SIRRIN ZUCIYA

Chapter nine

by @aysharano22

A baganren Ayaan kam bayan abin ya faru kuncin daya dingayi zaka rantse da Allah itace tayi mashi abinda yayi mata ba shine yayi ba tsabar yanda ranshi ya baci…kumafa shi ba wai bata mashi riga nema yafi bashi haushi ba aah wnn tsinannen hannunta data dora a jikinshi shine har yanzu idan ya tuna abin keyi masa ciwo…like how dare that girl zatakai hannunta jikinshi?…how dare she?…ko class bai iya komawa ba dukda yanada sauran lecture daya bai tsaya bi ta kanta ba ha shiga bolt App dinshi yayi ordering ride don yau Lee ne ya fita da mota.

Dama haka sukeyi duk wanda keda wani important task ko wanda keda uzururruka da yawa zaiyi using motar saiya hada da kai Kiara school da picking dinta yayinda shi kuma dayan sai yayi bolt ya tafi inda zaije abinshi.

In few minutes time ride dinshi ya iso, har cikin makarantar ya shigo ya daukeshi snn suka tafi bayan ya sanar dashi unguwar da zai kaishi.
sun bata lokaci mai dan dama a traffic as usual kafin su kai gidansu…driver na gama parking ya bude motar ya fita bayan yayi mashi transferring kudinshi kai tsaye ya nufi gate dinsu ya bude ya shiga ciki.

Har ya kama hanyar da zai sadashi da inda staircase dinsu yake kawai kmr wanda aka tsikara ya dawo a wani irin fusace ya nufi cikin gym din da waqa ke tashi ta cikin speakers din wurin da karfi har daga waje ma ana jiyoshi…tura glass door din yayi ya shiga wurin fuskar nan a tamke kmr wanda aka aikoma da saqon mutuwa…haka ya shiga taku yana wuce different type of mutane daketa workout dinsu a ciki duk suka bishi da kallo har ya karasa inda Victor ke coaching wata new client dinsu snn ya tsaya hannayenshi zube cikin aljihunshi yace  “Victor could you please help me reduce this volume?, am trying to sleep upstairs”…Victor da baima san yaushe yazo wurin ba sai mgnrshi kawai yaji yayi saurin juyowa yana dubanshi ya dan sakin murmushi yace. “oh Mr Ayaan!, yes I’ll do that right away, sorry for disturbing your sleep”…kai kawai ya gyada mashi yana gani yaje yayi reducing volume din ya dawo, a takaice yace mashi “thanks”,  snn ya juya ya fita duk aka bishi da kallo ganin yanda yayi ignoring kowa dake cikin wurin kawai yayi abinda ya kawoshi ya fice.

Yana haurawa sama direct bedroom dinshi ya nufa straight to bathroom ya cire kayan dake jikinshi tass ya saka cikin laundry basket snn ya dan watsa ruwa ya fito ya nemi amrless shirt da three quater ash color ya saka snn ya koma parlor ya kwanta kan three seater hade da lumshe ido sai sakin tsaki yake one after the other…jin yanda gidan yayi shiru yaji dama bai dawo ba yasan kuma yau tunda Kiara nada Islamiyya bazata tashi daga school ba sai wajen 4 hakan kuma na nufin bazaiga ko daya daga cikinsu ba sai 4 din yayi.

Mikewa yayi ya kunna tv ya dau remote ya shiga neman channel da zai kalla sai tsaki yake yana searching channels, shi sam ba gwanin yin kallo bane da dai Lee ne kam shi maitar kallonshi ma har yayi yawa musamman indian films. Wata bollywood channel yakai sai yaga sunsa wani film na Deepika baidai gane actor din ciki ba, har zai changing channel din sai kuma dai ya bari ya fara kalla, sai karema Deepika din kallo yake yana tuna yanda duk ake zancen ‘yan Bollywood Lee zaiyita kodata yana yabon kyanta da acting dinta  kai har smile dinta Lee cewa yake bai taba ganin macenda smile dinta keda bala’in kyau ba kmr nata…tsaki ya saki ganin shi duk baiga wnn abubuwan da Lee ke kodawa ba gameda ita ko dan bai damu da ’yan bollywood din bane oho, bama iya bollywood ba kadai har South Indian films dinma bai damu dasu ba inshort kallo ma gaba daya is not his thing saidai Lee da Kiara suyita fama don tsaf itama ya koya mata shegen son ’yan bollywood din nan da kallon films dinsu.

Lumshe ido yayi yana tunano rayuwar da yayi a India mai dadi kafin zuwan kaddarar data raboshi da can din…bude idon yayi da sauri jin zuciyarshi na sake tuno mishi wnn batu da ko kusa bason tunashi yake ba. Haka dai yayita juye juye shi kadai yana sakin tsaki duk yaji yayi regretting dawowa gidan ma da yayi in the first place, da ya sani yayi zamanshi a school.

Wnn dalilin yasa ya tsani kadaici don shine kadai abinda ke yawan sashi tunawa da past dinshi da ko a mafarki ba son tunashi yake ba…mikewa yayi jin ya fara jin yunwa ya shiga kitchen ya hadama kanshi coffee don baiji zai iyacin abinci ba ya koma parlor yana sipping a nutse…yana gamawa yayi sallahr la’asar dinshi anan ciki don ba masallachi ke dasu a kusa ba infact kaf unguwar ma babu masallachi tunda ba unguwar musulmai bane sai yayi tafiya mai dan nisa kafin ya samu masjid shiyasa most of the times yafi gane yayi sallahrshi a waje kafin ya dawo gida, shi kuma Lee ba musulmi ba balle su dinga jam’i tare.

Ya idar da sallahr kenan suka shigo gidan Kiara na gaba Lee a bayanta rikeda school bag da lunch bag dinta…tana ganin baban nata ta nufeshi da gudu ta fada jikinshi tana cewa”Mera Papa”(my papa)…rumguneta shima yayi yana cewa”Meri Beti”(my daughter)…dagowa tayi daga jikinshi tayi dage tayi pecking forehead dinshi kmr yanda yake mata kafin tace”i missed you Papa”…dariya yakeyi sosai kmr ba shine keta kunci yana sakin tsaki ba a while ago, yayi cupping face dinta itama ya manna mata peck din kmr yanda tayi mashi yace “missed you too. alot”…dariya itama ta saki tana kallonshi…Lee ya karaso cikin parlorn shima ya ajiye bags dinta dake hannunshi a gefe tareda zubewa kan two seater ya lumshe ido yana cewa “Godd, am so tired and exhausted and hungry”…kallonshi Ayaan yayi jin yanda ya jero abubuwa kawai ya shiga girgiza kai kafin yace  “that’s you ai…always tired and exhausted and hungry at the same time”…harara Lee din ya sakar mashi yace  “wai mema ya dawo dakai gidan nan da wuri?, i thought you said sai 5 zaka dawo yau?”…tabe baki Ayaan yayi gamida dan hade rai sbd tunawa da dalilin dawowan nashi da yayi yace  “well i changed my mind”…dage gira Lee yayi yana kallonshi don yasan definitely akwai wani abu a kasa yace  “anya kuwa na yadda da zancen nan naka?..anya kuwa?”…harara mai kyau Ayaan ya zabga mashi ya maida dubanshi ga Pookie da har snn ke jikinshi ya dagota yana ce mata  “jaawo Pookie, andhar chalo aur kapre badal lo mein aata hoon”(ki shiga ciki ko canza kaya, gani nan zuwa)..gyada mashi kai tayi tana cewa “Theek hai Papa”.

Daga haka ta nufi dakin da gudu yana ce mata “pookie banda gudu”…ba musu tayi slowing down ta dena gudun ya bita da kallo harta shiga dakin snn ya dawo da dubanshi ga Lee da yayi relaxing kan kujera, cikin son ignoring mgnr da yayi mashi dazun yace “should i warm something for you?”..karkata ido Lee yayi yana kallonshi instead ya amsa mashi sai cewa yayi  “tell me Ayaan meya faru yau a school?”…wani kallo Ayaan ke mishi yace”what do you mean meya faru yau a school?..am i a child?”…kai tsaye Lee yace  “i know you fa, nasan tunda ka bani wnn look din dole akwai wani a kasa”…murmushi Ayaan ya saki yana girgiza kai yace “bayeraben banza to ba akwai wani a qasa bane, it’s akwai wata a qasa”..kafada Lee ya daga yana cewa”whatever…dadin abun dai kaima ba bahaushen bane, dan ma dai Juwai….”,   ko karasawa baiyi ba sakamakon katseshi da Ayaan din yayi cikin wani irin karaji yace  “Lee can you plss stop?..what on earth is wrong with you”…ba musu Lee ya gumke baki yana shafa kai, cikin bacin rai sosai Ayaan ya shiga fadin  “why must you always do this to me, huh?…why must you always mention her fucking name idan muna mgn despite kasan banaso?”…dagowa Lee yayi yana kallonshi hadda wani karkata wuya kmr wanda zai fadi abin arziki yace  “ni yanzu yaushe rabon da kaji nace Juwairiyya a gidan nan indai ba sharrin ka ba Ayaan?”.

Murza goshi Ayaan ya shigayi lokaci guda face dinshi yayi jajawur tsabar bacin da ranshi yayi. Cikin daga murya yace “Fuck”.
Saida Lee ya toshe kunne tsabar yanda yayin mgnr, shi kuma kawai ya mike a fusace ya shige kitchen tareda banging kofar ji kake garamm kmr zai ballata…girgiza kai Lee yayi bayan ya shiga kitchen din shi har yanxu bai dena mamakin yanda duk wnn uban son da Ayaan yayima Juwairiyya ya rikide ya dawo kiyayya ba…ba don a gabanshi abun ke faruwa ba wlh bazai taba yadda bane, infact ko a mafarki bazai yadda hakan na iya faruwa ba don shi shaida ne na irin soyayyar da Ayaan yayima Juwairiyya, shi bai taba ganin ma irin wnn son ba tunda yake…ya sota ne fiyeda tunanin mai karatu ya kuma kaunaceta tsakani da Allah dukda tazarar shekaru dake tsakaninsu, qaddara ce kawai ta shiga tsakaninsu amma ko a yanzu idan yayi rantsuwa Ayaan na sonta yasan ba lallai yayi kaffara ba.

Mikewa yayi daga karshe ya bishi kitchen din ya iskeshi a tsaye rikeda kai ko abinda ya kawoshi kitchen din ya kasayi sbd takaicin daya kunsa mashi…a hankali shima Lee ya tsaya kusa dashi bayan ya kama hannunshi ya kwantar da murya yana dubanshi yace  “ok am sorry in Allah ya yadda daga yau bazan sake cewa Juwai…..”, toshe bakin yayi da sauri yana rarraba ido jin ya sake cewa Juwairiyya din.  Sbd takaici Ayaan kasa ce mashi komai yayi kawai ya juya zai fita Lee yai saurin tareshi yana cewa  “a’ah noww…i said am sorry in sha Allah bazan sake kiran sunanta ba, shikenan?”…harara Ayaan ya sakar mashi bayan ya zame hannunshi daga cikin nashi yace  “sai ka nema ma kanka abinda zakaci”…daga haka ya fita a kitchen din Lee ya bishi da kallo yana kunshe dariya.

Ko wnn kadai ya isa dalilinda zaisa ya gane har yanzu Ayaan nason Juwairiyya so mai tsanani ma kuwa.




Rano✨