Chapter 11
by @reza12
MATAR MAZA 11
(Life story)
Haka Hajiya ta dage da faɗin maganganu masu zafi haɗi da nasiha, har tana kuka, ita dai burinta ta zauna a gidan mijinta ta daina jawo mata magana irin wannan. Sosai taji zafin wannan faɗan da Hajiya ta yi mata, har sai da hakan ya nuna a fuskar ta, ta haɗe rai sosai duk haushin kanta ya kamata. Haka ta kamo hannun Sadiya har suka fito taskar gida. Daidai lokacin sai ga Jidda ta shigo gidan da sallama. Suka yi banza da ita, sai ta kallesu a takaice, ganin Sadiya na kuka Azima kuma ta haɗe rai sai cewa tayi "An dai ji kunya, ana kuka saboda saurayi yace baya so". Ta faɗa ba tare da ta nuna ta san da tsayuwar su ba. Har ta kusa shiga ɗakin Ammy taji an jawo wuyan rigarta ta baya, an bizgota da ƙarfi. Ta ce "Dawa kike yi dan uwarki?" Ta faɗa da ƙarfi wanda yasa Ammy fitowa daga cikin ɗakin idonta akan Azima tana shirin marin Jidda. Ganin fitowar uwar ta ta yasa Jidda faɗin "Ki sakar min riga tunda banyi dake ba". Ta faɗa a tsiwace. Sai ta turata gaba ta na cewa "Ashe ke ƙaramar mara kunya ce, ai da kin faɗi da wanda kike ki sha mamaki dan uwarki". Ta ƙaraso gurin Sadiya suka kama hanya. Har sun kusa fita suka tsinkayo muryar Ammy na faɗin "Shegu gaiyar tsiya a cikin gida, ai da kin taɓa ta Kinga abun da zai faru, kuma uwarki kika zaga gata cen tana jinki mara kunya wacce tafi ƙarfin uwarta". Sosai suka ji abun da ta faɗa, amma saboda tasan tana komawa maganar ce zata girma, kuma a halin da ta baro Hajiya, sai kawai ta danne abun da take ji har suka shiga motar da tazo da ita suka ƙara gaba. Basu tsaya a ko ina ba sai gidan Azima ɗin. Nan ta dinga lallashinta akan tayi haƙuri ta manta da Mansur tunda uwarsa bata to, har dai ta ɗanyi shiru kafin suka fara yin wata hirar ta da ban. Hakan yasa Sadiya take rokonta akan kar ta kai mamar Mansur ƙarar da tace ko dan saboda ita, tunda bata sani ba ko zuwa gaba zasu shirya kar azo aji kunya. Azima ta ce "Kina dai ji tace ko bayan ranta bata yarda ba, dan Allah ki cire wannan yaron gaba ɗaya daga ranki please". Ta fashe da kuka tana fadawa jikinta domin ji take kamar ba zata iya rayuwa babu shi ba, ta saba da shi, bata taɓa yin saurayi ba sai shi, kuma yana tausayinta sosai. Sai da suka zo kwanciya ta bata labarin Abraham da kuɗin da ya bata, ita kanta Sadiya ta tsorata jin yawan kuɗaɗen, musamman ma da ta ji wai ba musulmi bane. Ta ce "Anty kin fa ce ba musulmi bane, dan Allah ki rabu da shi, yaya zakiyi da Hajiya idan tasan baki da aure ko kuma tasan zaki auri wanda ba Musulmi ba"? "Nifa ban ce miki zan aure shi ba, kawai dai ya burge ni ne, kuma ni ban ma san yaya zan yi ba wallahi, kaina duk ya cika". "Kawai ki mayar masa da kudinsa kice ya fita a sabgar ki, kuma kice masa ke matar aure ce please". Sadiya ta faɗa iya gaskiyar ta. "Matar aure kuma? To yaushe nayi auran, nayi karya kenan nufinki?" Azima ta faɗa tana kanllonta. "To ƙarya kuma yau kika fara yi, ina ce ko yanzu ma kan ƙaryar kike, nifa Anty abubuwan nan naki sun fara bani tsoro, duk lokacin da Hajiya ta gano fa daga ni har ke muna cikin matsala, dan Allah ki rabu da wannan mutumin dan girman Allah domin wallahi ba alkairi bane a rayuwar ki". Azima ta ce "Babu yadda za'ayi Hajiya ta sani, sai dai ko ke zaki faɗa mata, kuma da kike cewa abubuwa na sun fara baki tsoro idan sun so ma su kashe ki, bana son iskanci, uwar mai nayi, ko aure haramun ne, kema kenan kina min irin kallon da sauran mutane suke min ko? To na gode Sadiya, Allah ya saka da irin wannan fahimtar". Ta faɗa tana yin abun tausayi ta juya mata baya. Da sauri kuwa ta fara girgiza kai alamar ba haka take nufi ba, ta rungume yayar tata ta baya tana ta kuka akan ita fa ba abun da take nufi ba kenan ta tashi ta fahimce ta dan Allah.
Tun daga lokacin Azima bata sake zuwa gida ba, a cewar ta ta zauna a gidan mijinta kaman yadda Hajiya ta nema. Kuma hakan yayiwa Hajiya dad'i domin bata son yawan zuwa gidan da take yi. Izuwa lokacin Mansur saurayinta bai sake nemanta ba, Bilal kuwa yaƙi hakura, ita kuma ta kafe akan bafa zata auri mai ciwon hiv ba, duk da kuwa ta yarda da cewar bashi da ita kaman yadda ya kawo mata shedar asibiti, amma ita tsoron aure a gidan sarauta kawai take yi. Haka shima Mansur saurayin Sadiya har yau bai sake kira ko zuwa kofar gidan ba kaman yadda mamarsa ta bashi umarni, itama kuma Sadiya ɗin haka Azima ta hana ta ko neman sa a waya duk yadda ta shiga damuwa kuwa. Bangaren Abraham kuwa tun bata bashi lokaci har dai ta saki jiki da shi, bashi da rowa, bashi da kyashi, kwai dai matsalar sa ba musulmi bane. A daidai wannan lokacin ta fara tunanin auransa amma idan ya yarda zai musulunta, kaga kenan daga haka tayi maganin matsalar ta, bata da fargabar komai, zai zama ta yi wani auran kaman dai yadda ake mata kallon mai aure. Sosai take ta tunanin hakan har dai ta amince da hakan a ranta, to amma ta yaya?.
Yau juma'a kuma sunyi da Narma akan zata je Campanin su yau, hakan yasa ta shirya sosai, ta ɗau wanka cikin shigar da zaka rantse da Allah ba yar musulma bace, kan nan nata ba ko dankwali bare hulla, ta yi shigar skeet da riga matsatstsu. Duk gurin da ta wuce a cikin gurin sai an bita da kallo har ta iso gurin da zata hau linta. Ta shiga tana jin san ganin sa haka kawai. Koda ta isa ofishin Namra sai ta ɗan tsaya na minti ɗaya kafin ta shiga. Ko zama batayi ba ya turo kofar ya shigo yana binta da wani irin kallon da ya bata tsoro kamar wanda aka turo shi. Ya tsaya daga gurin yana gyraa tsayuwar sa. Ita kuma ta samu guri ta zauna tana kallon Namra da ta ɗan haɗe rai. Namra ta ce "Good morning sir". Yayi Kamar bai ji ta ba. Ta dawo da kanllonta ga Azima da itama take kallonta. Ya ce "Good morning beautiful". Ya faɗa yana karasowa ya zauna. Sosai ta tafi da imaninsa. Ya kalli Namra ya ce "Bamu minti goma". Ta mike tana hararar su ta gefen ido. Tana fita ya sake matsowa kamar zai shiga jikinta ya ce "Kinyi kyau, kuma naji daɗin ganinki, Allah yasa dai kin zo ne ki sanar sani cewar kin shirya aure na?" Ta kawar da kai gefe bata ce komai ba, domin dai bata jin sakewa daga ita sai shi a haka. Ya sake faɗin "I'm serious zan aure ki, saboda ina sonki da gaskiya". Ta ce "Da gaskiya fa kace?" Ya gyaɗa kai. Ta ce "Idan nace ka musulunta zaka iya?" Ya danyi dariya kaɗan kumatunsa na lotsawa. Ya ce "Why not, mamata ma Musulma ce, muddin zaki yarda ki aure ni zan musulunta saboda ke". Ta sake cewa "Da gaske fa nake?" Shima ya tabbatar mata da gaske yake. Farko tayi tunanin wasa yake har sai da taga Shine ma da kansa yake azalzalarta. Sun daɗe suna hira da shi, a ranta ta gama yarda da shi, sai dai bata jin sonsa, amma idan ta tuno da Hajiya sai kawai ta sa a ranta zata aure shi ko dan kaucewa matsalar Hajiya, kuma gashi yana da kuɗi ba laifi. Sadiya ta fara faɗawa abun da take shirin yi, ai kuwa ta ce ita dai bata goyan baya, mai yasa ga musulmai nan ba zata zaɓa sai wannan, ita dai wallahi babu ruwanta, kuma ko ta fashe kar ta saka sunanta, kuma tana bata shawara akan ta daina irin wannan auran da babu wanda ya sani, amma Azima tayi banza da Ita.
Ranar Lahadi suka tafi gurin gyaran kai ita da Namra. A hanya take bata labarin cewa Abraham nada wata budurwa da suke rayuwa kamar mata da muji, kuma yarinyar yar balaja'u ce ta gaske, dan haka ta fita a harkarsa muddin tana son zaman lafiya domin yarinyar bata da hankali, kuma ta samu labarin yana dan tsalle-tsalle. Azima ta cika da mamaki, Sannan bata fahimci kalmar tsalle-tsalle ba, hankalinta sai yafi tafiya akan labarin budurwa tasa. Ta ce "To mai zata min, duka ko mai?" Ta faɗa da mamaki. "No kawai dai... "Kawai dai me?" Sai tayi shiru tana jin haushin kanta mai ma yasa ta faɗa mata, ai da ta barta har lokacin da zata samu labarinta. Tuni ranta ya ɓaci, domin tana da kishi sosai da sosai, haka kawai taji ranta ya ɓaci da batun yarinyar duk da bata santa ba. A haka aka gama musu komai suka fito da nufin tafiya. Kafin su kai ga shiga motar wayar azima ta fara ƙara. Ta daga tayi magana ta mayar da ita jaka. Ta ce "Ina so ki bani labarin ita yarinyar da kika ce suna tare?". Namra ta ja tsaki ciki-ciki domin dai har ga Allah bata son Azima da Abraham domin itama sansa take, sannan ta san halin yarinyar da yake tare da ita ɗin, tafi Azima iya iskanci yar tijara ce da gaske domin kaf family dinsu haka suke. Ko a lokacin da ta fara aiki a Campanin sai da tai mata gargaɗi mai lasisi akan kar ta sake wani abu ya shiga tsakaninsu. Ta ce "Ki bari gobe zan zo gida na same ki zan nuna miki harda hotonta da kuma komai nata". Azima tayi shiru tana tunanin anya kuwa zata iya auran irinsa wanda ya kula wata a waje. Kawai take ta yanke ta fasa auran, ba zata iya auran wanda yake kula wata ba, gara ta cigaba da zama har Allah ya kawo mata wani, ko kuma ta zaƙulo ɗaya daga cikin masu zuwa domin dai ya dace tayi aure a ɓoye kafin asirinta ya tonu. Da wannan tunanin ta iso gida. Tayi wanka ta ɗauki laptop ta kuna ta buɗe WhatsApp. Sosai take ta hira da ƙawaye harda wasu daga cikin zawarawan nata, sannan ko sau daya bata daina tunanin abun da zatyi ba. Har tayi niyyar kashe laptop ɗin sai taga sako da wata sabuwar number. Yana yin sakon yasa da sauri ta buɗe domin daga farkon rubutun ya nuna akwai matsala domin zagi ne a farkon hafin. Tana budewa sai ga sakon murya ya biyo baya na wajan minti arba'in kamar wani wa'azi. A fili ta karanta rubutun wanda zagi ne da kuma sharadi. Ai da sauri ta buɗe voice ɗin tana ji. Tana ji tana kokarin gane mai wannan muryar, sai dai har ta gama bata gane ba, bugu da ƙari kuma tana mamakin ƙarfin halin mai maganar domin harda kama sunanta alamun dai ta santa. Haka ta kwanta ba tare da ta bada amsa ba.
Washegari Litinin tana da tafiya Maroco hakan yasa ta kira Sadiya domin ta kula mata da gidan har ta dawo. Ta buɗe murfin motar kenan zata shiga taji ana zage-zage da mai gadi akan ya buɗe kofar yaƙi. Hakan yasa ta karaso tace ta buɗe. Ana budewa kuwa sai ga uwa da ƴa wanda ba sabbin fuska bane a gurinta, ta sansu sunanta farin sani kuwa. Budurwar ce ta fara fadin "Na samu labarin wai iskancin ki ya biyo ta kan saurayi na Abraham ko? To tun muna mu biyu ki fita a harkarsa, kin san wacece ni, kaman yadda nima na san wacece ke, dan haka na fara tura miki sako baki ce komai ba, shi yasa nazo da kaina domin zuwa da kai ya ɗara turo saƙo". Uwar ta ɗora da "Muddin kina son zaman lafiya a rayuwar ki to ki fita daga sabgar sa, domin Abraham na Mera ne ita ɗaya". Azima ta ce "Wai a kan wa koke magana ne duk ban ma sani ba?" Ta faɗa cike da rainin hankali. Ta ce "Abraham nake nufi wanda kika ce kina so tsabar rashin aji". "Okay mijinki ne shi ko kuma me?" "Saurayi nane, shi nake burin na aura, Sannan ina ma ruwanki ma ko menene?" Tayi murmushi ta ce "To Mera kaman yadda yake sauranki nima haka yake nawa, kuma aurena ya ce zai yi, kuma ba wacce ta isa ta hana wallahi". Ta faɗa tana sauya musu fuska ganin da gaske suke, dama ta kwana biyu bata yi rigima ba, sai gata har cikin gida.
Sosai ta sansu, da a ƙasan unguwar su suke, su ɗin yarabawa ne Musulmai irin wanda basu wani dauki addini da muhimmanci ba, babu wanda bai san rashin albarkar yan gidan nasu ba, wanda ko lokacin tana ƙarama sun sha yin rikici da yayyan Mera ɗin wanda duk sunyi aure, ko da girman nan nata ma sunyi da wasu daga cikin yan gidan, a baya sun sha haduwa suyi mata duka, ita kuma ta kama ɗaya daga cikinsu ta rama a kansu.
Mera ta saki wata dariya mai sauti jin abun da ta ce, dama ta san za'ayi haka da ita, shi yasa ta shirya saboda koya mata hankali. Sosai suka yi chachar baki dasu suna cewa idan bata fita a sabgarsa ba zasu sa a batar da ita. Ita kuma tana sake jaddada musu wallahi sai ta aure shi ko dan abada su. Ihunsu ne ya fito da Sadiya tana mamakin ganin su Mera a gidan. Sosai ran Azima ya ɓaci, a ranta tana jin ai ita irin wannan auran take sonyi, tuni ta ji har cikin ranta zata aure shi domin taga karshen iskancin su, tafiya Maroco ɗin ma tuni ta fasa shi. Ta ɗauki waya ta faɗa masa cewar ya shirya auranta a cikin sati ɗaya? Kuma zai musulunta a lokacin?" Da sauri ya amince yana tabbatar mata da cewar ya amince muddin haka take so. Ko Namra bata san da batun auran ba, hatta Sadiya ɓoye mata tayi, ba'a batun Kuma Hajiya ko yan gidansu, kawai dai tasa a ranta zata yi aure ne ba saboda da Allah ba, sai saboda nuna musu cewar taci uwarsu iya rigima, zata aure shi koda ba zata yarda komai ya shiga tsakaninsu ba. Ita kaɗai take ta shirinta a bangaren ta, har suka je gurin da aka bashi kalmar shahada, da suna Ibrahim. Kuma har lokacin babu rana da ta wuce basuyi zage-zage da su Mera ba, sai dai wannan karan batayi shirmen faɗa musu ranar da za'a ɗaura auran ba, amma dai ta faɗa musu dole sai ta aure shi ko zasu mutu. Ana gobe za'a ɗaura auran suka zauna domin tsara yadda komai zai tafi musu daidai, ta faɗa masa cewar a gidan ta zata zauna, sannan bayan sunyi aure zai daina alaƙa da duk wata mace, saboda yanzu ya dawo Musulmi kuma yayi aure. Sosai duk abun da tace yake amincewa yace ya yarda, komai dai wanda har abun yana bata mamakin yadda baya Kawo nasa sharadin, kaman dai akwai abu a ransa saboda shi bai ce komai ba fa.
Abun da Azima bata sani ba shine... Kaman yadda tayi auran manufa akansa to haka shima yayi auran sha'awa da ita, irin mai gigita zuciyar mutum ɗin nan, domin tun da yake bai taɓa ganin macen da yaji sha'awar ta kamar ita ba, farko yaso ya biyo mata ta bayan gida ne yadda zai more ta, amma aka tabbatar masa da cewar bata yarda da haka, sai dai aure da take yi da masu kuɗi, shi yasa yazo mata a haka, a duk lokacin da ya ganta sai jikinsa ya amsa, mafarki kuwa ya sha yi da ita a koda yaushe, har fasalta yadda jikinta yake yi da yadda zai sameta, hakan yasa ya ke jin zai iya komai domin ya ɗanɗani kogin zubar ta ko ta yaya ne domin baya gani ya gyale ko yar waye, ba ƙaramin ƙoƙari ya ke yi ba da ya danne abun da yake ji kanta. Ai kuwa rana bata karya, sai dai uwar ɗiya ta kwana tana kukan kunya idan bata shirya ba. A daidai ranar da suka shirya kuwa aka daura musu aure cike da amincewar junansu ba tare da kowa nasu a gurin ba, azima ta zama matar Abraham (Ibrahim), Abraham ya zama mijin Azima ba tare da sanin kowa nata da nasa ba. Aure mai cike da tarin matsalolin da zasu haifar da abun da rai da zuciya basu taɓa hasasowa ba...📝
Shin mai zai biyo bayan wannan auran da yafi Kowane rikici? Ga bangaren Mera, kuna ganin zata hakura. Kar ku manta wannan labari ne life story ya sha bambam da sauran, shi yasa zaki lura da irin tafiyar labarin ma da ban yake.
Shering ɗin ku, da comments dinku shi zai ƙara min ƙwarin guiwa wajen kawo muku labarin akan lokaci.