MUTUWAR AURE...! BOOK 1

22

by @aishatouuu

_Aishatou_

***
_________________


"Sunday me yama zaka dake shi?" Husna ta faɗa sanda ta iso wajen.
"Heee Achalugo welcome." ta harare shi,  cikin broken ɗin da har yau ta kasa iya wa tace "you want to put yourself in trouble abi? Wetin this man did to you?"
"Achalugo this madman ba hmmm, he just comes and carry my pure-water." 
"Kuma shi ne zaka dake shi?" 

Husna ta faɗa tana kallon mahaukacin dake tsaye har yanzu yaƙi tafiya, sai kuma tace "Nawa ne kuɗin ruwan na biya ka, kai wallahi ka fiya san kuɗi shi yasa baka kyauta baka sadaka." tayi maganar tana ciro kuɗi, Sunday ya washe baki yace "Naira Ashirin ne yasha ɗaya ga ɗaya a hannuna dana ƙwace." 

Husna ta bashi kuɗin shi, Indo na tsaye a gefan su tana kallon ikon Allah, ɗayan ruwan ta karɓa a wajen Sunday ta miƙa wa mahaukacin yaƙi karɓa, saida ta sake miƙa masa tare da cewa "karɓi na baka kyauta, bazai dake kaba." sannan ya miƙa hannun shi da yayi busu busu da datti ga wasu zaƙo zaƙon farata masu tsayi ya warce ruwan ya juya Husna tabi bayan shi da kallon mamaki, dogone sosai dan a tsaye zai kai shararren jarumin Indian nan Phrabas (Bahubali) tsayi, saboda tsabar cikar da fuskar shi tayi da gashi ko kaɗan bazaka iya gane kamanin sa ba bare ka ƙiyasta shekarun sa, gashin kansa yayi yawa sosai yayi tozo babu kyan gani ya taho ya zagaye fuskar shi da saje mai yawa har gemun shi ya taru sosai yayi tsayi, gashin girar sa kuwa harta haɗe waje ɗaya itama tayi yawa wannan yasa ba'a iya ganin idanun shi, gaba ɗaya suma ta yiwa fuskar shi rumfa, bazaka iya gane asalin yanayin zubin jikin saba saboda wata ƙatuwar jallabiya dake jikin shi me dogon hannu dan tayi masa yawa, duk tayi baƙi da dauɗa, tsabar ɗaudar da tayi baka isa ka faɗi asalin kalar rigar ba, ƙafafun shi banu takalmi sai wani baƙin abu daya rufe kafarshi mai kama da safa, a tsaye ƙam yake tafiya cikin sauri da sassarfa, yana tafe yana gyaɗa kai kamar yaro. hannun shi ɗaya riƙe da wani farin sanda (Stick ) siriri kamar na masu matsalar ido.
 
Husna bata daina binshi da kallo ba har saida taga ya hau gefan titi ya miƙe yana tafiya, sai taji ya bata mugun tausayi, a can ƙasan zuciyar ta tace "Allah sarki ko ina yan uwan shi suke?" 

Saida Indo ta taɓa ta sannan ta juyo ta kalle ta sai kuma tayi gaba ba tare data ce komai ba Indo ta biyo bayan ta suka jera suna tafiya a tare kamar yadda suka saba.

Suna tafe Indo na sake bata labarin mahaukacin.

"In faɗa miki Ma'u yau befi kwana biyu da zuwan shi garin nan ba, dan dai kwana biyu bakuyi abincin yamma bane shi yasa baki ganshi ba amma dakin ganshi, in faɗa miki tsirfa gare shi in fa mutane suka bashi sauran abincin da sukaci sadaka baya karba, amma in aka bashi sadakar kuɗi saiya karɓe kinga yadda ya warci ruwan da kika bashi ɗazu?" 
Husna ta dagawa Indo kai alamar tana sauraren ta, ita kuwa sai taci gaba da faɗin.
"To haka yake karɓar kuɗi in aka bashi, kuma baya kula kowa baya faɗa, a can kusa da masallaci yake zama ko bayan rumfar Mutumin ki Bahari."

"Ikon Allah ko daga ina yake?"

Husna ta faɗa daidai sun zo wuce rumfar Bahari mai saida fetir ya fara tsokanar ta kamar yadda ya saba.

"Ma'u kwana biyu bakya abinci wai ko dai kin karye ne? Ki faɗa kawai in kin karye saimu temaka mu ɗora ki." Buhari ya faɗa yana dariya Husna ta zuba masa harara.
Indo tace "kawo jarin na kai mata gida."
Bahari yayi dariya yace "ki bata ko kisa a aljihun ki. Kawai kice ta dena mana ƙumi tazo na taimaka mata."
"Ai wallahi kasan nafi ƙarfin ka taimaka min nawa ne ɗan jarin man naka da har zaka ɗora wani?" 
Husna ta faɗa tana banka mishi harara, tayi gaba Indo ta biyo ta da sauri, suka bar Buhari da dariya yana sake faɗar 
"Ma'u ki sauke kai ƙasa na taimaka na ɗora ki." Shi kaɗai yake maganar yana dariya dan tuni Husna da Indo suka bar wajen da yake.

.....Kaf garin Bahari ne saurayi ɗaya tilo da suke shiri da Husna, shima ba asalin ɗan garin bane ta dalilin abokin shi Ya'u da suka haɗu a Lagos wajen neman kuɗi ya zo garin har ya fara saida fetir.

              Kaf Samarin garin suna son yi mata magana, amma bata kula su, su Indo har sun fara zance.

Husna bata da saurayi ko ɗaya dan duk sanda Babanta ya zo inta rako shi waje zai tafi saiya ja mata kunnen yace kar ta sake yaji ta kula kowa, wannan yasa ko an aiko ana kiranta bata zuwa, Dije tayi ta zagin ta tana mata gori amma bata damuwa.

Hamisu (Ɗan Hajja) shi kaɗai ne saurayin daya maƙyale mata yayi ta cewa Samarin garin ita budurwa shi ce duk da bata taɓa kula shi ba, shi kaɗai yake kidan shi yayi rawar sa, haka zai zo har gida ya gaida Dije ya bata kuɗi ta amshe, duk dan Husna ta kula shi amma har kawo wannan lokacin bai ishe ta kallo ba, kuma tunda ya gane Dije mayyar kuɗi ce shike nan yake yawan zuwa ya gaishe ta ya bata kuɗi ita kuma tayi ta zagin Husna tana kozanta ɗan Hajja.

Har goro yake aiko wa Dije gida, da yake yaron akwai kuɗi a hannun shi sosai yake baza ƙarya da ƙafafar shi a gari, ƴan mata suyi ta binshi yana musu yanga shi sai Husna.

Hamisu da gaske ɗan Hajja ne dan uwar shi tana Makka kuma sosai take bashi kudi, yana cikin samarin dake fantamawa a garin har shago gare shi babba a tasha wanda yake saida kayan awu, haka kaf cikin garin shine mutum na farko daya ɗora ginin kwangiri (bulo da bulo) wannan gini da akaga ɗan Hajja nayi a garin ya sake siya masa mutumci da girma a idan mutane musamman kuma da yake yana da kyauta sam bashi da rowa, amma fa baya ji ko kaɗan saidai da yake yana da kuɗin shi kuma abinka da ƙyauye sai kaji shiru ko yayi wani abun ashshar ma maganar bata zuwa ko ina take mutuwa murus.

Da sallama Husna ta shiga gidan su tun daga nesa ta hangi mutanen gidan Zazzau ne amma bata gane su waye ba saida ta iso wajen sannan ta gane waye da waye a zaune dan yanzu bata iya gane waye a waje daga nesa saidai ta hangi alamar mutum amma indai bata matso kusa ba bata iya gane waye, kuma hakan ya faru da ita ne tun wani mugun ciwon ido da tayi mai wahalar gaske, sosai tasha wahala duk wani maganin ciwon ido da ake siyarwa a garin babu wanda batayi amfani da shi ba amma ido yaƙi warkewa daga baya sai Aramma ya fara yi mata rubutu tana wanke idon dashi, da ciwon yaƙi daɗi wata rana Ramma ta same ta a ɗaki tace "Ma'u mai zai hana kije ki samu Garba tunda yana da number Yaya kice ya taimaka ya kira miki Babanki ki faɗa masa ya aiko miki da kuɗi aje asibiti ko ya siyo miki magani, kinga idon naki kullum gaba yake sake yi." 
Husna ta amsawa Ramma da "to." Harta juya zata fita ta sake ce mata  "Amma fa ki faɗa masa karya bari Lirwanu ya sani kindai san halin shi yanzu sai yace ana kaiwa Yaya munafunci."

        Haka kuwa aka yi Husna ta samu Garba tayi masa bayani, take ya kira mata Baban ta suka yi magana yace "babu damuwa Husnah zan turo da kuɗin zuwa asibitin Ramma saita rakaki Doko?" 

Husna ta amsa sukayi sallama da Babanta tayiwa Garba godiya ta tafi.

Cikin rashin sa'a Mai Kano bata hannun Garba ya turo da kuɗin ba, kuɗi na shiga hannun Lirwanu shike nan suka zama labari dan tunda ya zuba su a aljihun shi ya fita shike nan ruwa tasha, da Husna tayi masa maganar zuwa asibiti kuma zagi ne ya raba su.

Rashin gata da kulawar uwa tasa harta warke babu wanda ya kula da halin da take ciki, tun daga wannan ciwon ido kuma ta fuskanci ta samu tawayar ganin abin da ke nesa da ita, wanda har kawo yau babu wanda yasan halin da take ciki sai ita, yayin da mutane inta wuce su ko ta nuna bata gansu ba suke ɗaukar hakan a matsayin wulaƙanci.

Akan turmi  ta zauna riƙe da baƙar leda Ramma ta dube ta tace "Sannu Ma'u ya kasuwar?" 
"Alhamdulillah kasuwa." ta amsa sai kuma ta dubi sauran matan tace "sannun ku." 

Mariya ta shaka saboda Husna tayi kamar bata ganta a wajen ba, har zata balbale ta da masifa sai kuma ta tuna abinda ya kawo ta tasan dole saita lallaɓa ta zata yarda.

Kamar gaske a hankali Mariya tace "Ma'u tunda ni ban isa ki gaishe ni ba wajen ki nazo." tayi maganar tana wani harare harare, a ɗage, Husna ta dube ta dan yanzu basa shiri da ƙanwar Baban nata tunda ta gane mugun san kanta ne da ita suka raba hanya, tace 
"Gani ai." 
"Dama shawara nazo muyi nace me zai hana kizo mu rinƙa yin abincin yamma ina miki kina kaiwa tasha kinga zamu samu alheri har kya samu kidan rinƙa tara sauran ciki (taron kwanuka da yammata ke yi na Aure) kuma ki samu na kashe wa."

Kaf matan wajen sai da suka saki baki da kunne suna jin wani mugun sankai irin na Mariya tafa san suna abincin yamma ita da Ramma amma tsabar mugun san kai da zalama zata kawo wannan maganar.
Husna tayi murmushin da Indo ke kira na rashin mutumci tace "shi kuma wanda muke yi sai a daina ko ƙaƙa za'ayi?"
"E mana ita Rammar ba kuna na rana ba sai ta barmin na yammar muna yin nima na samu." Mariya na dire maganar Husna tace "to bazan yiba, aini na dena yiwa kowa wahala, da de nayi yanzu kuwa an daɗe da rufe wannan shafin, su ƴaƴan ki basu da kan talla saini Husna? to bazan ɗauka ba, kuma babu wanda ya isa ya sani ɗauka." 
Maganar ta kular da Dije tace "har ubanki Mai Kano bai isa ba ko? Tunda yanzu kin raina Lirwanu a banza kike ganin shi." 

Husna ta dubi Dije tana jin wani baƙin cikin ta a rai tace "a'a shi wannan ya isa har yayi yawa amma fa wallahi inya sani na miki talla zan ɗauka sai dai duk abin da kika gani ke kika siya da kuɗin ki." Tana gama faɗin haka ta ɗauki faran tinta tayi ɗakin Ramma. 

Dije tabi bayan ta da kallon takaici tace "Kema Mariya ai na faɗa miki wannan tsinanniyar yarinya ba yarda zatayi ba, kuma kina ji dai tace ko an sakata dole baza'a wanye ƙalau ba, wallahi kuma zata aikata kinsan halin Ma'u bata da mutumci in bata so abu ba, kai mu dai Safiya ta haifa mana jaraba, yarinya ƙarama amma ta ishi mutanen gari ta ishi na gida, Lirwanun ma da take shakkar shi yanzu a banza take ganin sa kana mata maganar shi zata ce inya dake ta wajen zai huce."

Mariya da baƙin ciki ya hanata magana saita warci zani ta goya ɗan ta tace "ni na tafi." Fuuuuu tayi gaba ta kusa bangazar Zahara saida ta matsa da sauri tace "kinga bani na kar zomon ba, zaki mangaje ni haka kawai baga uwarta nan zaune tana ji ba." Mariya tuni tayi waje, Dije tace "dama ai ita ke zuga ta tunda tafi kowa morar ta a gidan nan." 

Tsaram Ramma ta tashi ta basu wajen, tana tafiya suka kafa gulmar ta.

          Husna na kwance a ɗaki Ramma ta shigo tace "Ma'u me yasa kika ƙi yarda? Kinsan cewa za'ayi ni ke zuga ki, gashi can Zahara harta fara faɗi." 
Miƙewa tayi zaune tana kallon ta tace "sun daɗe basu faɗa ba, ita kuma Zahara ai dama baƙar munafuka ce."

Ramma ta girgiza kai dan tasan halin ta tunda tace baza tayi ba tofa bazata yin ba, saida ta numfasa sannan tace
"Dama ɗazu aka aiko min an kawo doya zuwan Mariya ne yasa nace bazan siya ba tunda naji meya kawo ta." Ramma ta faɗa, Husna tace "kema dai kiyi ta bari suna miki iskanci, anjima zan je na karɓo mana, yawwa ga sakon naki na siyo."  ta turawa Ramma ledar data shigo da ita.

        Bayan sallar isha'i yan mata suka taru a Dandali ga farin wata fetal wajen yayi haske, Samari sai kiran ƴan mata suke hira, wasu kuma sun kafa gaɗa anata waƙe, Husna da Indo suna zaune suna cin amaro (gyaɗa mai gishiri) yaro ya zo in da suke yace "Ma'u wai kije inji Dan Hajja yana can ƙofar mai Gari." Kallon inda yaron yake Husna bata yi ba sai Indo ce tace "kai yi tafiyar ka ba zata jeba." 

Yaro ya juya yaje ya faɗa wa ɗan Hajja, sai gashi ya sake dawowa wajen kan yayi magana Husna tace "wallahi in ka sake zuwa nan saina maka dukan tsiya." Sanin halin ta yasa yaron ya koma yace wa ɗan Hajja tace "inna koma saita dake ni." 

Naira goma ɗan Hajja ya bashi ya tafi shi kuma ya koma wajen abokan su yana ƙwafa.
"Wallahi duk randa kika shigo hannu na Ma'u saina yi miki fata fata, banda ina sonki ai wallahi da yanzu nayi maganin ki." Ɗan Hajja ke tafe yana zancen a ranshi.

Can kuwa Indo ta kalli Husna bayan ta kora yaron tace "Ma'u me yasa bazaki kula ɗan Hajja ba? Kowa yasan fa yadda yake mugun sanki a garin nan yanzu harna Ma'u ake kiran shi."

Wata muguwar harara ta zuba wa Indo sannan tace "me zanyi dashi ɗan iska kawai."
Indo ta gyara zama saida ta kama baki sannan tace
        "Hmmmm ai baki sani ba in faɗa miki ranar nan ina ɗaki naji su Ladi suna faɗin halin ɗan Hajja wai cikin da aka yiwa Bari harda shi acikin mazan da suka mata, amma uwarsa ta shiga ta fita ta turowa mai gari kuɗi aka rufe bakin iyayen ta."

Husna ta dubi Indo tana taɓe baki tace "ai ita ma Barin shegiya ce san mazan jaraba gare ta ga kwaɗayi."
"Nima haka nace duk lefin tane muda bama kula su wa zai mana, yawwa wai dan Allah Bahari saurayin kine? Naji ranar ana gulmar a makaranta da muka je wanki randa baki jeba."
Husna tace "ƴan iska su Ummai ne ko?"
"Taɓ ke ai ba'a faɗa miki magana yanzu sai ki tare mutum ku fara faɗa." Indo ta faɗa, Husna ta harare ta "banza matsoraciya, ai nasan sune, Ummai ce ke sanshi shi kuma baya kula ta, amma ni ba saurayi na bane kinsan bani da saurayi."
Indo tace "Taɓ ke ɗin? Badai kya kula su."

.....Washegari da rana Iro ya kai wa Husna fantekar doyar ta tasha, Bahari na ganin ya aje kayan ya tashi yaje kan kayan ya tsaya Samari suka fara tsokanar shi da "mai gadin Ma'u." 

Yana dariya yace "na saba gwanda na jire mata kar kuyi mata gyaran fuska kanta iso." 
Kullum haka yake mata ana ajiye kayan abincin ta zaije kai ya tsaya duk da yasan babu wanda zai taɓa mata amma saiya tsaya a kai ya fake da gadi yake mata, tana zuwa kuma ya hau tsokanar ta daga karshe dai shi ake fara zubawa kan a siyarwa kowa.
Iro bai jima da tafiya ba sai ga Husna ta iso hannun ta riƙe da botikin miya.

"Dan Allah zoki fara zuba min wallahi yunwa nake ji kwana biyun nan da bakya yin abinci garin Kwaki nake sha." Bahari ya faɗa yana karɓar bokitin miyar, tasan da gaske yake tunda tasha ji abakin ƴan matan dake saida abinci a tashar suna faɗin in batayi abin siyarwa ba baya siyan na kowa, sai da ta harare shi sannan tace 
"Ai yau bazan siyar maka ba." Ya zare ido yace "yasin da wasa kike."

Bahari bai bar wajen ba saida ta zuba masa sannan ya tafi yana faɗin "yawwa na karɓi nawa yanzu kowa ma zai iya zuwa ya sai nasa."