MUTUWAR AURE...! BOOK 1

21

by @aishatouuu

_Aishatou_

***
_________________


"Wanne Baban?" Indo da Husna suka faɗa a tare cikin ƙarfin hali.
Sauran abokan tafiyar tasu kowa yayi cirko cirko.

Iro da kuka ya tiƙe da kyar yace "Baban mu mana."
"Baban mu?" Indo maimaita sai kuma tayi jifa da kayan kanta ta kwasa da gudu tayi cikin gari Iro ya rufa mata baya.

Husna kuwa waje ta samu ta zauna tana kuka, sauran kawayen Indo jikin su yayi mugun sanyi masu saurin kuka tuni suka fara.

Husna kuka take bil hakki saboda hankalin ta yayi mugun tashi, masu ƙarfin halin cikin sune suka kamo ta wasu kuma suka ɗebo musu kayan su.

          Lokacin da suka iso Kofar gidan su, sun tadda Maza danƙam abinka da mutum na mutane tuni garin ya amsa da labarin mutuwar Salisu ko ina ka gifta zancen ake.

Har cikin gidan suka raka Husna da kayan su. Gidan ya ɗinke da mata ko ina ka duba mata ne anata ihu da koke koke, can kofar su Ramma Husna ta hango Gaje da katon cikin ta a gaba haihuwa yau ko gobe mata sun zagaye ta tana rusa kuka suna bata hakuri, abin gwanin ban tausayi.

Waje Husna ta samu ta zauna a ƙasan bishiya tana kuka, Maza harsun fara shigowa ana shirin ɗora tukunyar wanka kan su ƙaraso da gawar.

Dije kuwa tana ƙofar ɗakin ta tsofaffi kamar ta sun sata agaba tana kuka tana surutu yadda kasan wacce ta samu matsala cewa take.
"Wayyo Allah wayyo ni Dije gata na ya ƙare shike nan na fito rana, Salisu yaron kirki ɗa mai albarka, baya bari muyi kukan rashi, Salisu bai bari mun rasa komai ba, ko ɗazu da safe saida ya bamu kuɗin kashewa harya fita ya sake dawowa ya tambaye mu koda wani abu nace babu ashe tafiyar ke nan, Salisu ashe tafiyar ke nan." Sai kuma ta hurma ihu su Madiga na bata haƙuri.
"Shike nan yanzu asirina zai tonu, mutane zasu mana dariya, Salisu ya tafi, ka tafi Salisu ka barni, ina zaune anan ina auna hatsin tuwo kawai sai ganin Lirwanu nayi ya shigo yana kuka jikin shi yana rawa yake faɗa min an bugo masa waya motar su Salisu tayi haɗari duk sun mutu."

Dije tana kuka tana bada labarin bakin ta yaƙi shiru.

             Ƴaƴan shi kuwa sun haɗa kai a waje ɗaya suna nasu kukan dole inka kalle su su baka tausayi.

Gawar Salisu da Mai Kano tare suka iso, saida ya zo garin ma ya gane wanda ya mutu dan da Lirwanu ya kira shi cewa kawai yake "Yaya Mai Kano ya mutu shike nan wallahi ya tafi ya barmu."  

Haka ya rinƙa faɗa ya kasa faɗa masa ainahin wanda ya mutum, wannan yasa hankalin sa a mugun tashe ya taho ko gida bai tuntuba ba.

Sanda ya iso Kofar gidan su yayi daidai da ana fitowa da gawar Salisu daga mota, ta cikin taron Mazan yabi ya iso inda motar take, hanya mutane suka rinƙa bashi yana wucewa suna binshi da sannu.

Dashi aka riƙo gawar ɗan uwanshi da besan shi ne ba kwance babu rai saida yaji mutane na fadin "Allahu Akbar bawan Allah mutumin kirki Salisu Allah ya gafarta maka Manzon rahama ya karɓi baƙuncin ka."

Lokacin da kalaman nan suka sauka a kunnen Mai Kano Ƙarfin zuciya da jarumta ce kawai ta kai ƙafafun shi cikin gida, su huɗu suka kamo gawar har zuwa tsakiyar ɗakin shi, shigowa da gawar cikin gida ta sake ruda mutane kukan jama'a ya sake ƙarfi. Gaje kuwa suna giftata da gawar ta sume.

Baba Adamu wanda suke ƴaƴan Maza shiya tsawatar yace a daina masa kuka haka sannan matan suka rage ife ifen da suke.

                 Aramma ne yayi masa wanka da taimakon su Mai Kano, Salisu fuskar shi fes babu ciwo ko kaɗan kamar ka kira shi ya amsa, sai kafar shi da gefan cikin shi anan ne jini keta zuba.
Saida aka shirya shi Aramma ya tsuguna yayi masa addu'a ya roki Allah ya yafe masa yace shima ya yafe masa sai anan ne ma wani kuku mai ciwo ya taso masa.
Mai Kano kuwa da sauri ya juya ya kife kanshi da jikin bango, su Baba Adamu suka fara basu hakuri, saida suka yi shiru sannan aka shigo da Dije suyi sallama, ta rungume gawar tana kuka tana surutu addu'ar ma ta kasa yi masa Gaje kuwa da yaran shi kowa yaga yadda suka riƙe makarar suna faɗin bai mutu ba dole su baka tausayi.

Masoya na kuka da ihun kar a tafi dashi haka ɗaru ruwan mutanen gari da baƙin da suka zo suka raka Salisu makwancin sa gidan shi na gaskiya, saidai muce Allah ya gafarta mana da iyayen mu gaba ɗaya.

       Ana fita dashi kuma naƙuda ta tasowa Gaje aka rufu akanta, cikin ikon Allah bata jima tana naƙudar ba ta haifi ɗanta Namiji, yadda ya diro duniya maraya yana kuka haka Gaje da sauran al'ummar da suka ji kukan shi suka sake fashewa da kukan tausayin sa.

              "Sunanka Salisu, sunanka Salisu, Sunan ka Salisu Aramma ya faɗi haka a kunnan yaron sau uku bayan an gyara yaron an kawo masa shi yayi masa kiran Sallah da huɗu ba da sunan mahaifinsa.
"Allah mai kyauta da ƙari, Allah buwayi gagara misali, Allahu kaike karɓa kuma kaike bayarwa, Allah mun gode maka muna sake gode maka, Allah komai ka tsara mana daidai ne." Aramma ke jerowa Allah godiya su Mai Kano suna zaune a gefan shi suna amsa wa da Amin.

        ƙofar gida an shimfida manyan taburmi anata karɓar gaisuwa. Cikin gida kuma ana karbar gaisuwa ana barkar haihuwa tare da taya Gaje murnar fita daga takaba.

_Allah ke nan_

Sai yamma Nana da Ni'ima suka iso, Nana ta shigo gidan da tsohon cikin ta dan harya fito sosai, Ni'ima tayi kukan mutuwar Salisu dan tana son Baba Salisu saboda kirki da kyautatawar shi gare ta.

Haka aka rinƙa karɓar gaisuwa, tako ina mutane zuwa suke dan Salisu mutum ne na mutane, gashi da kyauta kowa nashi ne bashi da wani abokin faɗa.

Kamar yadda ake yi a garin in akayi mutuwa  ba'a ɗora tukunya sai bayan sadakar bakwai, to ga mutuwar Salisu ma haka ce ta faru, tun da aka yi mutuwar ba'a ɗora tukunya ba daga ko wanne gida a cikin ƙyauyen ake kawo marar tuwo da miya ana karɓa ana kaɓacewa a ƙwarake, wannan tuwon shi mutanen gidan zasu ci da ƴan zaman makoki, haka da safe za'a rinƙa kawo kwanukan koko da kosai wanda dashi mutanen gidan mutuwar zasu karya, da rana ma haka ko wanne gida sai an kawo abincin rana, kuma ko bakuyi girkin rana ba sai an siyo a tasha an bawa yaro ya kawo ko babba.

Ranar sadakar uku kuma matan abokan shi suka rinƙa kawo waina da gumba kaɓaki kaɓaki.
 
Ranar da akayi sadakar bakwai ranar aka yi wa Salisu ƙarami yanka, Salisu Babba kuma akayi taron yi masa sadaka da addu'a, ƴan uwa na nesa dana kusa kowa ya fara tafiya, ƙofar gida ma zaman makoki ya ƙare kowa ya tafi, Nana ma suka fara shirin komawa Kano washegari, a tsarin tafiyar tasu kuma babu Husna dan kuru-kuru Nana tace mata "su Ma'u kuma an zama ƴan matan ƙyauye, keda Kano ai saida yawo." 
Hakan kuwa aka yi washegari suka shirya suka koma, halin jimamin mutuwar da ake ciki yasa Aramma baiyi wa Mai Kano magana akan tafiya da ita ba. 

Gida ya watse kowa ya kama gaban shi ya zamana gidan babu kowa sai ƴan gida, babu baƙon daya rage sai ƴan gidan kowa ya tafi.

.........Sannu a hankali mutuwar Baba Salisu ta fara nisa, haka a hankali abubuwa suka fara canjawa, rayuwar gidan ta fara juyawa tana canja salo, Gaje na gidan tana renon ɗan ta duk da ƴan uwanta sunso ta koma gida tunda ta riga ta fita daga takaba amma sai Aramma ya hana yace suyi haƙuri tadan sake kwana biyu kanta tafi.

         Sannu sannu abincin rana ya fara yanke wa a gidan dama Salisu ne ƙarfin gidan shike sawa ayi, yaran shi kuwa yanzu babu mai basu kuɗin kashewa kona siyan abinci da rana, Aramma na iyaka kokarin shi akan su dan kullam da safe sai ya siya musu kosai, Lirwanu kuwa baiwa ƴaƴan shi bama bare na wani.

Yanzu babu me kawo ruwa gidan saidai Husna da Indo suje su ɗebo, dama Salisu ne ke biyan kuɗi a kawo kullum, to yanzu an wayi gari babu shi, tuni Husna da Indo suka shige sahun ƴan matan garin dake sunturin ɗiban ruwa.

Husna ce kedan jin wahalar ɗiban ruwan saboda rashin sabo.
Ranar da ta sake kukan rashin Salisu kuwa shi ne randa ta tambayi Lirwanu kuɗin sabulun wanki ya balbale ta da faɗa kamar zai yi mata duka, ya koreta.
Tana barin inda yake ta samu waje ta zauna sai kuka, Ramma tazo ta same ta tana kuka tace "meya faru?" Ta faɗa mata akan ta tambayi Baba Lirwanu kuɗin sabulu ne yace inta sake tambayar shi sai ya zane ta.

Ramma tayi shiru tana jinjina hali irin na Mijin su, amma yata iya haka yake bashi da daɗi.
"Kinga karki sake tambayar shi kinji?" Husna tace mata "to wazai na bamu kuɗin siya tinda kinga Dije bata bamu." 
Ramma tayi shiru tana tunanin sai kuma tace "zamu nemo wata hanyar, ai Allah na nan."

Dije kuwa wannan mutuwa ta Salisu ba ƙaramin taɓa ta tayi ba, dan Allah ne gatan ta Salisu gatan tata,  takamar ta a gidan nan Salisu ne, dan yanzu kuɗin kashewa ma nema yake ya gagare ta, to dama shike basu kullum wanda Mai Kano yake turo musu kuma ya zame mata bonus, yanzu kuwa babu wannan maganar wanda Mai Kano ya aiko shi ne na kashewar ta da sauran bukatun ta.

.......Sannu sannu rayuwar gidan ta fara wargaje wa tana ɗaukar wata hanya ta daban, yanzu kowa ta kansa yake yi a gidan, dumamen safe ana sauke shi a wajen ake kasawa kowa ya dau nashi in baka ɗauka ba kayi jinkiri to bazaka samu ba, tuni Husna ta ɗauki kwanon talla a gari, ita ce tallar kosan safe ita ce tallar Awara da rana, yara da yawa a garin suna talla ne dan su tara kuɗi su sai kayan ƙyali da ado irin na sauran yara amma banda Husna da ita tana tallane dan ta kashe yunwar cikin ta da buƙatun ta na yau da kullum, dan yanzu bata da mataimaki sai Allah sai Ramma baiwar Allah data riƙe amanar da Aramma ya bata da hannu bibbiyu, abincin gidan su kuwa iya tuwon dara ake yi yanzu sauran abinda ya rage da safe a dumama da rana kowa yaci da kanshi.

Duk wannan faɗi tashi da ake kuma har zuwa wannan lokaci Mai Kano bai daina yiwa Husna aiken kuɗin kashewa sabulun wanka na wanki da man shafawa ba, kai wasu lokutan harda abun taɓawa yake siya ya aiko mata da shi, saidai kamar yadda bai daina ba haka Dije bata daina karɓe wa ta hana ta komai ba.

Cikin lokaci kankani Husna ta canja tayi wani iri tuni ta fara sajewa da sauran yaran gari.

Yau tun safe Indo ta tashi bata jin daɗi wannan yasa Husna ce kadai taje ɗiban ruwa, hakan kuma yasa bata samu kawo ruwan da wuri ba saboda dama Indo ce ƙarfin ɗiban ruwan, gashi tana kawo sahun farko Zahara ta kwashe tayi wanke wanke da wanka, wannan yasa har yamma gidan babu ruwan kirki.

Lirwanu ya shigo ya tadda gidan babu ruwa ya hau faɗa da zugawa Indo da Husna zagi, yana cikin faɗan Husna ta shigo da ruwa.

Babu jira babu bin ba'asi ya bita da faɗa ya hau zage zage, ran Gaje yayi mugun ɓaci daman kuma a wuyan ta yake tana kulle dashi, ai kuwa ta fito cikin gidan suka fara cacar baki.
"To wallahi tunda abun naka iskanci ne da wulaƙanci Indo ta dena ɗiban ruwa a gidan nan, ai ba baiwar ka bace da kana can tasha zaman rashin abunyi, suna maka wahala kuma kazo kana zagin su harda cin alwashin duka to wallahi baka isa ba."
"Na isa har nayi yawa kuma ɗiban ruwa a gidan nan yanzu Indo ta fara, ke komai akan ƴaƴanki saikin shiga sai kace ke kaɗai ce mai yara." Lirwanu ya faɗa yana huci, Gaje tayi shewa tace "sannu isasshe to maji kuma ma gani Indo dai nice na haife ta kuma nice uwar ta, nace ta daina ɗiban ruwa, in kuma da ubanda ya haifa min ƴaƴan sai naji, inta dena ɗiban ruwan kuma daga yau ka dena mata abinda kake mata, asarrare mara zuciya."

Gaje ta mayar masa da martani a zafafe.
Nan fa rigima ta kaure a tsakanin su, Lirwanu yaƙi bar mata ita kuma yana rufe bakin shi zata ɗora nata.

Faɗan yaƙi ƙarewa saida aka kira Aramma sannan suka yi shiru.
"To kai Lirwanu me yasa kake haka ciwo ai yana wuyan kowa kuma yaran nan suna kokari." Aramma ya faɗi haka ranshi ɓace yana duban Lirwanu bayan ya gama jin abinda ya haɗa faɗan.

"To ya zata zo tana zubawa mutane iko a gida, ai dole a faɗa mata bata isa ba." Lirwanu ya faɗa bakin shi na kumfa.

Aramma ya rufe shi da faɗa ya kuma ce kada ya sake yaji ya daki wani yaro a gidan.

Tun daga wannan faɗa da aka yi Gaje ta kafa ta tsare Indo ta dena zubawa kowa ruwa a gidan, iya karta randar ta.

Husna kuwa da bata da gata sai Allah hawalar saita ƙara mata yawa, kullum ita ke zuba ruwan gidan randa aka samu matsala bata zuba akan lokaci ba Lirwanu ya sakata a gaba da ruwan ashar, tunba in Aramma baya gida ba ai in ba Allah ne ya taimke taba harda duka saiya haɗa mata.

Wannan hali da Husna ta tsinci kanta a ciki ya sake saka rayuwar ta acikin mugun duhu da kunci, gashi yanzu Babanta sai yayi wata biyi kanna uku baizo garin ba, kayan sawarta tuni suka fara fari saboda garin soda da suke sha wajen wanki, dan yanzu bata wanki da sabulu Soda take siya ta jiƙata da ruwan ɗumi dan tafi arha, wannan yasa atamfofin ta duk suka fara koɗewa, dogayen rigunan ta kuwa wasu duk sun dage mata.
         
Yau sunada Aro (party) babar ƙawar suce ta haihu zasu je gidan suna, Allah ya taimaki Husna da wuri ta gama ɗiban ruwa, tayi wanka Ramma tace "ko zaki je gidan Mariya kice ta baki wani a cikin kayan ki kisa kinga duk kayan ki babu wani na kirki yanzu." Husna tace "to." Ta tafi gidan Mariya tayi sallama, a inuwa ta same su suna surfe, ta gaida matan gidan sannan ta cewa Mariya "kayana na wajen ki zaki bani nasa zamuje Aron gidan su Funi."
"Wanne kaya kuma? Ka jimin yarinya zata min iyayin banza, kin tafi kin bani waje ko sai naci uwarki a nan." Mariya tayi kan Husna da faɗa tana bambamin wani kaya zata bata.

Ramma tayi shiru tana sauraren abinda Husna tace Mariya tayi mata, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya tace "dama nasan za'ayi haka, bari mu duba ko a cikin rigunan kine dogwayen saiki saka wata." 

Ramma ta faɗa tana burkita akwatin Husna, da kyar aka samu rigar data ɗan sakko mata tasa ta dakko awarwaron data ɓoye a ɗakin Ramma ta saka, yanzu ma baya zama a hannun ta yayi mata yawa dole ta cire ta sake ɓoye wa kamar yadda Ramma ta koya mata.

Gidan suna ya cika yara suna ta wake saiga Sajida ƴar gidan Mariya sanye da wani lace ɗin Husna tana ta fasa kai da ƙumi (yanga), Husna ta kalleta ta kalli kayan jikin ta, nan fa babu zato babu tsammani faɗa ya tashi tsakanin su dan Husna taci kwalar Sajida tace saita cire mata kayan ta dake jikin ta.

Sajida tasa kuka tana ƙaryata Husna nan fa sauran kawayen su suka hau yiwa Sajida ihu da shewa, abunda ya sake rura wutar faɗan ke nan dambe ya kaure tsakanin su.

Sajida ta ɗauka zataci ribar faɗa da Husna saida faɗan yayi nisa sannan ta gane tayi kuskure dan ɗan karan duka Husna tayi mata sannan ta yaga kan ɗinkin rigar lace ɗin.

Sajida taje gida ta faɗa wa Mariya abinda ya faru sai ta saɓo gyale tayi gidan su da burin taje ta samu Husna taci mata mutumci amma sai tayi rashin sa'a dan tana zuwa gidan ta iske Aramma yana nan, taso tayi maganar a gaban shi Dije tayi wuf ta hana ta.

Saida Aramma ya fita Dije tace "ashe baki da wayo ban sani ba? Yo wannan magana yanzu kina yinta a gaban Aramma ai saiya saka kin fito da sauran kayan wajen ki gaba ɗaya, kinga yanzu kama hanya ki koma gida zanyi maganin Ma'u inta dawo gidan nan."

Haka Mariya ta sake sabar gyale ta koma gida tana huci dan ba haka taso ba.

Tun daga lokacin kuma kamar wanda aka yiwa Husna huɗu ba, duk sanda taga Sajida da kayan ta sai sunyi faɗa kota rinƙa yi mata ihu da gorin kayan tane aka ɗauka aka bata, wannan yasa yaran gari suka saka Sajida a gaba da tsokana, bata isa da fito da kaya mai kyau ba koba na Husna bane yanzu yara zasu ce kayan Husna ne suka kwashe.

Wannan rigima tsakanin Husna da Sajidar Mariya bata mutu ba saida aka dangana maganar da gaban Aramma dan Dije tayiwa Husna zagin dacin mutumcin amma a banza haka tasa Lirwanu ya dake ta amma tana fita ina taga Sajida da kayan ta saita sake tara mata yara.

Sanda Aramma yaji kan zance ran Mariya da Dije yayi mugun ɓacin da basu yi tunani ba dan cewa yayi Mariya saita biya kayan data ɗauka, da ƙyar dai aka samu zancen ya mutu bayan dogon faɗan da Mariya tasha, Husna kuma da kanshi ya bata haƙuri tare da alkawarin zaisa Baban ta ya sake ɗinka mata wasu.

Wannan sulhu da aka yi shiya kashe rigimar gaba-daya.


________________________

_BAYAN SHEKARA BIYU A 2011_

Yamma ce sakaliya Motar Naira data ɗebo ƴan mata daga cin kasuwar Litinin beguwa ta tsaya a tasha suka fara Sakkwato suna shewa kowa yana maida yadda aka yi da yadda kasuwa ta kama.
Indo da Husna ne karshen sakkotawa ko waccan su taci damara da gyalen ta, Husna ta ƙara girma da tsayi sak ta saje a cikin matasan yan matan garin, gaba ɗayan su baza su wuce shekara goma sha huɗu huɗu ba.

Husna da farantin silver ta ta fito Indo tace "kai Ma'u yaufa kinci kasuwa koda yake dama ke fa mai sa'a ce komai kika ɗauka sai kin siyar." Sauran yan matan suka fara cewa "kai ai Ma'u badai kasuwa ba."

Husna na jinsu tana murmushi dan ta daɗe da sabawa da jin irin wannan maganganu a bakin ƴan garin bama Kawayen su kadai ba, sukan ce wai "ko kwantai kake in Jikar Dije ta dau kayan ka saiya ƙare."

Aramma kuwa in yaso tsokanar ta yakan ce mata "kaga Jikar Dije kan talla."

Musamman yanzu data zama uwar kanta gashin kanta take ci a gidan, inka cire Ramma da Aramma kuwa babu wanda take ragawa, ko Dije tayi mata yanzu ramawa take sai dai in Lirwanu ya dawo tasa ya dake ta ita kuma tace duka baya kisa, gobe ma inta shiga sabgar ta saita shimfiɗa mata rashin mutunci.

Gaje ta daɗe da komawa gidan su har tayi sabon Aure anan cikin gari, Indo kuwa da Sa'a suna gidan su Gaje wajen kakar su ta wajen uwa, Indo bata ma fiya zuwa gida ba sai ta kama, ita da Husna sun ɗinke sun zama kawaye sosai.

Rayuwa tasa idan Husna ya bude da neman kuɗi sosai ba tallar cikin gari ba harta ƙauyuka tana yi, ta kasuwa kuwa dama wannan ta zama kamar al'adar ƴan matan garin duk ranar kasuwa sai sunje tallar barkono. 

               Indo ce ta zungure ta  tana nuna mata Sunday tace "kinga Sunday can shida sabon mahaukacin dana ke faɗa miki, kome ya haɗa su yake korar shi oho."
Husna ta ɗaga kai taga Sunday riƙe da zabgegen karan dawa yana korar mahaukacin shi kuma yana dagewa yaƙi tafiya.
"Zo muje." 
Husna ta faɗa tana yin gaba Indo ta biyo ta a baya....