24
by @aishatouuu
_Aishatou_
***
_________________
Suna zaune suna hira har baƙon ɗan Hajja yazo sukai waya ya ce gashi a tasha ɗan hajja ya daga masa hannu ya ƙaraso inda suke, shima saurayi ne matashi ba zai wuce sa'an ɗan Hajja ba akan mashin ɗin sa Bajat yazo a gaban su Gambo Ɗan Hajja ya fara masa magana akan aikin da zasu yi shi kuwa bakon ganin su Gambo a wajen sai ya basar, ganin Dan Hajja nata magana a gaban abokan shi yasa abokin tafiyar tasa yace "mu ɗan yi magana a sirri mana."
Ya faɗa yana yin gaba ya tsaya a jikin bishiyar da yake zaune tun ɗazu.
"Kai baka da hankali ne kake maganar a gaban mutane? In wani a cikin su ya zagaye ya faɗawa jami'an tsaro fa? da alama Oga baima kashe ɗin aikin mu sirri bane ko?"
Ɗan Hajja yayi murmushi yace "karka damu Abokina waɗannan da kake ganin su kaf na hannun dama ta ne, ko kuɗi ka basu bazasu faɗawa kowa wannan aikin nawa ba."
Kallon baka da hankali bakon yayi masa yace "Gaskiya baka da tunani kai kasan halin mutane kuwa akan kuɗi? to kai banda rashin wayo ma ya zaka bude wa mutane hanyar neman ka, ai sai suma baƙin ciki."
"Nace karka damu bani da matsala dasu dukan su a ƙasa na suke ci, amma babu matsala zan dena faɗa musu shine nan?" Matashin ya bi Dan Hajja da kallon kai wawa ne, suna juyawa zasu tafi saurayin nan yaga mahaukaci zaune a gefan su yana gangadi ɗan jim yayi yana kallon shi sai kuma ya dubi Dan Hajja yace "wannan fa?"
Dan Hajja ya kalli mahaukacin saida ya yiwa wancan dariya sannan yace "wai kai meye duk ka wani tsorata ne? Bafa a shiga dawa dan ƙarya ina faɗa maka aboki na a shirye nake, wannan kuma kamar yadda ka gani mahaukaci ne ko magana bayayi ko mutum ka kashe a gaban shi saidai ya kalle ka ya wuce shike nan kaci banza ba zai wata magana ba, kaga zo muje dan Allah muna bata lokaci."
Ɗan Hajja ya faɗa bai tsaya jin mai zaice ba yayi gaba, shima kan mashin ɗin sa ya haye suka yi cikin gari da mugun gudu suka ɗauki hanyar da zata kaisu Kabawa suka danna cikin jeji suna gudu kamar zasu tashi sama.
Bayan tafiyar su ɗan hajja ya daɗe a wajen a zaune har saida aka fara kiran sallar Magarba sannan ya tashi ya mike titi dama tunda ya zo garin Magarba nayi yake miƙe titi ya tafi shike nan kuma sai gobe wannan yasa mutane ke ɗauka a makaranta yake kwana.
*****Husna bata koma gida ba sai bayan sallar isha'i, tana shiga gidan Ramma tazo inda take da sauri tace "yau karki shiga wajen mu Lirwanu na fakon ki kema Ma'u waya kaiki kin ɗebo ruwan bayan kisan halin shi."
Ramma na rufe baki ya fito daga wajen shi, Husna tayi kamar bata ganshi ba tayi lungu Dije data jiyo maganar Aramma.
"Kin fara zama Munafuka ko Ramma?" Lirwanu ya faɗa yana bin bayan Ma'u da sauri, bata ƙarasa shiga lungun ba yayi tsalle ya ciro tsimagiyar maina yayi kanta zai daketa ta taka da gudu ya rufa mata baya suka fara zagaye cikin gidan, yana binta zai daka tana zillewa yana dura mata ashar, Aramma ya fito kanshi ko rawani babu yana kiran.
"Kai Lirwanu baka da hankali ne? Meta maka da daran nan? Ba magana nake maka ba? Bazaka dena binta ba?"
Lirwanu bai saurari Aramma ba Husna tayi wuf ta fice ta kafar gidan su Naja yabi bayan ta da gudu, ta fito waje tacan kofar gidan ya biyo ta dai-dai duhuwar Mainar ƙofar gidan yaji an taɗe masa ƙafa yayi gaba zai faɗi aka riƙo shi ta baya, kanya dawo daga firgicin muguwar faduwar da yaso yi yaji an kifa masa marika masu azabar zafi ta hagu da dama, dummm......yaji kunnen sa da kansa sun ɗauke, kanya dawo dai-dai aka shaƙe masa wuya a cikin duhun ya buɗe baki zai yi ihu aka kiɓa masa naushi a baki saida yasha maruka masu ƙyau sannan akayi jifa dashi kansa ya bugu da jikin bishiya baki a kunbure babu damar ihu, yana jin an sake shi ya kwasa da gudu ya koma cikin gida dafe da bakin shi.
Matan gidan na tsaye cirko cirko Aramma ya fita neman su ta Kofar gida Lirwanu ya shigo da gudu ta gidan su Naja ɗakin Dije ya shige ya turo ƙofar ya rufe jikin shi na rawa.
Dije da matan shi suka rufa masa baya.
"Kai Lirwanu buɗe ƙofar mana, lafiya kuwa? Ina ita Ma'un?" Dije ke faɗa tana buga kofar Lirwanu yaƙi budewa.
Fir Lirwanu yaƙi buɗe kofa saida Aramma ya zo yayi masa magana sannan ya buɗe yana haki.
"Lafiyar ka kuwa Lirwanu ina Asma'ullahin?"
Aramma yayi masa tambayar yana duban shi hannu dafe da baki, Saida Aramma ya sake masa magana sannan da ƙyar yace "wallahi Aramma nayi gamo dan Allah kamin addu'a gamo nayi da sheɗanu dubi yadda suka fasa min baki suka shaƙemin wuya Aramma nasha marin da ban taɓa jin irin sa a duniya ba."
Yadda Lirwanu ke jero maganar yasa Zahara komawa da baya tana kumshe dariya a ranta tace "wallahi kome yasa Lirwanu wannan tsoratar zan so na ganshi." Sai kuma tace "alhakin zagin iyayena da kayi ne ɗazu Allah ya saka min."
Duk hasken wutar Shekarau ya gaza ɗin daya haske ɗakin Dije saida Aramma ya sake kunna tochligh ɗin sa ya haske fuskar Lirwanu da tayi fushi lokaci ɗaya, ga kwanciyar yatsu miyar nan a ko wanne kunci hagu da dama bakin sa kuwa tuni ya haye yayi suntun ta gefe kuma ya fashe, haka wuyan rigar shi inda aka shaƙe sa ya cukwikwuye.
"Subhanallah kaida waye haka Lirwanu? ina ita Asma'ullahin?"
"Aramma bansan inda tayi ba ina binta a baya muna fita ƙofar gidan su Amadu naji......shuuuuu...anyi sama dani an min ɗaukar Amarya kan a sauke ni ƙasa saida akamin marika huɗu a jere, wallahi saida idona ya makance saboda azaba, zan yi ihu naji kummmm....an shaƙe wuyana an dagani sama an sakarmin naushi a baki sannan akayi jifa dani na faɗo kasa tim."
Ramma ta koma baya tana rufe baki saboda dariyar data taso mata dan yadda Lirwanu ke fasalta yadda akayi dashi dole yasa ka dara, shi kansa Aramma saida ya murmusa sai kuma yace "babu wani sheɗanu ko dai faɗa ya haɗa ka da mutanen ka can, ni bari na duba inda Asma'ullahi tayi kada tsoro yasa tayi wani wajen."
Aramma yayi maganar yana ficewa daga gidan.
Dije ta dubi Lirwanu tace "kaima me yasa ka bita har waje? Baka bari saita kwanta ka ritsata kayi mata duka, shegiyar yarinya zata ja a illataka a banza, yanzu haka bayin Allah nan (aljanu) ka taka suna zaune, bari na baka hayaƙi kayi, ke Zahara ku bani garwashi." Dije ta faɗa tana sake duba fuskar Lirwanu.
...... Husna kuwa tana gudu ta juya taga baya binta kawai sai tayi tafiyar ta Dandali dan har an hura wutar kara yan mata sun fara gaɗa.
Indo ta fara nema saida ta kutsa kai cikin ƴan gadar sannan ta ganta a cikin su tana rawa, bata tsaya a wajen ba ta fita, tana zuwa inda suke zama da Indo mamaki ya kashe ta dan shi ta gani a zaune yana babbuga Sandar shi a ƙasa, Husna bata ji tsoron ganin sa ko tunanin meya kawo sa wajen ba ta cire takalmin ta ta zauna a gaban shi tana murmushi kamar mai magana dame lafiyyan tunani tace "kaima daman kana zuwa Dandali?"
Tafa san ba zai amsa ba amma sai taci gaba da cewa "ai dai nasan kana jina ko bakayi magana ba" Ta faɗa tana kallon shi kamar me jiran ya bata tabbacin haka.
Sai yanzu ya ɗaga kanshi ya dubi fuskarta, ita kuma ta kalli fuskarshi data cika da gashi tace "nifa bana son naji ana cema mahaukaci nasan fa kai ba mahaukaci bane." Sandar da yake dokawa a ƙasa ya ɗan tsaya da bugawa yayi kamar yana sauraren ta, ita kuma hakan da taga yayi saita sake zagewa tace
"Ai nasan baka da lafiya ne, kuma Mamana tace duk wanda bashi da lafiya addu'a ake masa ya warke, kaima kana so na rinƙa yi ma addu'a?"
Yanzu ma shiru babu amsa haka kuma bai saka Husna yin shiru ba taci gaba dayi masa surutu.
"Kaga ni inada Yaya sunan shi Baffa yana can Kano, shida Mamana suka tafi shike nan ban sake ganin suba."
Sai kuma tayi shiru kamar me tunani muryarta a hankali tace "dan Allah na rinƙa kiranka Yaya kana so? Tunda kaga yanzu bani da Yaya shike nan saika zama sabon Yayana ka yarda?" Shiru babu amsa, tace
"Shike nan ma nasan ka amince daga yau ka zama Yayana duk wanda ya sake cema mahaukaci zance masa sunan ka Yayan Husna."
Husna ta faɗa tana murmushi yayin da shi kuma ya tsaya kallon ta da rufaffun idanunsa.
"Ma'u.....ke Ma'u..." Taji muryar Indo tana ƙwala mata kira, ta juya sai taga tana tahowa inda suke Indo bata kula da waye a zaune ba saida ta ƙaraso.
"Ke Ma'u dama keda mahaukacin nan ne kika zauna a gaban shi ko tsoron sa bakya ji? Allah kefa wani lokacin baki da wayo sai kinje wata ran ya miki duka, ki taso muje Aramma ne yake ta neman ki tun ɗazu."
Indo ta faɗa tana tsayawa daga bayan Husna dan ita tsakanin ta da Allah tsoron shi take ji fuskarshi mai gashi kuwa tafi komai bata tsoro.
"Dalla Malama ba mahaukaci sunan shi ba daga yau sunan sa Yayan Husna."
Ta juyo zata yi masa magana taga yana kallon ta.
"ko yaushe ya ɗago oho?"
Tana masa murmushi tace "kaga Aramma yana kirana dama fa Baba Lirwanu ne zai dake ni na gudu bai kama niba."
Sai kuma ta mike tsaye tace "Na tafi Yaya saida safe." tayi maganar tana juyawa Indo ta biyo ta a baya tana mata masifar danme zata je ta zauna kusa da mahaukaci.
"Wallahi ma'u ki kiyayi kanki Hmmm! Haka kawai kije ki zauna kina masa zance sai kace wani me hankali to wallahi sai kinje wata ran ya yi miki illa, kina ganin shi kullum yana yawo da sanda kamar Bafulatani."
Aramma ya gano Indo da Husna suna tahowa tare ya sauke ajiyar zuciya, dan harga Allah yaji tsoron kar tayi wani wajen saboda gudun duka.
"Indo a ina kika gano ta?"
Husna ta riga Indo magana da cewa "inda muke zama naje na zauna."
"To sannu A'ishatu da kika samo min ita na gode miki." Indo tayi murmushi, Aramma ya cewa Husna suje gida Indo ma ta biyo su suka taho gaba ɗaya.
Lirwanu yasha hayaƙin korar aljanu sai tilliƙa tari yake, Ramma tace "ko a ɗora ma ruwan zafi kayi dundumi sai kasa rof wajen bugun zai saki." Dije ta gwasale ta da cewa
"Wani dundumi kuma abun iska ne fa kafin safe zai baje ai sunji hayaƙi."
Zahara kuwa daga Sannu bata sake cewa komai ba ta kama bakin ta ta tsuke.
Hankalin Husna kwance suka shigo cikin gidan tasan ta tsira tunda Aramma yana kusa wannan yasa har suka gama hirar su ita da Aramma bata da fargaba, sai can dare Aramma yasa Indo a gaba ya raka ta har gida, yau Husna bataje ɗakin Ramma ba dan acan take kwana in Lirwanu na ɗakin Zahara, ɗakin su da Indo nada da yanzu ita kadai take kwana aciki ta shige ta kwanta, yau ko fitilar ma bata nema ba a duhun ta laluma ta karkade gadon karar ta tayi kwanciyar ta.
Washegari Lirwanu ya tashi baki ya sake haye wa danfa ya daku a wajen, fuskar shi duk ta kukkunbura, daga karshe dai dole shawarar Ramma ta jiya aka ɗauka Dije da kanta tayi masa dundumin ya shafa rof a wajen, tanayi masa gashin tana tsinewa Husna dan tace ita ce taja Aljanu suka buge shi, Aramma kuwa daga sannu bai sake bi takan suba ya fice.
Koda suka haɗu da safe lirwanu be yiwa Husna magana ba saboda ta kansa yake.