28
by @rufaidaumar
ALWASHI
53
Dukkan ƙarfinta ta saka ta ture fuskarsa, don kansa ya saki fuskar. Laila za ta ja baya amma ina, ƙarfin ba ɗaya ba. Kuka kawai ta shiga yi iya ƙarfinta.
"Don girman Allah kar ka min haka."
"Sorry." Ya furta da muryar da ba ta taɓa saninsa da ita ba.
A wannan daren, a wannan lokacin, duk wani yakushi, cizo da zagi irin mahaukacin nan zagin nan, bai sa Areef fasa abin ds yake ba, burinsa kawai ya samu tabbacin abin da yake zargi. Cak kuma ya dakata, kallonta yake yanda take kuka da ihu da kai masa duka da zaginsa. A hankali ya rabu da jikinta ya miƙe maida Pyjamas ɗinsa ya bar ɗakin cikin jin wani irin sarawar kai.
Ya bar Laila duƙunƙune a bargo tana kuka, kukan da sam ba ya fita sakamakon muryata da ta yi masifar shaƙewa. Wannan farar fatar nata ta koma jazur kamar ɗanyen nama. Ban da majinar da ta yi mata kaca-kaca. Baƙin ciki, shi ya mata dirar mikiya a sannan. Ta jima tana kukan nan kanta na masifar sarawa. Ta kalli kanta ta ƙara ƙarfin kukanta, kukan baƙin ciki, koda ace yau bai kai ga keta mata alfarma ba, ai ta sani tunda ya soma gwada mata akuyancin da ya saba, watarana zai iya raba ta da budurcinta. A fili ta firta.
"Allah ya isa tsakanina da kai Areef. Har abada ba zan taɓa yafemaka ba. Kuma wallahi ka shirya yanzu ne zan ɗauki mummunan fansar abin da ka aikata wa zuri'armu. Na maka tsanar da zan iya kashe ka."
Da wani irin kuzari ta miƙe tunawa da ta yi gaba ɗaya kafatanin jikinta ƙamshinsa ke tashi. Kai tsaye wanka ta shiga. Har na tsarki sai da ta yi tunda dole ya wajabta mata. Brush kuwa ta yi har kashi uku tana tofarwa idan ta tuna bakinsu ya haɗu wuri guda. A ƙarshe sai ta ɗora alwala ta fito. Har a lokacin Laila kuka take. Sallah ta yi raka'a biyu daƙyar, tana mai jin a ranta kamar ta aikata wani babban zunubi, hakan yasa a cikin sujjadar ƙarshe ma ta jima tana kuka. Nan kan dardumar ta kwanta tana jan istigfari kai ka ce zaman dadiro suke. Koda dai ita a ganinta ma sam wannan ba aure ba ne tsakaninsu, ita ta ƙayyadewa kanta lokacin barin gidansa, bari na har abada kuwa. Haushin komai a ɗakin take ji, ƙamshin turarukan Areef ke tashi a ko'ina na ɗakin. Ba ta san sadda bacci ya yi awon gaba da ita ba nan saman dardumar.
***
A ɓangaren Areef kuwa, wanka yake amma kuma zuciyarsa cunkushe da tunanuka. Koda ya kammala ya fito, gefen gadonsa ya zauna. Kansa masifar ciwo yake yi. Daƙyar ya iya shan magani. kwanciya ya yi amma baccin ya ƙi zuwa.
'Budurwa ce wannan, kenan Laila ce?'
Ya tambayi kansa, lokaci guda ya runtse idanu. Miƙewa zaune ya yi. Zuwa yanzu dai ba shi da kokwanto a rai cewar Laila Adam Kibiya ya aura ba Sameera Adam ba. Tunaninsa ina Sameera ta ke? Tana raye? Idan tana raye meyasa bai sanya ta a idanu ko sau ɗaya ba? Meyasa bai ji ana zancen ta ba. Kai koda wasa wani a gidan bai mishi maganar su ɗin ƴan biyu ba ne.
'Sau nawa ta bari ku ka haɗu ku ka yi doguwar magana da iyaye ko ƴan uwanta?'
Ya tambayi kansa, tabbas bai wani yi haɗuwar kirki da wani nata ba. Haseenah duk surutunta bai san dalilin da ba ta taɓa yi mishi batun kasancewar su Laila tagwaye ba. Shirunsu na nufin abubuwa da dama, kodai Laila ta aure shi da saninsu domin ta ɗauki fansar abin da ya faru ga Sameera, ko kuma ba su san komai ba, Laila rufe su ta yi.
Wayarsa ya ɗauko zai kira Ma'aruf, sai lokacin ya tuna fa tsakiyar dare ne. Don haka ya maida ya ajiye. Runtsawar kasa yi ya yi, daga ya rufe idanu sai ya tuna da yanayin da ya bar Laila cikin kuka. Miƙewa ya yi da nufin komawa don duba lafiyarta amma ya fasa, ya sani ko me zai ce ba za su fahimci juna ba. Ya sani dai ba ta yi yarintar da za ta gane cewa wani abu bai gudana tsakaninsu ba, bai karɓe mata budurcin da take ta magiya da ihun kar ya raba ta da shi ba. Kokwanton da yake ne, kuma yanzun ya yi watsi da hakan.
Ya riga ya saka a rai cewa ta aure sa ne kawai madadin ƴar uwarta, burinta bai wuce ɗaukar fansa ba. Don haka, koda ya je, baƙaƙen maganganun da suka yi saura ba ta furta garesa ba a ɗazun, su ne za ta faɗi. Tunanin hakan ya sa ya fasa fitar, ganin baccin ya ƙi zuwa ga ciwon kai ya ƙi sauka ya sa dole ya miƙe ya sha magani. Alwala ya ɗauro ya yi nafila ya yi addu'a. Bai kai ga rufe addu'o'in nashi ba ma bacci ya soma fisgarsa. Hakan yasa koda ya koma gadonsa, bacci mai nauyi ya ɗauke shi.
***
Washegari sun tashi ran kowannensu babu daɗi. Ga Laila, koda ta yi wanka ta gyara gadon. Hawayenta ba su daina zuba ba, ƙarshe fitowa ta yi ta koma ɗayan ɗakin saboda ji ta yi komai na ɗakin ya ƙi rabuwa da ƙamshin Areef, ga kuma uwa uba ba ta son tana tuna wai ya taɓa mata jiki ma. Don haka koda Lubna ta zo mata da abin kari daga wurin Hajja Zayha, karɓa kawai ta ajiye da godiya. Lubna dai ta dinga ƙaremata kallo, tana kula da yanda idanunta suka kumbura. Da kuma yanda take murmushin da bai kai zuci ba.
"Anti ni wallahi sai naga kamar na sanki."
Laila ta dube ta.
"Ko? Ƙila za ki iya sani na ai tunda a shekarun baya na shishshiga gidanku ɓangaren Mami."
Lubna ta ɗan yi shiru, can ta dube ta ido a ɗan waje.
"Ki na kitso?"
Ta yi tambayar cike da shakku. Gani take kamar ita kamar ba ita ba. Fuskar Laila a sake ta na kallonta cikin ido ta gyaɗa kai kawai.
Lubna ai sai ta ruɗe, ba ta ƙara maganar ba kawai ta yi mata sallama ta fice. Laila ta bi ta da harara sannan ta kawar da kai ta ja tsaki. Wayarta ta ɗauka ta shiga dannawa, tun safe suka yi waya da Momi Fannah da Gwaggo Samha. Mama kuwa sai text ta yi mata a waya. Kiran Zakiyya ya shigo daidai lokacin. Ta miƙe ta shige ɗakinta na biyu ta rufe da muƙulli.
"Laila, ina fatan komai lafiya? Bai shigo ba ko?"
Zakiyya ta yi tambayar jin kalar muryar da ta amsa mata sallama da ita. Duk yanda ta so ta danne damuwarta hakan ya faskara. Kawai sai ta saki kuka.
"Zakiyya, Areef ya cuce ni."
"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Kar ki ce min ya kusanceki Laila? Garin yaya?"
Laila ta share hawayenta.
"Bai kai ga yin komai ba Zakiyya, ban kuma sani ba ko zagin da na dinga ɗura masa da magiyar kar ya raba ni da budurcina ne ya sa ya fasa oho. Amma babu abinda bai gani ba, babu inda hannunsa bai kai ba. Zakiyya ƙyanƙyamin komai nawa nake yi. Anya zan iya?"
"Laila, bai yi komai ba? Me hakan ke nufi? Kodai ya gano ba ke ce Sameera ba?"
Laila ta ji ƙirjinta ya ɗan ba da dam, ita wannan tunanin ma bai zo kanta ba. Shirunta ya sa Zakiyya ɗora zancen.
"Laila maganar kenan! Areef ga dukkan alamu ya gane wani abu. Amma kin gane, kar ki yi saurin ce mishi komai. Mu zuba ido mu ji me zai ce maki. Koda ace ta gano ɗin, ai bakin alƙalami ya riga da ya bushe tunda kin riga kin zama matarsa. Ina fatan dai a kalar zagin da kika yi masa ba ki yi wani furuci mai kama da na fallasa sirrinmu ba ko?"
Laila ta girgiza kai tana cije leɓɓanta na ƙasa cike da sanyin jiki ta amsa.
"Ko ɗaya, ban yi ba. Zagin uwa da uba dai ya sha. Ina da yaƙinin ba zai ƙara kwatanta abin da ya yi min ba. Ba kuma zan ƙara yin saken da hakan za ta faru ba. Sannan koda ya gano ɗin kamar yanda kika ce ai bakin alƙalami ya riga da ya bushe, sannan muna da Plan B. Areef ɗan akuya ne Zakiyya. Ina faɗamaki ba zai taɓa daina neman mata ba. Tunda ya cire kunya ya murje ya neme ni a karo na biyu duk da aure muka yi, a zaton kuma Sameera ce. Toh ki saka a rai Sameera ce madadina, yanzu sai ya mance cin zarafin da ya yi mata kawai ya nemi ganinta a shimfiɗa? Zakiyya sai na ruguza rayuwarsa zan samu nutsuwa."
Zakiyya ta numfasa wanda har ta cikin wayar Laila ta ji.
"Da ciwo Laila, ki yi haƙuri. Na faɗamaki muddin muna son yin galaba a kansa, sai kin yi haƙuri an bi komai sannu. Ki rage zafin ƙiyayyar ko yaya, a hankali kika shige shi sai mu san duk wasu take-takensa. Amma kika ja baya da shi sosai, to ba za ki iya aiwatar da komai ba. Sannan fa ki shirya don na sani a kowane lokaci iyayensa da ƴan uwansa zasu ɗago ki a matsayin Sameera."
Laila ta yi murmushi, karo na farko da ta murmusa tun daga zuciyarta a kwanakin nan. Ta yarda babu abin da ke faranta mata rai yanzu face ta ga wani abu da zai sosa zuƙatan bayin Allahn nan. Nan ta labartawa Zakiyya yanda suka yi da Lubna ɗiyar Hajja Zayha yanzun. Ta ƙara da faɗin.
"Na sani tana can tana yamaɗi..."
Murmushi Laila ta faɗaɗa jin wani sabon bugun ƙofa daga falon.
"Au, kin ji ma ana ƙara knocking, bari na je, ƙila saƙon ne ya isa."
Dariya Zakiyya ta yi ta ɗora da faɗin "Ki dai kula."
Daga haka suka yi sallama. Ta fita a nutse ta ƙarasa falon ta buɗe. Afrah ce da wata cousin ɗinsu, hannuwansu ɗauke da kwando sai ɗaya riƙe da ƙaton filas na ruwan zafi. Idanu waje Afrah ke dubanta har da sakin kwandon da ta riƙo, don ma babu wani tangaran da a lokacin zai yi nasa wajen.
"Sameera!"
Ita dai abokiyar rakiyar ta tsaya tana kallon ikon Allah don ba ta san me ya razana Afrah haka ba. Wani ƙasaitaccen murmushi Laila ta jefa wa Afrah gami da ɗan ɗaga gira.
"Laila, sunana na yanka Laila not Sameera. Sameera kawai suna ne na laƙani."
Kawai sai Afrah ta juya da sauri. Ita kuwa Laila ta dubi abokiyar rakiyarta har a sannan tana murmusawa.
"Shigo mana." Ta ba ta wuri, ta girgiza kai ta ce.
"No bari na bi bayanta. Ga shi Mami ta ce a kawo."
"Ai tuni mun karya, Hajja ta aikomana da abin kari. Ki mayar kawai."
Daga haka ta rufe ƙofar. Cikin rashin fahimtar komai budurwar ta haɗa da kwandon nan ta bi bayna Afrah zuciyarta cike da tunani kala-kala.
***
Mami ta miƙe tsaye tana mai fiddo idanu.
"Me kika ce?!"
Afrah da rawar baki ta ce.
"Sameera ce matar Yaya Areef. Sameera mai yi mana kitso a can baya."
Mardiyya da Maryama suka dubi juna gami da riƙe kai. Sun gani, tun jiya sun ga komai a buɗar kai, Afrah ce dama ba ta je ba don sun fita. Benazir kuwa duk irin waɗannan abubuwan ba su wani dame ta ba. Hankalinsu ya tashi da suka fahimci wa Areef ya aura, sai dai sun ja baki sun yi shiru ba su son Mami ta ji komai daga bakinsu, tunaninsu su fara neman Areef kafin a tunkari Mami da Abba, amma kuma dama sun san ba zai je ko'ina ba tunda ta riga ta shigo cikin dangi.
"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Kai ku kawo ruwa! Salma! Salma!"
Hankalinsu ya kai ga abin da ke faruwa, ashe tsananin tashin hankali ne ya sa Mami kifewa a tsakar falon sumammiya.
©Rufaida Umar