GADAR TSAUTSAYI 26
by @nusybee143
Page 26
Shiru ya yi ba tare da ya ba ta amsa ba, cikin ɗaga murya ta ce"tambayarka nake yi Arnold!dama yaudarata kake yi?ba musulunta ka yi ba dama?
Har ka sa na aure ka?ka bani amsa!"
Kallonta ya yi ya watsar ba tare da ya yi magana ba,sai kuma ya miƙe zai bar wajen, cikin gushewar hankali Shaheeda ta shaƙo masa wuya tana faɗin "ka cuce ni,ka cutar da ni,ka halaka min rayuwata,ka mayar da ni inda ka ɗauko ni,ba zan sake kwana da kai a cikin gidan nan ba,na tsane ka,na tsane ka...."hankaɗe ta ya yi,ta yi baya taga-taga, amma kafin ta faɗi ya yi saurin riƙo ta, cikin idanunta yake kallo,a hankali ya furta "a tsawon watannin da muka ɗauka muna rayuwa tare da ke a cikin farin ciki a gidan nan kowa yana bin addininsa ne,don haka yanzun ma za mu iya cigaba,kowa ya cigaba da bin addininsa,amma tabbas na aure ki don ina sonki,kuma zaman aure yanzu muka fara da ke,ya rage naki ki karɓi addinina ko ki cigaba da bin naki,amma zama da ni yanzu kika fara"ya zaunar da ita a gefen gadon dake ɗakin sannan ya juya ya fice daga ɗakin
Cikin tashin hankali mai tsanani ta bi shi da kallo,kukan ma da take yi tuni ya tsaya sai sauke ajiyar zuciya da take yi,a hankali hawaye suka zubo mata,tana tuna maganar yayanta Muyassar
"Ya musulunta ne don Allah ko ya musulunta ne don zai aure ki?"
Ya yaudare ta kenan?in dai haka ne ai babu aure a tsakaninsu yanzu,tuni kuka ya kubce mata,take ta fara wata iriyar nadama,ta gudu ta bar abbanta da yake bala'in sonta,ta bar Ummeenta da ita kaɗai ta mallaka,ta bar masoyi na ƙwarai Muyassar ta biyo maƙaryaci, mayaudari, munafiki kuma azzalumi,to yanzu ya zata yi?
Da wanne ido zata kalli iyayenta a lokacin da ta koma gare su?
Da wanne idanu zata kalli Muyassar masoyinta, wanda ya so ta so na gaskiya,ya ƙaunace ta,ya zama gatanta?
Take ta fashe da kuka sosai, ta jinginar da kanta jikin bango tana rera kuka zuciyarta cike da nadama da danasani
Bata sake saka Arnold a idanunta ba,sai bayan kwana uku,a lokacin da aka ɗauki azumin farko,tana idar da sallar la'asar ya shigo yana bin ta da kallo
Kallonsa take yi itama,bata yi mamakin kwanakin da ya ɗauka baya nan ba, dama wani lokacin idan aiki ya riƙe shi a company yana yin waɗannan kwanakin,amma su kan yi waya,sai dai wannan karon ba su yi wayar ba saboda ta kashe tata wayar
Kallonta yake yi cikin kulawa yana murmushi,da alamu ma ya manta abin da ya faru kafin ya fice ya bar gidan
Cikin kulawa ya ce"ba ki da lafiya ne?ko dai baby ne yake wahalar min da ke?"banza ta yi masa,bai yi fushi ba ya miƙe ya tafi kitchen,jum kaɗan sai ga shi ya dawo hannunsa riƙe da Plate mai ɗauke da wani nau'in wainar kwai da dankali,yana zuwa ya ajiye a gabanta,ya sa cokali ya ɗiba ya kai bakinta
Kallon abincin ta yi ta ɗauke kai, murya ƙasa-ƙasa ya ce "ki ci abinci mana,kin san ya kamata ki rinƙa yawan cin abinci fa"
Tana kwance kai tsaye ta ce"na gaya maka azumi nake yi"
"Azumi?
Azumi kika ce?
Ba na gaya miki ba za kiyi azumin nan ba?
To ko ki ci abinci ko ranki ya ɓaci"
Kai tsaye ta dube shi ta ce"ɓacin rai kuma ai na gama tunda na aure ka,ka cuce ni ka yaudare ni kuma ka zalunce ni,ka tashi ka ba Ni waje kafin raina ya ɓaci na aikata duk abin da ya zo min kaina,tashi ka matsa nesa da ni"
"Duk abin da za kiyi ban hana ki ba,amma ba ki isa ki cutar min da ɗana na zuba miki idanu ba
Tunda kin nuna ba kya ra'ayina ba zan yi miki dole ba,amma za ki haihu ki ba ni ɗana sannan ki kama gabanki,a lokacin da kike ɗauke da cikina ya zama dole ki kular min da ɗana har ya zo duniya
Don haka ki tashi ki ci abinci kar ki bar min ɗana da yunwa"
Ko kallon banza ba ta yi masa ba, hankalinta ma yana wajen tunanin yadda zata yi da wannan ƙaddarrarriyar masifar da ta gayyatowa kanta ta auren Arnold,shi kuwa Arnold ganin ta yi masa banza ya sa zuciyarsa ta yunƙuro,tun ba yanzu ba ta karantar da shi abubuwa da yawa a addinin musulunci,har da wanda yake karya azumi,don haka bai yi wata-wata ba ya afka mata a lokacin
Duk yadda ta so ta ƙwaci kanta hakan ya gagara,dama gashi ta galabaita,kuma ba ƙarfin su ɗaya ba,ya gama abin da zai yi ya ɗaga ta zaune,ya ce"ki ci abinci ki daina wannan kukan,amma na yi miki alkawarin duk lokacin da kika yi azumi sai na karya shi,sai anjuma "ya fice daga ɗakin ya koma parlour
Tun daga ranar bai sake barin ta ɗauki azumi ba,da kanshi yake zaunar da ita da safe ta ci abinci,idan ta ƙi kuma ya mu'amalance ta ta ƙarfi,ya sake ba ta abinci sannan ya fice daga gidan
Sai abu na gaba da ya ɓullo ganewa da Shaheeda ta yi yana shaye-shayen giya, ƙwayoyi da sauran kayan maye,shisha kuwa a parlourn yake baje ta ya yi ta zuƙar abinsa,bata taɓa damuwa ba,ko nuna masa ta damu da hakan
Akwai abin da ta fuskanta game da ƙwayar da Arnold yake sha,tana saka masa bacci sosai a duk lokacin da ya sha ta,kuma ko da a ce yana cikin damuwa ya sha yana kwanciya bacci idan ya tashi zai tashi zuciyarsa wasai,ya yi ta harkokinsa cikin farin ciki
Daga haka zuciyar Shaheeda ta kwaɗaita mata shan ƙwayar don ta samu ta yi baccin da damuwa take hana ta, sai ta kwashi kwanaki masu yawa damuwa bata bar ta ta yi bacci na cikakkun awa biyu ba,don haka kanta tsaye ta nufi inda yake ta ce
"Wannan ƙwayar da kake sha take saka ka bacci nake so ka ba ni"
Kallonta ya yi ya ce "ba kya samun bacci ne?"
Bata yi magana ba sai jinjina kai,babu musu ya ɗauko ya miƙo mata
Da farko ɗaya ta fara sha, ganin ta fara jin jiri ya sa ta kwanta, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci bacci mai nauyi ya ɗauke ta
Daga lokacin Shaheeda duk lokacin da damuwa ta ishe ta sai ta ɗauki ƙwayar ta sha,tun ɗaya tana iya kwantar da ita har ta daina, ta koma shan biyu
A wannan tsukin ne cikinta ya kai watanni shida,kuma a waɗannan watannin ko sau ɗaya bata taɓa yarda ta haɗa jiki da Arnold ba,shima kuma tunda ta haƙura da yin azumi ya daina kusantarr ta ta dole
Tuntuni suka raba ɗakin kwana,yana ɗakinsa itama tana nata
A wannan halin ne tana zaune a ɗakinta ta ji muryar Arnold da kamar muryar mace,da sauri ta leƙo tana kallonsu gabanta yana faɗuwa, yarinyar da ganinta baturiya ce yar asalin ƙasar Spain ɗin,kayan da suke sanye a jikinta ya tabbatar da wacece ita
Da sauri kuma a firgice ta ƙarasa inda suke tana kallon yarinyar idanunta a rufe da kishin da har yanzu bai rabu da zuciyarta ba, dukkansu tsayawa suka yi suna kallon ta, cikin harshen dutch ta ce"Arnold wacece wannan?"
Kai tsaye ya ce"ita ɗin budurwata ce,akwai wani abu ne?"
Shaƙe shi ta yi ta ce "budurwarka?ko karuwarka?
Ta fice min daga gida ko na illata ta,ta fice min ko na kashe ta!"
Arnold ya ƙwace wuyan rigarsa yana aika mata da wani kallo ya ce"da gaske kike?
Ta fice miki daga gida?ko kin manta ba wajenki ta zo ba?wajena ta zo?
Ai ba don ke ta zo ba, don ni ta zo,ta zo ne don ta yi min abin da ke ba kya yi min,don haka ba ki isa ki hana ta shigowa ba"ya ture Shaheeda gefe ya kama hannun budurwarsa da sam bata ma san me suke cewa ba kasancewar ba da Spanish suke magana ba suka shige ɗakinsa
Abubuwa suka sake taruwa suka yi wa Shaheeda yawa,ga damuwa da ta yi mata yawa amma bata da mutum ɗaya da zai ba ta shawara,kullum cikin kuka da tashin hankali,a yanzu Arnold ya daina damuwa da ta ci abincin ma ko ba ta ci ba, tuni shan ƙwayoyin saka baccinta suka ƙaru,ta zama kusan kowanne lokaci tana cikin shaye-shayen ƙwayoyin don ta hana kanta damuwa
Cikinta yana da watanni bakwai yanzu, gaba ɗaya ta rame ta yi baƙi sosai, tamkar ba Shaheeda yar ƙwalisar Ummeey ba,sam fara'a da walwala sun kaurace mata, dama ita sam ba shiga sabgar mutane take yi ba, mijinta kawai ta sani,ko da yake saka ta interaction da abokansa dama can bata wani sakar musu fuska ballantana yanzu da ta san wanene ainihin wanda take kallo a matsayin mijin nata
A yanzu ta sake tabbatarwa Arnold ba musulmi bane,kuma addinin nashi na Christianity ɗin ma ba damuwa ya yi da shi ba,don ita idan banda ya faɗa ma cewa zata yi bashi da addini
A yanzu Arnold ya daina ɓoye mata shan giya ko neman matan da yake yi,dama tuntuni ya daina attempting ko da taɓa ta ne kamar yadda ta buƙata,amma idan ya ga dama zai kawo ko ma wacece ya so,su yi abin da suka ga dama ko da a parlournsu ne,ba a ɗaki ba, sai dai ita ta tashi ta ba su waje
A baya Shaheeda tana cikin tashin hankali da taraddadin abin da zata je ta gayawa iyayenta game da wannan auren kasadar da ta yi wanda ya zame mata GADAR TSAUTSAYI da ya jefar da ita zuwa ga kwatamin dana sani,da wanne idanu zata kalli Ummeey da abbanta?akwai mutanen da suka so ta,suka nuna mata ƙauna,ta ba su kunya, irin su Muyassar,akwai mutanen da irin wannan faɗuwar tata suke jira,irin su mahaifiyar Muyassar, kakarta da sauran matan gidansu,ta san wadannan mutanen sun yi farin ciki sosai, Allah sarki!ko a wanne hali mahaifiyarta take ciki?
Hawaye suka zubo mata,ita kaɗai Ummeey ta haifa,bata da wata sanyin idaniya sai ita,ta san ta yi kukan rashinta har hawaye sun ƙare mata,a fili, cikin harshen Hausa da ta daɗe bata yi ba,ta ce "Allah sarki Ummeeyna!
Ki yafe min!ki yafe min Ummeey!!na san alhakinku ne yake ya bibiya ta har yanzu,na san alhakinku ne ya hana ni jin daɗin rayuwa,na bijire muku, kuma gashi a ƙarshe ina karɓar sakamako mafi muni da ciwo,ku yafe min"ta sake rushewa da kuka sosai tana dafe kanta,ita kaɗai ta san yadda take ji,da mummunan halin da take ciki
Tana nan a zaune,bata san ma lokacin sallar maghriba ya yi ba, sai duba agogo ta yi ta ga lokacin sallar isha'i ne,ta miƙe jiki a mace ta nufi ɗakinta don ta yi alwala ta yi sallah
Ko da ta idar da sallar ma kwantar da kanta ta yi a jikin gadonta tana cigaba da zubar da hawaye, idanunta sun kaɗa sun yi jajir,gaba ɗaya ji take yi ta rasa hope, tunaninta ya koma kan yadda zata bar Spain ta koma ga iyayenta ta nemi yafiyarsu
Motsin da ɗan cikinta ya matsa mata sosai da shi ne ya sa ta miƙe cikin sanyin jiki ta nufi kitchen don samarwa kanta abin da zata ci ko babu yawa,don rabonta da cin abinci tun karin safe, shima kuma ɗan kaɗan ta iya ci
Yanzun ma da ƙyar ta samu ta sha tea ta sake komawa parlourn ta zauna tana tunanin irin rayuwar da ta yi a baya,da yadda ta jefa kanta a kogin danasani
Tana nan zaune Arnold ya shigo yana tangaɗi,da alamu giya ya sha ya yi mankas,ita mamaki ma abin yake ba ta,zai ƙaraci shaye-shayensa sannan ya hau titi ya ce zai yi driving
Tana ta kallonsa yana ta tamɓelensa a tsakar parlourn kafin ya tunkare ta,kamar ba mai ciki watanni bakwai ba ta yi wuf ta matsa,ya sake tunkaro inda take,ta sake matsawa tana watsa masa wani mugun kallo,kafin ta ce "wai menene haka?
Me giyar ta gaya maka yau ne da kake zuwar min haka?
Bana so!"
Yana tangaɗi ya ce "na gaji!na gaji da hana ni kanki da kike yi, Fatima bana buƙatar wata mace a duniya idan ba ke ba,don haka yau dole ki ba ni haɗin kai"
Tsaki ta yi ya juya zata shiga cikin ɗakinta,ya damƙo ta, tuni ta manta da wata kasala da nauyin jiki ta fara yunƙurin ƙwatar kanta, ganin ba zata iya ƙwatar kanta ba ya sa ta ɗaga flower vase ta rotsa masa a kai,tuni jini ya wanke masa kai,ita kuma ta samu ta gudu zuwa ɗakinta
Sai da ta rufe ɗakin sannan tsoro ya ɗarsu a ranta,ganin jini yana gudana akan Arnold, jikinta ya fara rawa,ta samu waje ta takure,ta zauna tana tunani
A haka bacci mai nauyi ya ɗauke ta,mai cike da mafarki iri-iri marasa daɗi
Can cikin baccinta ta ji ana buga ƙofar,a firgice ta tashi zaune,da gaske ne bugu ne,kuma muryar mutane take ji,da alamu ma ba iya Arnold kaɗai bane, tsoro ya ɗarsu a ranta,ta leƙa ta window a hankali
Gabanta ya faɗi ganin ƴan sanda,ta yi saurin saka hijabinta ta fita a tsorace tana kallonsu
Ɗaya daga cikinsu ne ya gaishe ta cikin harshen Spanish, sannan ya ce "Madam mijinki ne ya yi hatsari a mota yanzu,mun yi gaggawar kai shi asibiti,a can yana ta kiran sunanki,a takaice dai yanzu, mijinki Arnold Liam Lambert yanzu ya riga mu gidan gaskiya,amma kafin ya rasu mun ga ciwo a kanshi,kuma ya tabbatar da cewa ke kika ji masa, don haka yanzu za ki bi mu zuwa office ɗinmu,za mu tsare ki har sai an gama bincike,sannan sai mu ga abin da ya dace"
#Nusy_bee