tare zamu kwana." 
Ya faɗa yana ɗan dariya kaɗan dan ba ƙaramin tsoro da firgicin ya hanga a cikin idanun taba, kai ta ɗago ta zuba masa ido cikin son tabbatar wa ya jinjina mata kai alamar "da gaske yake."

Matsowa tayi ta kwanta tana kallon shi, yace "ko zaki ƙarasa shan furar ki?" 
"Um um." Ta faɗa a hankali muryarta bata wani fita sosai.

Ɗakin ya fude ya koma ɗaki ya ɗakko Sallaya ya shimfida a ƙofar ɗakin ta waje yadda zata rinƙa ganin sa, Alwala yaje ya dauro yazo zai tada Sallah Nana ta fito tana kallon shi da ɗan Mamaki, sai kuma tace "A'a yau kuma anan zakayi sallar Baban Ma'u?" 
"Eh." 
Shi ne kawai amsar daya bata, ta sake cewa "to bakaci abinci ba, ko a kawo ma nan?" 
"A'a na koshi naci da safe in Allah yasa muna raye." 
Yana dire maganar bai bata damar sake cewa komai ba ya tada Sallah.

Sororo Nana tayi tana duban sa, ta ɗan jima a tsaye tana tunani sai kuma ta koma ɗaki ta kwanta tana jiran shigowar sa.

Husna kuwa ganin Babanta na Sallah a ƙofar ɗakin yasa hankalin ta ya kwanta tsoron da take ji ya ragu, har bacci ya ɗauke ta tana ganin sa yana Sallah, sai dai tsoron data kwanta ta dashi yasa har cikin bacci take ɗan kiran sunan shi, wasu lokutan kuma saita farka ta kalli ƙofar ɗakin da sauri inta ganshi har yanzu yana wajen saita sake komawa baccin ta.

         Nana tun tana jiran shigowar sa har ta gaji ta kwanta bacci ya ɗauke ta, bata farka ba sai wajen uku na dare da mamaki take kallon ɗakin taga baya ciki, tsakar gidan ta leƙo sai ta ganshi tsaye a ƙofar ɗakin yana Sallah har yanzu. 

           Shi kuwa Mai Kano kwana yayi yana gadin ƴar sa yana kuma kai kukan shi wajen Ubangiji, sosai yayi Sallah yayi doguwar sujuda in ya gaji yakan zauna yayi karatun Alkur'ani yayi wa Annabi SAW Salati yayi istigfari da hailala, kafin ya sake miƙe wa ya tada wata sallar, ranar kwana yayi yana Sallah da zikiri har asuba.

Saida aka kira sallah a masallaci sannan ya tashi ya duba Husna jin garin sanyin asuba ya sauka sai ya koma ɗaki ya ɗakko malum malum ɗin shi ya rufa mata sannan yayi Alwala ya fita zuwa masallaci dan bada jam'i.

Yaɗan jima bai shigo gidan ba saboda sun tsaya da malam Malam a waje, anan Mai Kano yake faɗa masa Abba ma bai kwana a gidan ba.

Lokacin da ya shigo gidan gari yaɗan fara haske, ɗakin Husna ya koma ya tashe ta tayi Sallah, bayan ta idar tace masa ina kwana, ya amsa mata da kulawa yana tambayar ta jiki tace da sauƙi.

         Ya tashi zai fita dan so yake yaje ya ɗan kwanta kan a jima, har yasa kafar sa a waje yaji ta kirasa.
"Baba."
Ta kira sa da muryarta data sake sanyaya.
Juyowa yayi yaga yadda take kallon shi, sai kuma ya dawo kusa da ita ya zauna yana fuskantar ta yace "ya ya aka yi Husnan Baba?"
Kanta ta sauke ƙasa wahaye na taruwa a idanun ta, muryarta harta fara rawa tace "Baba dan Allah, dan Allah, Baba dan Allah ka kaini wajen Yayana dasu Maman Sama dan Allah Baba ka kaini can, ni bana son zaman nan can nake so." Ta ƙarasa maganar kuka na kwace mata.

Sosai maganar ta tayi melting heart ɗin sa, yasan abinda take tsoro kuma shi ma shi yake tsoro da gudu, tabbas kuma ko bata roƙa ba ta gama kwanan gidan nan daga yau dan ba zai yiwu ba yana ji yana gani a lalata masa ita ba, ko babu Safiya a duniya bama a gidan shiba, yana sane dai ba zai taɓa bari a wulakanta rayuwar ƴar suba.
"Baba zaka kaini ko?" Husna ta sake jefo masa tambayar tana riƙe hannun sa.
"In sha Allahu anjima zamu tafi daga nan kinji." Ya bata amsar yana ɗan sakar mata murmushi.
"Wajen yaya zaka kaini ko Baba?" Ta tsare shi da idanun ta da har yanzu basu koma daidai ba.

Basu rene ta da ƙarya da kwana kwana ba, haka basu mata renon faɗa mata abunda ba zai yiwu ba da sunan hillata ko yiwa yaro wayo, sam Safiya bata yarda da wasan yiwa yaro ƙarya ko cewa zanyi maka kaza ko zan siya maka kaza dan yaro yayi shiru ko kar yayi rigima ba, a'a ita kai tsaye takewa yaran ta magana in akwai abu akwai, in babu ta baka haƙuri.

Yakan tuna wasu lokutan da inzai tafi kasuwa Husna kan bashi sautukan "Baba ka siyo min kaza da kaza." Sako dai irin na yara ga Iyayen su, duk lokacin da ta faɗi wani abu da bazai yiwu ba kan ya bata amsa Safiya zata ce "Husnah Baban ki bashi da kuɗin siyan jirgin sama kiyi addu'a Allah ya kawo su." A lokacin sai dai yayi dariya yace "ke kuwa Safiyya ki barta mana yarinta ce fa, kuma wannan dogon bayanin naki shekarun ta ba zasu gane ba."
"Zata gane tunda tana da Allah, ƙwaƙwalwar Yaro bata rena magana yanzu saita koyi ƙarya da yaudara." Duk sanda suka yi haka da Safiya sai dai yayi dariya ya fice.

Bai fara gano ma'ana da amfanin yin haka ba saida Husna ta fara girma. 

Wannan tunanin yasa ya dubi ta ya dafa kanta cike da soyayya ya ce "zan kaiki wani waje da ban amma ba wajen Yaya da su Momma ba kinji?"
Duk da Husna ba haka taso ba amma saita daga kai kana duban sa, ita dai indai za'a bar nan ɗin to shike nan buƙatar ta ta biya.


      _NI A'ISHA A ZUCIYA TA NACE "SHIKE NAN AMMA FA BA SHI KE NAN ƊIN BA ASMA'ULLAHI HUSNAH_.



Nana na zaune a ɗaki ta cika tayi fam Mai Kano ya shigo, kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kanshi ya fara shirin kwanciya.
"Baban Ma'u ban gane abinda kake nufi da kwana da kayi kana gadin Ma'u da sunan Sallah ba?" 

Ba gaisuwar safe babu tambayar ya ya tashi kawai ta haushi da mita, akace wai sanin hali yafi sanin laya, bashi da lokacin fitina da ƙananun maganganun ta bacci yake son ragewa kansu tafi.

"Dan Allah bacci zan yi Nana karki samin ciwon kai, yi haƙuri kije waje inna tashi mayi maganar." Ya faɗi yana duban da da kyau, dan baya son ta sake masa wata magana kuma.

Ƙwafa tayi a ranta tana fitowa waje ta fara shara da hura wutar karin safe.
"Ai zaka tashin, dan wallahi bazan yarda da wannan sabon iya Shegen ba." Nana ke sharar tsakar gidan tana mita.

Bai tashi daga baccin ba sai goma saura, sosai yaji daɗin jikin sa nauyin da zuciyar shi tayi masa yaji ta ragu. 
"Ina kwana Baba?" Ni'ima ta faɗa lokacin da ya fito tsakar gidan.
"Lafiya lau ƴar Iya." Ya amsa mata yana duban Husna dake juya kofin kokon dake gaban ta.
"Husnan Baba ko jikin ne har yanzu?" Ya tambaye ta, kai ta girgiza masa, ya sake tambayar ta tasha maginta na safe.
"Uhm." Ta amsa har yanzu kanta na ƙasa. 
Yasan tasha ɗin tunda tace tasha dan bata da kin magani dama dai allura ce to nan fa ɗaya.
"A kaima ruwan wankan ne?" Nana ta tambaye shi, yace "A'a sai an ɗan jima." Ya bata amsar yana shigewa ɗakin da Husna ke kwana.
         Kayan sawarta ya gyara ya kwashe masu dattin ya zuba a jakar sama, saida ya gama haɗa kayan waje ɗaya sannan ya zuge ƙatuwar akwatin kayan nata, sauran na jakar kuma ya barsu a buɗe bai rufe ba, doguwar rigaa baƙa ƴar Saudi ya ciro mata wanda zata saka in zasu tafi sannan ya ciro mata sabon hijabin ta fari ɗan ƙarami mai kyau ma haɗin rigar ya ajiye akan katifar.
Waje ya fito yace "Husnah tashi kiyi wanka rana na sake yi." Yana faɗa mata haka ya ɗakko botiki da kanshi ya zuba mata ruwa, ruwan zafin da Nana ta ɗora masa na wanka ya ɗebo ya sirka mata ruwan sannan ya kai mata banɗaki yace "jeki kiyi wankan ina jiran ki maza." 

Nana baƙin ciki ya sake kashe ta a zaune. 
"Ai wallahi da nasan ita zaka bawa ruwan nan daban ɗora maka ba." Tayi maganar a ranta a fili kuma saita ɗan ja tsaki ƙasa ƙasa yadda ba zai jita ba.

Ni'ima ta dubi Baban nasu tace "Baba wani wajen zaku?" 
Yace "eh ƴa Iya." 
"Allah ya kiyaye hanya." Ni'ima ta fada, Nana ta harare ta dan ba haka taso tace ba taso ta tambaye shi inda za su dan tasan halin baƙin zurfin cikin sa inba shi ya gadamar kaji abuba to duk nacin ka baka isa ya faɗa maka ba.

Husna na fitowa daga banɗakin ya ce ta zauna ta sake wanke kafarta, sannan ya shiga shima yayi wanka.

        Ƙarfe sha ɗaya mai kyau sun gama shirya wa, Nana nata bugun cikin shi taji inda zai kai Husna dan taga ya fito da duka kayan ta ya ɗaure katifarta amma sai yayi mata banza dan fes ya gane nufin ta.
"Koma inane ai maji daga baya." Nana ta faɗa a ranta, lokacin da suke ficewa daga gidan yana riƙe da hannun Husna.

Ɗan sahun daya ɗakko su na tsayawa a cikin tashar Yankaba inda ake hawan motar Gumal ƴan Union suka fara tambayar.
"Alhaji tafiya ne? Ina zaku je? Gumal ne ko Garki, Mai gatari, Malam madori ko Hadeja?"
"Gidan'ri zamu." Mai Kano ya basu amsa bayan ya sallami me mashin ɗin daya kawo su. 
"Kai ɗan Small gana Gidan'ari sasu a motar Garki."
Kujerar baya ya biya kuɗin mutum uku aka ƙara mutum ɗaya suka zauna a wadace.
Basu jima ba motar ta cika suka tashi, kansu tafi sai da ya siya wa Husna lemon bawo suna fara tafiya ya rinƙa ɓare mata yana bata tana sha dan ya santa da aman mota sam bata son warin fetir.

Gidan'ari babu nisa titin Hadeja road wanda zai kaika Gezawa shizai kaika har garin babu kwana, dan tafiyar bata wuce awa ɗaya ba, kana zuwa Gezawa kayi rabin tafiyar, Gidan'ari ƙyauye ne amma a bakin titi yake kamar yadda Gezawa da Gabasawa suke a bakin titi, haka titin shizai kaika Doko, Garki Har zuwa Mai Gatari.


_To fa, ga rayuwa ta sake ɗauke Husna daga Birnin Kano zuwa garin su Mahaifin ta a cikin Jihar Jigawa, cikin wani ɗan ƙaramin ƙyauye da ake kira Gidan'ari._