BARRISTER SUHAIL

46

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️-----46 

Zeenah taji haushin yadda ya fita bai kula taba 

Kitchen ta koma ta iske Jummai tana wanke-wanke da kunya ta tambaƴeta ina abincin data kawo mata hakan yasa ta fara dube duben a Kitchen din cikin Sa'a ta gansa a gefe guda ta dauka ta fara ci tamkar wanda ta kwana biyu bata ci komai ba 

jummai ko sai kallon ta take mutun min da yace baya cin local food, yunwa dai bata da girman kai 

murmushi ya subuce mata zeenah ta harare ta ta cigaba da cin abincin ta 

sai da taci biye da rabin abincin ta fito ta koma dakin mami 

suhail na fita daga part din mami ya koma part din sa 

wanka yayi ya shirya cikin wani black yard yayi masa kya sossai ya dauki key motar ba ya fita bai tsaya ko ina ba sai kofar gidan malan 


already ya gaya ma iman zaizo ya dauke su je gidan Sameer hakan yasa ta kasance cikin shiri 

tana zaune a dakin Ammi kiran sa shigo wayar ta sunan my councel ya bayyana kan screen din sabuwar wayar ta 

tashi tayi daga kusa da Ammi ta koma ciki Ammi tayi murmushi ta bita da kallo 

koda ta daga ya sheda mata yana kofar gida well ironing hijab milk colour ta dora kan doguwar rigar atamfar jiki ta 

Hijabin yayi matukar yi mata kyau ya haska fair complexion din fatar ta jakar ta dauko ta fito 

Ammi ta ce"Iman Suhail har yazo ne"

"Eh,Ammi yana kofar gida"

"gashi zaki tafi kuma malam bai dawo ba"

kan ta rufe baki suka ji sallamar malan yana kiran Iman fitowa tayi ta ce"malan gani"

"kije waje mijin ki na jiranki"

Sallama sukayi da Ammi.
Ta juya ta fita
A kofar gida ta sami Suhail ya jingina da motar sa
Black yard ɗin da ya saka ya ƙara fito da ƙyawun sa da kwarjinin sa
Tun daga lokacin da ya hango ta fitowa idanunsa suka bi ta
Milk colour hijab ɗin data saka ya yi matuƙar karɓar fatar ta.
Kallon ta ya ɗan yi na wasu sakanni kafin ya ce"you look so cute my Little Iman"

a yadda ya kirata da Little iman sai zuciyar ta buga for the first taji dadin sunan fiye da ko yaushe 

da ka shi ya buɗe mata front seat ta shiga

har suka fara tafiya babu wanda yayi magana dai kamshin turaren iman daya hadu da sanyi Ac ya bada wani vibe na daban 

hanyar gidan Sameer ya nufa kamar yadda yayi masa Alkawari zai kawo iman 

tafiyar mintuna talatin ta kaisu kofar gidan

bayan yayi  parking ya kira Sameer ya sheda masa da zuwan sa ba ɓata lokaci ya buɗe masa gate Nihal na biye dashi a baya 

idanunta na sauka kan suhail ta rugo da gudu ta rugume sa 

"daddy"

daukar ta yayi yana mata wasa 

iman ta kafe su da ido tausayin Suhail ya kamata ta ganin wani irin so da kauna yara da Suhail ke dashi  

Iman ta lura yadda fuskar Suhail ta canza gaba ɗaya yayin da yake tare da yara
Kamar wani sabon Suhail ne ta gani a gabanta

a hankali ta shafa cikin ta tare da yin masu addu'a suma Allah ya basu yara na gari masu albarka 

suhail ya kalli nihal ya ce"i Miss You my Princess"

murmushi tayi wanda ya Bayyanar da dimple din kan fuskar ta ce"miss you too my dad"

Sameer ya ce"nifa na lura kamar  nihal ta fika son mu"

murmushi Suhail yayi ya ce"kaga laifin ta"

Maryam matar Sameer ta fito ta musu iso cikin falon cike da murnar ganin iman 

kullum tana w
a Suhail mita akan ya kawo ta su gaisa sai yau Allah yayi 

kan kujera suka zauna iman ta fara gaishe su Maryam tayi murmushi ta ce"Iman ina fatan dai Yanzu kin daina tsoron Allura"

murmushi tayi sai lokacin ta tuna Abinda ya faru ranar da bata da lafiya 

ƙasa tayi da kanra tana murmushi Suhail ya kalleta har lokacin Nihal na zaune a jikin sa

sameer da Suhail suka soma hirar su 

Maryam ta kama hannun iman zuwa ciki dan su basu damar yin hirar su 

sameer ya ce"2 star man ina kuma Amarya zeenah ai na dauka tare zaku zo"

murmushi Suhail yayi ya ce"tana gidan Mami"

a yadda yayi Maganar Sameer ya lura da damuwar dake kan fuskar Suhail

"Suhail lafiya kuwa"

Wani nannauyan ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ɗaga kai ya kalli Sameer

"sameer i'm confused,yadda zeenah gaba daya ta chanza ba Zeenah da ka sani bace wanda mukayi University the girl who Always begged for my love,yanzu ta chanza tana fito da wasu sabbin habit wanda ban santa dasu ba,Abinda ke bani haushi da ita she don't even know how cook"

Sameer, ban damu da rashin iya girkin taba Amma girman kai da rashin girmama shi yafi bani takaici 

Sameer ya yi shiru na wasu sakanni yana kallon abokin nasa 
Tun shekaru da dama da suka yi tare yasan Suhail ba mutun bane mai korafi musamman ma akan mace

sameer ya ce"to daga ina matsalar take"

Wallahi Sameer ni kaina ban san inda matsalar take ba

“Na yi ƙoƙarin fahimtar ta na yi haƙuri, amma kullum sabon hali take fito dashi"

sameer ya ce"ka cigaba da hakuri da kuma kwatanta Adalci tsakani su"

a daki kuwa Maryam ce da Iman suna tasu hirar 

gefe guda kuma nihal nayin nata wasa 

Maryam ta ce"iman kinga yadda kika kara kyau"

murmushi kawai tayi 

Maryam ta cigaba da magana "ki godewa Allah daya zaba maki Suhail a matsayin miji,domin ba kowa Allah ke wa Wannan ni'imar ba Suhail mutun ne mai tsaron Allah tunda suke zuwa wajena da sameer ban taba jin wani bacin saba 

Abu daya na sani ga Suhail shine yana matukar san yara 

wannan yasa kika ga Nihal na matukar sansa 

“Kuma duk lokacin da Nihal take tare da shi, sai ya ce min wata rana zai so ya ga nasa yaran haka"
Maganar ta sa zuciyar Iman bugawa da ƙarfi
A hankali hannunta ya sauka kan cikinta

ba iya Suhail kadai ya damu akan son yara ba itama,har ranta tanaso wata rana ta wayi gari taga nata yaran ko zasu zama sanyin idaniyar Suhail"


kimanin shekara guda da wata biyu kenan da auren su Duk da cewa ba ta taɓa nuna damuwa a fili ba, wani lokacin idan ta tuna har yanzu babu wani labari sai zuciyarta ta yi mata nauyi

Duk da cewa ba a taɓa nuna damuwa a fili ba, wani lokacin idan ta tuna har yanzu babu wani labari sai zuciyarta ta yi mata nauyi

Sameer ya shigo ya kira ta fito zasu tafi 

tare da Maryam suka fito ta ce"yaya Suhail bazaku tsaya kuci abinci ba"

murmushi yayi ya ce"sai wani lokacin idan mun dawo yau kam tafiya zamuyi kuma a yau zamu koma Abuja in sha Allah"

Iman ta yi musu sallama 

Maryam ta hadowa iman spices na girki kala kala 

tayi mqta godiya har bakin gate suka   raƙo su da Sameer ya banbare Nihal daga jikin Suhail ita a dole sai ya tafi da ita 

A hanya babu wanda ya yi magana

har duka ƙarasa gidan Abba 

Suhail a kofar gida yayi parking 

"yaya suhail"

iman ta kira sunan shi 

ɗago idanunsa yayi yana kallon ta

"da gaske kana son yara"

murmushi yayi ya ce"fiye da tunanin ki iman cikin ya shafa a hankali ya ce"can't wait to welcome my new baby from You"

ajiyar zuciya ta sauke damuwa ta bayanan ƙarara kan fuskar ta 

Suhail ya lura da hakan,Amma bai ce komai ba.

like 
share 
and comments