SIRRIN ZUCIYA

Chapter ten

by @aysharano22

Da kanshi ya bude freezer ya fiddo abinda yakeso ya deba daidai wanda zai ishesu har Ayaan din don yasan shima baici abincin ba, yayi microwaving snn ya zubama kowa nashi ya hadasu gaba daya kan tray dasu ruwa da drinks snn ya fita musu dashi parlor ya ajiye kan center table. Daga nan ya nufi dakin Ayaan din don ya kirasu ganin har snn basu fito ba.

A gidansu Suhana kam daren ranar da kyar bacci ya dauketa tsabar damuwan data sama ranta.  Har yanzu ta kasa mancewa da humiliating dinta da Ayaan yayi haka nanny tayita aikin rarrashi hade da ban baki kafin a samu bacci ya saceta sai kace wata jaririya.

Da safe ringing da wayanta keta yi ne ya tasheta non stop wani na katsewa wani ke sake shiga ita duk anbi an dameta an takura mata baccinda jiya ba samun yinshi tayi da wuri ba…hannu ta miqa ta janyo wayar daga inda yake ajiye ba tareda ta duba ma wanda ke kira ba kawai tayi sliding tareda kaiwa kunnenta.

Muryar Desmond taji daga can bangaren yana cewa  “babe are you there?”…dan tsuke fuska tayi kmr yana ganinta tace “baby am sleeping”.  Shiru taji yayi kmr bazaice komai ba kafin can kuma taji yace  “oh you are sleeping?”…bata rai tayi tana cewa  “yes”  jin kmr tambayar ta rainin hankali ce, bata dai sake cewa komai ba shima yayi shiruu kafin can dai ya numfasa snn yace  “alright baby kici gaba da baccinki…just put your phone on silent kicigaba da baccinki”…shiru tayi kmr tayi sensing wani abu cikin mgnrshi amma dai batace komai ba kawai ta amsa mashi da toh shi kuma bai sake jan mgnr ba sukayi sallama ya katse kiran.

Tana kokarin ajiye wayar message din Lilly ya shigo don haka ta shiga messages dinta don dubawa nan taci karo da kusan 20 messages from different people…na Lilly dake sama ta fara budewa sai ta gansu kusan guda biyar saita karanta na karshen data rubuta mata  “Su, stay away from social media plss, i dont know how this happened”…fita tayi ta duba na Esther itama still ce mata take tayi avoiding social media, nan take taji hankalinta na neman tashi..to me yake faruwa a social median da basaso ta gani?…fita tayi daga messages din ta shiga call logs dinta nan ma tasha mamakin ganin calls rututu har na wanda batama san su waye ba…duk hankalinta taji ya karasa tashi ba abinda takeso kmr ta shiga social media din ko zataga abinda ke faruwa amma kuma tsoro takeji…what if taje ta gano ma kanta abinda zai tashi hankalinta?…qundunbala kawai tayi ta fita daga call logs din direct ta bude Instagram dinta and abu na farko data fara cin karo dashi bayan ta bude App din saida breathe dinta ya dauke na wucin gadi…ta wara idanuwa sosai akan videon tana sake kallonshi da kyau sai taji kmr yanxu abun ke faruwa…video din abinda ya faru tsakaninta da Ayaan ne jiya a cafeteria mutane sai Allah wadai suke da abinda yayi mata a yayinda wasu kuma suke nuna jin dadinsu akai…scrolling ta shigayi aiko duk inda ta shiga videon ne kadai ke trending kowa yana tofa albarkacin bakinshi.

Ta fita daga Instagram ta shiga TikTok sai taga abinda ke faruwa a TikTok din ma yafi muni don mutane da dama cewa suke wai ta dade tana sonshi ne shi kuma bai sonta shine yayi mata haka…wasu kuma sukace dama can saurayinta ne suna soyayya tayi cheating on him da wani shine yayi breaking up da ita, ita kuma taqi hakura tanata bibiyarshi shine yayi mata haka, maganganu dai gasu nan marasa dadi.

Tsabar tashin hankali batasan sanda tayi wurgi da wayar tana fashewa da wani wahalallen kuka ba…kuka takeyi sosai tana sakin ihu da karaji duk a lokaci daya as gaba daya ji take kmr ta hadiyi zuciya ta mutu…wnn wane irin tashin hankali ne?…wane irin calamity ne wnn yake sauka a kanta one after the other…a rikice nanny ta shigo dakin don tun daga dakinta take jiyo sautin kukanta…tana ganin halinda take ciki ta isa wurinta da sassarfa ta zauna nan kusada ita lokaci daya ta jata izuwa jikinta ta rungume tana shafa bayanta tace  “Suhana menene haka?…meya faru?…why are you crying?”…kuka kawai takeyi a jikinta kmr ranta zai fita don ko mgn ma kasawa tayi…ganin halinda take ciki nanny bata sake tambayarta ba tadai cigaba da lallabata tana shafa mata baya har kukan ya danyi sauqi snn ta dagota tana karasa goge mata tears da sukayi saura kan face dinta tace  “now tell me plss…meya faru again?”…lumshe ido Suhana tayi hawaya suka sake wanke mata fuska muryanta na fita a sarqe ta fadama nanny duk abinda ke faruwa a social media, itama kuwa take nata hankalin ya tashi don tasan yanda Suhana ta dauki harkan social media dinta da muhimmanci ko karatu bata daukeshi da muhimmanci haka ba.

Kuka takeyi sosai bayan ta gama bata labarin tace  “yanzu shknn anyi tarnishing reputation dina nanny so suke suyi ruining image dina as an influencer”…shafa bayanta nanny keyi itama duk kmr zatasa kukan tace  “no don’t say that, in sha Allah ba abinda zai samu harkan influencing dinki sai alkhairi kinji?..calm yourself down nothing will happen to you”…girgiza kai kawai takeyi tace  “you need to see what people were saying in the comments section…they were saying all sort of things nanny why would somebody do this to me?”…shafa bayanta har snn nanny keyi tana cewa “shushsh, stop crying pls, you don’t want to develop fever do you?…komai zai wuce, i promise”.

Haka dai nanny tayita rarrashinta da fada mata kalamai masu dadi amma Suhana ta kasa dena kuka…ko tayi kmr zata bari tana tuna me mutane ke cewa a comment section sai taji kmr zata hadiye zuciya ta mutu…suna nan a haka bayan kusan 40 mins sai ga Esther da Lilly sunzo a tare don hankalinsu kasa kwanciya yayi da ganin abinda ke faruwa dole suka taho ganinta.

Matsawa nanny tayi ta basu wuri bayan sun gaisheta suka zauna nan kusada ita ya zama sun sanyata a tsakiya, aikuwa kmr jira take ta rungume duka su biyun tana cigaba da kuka suma sunaji kmr su tayata. Bayan kusan 15 mins Lilly ta dagota tareda kama hannunta tace “cry no more butter everything has been taken care of”…da mamaki take kallonta jin abinda ta fada saidai kafin takai ga fadin abunda ke ranta Esther ma ta kama dayan hand dinta tana dubanta da murmushi kan fuskanta tace “Lilly is right Su, everything is under control now”…da mamakin har yanzun take kallonsu tamkar bata fahimci abinda suka fada ba, ganin haka Lilly tace “ok what happened is that…damu da fans dinki munyi reporting duk accounts da akayi posting wnn video tareda boycotting dinsu, nasan by now ma sun fara taking down video din”…wani irin buda idanuwa Suhana tayi irin she’s really suprised din nan and impressed at the same tace “really?”…wnn karon Esther ce tace  “yes really, kuma kinga tunda munada yawa dole TikTok da Instagram baza suyi ignoring reporting dinmu ba”…lokaci daya kunci da damuwar dake shimfide fuskarta suka ragu, sai kuma ga mamaki, excitement da kuma murmushi sun maye gurbinsu, ta wani lankwasa wuya kmr zata fashe da kuka tace  “you guys really did that for me?”…dafa shoulder dinta Lilly tayi tana cewa  “we’ll do more than that for you Su you are our best friend, so we are together in this”…Lilly na rufe baki Esther tace  “yes forever and ever and ever”.

500 ne kacal a 0013569116 Aisha Ahmad Tijjani Jaiz Bank, sai a turamin evidence ta ***.




Rano✨