MUTUWAR AURE...! BOOK 1

18

by @aishatouuu

_Aishatou_

***
_________________


A 2009 
Husna ta shigo cikin garin su mahaifin ta da sunan zaman ɗan wani lokaci.

Aramma dake sauraren bayanin da Mai Kano ke masa akan ɗan abokin shi ya girgiza kai yana ambaton sunan Allah.
"Ashsha gaskiya Sale yana cikin jarrabawa, Subhanallahi, Allah ya shiryi masa wannan Yaro, karka damu saita zauna a nan ɗin hankalin ka zaifi kwanciya gaskiya, in yaso inka gama ginin sai kazo ka ɗauke ta, Allah dai ya sake taimaka wa ya rufa muku asiri duniya da lahira." Aramma ya faɗi maganar yana jin tausayin Sale.

Dije dake gefan shi a zaune kuwa baki ta kama tace "kai amma wannan anyi shaiɗanin yaro mara ta ido, to Allah dai ya rabaku dashi lafiya dan irin waɗan nan yaran zama dasu sai ana kulawa, sam baiyi halin ubanshi ba, uwarsa ma ai mutuniyar kirki ce bakaga abun arzikin da take min ba innaje, kayya albasa batai halin ruwa ba."

"Kayya kayya Hadiza wannan wacce irin magana ce haka? Ina hanaki aibata ƴaƴan wasu ba kya ji ko? Kai da kake da ya'ya ga jikoki nan turmus wasu ma ba'a haife suba, wasu kuma saika mutu zasu zo duniya amma shine kike wannan magana haka mara daɗin ji akan ɗan wasu? Dije waya aike ki irin wannan zance? Kayiwa ɗan wani fatan Alkhairi Allah saiya gyara maka naka. Karna sake ji dan Allah." Aramma ya tari numfashin Dije da tsawatar wa akan abinda tace.

Aramma ya dubi Mai Kano yace "ai kace karshen watan nan zaka fara ginin ko?"
"Eh in sha Allahu haka nake fata, ko ɗaki biyu na samu na rufe kawai saimu koma."
"To hakan yayi Allah ya taimaka yasa Albarka, ke Asma'ullahi Husnah zomu gaisa mana kwana biyu baki biyo Babanki kunzo tare ganin tsohon angon naki ba." Aramma yayi magana yana kama hannun Husna dake zaune a kusa da Baban ta.
"Ina kwana?" 
Aramma yayi dariya yace "ai kina shigowa muka gaisa ko dai harkin fara tsufa ne Husnatu." Da tsokana irin ta kaka da jika Aramma ke yiwa Husna magana, Dije kuwa taɓe baki tayi, dan tunda suka shigo Husna ta gaishe ta ta amsa sau ɗaya bata sake kallon inda take ba.

Mai Kano ya ware kayan sawar ta mai datti yace "wannan masu datti ne." Aramma ya dubi kayan yana Murmushi yace "Asma'ullahi dai ba zata iya wanki ba tunda ba renon mu, bace wannan riƙon shayi da Burodi ce bata da ƙarfi, saina bata tuwon gitti da miyar kuka tukunna zatayi ƙwari. Aramma ya faɗa yana Murmushi sai kuma yace "babu komai inaga sai a kaiwa uwarta Mariyatu ta wanke mata masu dattin ko?." Dije tayi caraf tace "yanzu wannan ƙatuwar budurwar ce za'a ce sai anyi mata wanki banda dai san ɓata yaro irin naka Aramma? Sa'ar Sajidan Mariya ce fa, yanzu meye Sajidan batayiwa kanta."
"Ke matsala ta dake rashin gane wa Hadiza in sa'anin juna ne yanayin tasowar su ai ba ɗaya bace, yaran Maraya (binni) kamar wannan basa wanki, kuma in kinyi haƙuri ma zaman nata anan duka duka na kwana nawa ne zata koma inda ta fito." 
Mai Kano dai yana zaune yana jinsu haka Husna dake zaune a kusa da Aramma.
"Kinga tama fasa zama a ɗakin ki dan naga alamar bazaku shirya ba, a matan gidan nan zan yi mata uwa da kaina saboda naga alamar bazaku daidai ta ba." Aramma ya faɗi yana ƙwala wa yaran cikin gida kira, basu jiyo shiba, ya dubi Husna yace "Asma'ullahi maza jeki cikin gida kice Ramma tazo injini." 
"To." Ta amsa mishi tana miƙe wa ta fito waje, dan tasan duka matan gidan tunda suna zuwa da Maman ta.
           Bata jima da fita ba sai gasu sun dawo tare da da Ramma, a ƙofar ɗakin Ramma tayi sallama, daga cikin ɗakin Aramma da Mai Kano suka amsa, sai kuma ta durƙusa tace "Aramma gani."
"Dama ƴace nayi miki gata nan Asma'ullahi zata zauna damu na ɗan wani lokaci." 
Cikin girmamawa Ramma tace "to Aramma nagode." Ta faɗi da murnar ta dan bata da yaro ko ɗaya a gidan wajen shekarar ta guda ke nan da auran Lirwanu amma har yanzu Allah bai bata haihuwa ba, sannan tasan Maman Husna duk da baifi sau biyu ta taɓa ganin taba amma ita kanta ta shedi kirkin matar.

Aramma ya sake cewa "Yawwa ki duba cikin gida insu Iro na nan kice nace suzo su kawo miki kayan sawar ta."
Ramma ta amsa wa Aramm da "to." Ta miƙe ta koma cikin gida.
Dije kuwa saita taɓe baki tace "nima na huta gwanda ma daka haɗa su can su karata."
Aramma baibi takan zancen taba suka ci gaba da magana da Mai Kano.

                    Yara na fita da kayan Husna Lirwanu ya shigo ɗakin da Sallama.
"A'a harka dawo daga ɗan bagajen ke nan?" Dije ta faɗa, saida ya zauna a kusa da Mai Kano sannan yace "eh nadawo dama ƴan gaisuwa nakai ina kaisu kuma na juyo.Yaya Mai Kano sannu da zuwa?" 
"Yawwa Sannun ya gida da iyali?" 
"Lafiya Alhamdulillah a'a Ma'u yau tare kuke ke nan?"
Husna ta ɗan zamo ta rusuna kamar yadda ta saba tace "ina wuni." Yana cika baki da ruwan tsaki da kanwar daya gani a gaban Aramma ya amsa mata.

          Aramma ya dube shi sai kuma ya girgiza kai ya mai da hankalinsa wajen Mai Kano yace "kaga wannan kanin naku sai kuna masa addu'a ni bansan ina Lirwanu ya kwaso halin shiba, kowa na neman yadda zai rufawa kanshi asiri amma banda shi gashi da mata da yara amma har yanzu hankalin nashi da saura."
"Wani abun ya kuma yi ko Aramma?" Mai Kano ya tambaya yana duban Aramma dan yasan halin Lirwanu da rashin sanin ya kamata.
"Hmmm! Ɗan mashin ɗin da Salisu ya haƙura yabar masa yana acaba dashi tunda yaƙi zuwa kasuwa ya nemi kuɗi, to shiya ɗauka ya siyar shekaran jiya."

Mai Kano ya buɗe baki yana duban Lirwanu da mamakin jin maganar yace "Kai to me kayi da kuɗin?"

Kan yayi magana Dije tace "kaji Mai Kano da wani zance yanzu magidanci kamar Lirwanu har a tambaye shi me yayi da kuɗi."
 Aramma ya dube ta cikin takaicin zancen ta yace "da yake shi kadai ne me Iyali ko? Wai me yasa duk lokacin da Lirwanu yayi abu bakya bari ayi masa magana ne Hadiza? Yanzu bama wannan ba ki faɗa min me yake siya a gidan nan na hidimar Iyali wanda zai sa har ya dauki mashin ya siyar?"
"Sabulun wanka dana wanki mana Aramma ai kasan dai shi yake siyawa matan shi."
Baƙin cikin managar ta ma saiya hana Aramma sake cewa komai.
 "wai sabulun wanka dana wanki." Dan Allah ji wani zancen banza.
        Mai Kano ya gyara zama zai yi magana sai kuma ya cewa Husna "jeki cikin gida wajen su Indo kuyi wasa, bari nayi magana da Babanki kinji?" 
Kai ta ɗaga masa ta fita daga ɗakin, shi kuma ya fuskanci ɗan uwan nashi ya fara masa faɗa da nasihar da in haddace wa ce ma ya kamata ace zuwa yanzu ya hadda ceta tsaf babu gyara saboda kusan duk sanda yazo garin saiya biya masa ita kanya tafi sai dai in basu haɗu ba.

....... Husna na fitowa ta gaida matan gidan, ta samu waje ta zauna a ƙasan unuwa, sauran matan sai tambayar ta suke tana daga masu kai, Indo ƴar gidan Salisu da suke kusan sa'ani duk da ta ɗan girme mata kaɗan ita ce tazo wajen ta tana mata surutu, ita ma bata wani kula taba sai kallo da take binta dashi.
A gaban ta su Zahara da sauran matan makota suka kafa gulma harda masu ƙarfin halin tambayar ta ko an dawo da ita nan da zama.
 
"Allah na tuba dama fa Nana bazata riƙe wa Yaya na Kano ƴa ba, a banza ma tana son nuna isa da ƙafafa bare yanzu tayi nesa da gida babu mai saka mata ido, ai sai abinda ta shuka." Zahara ta faɗa, Naja ma ta kama baki tace "yo Miji ne Allah ya wanke ya bata irin Yaya Mai Kano da indai yana dashi babu mugunta, ai kuwa yanzu zata fantama san ranta."
Gaje ta ɗago kai ta dube su baki a taɓe tace "hmmm ai nizan baku labarin Nana tunda munɗan zauna tare, bata da kirki ga baƙin cikin tsiya ta tsani taga Yaya Mai Kano ya yiwa wani abun arziki, yanzu bagashiba ta ɗauke tata yar ta turo ta kishiya ƙyauye."

Haka suka yi ta caccakar Nana daga baya kuma gulmar ta koma kan Dije duka Husna na zaune tana jinsu, Ramma bata wajen tana murhu dan ita ce da girki.
    
             Ana kiran sallar la'asar Aramma suka fito daga ɗaki, Dije na biye dasu a baya, alwala suka yi, Husna ta tashi taje wajen Baban ta.
"Bari naje masallaci na dawo ko?" Ya faɗa yana duban ta, kai ta ɗaga masa.
       Sun zo zasu fita yaga kayan dattin Husna da Ramma ta wanke ta shanya su akan danga, hakan yayi masa daɗi sosai, dama ɗazu Aramma ke sake faɗa masa halin kirki da nutsuwar Ramma.

Ya ɗanyi gaba da matan gidan ya kira Husna ta zo wajen shi, hannu yasa a aljihu ya ɗakko ƴan ɗari biyar biyar guda biyu ya miƙa mata.
"Ga wannan ki kaiwa sabuwar Maman taki kice kusai sabulu, in sha Allah zan bada sabulun ma a kawo muku sauri ne yasa na manta bamu siya ba."

Husna ta dub Babanta da son ƙarin bayani dan bata gane wace sabuwar Maman taba, murmushi yayi yace "gata can wacce tayi miki wanki, aikin gane ta ko?."
"Eh." ta faɗa tana karɓar Kuɗin, tace "Nagode Baba." Sannan ta juyo cikin gidan.

Duk abin da ke faruwa tsakanin Husna da Baban ta Dije na kallon su, duk da batajin me yake faɗa mata ba amma taga sanda ya bata kuɗi.

        Husna ba munafunci dan bata san wani a abu wai a ɓoye abu ko a aike ka kaƙi bayar wa a gaban mutane ba, zuciyar ta ɗaya ta miƙa wa Ramma kudin tace "Gashi inji Babana yace kuɗin sabulu ne."
Baiwar Allah Ramma da hannu biyu ta karɓi kuɗin kamar shiya bata da kanshi tace "an gode."

Nan fa matan gidan suka fara mata tsiya da shewa.

"A lallai riƙo ya fara rana tab jaka biyar zuwait da marecen nan lallai Ramma yau shar dake."

Suna mata karaɗin tana murmushi Dije tazo kansu ta tsaya tana cunkushe fuska ta cewa Ramma.
"Bani kuɗin da Mai Kano yasa Ma'u ta kawo miki." 

Gaje tayi caraf tace "Ah uwar Mari kuɗin Sabulu ne fa bakiga tayi mata wanki ba?" 
"Ban gani ba nace ban gani ba ƴar me baki a sama, caraf harkin karɓe zancen kamar kena tambaya." 
Zahara da kishi da bakin cikin kuɗin ke cinta arai tace "A'a ke ma Ramma dama ai ba duka zaki riƙe ba, na ɗauka dama bayar wa zakiyi Iya ta cire miki kuɗin sabulun ki sauran a kasawa yan gida."

Ramma bata ce komai ba ta ɗakko kuɗin zata bayar Naja ta rinƙa kifta mata ido ta rage amma, sai bata kula ba ta bawa Dije duka, ta kuwa sa hamnu ta amshe tana faɗin.
"Ah lallai keda saiki riƙe duka jaka biyar ɗin da sunan kuɗin Sabulu, saboda haɗa ma?" Ramma dai bata ce mata komai ba, Dije ta kun ce zanin ta ta ɗakko tsohuwar Jaka guda a cikin Kaja (yar jakar da tsaffi ke daurawa akan siket) ta miƙa wa Ramma tace "gashi kuɗin sabulun harda riba." 

Gaje kamar ta hana Ramma karɓa amma babu dama, dan ita dama basa zaman daɗi da Dije saboda bata bar mata, duk wani iko da mulkin da Dije keyi a gidan bata wa Gaje dan ita ma da ɗuwawon ta take zaune a cikin gidan. Wannan yasa kullum Dije inta zauna saita zagi gaje tace sun yiwa Salisu asiri ita da Uwarta sai abinda suka ce masa. Duk sanda Dije ta faɗi haka Gaje saidai tayi murmushi ta manna mata hauka randa ƴan rigimar ke kanta kuma ta kulata suyi, amma duk da wannan Dije bata iya ɗaukar wani matakin arziki akan gaje saidai zagi da baƙaƙen maganganu.

                  Baiwar Allah Ramma kuwa hannu biyu tasa ta karɓi ɗari biyun harda godiya.

              Magarba na kawo kai kowa ya koma kewayen shi, Ramma taja Husna suka shige wajen su ta nuna mata taburmar data shimfida ta zauna akai, tana kallon ko ina a lungun, bawai dan bata san gidan da mutanen gidan ba Zaman jiran shigowar Baban ta take tun dazu, dan tunda suka fita Sallar la'asar basu dawo gidan ba gashi har ana kiran sallar Magarba yanzu.

        Yayin da Husna ke can zaune tana zaman jiran dawowa Babanta, shi kuwa tuni ya tsufa a Kano dan dama saida yayi sallama da Dije kanya fito daga gidan, suna idar da sallar la'asar ɗin kuwa bai jima a tashar ba ya hau mota ya dawo gida.
Da gangan kuma yayi haka, yaƙi komawa gidan ne saboda yasan muddin Husna zata ga tafiyar shi to sai tayi kuka tace ba zata zauna ba, wanda shi kuma haka ne baya so ya gani, wannan yasa ya sulale yayi tafiyar sa ba tare data sani ba.

Karfe shida a gida ta same shi, bayan ya huta Ni'ima ta dakko wata farar leda mai dan girma ta aje a gaban shi tace "Baba wannan kayan Ma'u ne, ɗazu baku jima da tafiya ba wani yazo a mota neman ta, nace masa kunyi tafiya shi ne yaban wannan yace na bata zakuyi waya dashi."

Mai Kano ya ɗanyi shiru yana tunanin to waye wannan, saida yaji Ni'ima ta sake cewa "Baba na sanshi fa in muka je gidan Alhajin Birget ina ganin shi, wani da Ma'u ke kira Abba."
Sai yanzu ya gane waye "oh Abdussamad ne." Ya faɗi yana duba ledar, kayan ciye ciye ne irin na yara. Ni'ima ya cewa ta ɗauki ledar duka kayan ciki ya zama nata, sai kuma ya ɗora da faɗa mata.
"Husnah bata nan na kaita Gidan'ari ki ɗauka duka ya zama naki." Ni'ima ta ɗauki ledar tana murna, yayin da Nana taji saukar maganar shi kamar yayyafin ruwan sanyi a cikin zuciyar ta.
"In Allah yaso ta tafi ke nan, can zata ƙare rayuwar ta." Nana ta faɗi haka a ƙasan zuciyar ta, tana shewa ranta fari tas.

A fili kuma sai ta murje taci gaba da uzurin dake gaban ta kamar bata san wainar da suke toyawa ba, tana jinshi suna hira da Ni'ima yanata bata labari, Nana tayi musu fakare kamar bata gidan.


*****Har bayan sallar isha'i Husna bataga Baban ta ya shigo ba, nan fa ta fara zare ido zatayi kuka, tuwon da Ramma taje ta sako mata a ƙofar Dije ma kasa ci tayi ta sashi a gaba tana juyawa.

Lirwanu ne ya shigo wajen nashi ya ganta a zaune tana juya tuwo Ramma na gefan ta tana irga sauran alewar da take siyar wa, taga ta nawa ce ta rage.
"Sannu da zuwa." Husna ta faɗa muryar ta na rawa.
"A'a Ma'u kina nan ashe?" 
Ramma tace "ka ganta nan tana zaman jiran shigowar Yaya".
"Wanne yayan kuma? Badai Babanta ba ko? Dan shi yanzu ai ya daɗe da zuwa gida." 
Ai Husna najin haka ta fasa kukan da take ta riƙe wa, duka sai suka tsaya suna kallon ta, kuka take bin hakki harda sheshsheka, tausayin ta ya kama Ramma ta fara lallashin ta amma fir taƙi yin shiru, Zahara ma tasa baki taƙi kula su, Lirwanu da haushin ta ya kule ya daka mata tsawa.

"Ke yimin shiru anan ko nabi ta kanki, ƙatuwa dake zaki samu gaba kina mana kukan iskanci dan ance ubanki ya tafi, to da sakaki zai yi a gaba yana kallo? Naji kin ƙara bude bakin ki anan saina tattaka ki." 
Gum Husna ta rufe bakin ta da hannu amma kukan har yanzu take saidai ba sauti sai gurnanni.

Aramma da shigowar shi gidan ke nan yaji hargowar Lirwanu yace "to shi kuma wancan shida waye yake wannan faɗan?"
Dije ta ce "shida Ma'u mana, ina nan naji kukan ta nayi lungun nasu sai naji wai ashe kukan tafiyar uban take shi ne na fasa shiga na dawo."
"Yanzu Asma'ullahin Lirwanu yake wa wannan tsawar sai kace wata babba?" Aramma yayi maganar yana fasa zaman da zai yi ya fara ƙwala mata kira "Asma'ullahi! Asma'ullahi!!! Ke Indo kiramin ita a wajen Lirwanu, haka kawai yasa yarinya a gaba yana mata hargagi wannan ai saiya sake fitgita ta."

Indo ta tafi kiran Husna Indo na shiga lungun tace "Ma'u kizo inji Aramma." Husna ta miƙe zumbur tana haɗa hanya tabi bayan ta.

"Zo nan kusa dani ki zauna kinji mai sunan manya, yi haƙuri dena kukan haka." Aramma ke lallaɓa Husna lokacin da Indo ta rakota wajen shi.
Kusa da shi ɗin taje ta zauna amma sai kukan da Lirwanu ya hanata yi ɗazu ya kwace mata, ta kife kai a jikin gadon da Aramma ke zaune ta ci gaba dayin kukan, Aramma yayi shiru yana sauraren ta, tausayin ta na tsarga masa zuciya.
Dije kuwa haushin ta ya sake cika ta.
"Yi hakuri bar kukan haka taso muyi magana kinji Asma'ullahi?" Aramma yayi maganar cikin sanyi rai yana ɗago ta ta zauna akan gadon da kyau. 
Da kanshi ya share mata hawaye tana haɗiyar zuciya ya fara mata magana cikin iya zance da kwantar da hankali.
              "Kiyi haƙuri Asma'ullahi, kiyi hakuri kinji? Komai da kike gani a duniyar nan yana da farko da kuma ƙarshe amma fa banda Allah da ikon shi, ke taki jarrabawar ce a haka, kuma in sha Allahu zaki ci ribarta a gaba. Ki kwantar da hankalin ki, Baban ki yaƙi yayi miki sallama ne dan baya son ganin kukan ki, amma zai rinƙa zuwa yana ganin ki akai akai, kuma kinga ai yace yana gama gina muku gida zai zo ya ɗauke ki ku tafi ko? Ko kinfi so ki bishi ku koma Abba ya sake dukan ki?"

Aramma ya jerowa Husna maganganun duk da yasan wasu ba lallai ta gane me yake nufi ba amma yasan dole zata fahimci wasu.
A tunanin Aramma ke nan, Husna tasan sunan ƙaddara da jarrabawa saidai bata san asalin ma'anar su a zahiri ba, sai yau, yanzu da Aramma ya kira halin da take ciki da ƙaddara sai ƙwaƙwalwa da tunanin ta ya hasaso mata kalmar a zahirin ta.
Haka Aramma yayi ta lallaɓa ta da maganganu masu daɗi har tayi shiru.
"Yawwa kullum in kinyi Sallah kina wa Baban ki addu'a ya samu ya gama yi muku aikin gidan ku da wuri, dan yazo ku tafi kinji Asma'ullahi?"
"To." 
Ta amsa wa Aramma tana sake share idanun ta.
Suna haka Salisu yayi sallama ya shigo, dawowarsa ke nan daga kasuwa dan yau Talata yaje cin Kasuwar talatar Kanya.

Saida suka gaisa da Aramma da Dije sannan ya kula da Husna yace "A'a Asma'u yaushe suka zo?" Ya tambaya yana gyara zaman shi.
Aramma ne ya bashi amsa da cewa "ɗazu Abdullahi ya kawo ta nan."
Sai kuam ya kashe duk abinda ya faru ya fada masa da rigimar da take yanzu na tafiyar Baban ta....