MUTUWAR AURE...! BOOK 1

23

by @aishatouuu

_Aushatou_
         ***


Bata jima da zuwa ba Indo ta iso da nata kayan siyarwar.
Sunday ne ya leƙo daga shagon shi yace takai masa farar doya, ta tafi kai wa taga mahaukacin jiya a zaune ta gefan shagon shi yana karta Sandar hannun shi a ƙasa kamar wani ƙaramin yaro, tausayin shi taji ya kamata tana dawowa daga wajen Sunday ta zuba doya mai yawa taje wajen shi ta basa amma sai yaƙi karɓa, taɗan tsaya tana kallon shi sai kuma ta sake cewa 
"Ka karɓa nina baka kyauta." 
Nan ma yaƙi ɗagowa ya karɓa, Sunday ne ya fito wanke kwanon shi ya ganta a tsaye tana roƙon shi ya amsa.
"Achalugo ai besan me kike faɗa ba bashi da hankali, sai da nakore shi ashe nan yazo ya zauna." 
Husna ta harari Sunday da yayi maganar tace 
"Waya cema bashi da hankali? Rashin lafiya yake yi kuma zai warke." Dariya maganar ta ta bawa Sunday saida ya dara sannan ya koma cikin shagon shi.

Husna ta gaji da roƙon mahaukacin ya karɓi abincin data kai masa amma yaƙi amsa, kai ko nuna yasan tazo inda yake ma bai yi ba, haka zuwan ta baisa ya daina tonon kasar da yake yiba, dole ta koma wajen saida abincin ta Indo tace "kema Ma'u an faɗa miki baya karɓar abinci, amma naga yana zuwa wajen Safe mai fura ya bata kuɗin da ake bashi sadaka ta bashi fura, itama data dama mishi a ƙwarya kin karɓa yayi saida tasa masa a leda." 

Husna bata cewa Indo komai ba ta tashi ta karɓo leda a wajen Sunday ta zuba farar doya kamar tasa masa miya sai kuma ta fasa ta kai masa.
"Gashi na baka." 
Ta sake faɗa a karo na biyu tana miƙa masa ledar hannun ta, ga mamakin ta sai taga yasa hannu ya warce ledar kamar yadda ya karɓi ruwan jiya. tadan tsaya tana kallon shi, sai kuma tayi murmushi.

Ledar ya buɗe ya ɗan yi jim yana kallon doyar kamar mai hankali sai kuma ya fara ci daga cikin ledar.

Husna ta karɓo masa pure-water guda biyu a wajen Sunday ta kawo masa ya karɓa, kaɗan yaci doyar yayi jifa da sauran sai kuma ya shanye ruwan duka sannan ya tashi yabar wajen. Husna ta binshi da kallo tanajin tausayin sa na sake huta mata zuciya.

 Bata jima a tashar ba ta saida abincin ta Bahari ya ɗakko mata kayan ta saida ya rakata har ƙofar gida sannan ya koma tasha.

         Washegari ma haka ce ta faru, Husna ta bawa mahaukacin nan abinci, da tayi Kunun yamma ma ta zuba masa a leda kuma ya karɓa sai taga shi bai rage ba duka ya shanye har saida tace "na ƙaro maka?" Yayi mata banza, ganin ba zai amsa ba yasa tabar wajen tana waiwayen shi.

Tun daga lokacin kuma take bawa mahaukacin abinci, tunda ta gane baya karɓa a roba sai take siyan leda a wajen Sunday ta zuba masa, haka ruwa kullum saita siya masa.

Sauda dama Indo in taga tana wa mahaukacin magana takan ce mata "kema Ma'u ina kika taɓa ganin mahaukaci yasan daidai daba daidai ba? saiki rinƙa tambayar shi ya koshi ko me yake so? Sai kace wani mai hankali."

Duk sanda Indo tace l haka sai dai Husna tayi murmushi tace "Indo ba mahaukaci bane wannan sai dai mara lafiya, tunda kinga shi baya duka kuma baya ɗaukan kayan kowa."

             Sannu a hankali ya fara gane ta, yana ganin ta zo tashar zai zo kusa da inta take ya tsaya, har mutane suka fara gane dan ita yake zuwa wajen tunda ita kaɗai ce me bashi abinci, sannan inba zuwan tayi ba baya zuwa wajen, haka baya shiga cikin mutane kuma baya shiga cikin gari, kullum zaka ganshi zaune shi kaɗai ko a kusa da masallaci gefan wajen da su Aramma ke zama ko ka ganshi tsakanin shagon Dan Hajja da rumfar Bahari, in kaga ya zo wajen shagon Sunday to ruwa yake son sha, wannan yasa ko Husna bata ganshi ba sai wani yace mata "Ma'u ga mutumin ki can." 

Sam baya zuwa inda mutane suke kullum yana gefe guda yana tona rami da Sandar shi, ganin bashi da faɗa yasa mutane babu ruwan su dashi haka Aramma da kanshi ya hana yara tsokanar sa.

Yauma zuwan Husna tashar ke nan ta hango shi can kusa da majalisar Dan Hajja tsaye a jikin bishiya yana kallon titi. 
Bahari na karɓar abincin shi ta biyo shi da ledar data zuba masa nashi abincin suka jera suna tafe yana mata hirar gobe zashi gida yaga matar shi tace "In kaje kace ina gaishe ta kuma kace nace Mijin ta Bahari ƴan mata gare shi da yawa a garin nan." 

Buhari ya sheƙe da dariya yace "kut amma dai bani ne zankai wannan sakon bako? Ai na faɗa miki ko sakon gaisuwar ki ban taɓa faɗa mata ba, ke kinsan kishin Matata kuwa?" 
Husna tace "Allah dai ya haɗa ni da ita wata ran saina faɗa mata duk kula kulan matan da kake yi." 

Kan ya sake magana tayi gaba, Bahari ya zauna a kan bencin shi ya fara cin abincin sa.

            Yana tsaye yana kallon titi kamar me lissafa adadin motocin da ke wucewa, ya dogare kafar shi da Sandar da baya rabo da ita Husna ta ƙaraso wajen tayi masa sallama kamar yadda ta saba yiwa kowa.

"Ga abincin ka." 

Ta faɗa tana miƙa masa ledar hannun ta, bai waiwayo ba saida ta sake maimata wa sannan ya juyo, maimakon ya karɓi ledar abincin sai taga yaɗan tsaya yana kallon fuskar ta, ita ma kallon shi take saidai ita bata iya ganin asalin fuskar shi saboda tarin gashin daya cika fuskar, haka bata iya ganin asalin ƙwayar Idanun sa dan girar shi data cika da suma, gashin Idanun sa masu tsayi suka sake taimakawa wajen ɓoye Idanun sa.
"Ka karɓa mana." 
Ta sake faɗa tana miƙa masa ledar.

Kanshi ya ɗauke ya maida kan titi yaƙi karɓar abincin abun ya bawa Husna mamaki dan tunda ta fara bashi abinci bai taɓa kin karɓa ba, sai dai yaci kaɗan yayi jifa da sauran.
"Yau bazakaci ba?" Tayi masa tambayar da sanyin murya kamar wacce take magana dame hankali.

Daga bayan ta taji ance "A'a yau mutumin naki baya son abincin ne?" 
Husna ta juya su kayi ido biyu da Dan Hajja, tunda ta tsaya a wajen ɗan hajja ke kallon su daga kofar shagon sa ganin ta daɗe a wajen mahaukacin yasa shi tasowa yazo inda suke.

Kallo ɗaya Husna tayi masa ta watsar, sai kuma ta juya da ledar abincin tana jin zuciyar ta babu daɗi, Ɗan Hajja yabi bayan ta da kallo yana girgiza kai a fili yace "wallahi Ma'u saina Aure ki duk masifar ki saina shafe mazaunan nan." 

                Ran Husna a ɓace ta aje ledar Indo ta ta kalle ta tace "a'a yau be karɓa bane?" 
A takaice tace "e."
Sai kuma ta tafi wajen Sunday ta karɓi pure-water guda biyu takai masa, yanzu ya karɓa, ta saki Murmushi lokacin da ya warci ruwan a hannun ta ya fara sha, ta zuba masa ido sai yaɗan tsaya dashan ruwan kamar wanda aka tsayar sai kuma yaci gaba da sha, Husna nata kallon shi saida taga ya shanye duka sannan ta juya ta tafi.

A hankali sabo ya fara shiga tsakani Husna da mahaukacin da babu wanda ya taɓa jin ko tarin sa, ita kanta bata taba ganin ko haƙorin saba bare taji maganar sa.

.......Yau ranta a mugun ɓace ta fito tashar saboda kuɗin ta da take tarawa a wajen Ramma ɗazu da safe tace ta bata sai ce mata tayi, tayi hakuri Lirwanu ya karɓe su jiya, taso ta hanashi ya fara zuga mata zagi dole ta ɗauka ta bashi.

Kuɗin da take tarawa dan ta siyi hijabin yayin da za'ayi wannan shekarar shi ne ya karɓe, dama ya saba yi mata haka duk lokacin da ta tara kuɗi saiya bi baya ya karɓe. 

Saboda baƙin ciki Husna har kukan kuɗin saida tayi dan tasan ruwa tasha ke nan sai dai kuma ta nemi wani, wannan yasa ta fito tashar yau a tunzure, Bahari yazo harkan ta yana mata magana taƙi kula shi dole haka ya koma wajen saida fetir ɗin shi ya rabu da ita, dama ya san halin ta duk randa aka kunno ta daga gida bata kula kowa.

Duk halin baƙin cikin da take ciki bata manta da shiba tana hango sa ta zuba abinci takai masa ya karɓa yau bata tsaya taga ya fara ci ba ta baro wajen ruwan ma sam ta manta bata kai masa ba. 

Tana zama Indo ta fara bata labarin Gaje ta bada kuɗin Hijabin su ita da sa'a ɗan koli in yaje Kano zai taho musu dashi.

"Ma'u ki bada naki kuɗin ya siyo miki kinga in Sallah ta matso kuɗi zasu ƙara."

Wannan magana ta Indo ta sake tunzura zuciyar Husna, ita shi ke nan bata isa tayi abun kanta irin na sauran yara ba, komai ta ajiye sai Baba Lirwanu yabi ya karɓe, inta faɗawa Baban ta ya siya mata kuma har yayin abun ya wuce ba zai aiko mata dashi ba, sai dai in yazo garin yace tayi haƙuri mantawa yayi, wannan yasa gaba ɗaya ma yanzu ta dai na tambayar shi abu, gaba ɗaya Baban ta ya canja ya zama kamar wanda aka kaɗewa hankali a kanta kwata kwata baya ta tata sai in ya zo garin, yana tafiya kuma shi ke nan, gashi yanzu baya yawan zuwa sai ya dau dogon lokaci bai shigo ba.

Ita ce kullum gantalin talla amma bata da kayan sawar arziki, bata da kayan ado irin na sauran ƴan mata, tsakanin ta da Babanta kuwa dinki sai na Sallah shima kala ɗaya ne zai mata da hijabi ɗaya shike nan sai wata sallar kuma.
                
                Harta gama saida abincin ranta a cunkushe yake ta ɗauki fantekar ta da kanta dan Bahari bai sake zuwa inda take ba tun da yasan yau kozai kwana yana mata magana baza ta kula shi ba. 

Ta bayan masallaci tabi maimakon ta shige gida saita zauna a kan wani ɗan ice da aka aje a wajen saboda masu alwala, wajen ya daɗe da zame mata wajen faɗin duk halin da take ciki na damuwa duk lokacin da aka yi mata wani abu mara dadi nan take zuwa ta zauna tayi kukan ta ta more babu wanda ya sani, tayi suturun ta kamar wacce ta samu matsalar taɓin hankali, duk sanda tayi haka kuma sai taji zuciyar ta tayi sanyi.

              Yauma kamar yadda ta saba kwanunkan ta tasa a gaba ta kife kai akan cinyarta ta fara kuka, kuka take sosai duk lokacin da Indo ta bata labarin Gaje ta siya musu abu, ko tsautsayi yasa ta taɓa kayan Zahara tayi mata gorin uwa da rashin gata babu wanda ke faɗo mata a rai sai Mamanta da yayan ta, tasan da suna nan a tare babu abinda zai kawo ta nan garin, a hankali muryarta na rawa saboda kuka tace "Nasan yanzu kin manta dani ko Mama? kin daina sona, Yaya kaima ka dena sona ko?" 

Tayi maganar kamar tana kallon su, sai kuma ta yi murmushi tana share hawayen fuskarta tace "nima yanzu bana son ganin ku amma Inason ganin ƙanina da kika haifa Baba yace min yana wajen ki, Mama dan Allah karki bawa Baba shi, Nana zata dake shi Baba kuma zai kawo shi ƙyauye kamar ni, kinga nima tunda ya kawo ni bai zo ya mai da niba, kuma yasan kowa baya sona a nan sai Aramma da Ramma, Yaya kullum sai nayi talla na ɗebo ruwa, kaga yauma Baba Lirwanu ya karɓe min kuɗina da nake tarawa, yanzu shike nan bazan siyi hijabin yayi ba, nasan inna tara wani ma kwacewa zai yi....." 
Sai kuma kuka yaci ƙarfin ta ta kasa ƙarasa maganar.

            Motsin da taji a bayan ta yasa ta ɗago a ɗan firgice ta juya dan tasan wajen ba hanyar wucewar mutane bace, kuma ba lokacin sallah bane bare tace wani ne ya zo yin alwala.

Tana ɗago kai ta ganshi tsaye a kanta yana riƙe da Sandar shi..

da mamaki Husna ta mike tana kallon shi sai kuma ta tuna kuka fa take, da sauri tasa hannu ta share hawayen fuskar ta tace "me kazo yi nan?" 

Kamar yadda ta kwana da sanin ba magana zai mata ba haka shima baice mata komai ba, sai ƙare mata kallo da yake ta ƙasan ido.

Ko kaɗan Husna bataji tsoron ganin shiba haka bata kawo wa ranta komai ba ta ɗakko Naira Ishirin ta miƙa masa tace "gashi kaje wajen Sunday ya baka ruwa ɗazu mantawa nayi ban kawo maka ba." 

Bai Karɓi kuɗin ba haka bai bar wajen ba kamar yadda bai dena kallon taba.

"Yunwa kake ji?" Nan ma yayi mata shiru sai kallon ta da yake yi..
"To matsa naje na siyo ma ruwan da kaina." 

Ta faɗa tana barin kayan kwanunkan ta a wajen kamar wanda ya gane me take nufi saiya matsa gefe ya bata hanya ta wuce yabi bayanta da kallo sai kuma ya ɗauke kansa zuwa gefe guda, Allah ya taimake ta harta siyo masa ruwan ta dawo Aramma bai ganta ba dan ya hanasu bita wajen.

Saɓanin yadda ta barshi yanzu zaune ta same shi a inda ta tashi yasa kwanukan ta a gaba yana caccaka rami da Sandar hannun shi, harta iso wajen bai ɗago ba saida ta miƙa masa ruwan tana cewa "gashi to." 

Sannan ya ɗago ya amsa yana kallon gefe.
Ga mamakin Husna sai taga yau bai warci ruwan kamar yadda ya saba ba a nutse ya karɓa kamar wani me kan gado.

bata kuma duban inda yake ba ta dibi kwanukanta tabi ta gaban shi ta shige cikin gida, shi kuwa ya raka bayan ta da kallo.

          Tunda Ramma ta hango ta tana shigowa ta kewaye tasan yau ƴar riƙon nata sai a hankali, ita kanta ba'a san ranta take bawa Lirwanu kuɗin taba, to amma babu yadda ta iya, randa ta taɓa hanashi kuɗin shida Dije ba ƙaramin zagin cin mutunci suka yi mata ba, dan Lirwanu bai ɗauki zagin mace a bakin komai ba, gwamda ma ita yana ɗan raga mata saboda bata fiya shiga sabgar shiba bare ta hado su amma Zahara basa kwashe sati a gidan nan saiya zage ta saboda ita bata bashi kuɗin ta, duk jarabar shi saita gadama yake cin ficikar ta, ita kuwa tuni ya gurgunta ta ɗan jarin Alewar tata ma tuni labarin ta yabi iska dan ƴan uwanta harsun gaji da ɗora mata jari yana cinyewa.

Yanzu a gidan nan Allah ne gatan ta Husna da ƴan uwanta ne gatan ta, wannan yasa Dije ta sata a gaba da gorin rashin haihuwa kuma Zahara ke sake zugata a fakaice.

"Sannu Ma'u."

 Ramma ta faɗa, Husna ta aje kwanunkan a gaban ta, bata ce mata kala ba ta wuce ɗaki.

Ramma da kanta ta wanke kayan abincin sannan ta biyo ta ɗakin ta same ta a kwance a ƙasa tayi rufda ciki tace "Kiyi haƙuri Ma'u, in sha Allah zanwa Yaya Gali magana in ya shiga Binni saiya siyo miki hijabin."

Husna ta tashi zaune tana kallon Ramma tace "niban saki ba, ai bake kika ci kuɗin ba bare ki biya, ni kawai tunda nace ki dena bashi kuɗi na kinki denawa daga yau zan dinga aje abuna da kaina kuma bazan aje a gidan nan ba bare ya lalume ɗakin ya kwashe." 

Tana faɗin haka ta ciro cinikin yau ta bata ta fita ta ɗibi ruwa ta shiga banɗaki saida ta cire kayan ta sannan taga kwandon wankan nasu ma babu sabulu, dole haka ta sheka ruwan ta fito.

Zanin atamfa ashirille (Yadi/ roba) ta ɗaura tasa riga bulawus ta ɗaura kallabi tasa hijabin ta tun na sallar bara, hijabin ya dage mata sosai dan da kaɗan ya wuce rigar jikin ta, bata yi kwalliya irin ta sauran ƴan matan garin ba ta fito tayi waje, tunda Ramma taga haka kuma ta fasa kai niƙan kunun yamma dan tasan yau ba zata fita ba ke nan.

Husna na zaune a ƙasan kargon kofar gidan su har aka yi sallar la'asar rana ta fara ja, Aramma yazo shiga gida ya ganta zaune ita kaɗai yace "a'a Asma'ullahi yau babu Kunun yamma?"
"Eh Aramma sai gobe." Ta bashi amsa, ya gyaɗa kai yace "to a huta Allah ya kaimu goben." 

Ya shige gida, Aramma be daɗe da shiga gidan ba sai ga Baba Lirwanu fuskar nan tashi a cunkushe, Husna ko dar bata jiba dan yanzu bata wani tsoron shi.

"Ke ya akayi baki zuba ruwa a randar Zahara ba yau?" Ya dafa yana cogewa a gaban ta.
"Ka tambayi matan gidan zasu faɗa maka ita na fara cikawa randa aika santa bata ganin ruwa ta bari." 
"Ke dan ubanki ni kike cewa na tambayi matan gidan dan kin raina ni? To muje ciki saikin sake ɗebo wani danta juye na ban ruwan shanu a randar ta." 

Yana yin maganar yayi gaba Husna bata yi mamaki ba dan tasan Zahara ta saba yin haka saita ƙarar da ruwan randar ta sannan tabi na Shanu ta juye in Aramma yazo musu banruwa yaga babu dole yasa Lirwanu ya ɗebo, shi kuma inta dawo gidan ya rufe ta da zagi randa ƴan muguntar shi ke kusa kuwa sai tasha mari.

Husna na ganin ya shige gidan tayi tafiyar ta ƙwalam ɗin yamma tana faɗin "wallahi bazan ɗebo ba duka ne ka daɗe baka daka ba, mara imani kawai." 

          Lirwanu ya ɗauka ta shigo ta ɗauki jarakunan saida yaji Aramma ya fara kiran shi ya zo ya samo ruwan da zaiwa shanu banruwa sannan ya gane bata shigo gidan ba.

A zafafe ya fito, Zahara na masa maganar ya bata kuɗin magin miya ya sauke mata haushin da yake ji ta hanyar luƙa mata zagi.
"Ai kuwa yau kome Aramma zaimim sai naci uban Ma'u a gidan nan." Lirwanu ya faɗa yana fita daga gidan zuciyar shi a sama.

......Tunda aka idar da sallar la'asar yake kallon inda take zama ta saida Kunun yamma amma sai be ganta ba har rana ta kusa faduwa babu ita babu dalilin ta.

Shi kansa ba zai iya tantance yanayi ko halin da yake ciki saboda rashin ganin Husna ba amma tabbas yasan baiji daɗin rashin fitowar tata ba.

Garba ne ya ganshi yana ta zagaye a tsakanin shagon Sunday da inda su Husna ke zaman saida kunun yamma, tsam ya miƙe yaje ya siyo masa ruwa kamar yadda yaga Husna nayi masa amma ga mamakin sa daya bashi ruwan sai yaga yaƙi karɓa, daga karshe ma wajen ya bari gaba ɗaya ya koma can kusa da majalisar Dan Hajja ya zauna yana jijjiga kai kamar yadda yake yawan yi indai yana zaune.

Yana zama a wajen babu jimawa majalisar ɗan Hajja ta cika da abokan shi suka fara shewa da hira irinta Samari.

"Kai ɗan Hajja yau bazaku yi mana kunun yamma bane? Ga mahaukacin ku nan yazo ya zauna ata bayan mu ina kallon shi yana zagaye inda taka ke zama." 

"Wai Ma'u kake nufi? Ai Gambo Ɗan Hajja ɓatawa kanshi lokaci kawai yake yi, duk matan garin nan ya maƙale wa Ma'u tana masa wulaƙanci, kullum fa sai yaje kiranta amma bata zuwa, wallahi bana jin ma ta taɓa yi masa magana." Wani daga cikin Samarin ya tari numfashin wanda yayi maganar farko.

"Kaifa banza ne, yama zaka haɗa Ma'u da matan garin nan? Ai kana ganin Ma'u kaga matar manya, haba Malam kai kaga tudun bayan ta kuwa? in tana tafiya Uhmmmmm!" 
Ɗan Hajja yayi wani murmushin iskanci yana shafa kai yaci gaba da cewa "tunfa bata ji Maza ba ke nan malam? Wannan in namiji ya buɗe ta Hmmm." 

Ɗan Hajja ya ƙarasa maganar yana wani kaɗa kai cikin nishaɗi, sauran matasan wajen suka kashe da dariya.

"Yanzu dai haka zakayi ta binta tana ma wulaƙanci ke nan? Wani a cikin su ya jefa masa tambayar.

"Ina ai ina faɗa muku Kakarbaɗi (shekara mai zuwa) ya wannan na Aure ta, wancan gidan dana gama na Ma'un Dan Hajja ne, Malam zan sha shagali fa." 

Gambo yace "taɓ ai kuwa saika dage ka shawo kanta tunda bata kula Samari, ni Bahari ma da farko da naga suna shiri da ita na ɗauka santa yake sai daga baya na gane kawai mutumci suke."

Ɗan Hajja yace "ai da farko nima na ɗauka haka ne harna fara yi masa shirin wulaƙanci sai kuma naga e.....ita ta wajen nawa ma babu wani abu a tsanin su. Ina so naje na gaida Kakar ta ma anjima kaɗan na ɗan bata wani abu, Kusan kafar ta na riƙe kuma tace min karna damu zasu bani ita, amma Ogan sama ya kira ni ɗazu yace akwai wanda zai zo muje mu duba masa hanya anjima, akwai kayan sa za su wuce cikin satin nan, kunga dole a soke zuwa gaida tsohuwa."

Sauran ƴan majalisar suka zuba ihun murna suna kiran "sai ɗan Hajja sai Foma ɗin mu saika Auri Ma'u malam zamu sha shagali." 

Duk wannan kirarin suna masa ne dan sunji ya ambaci aikin Oga sama dan sunsan indai yayi aikin ogan sama suma suna wata yawa, dan kowa saiya samu wani abu.

                Ogan sama mai gidan Dan Hajja ne, a sanin su yana shigo da buhhunan Madara da sauran kayan masarufi ta marauniyar hanya, ta Niger yake shigo da kayan shi ya biyo dasu ta ƙyauyu kan Jigawa saboda gudun custom da sauran jami'in tsaro, ogan sama yana da yaran dake duba masa hanya a kusan ko wanne ƙauyuka na Jigawa har kayan shi su tsallake iyaka, kuma sosai yake biyan su da manyan kuɗaɗe naban mamaki, duk sanda ya shigo da kaya suka wuce lafiya suna samun alheri, Dan Hajja na cikin yaran shi da suke masa aikin duba hanya, a garin kuma babu wanda yasan yana wannan aikin sai abokan shi na kusa irin su Gambo....