GADAR GIWA... (Toro ke buga mata ganga)

Gadar giwa

by @auntyindo

"Wai me ye damuwarka ne Yaya?"
a ɗan zafafe Hamdan ya ɗago yana zuba masa wani shegen kallo fuska a murtuke, cikin dakakkiyar murya ya ce "Wace irin tambaya ce wannan ta raini?" 

Zama Sabran ya yi yana cewa  "Yi haƙuri, ina nufin kana cikin damuwa"
"Ƙarya kake!"  Hamdan ya ba shi amsa kai tsaye,  ɗan murmushi yayi kafin ya ce "Ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba kana cikin damuwa,  amma ba komai,  saboda na damu da kai ne shi ya sa ma nake tambaya, nima karambanina ne ya kaini"

Ɗan jim! Hamdan ya yi yana nazartar kalamin ƙanin nasa, sosai maganar ta daki zuciyarsa kuma ta sa shi yin laushi lokaci guda, sai dai ba zai bari hakan ya zama lagon gane abunda ke ɓoye a rayuwarsa ba.

Ƙara haɗe fuska ya yi gami da cewa "Ka rabani da Tsugudidin nan naka Sabran!, wai ina ma aikin da na baka ne? har yau fa baka taɓa min magana akai ba  sai akan abunda kawai hasashen gaibu kake yi"

"Akan maganar na zo, sai kuma na ga ya kamata in tambayi damuwarka"      "To ni ba ni da wata  damuwa, kayi maganarka kai tsaye"  amsawa Sabran yayi gami da gyara zamansa sannan suka fara maganar.

   Hibba...
Yau sai kusan shida ta dawo gidan, cikin sauri ta fara ayyukan girke-girke  da ɗan abunda ba a rasa ba, gabaki ɗaya hankalinta yayi sama sai gaggawa take, gashi duk da haka ba ta ganin saurin aikin.

Sassauƙan girki ta yi tana gamawa ta yi wanka  tayi ƴar kwalliya  sannan tafito Falo ta kwanta tana sauraren irin ciwon da jikinta yake yi tamkar anyi mata shegen duka.
Haka kawai take jin kamar ta sa hannu a ka tai ta ɓarza ihu ba tare da ta san dalili ba, hirar da Malika take mata ma  ɓata mata rai take don haka ta yi mata shiru,  a haka bacci yayi awon gaba da ita.

Cikin baccin ta ji Malika  tana magana da Hamdan, a hankali ta buɗe idanunta da sukai wani mugun nauyi, tashi ta yi ta zauna tana rarraba ido tsakanin Hamdan da Malika, ganin yadda ya murtuke fuska lokaci guda yasa zuciyarta ta yi wani ƙwaƙƙwaran tsalle, da ƙyar ta iya kalato jarumta  ta gaishe shi,  amsawa yayi murya a ciki-ciki sannan ya cigaba da cewa "Yau ma Napep ne ba ki samu da wuri ba ko?"  ta zaro ido tana kallonsa kafin tayi magana cikin rawar baki "Am, a'a, dama..." katseta yayi da cewa  "Dama bakiyi niyar dawowa da wuri ba ko?"  ƙasa ta yi da kai ba tare da ta bashi amsa ba,  ya cigaba da cewa "Kenan ba zaki iya bin Dokata ba ko?,  to ai sai ki ƙara fita in gani,  faɗan ma na gaji yi  ba zan ƙara ce miki bari ba, sai ma in kin fitan ne za ki ɓata min rai"

Salati da sallallami ta shiga jerawa a cikin ranta, lokaci guda zuciyarta ta karye, tuni hawaye suka fara tsere akan fuskarta,   tunanin ma dalilin da yasa take kasa kiyaye dokar tasa ta shiga yi sai dai ba ta samu wani ƙwaƙƙwaran dalili ba,  tana son  ta dinga dawowa da wurin amma ba ta san me yasa ba take kasawa.

  Haƙuri ta shiga ba shi cikin muryar kuka,  shiru bai ƙara bi takanta ba  ya dakware a zaune fuskar nan murtuke tamkar bai taɓa dariya ba, daga ƙarshe ma sai ya tashi yana shirin bar mata gurin,  ita ma saurin miƙewa ta yi tana cewa "Don Allah kayi magan..."    tsinkewa maganar tata ta yi saboda jiri da ya ɗebe ta  luuuu tayi ƙasa.

Cikin sauri ya cafkota   ta faɗo jikinsa, kiran sunanta ya shiga yi cikin kaɗuwa da  tashin  hankali.....    cikin muryarta da ta dashe ta ce "Lafiyata ƙalau fa, kawai ɗan duhu nake gani"   nannauyar ajiyar zuciya ya sauke  yana ƙara gyara mata zama a cikin ƙirjinsa.

Ture shi tayi da sauri tana faɗen "Sake ni don Allah, wari kake yi wallahi, wannan turaren naka irin na Gawa ne fa!"       gefe ta yi tana tattaɓe baki  ta cigaba da yin kuka.

Ƙamewa yayi yana kallonta  baki a sake,  sai kuma ya saki dariya,  komawa yayi kan kujera ya zauna yana ƙara bin ta da ido,    ya jinjina kai  kafin ya ce "Tab! ikon Allah, da alama dai rabon  kwaɗon da ya hau sama ya riga ya sauko!"     maida kallonsa ya yi kan Malika da ke can gefe tana jagula rubutu a littafanta ya ce "Ke Malika ɗauko wa Antinki Hijab ɗinta, ke ma ki ɗauko naki"  Malika ta tashi da sauri tana cewa "To"

cikin rashin gane manufarsa Hibba ta ce cikin shagwaɓa "To ina zaka kaimu kuma?"    "Siyar da ku zan yi"  ya faɗa yana binta da wani shu'umin kallo kamar zai maida ita ciki.

Turo baki gaba tayi bata bashi amsa ba ta cigaba da kukanta wanda ya juya zuwa na shagwaɓa.

   Duk inda ya ja ta binsa kawai take ba musu har suka isa wani ɗan madaidaicin Clinic.
Ita dai guri ta nema ta zauna tana kallonsa yana shige da ficen nemo Babban Dr na gurin, ita dai nata ido.

  Tare da wata Budurwa suka dawo sai murmushi take zubawa, cike da kulawa ta ce "Hajjaju ki  ɗan taso zan ɗan ɗebi jininki"     Hibba ta zaro ido tana faɗin "Ba ni da lafiya fa!"     Hamdan ya kwashe da dariya kafin ya ce "Ba fa duka zasu kwashe ba, na test kawai za a ɗiba"   cikin kukan shagwaɓa Hibba tance "To ai na zata kai za a ƙarawa jinin nawa!"     "Idan ya miki yawa ne   ai  sai a ɗebi na sadaka"   ya faɗa cikin sigar zolaya.

Ƙin tashi tayi sai da  Malamar asibitin ta dinga rarrashinta sannan   ta bi ta.
Bayan sun gama cajeta ta fito tana kuka tana fyacewa ta dawo ta zauna, nan fa Hamdan ya shiga rarrashinta,    sai tayi kamar ta dena sai kuma ta cigaba da wata sigar.

Bayan ɗan Lokaci aka sanar dasu Dr Kubrah tana nemansu,  Hamdan ne yayi saurin tashi tare da amsawa, Hibba kuwa sai ta turo baki gaba ta gyara zamanta,   sai da ta ga yana neman kinkimarta sannan ta tashi tana ɗan jan ƙafafunta saboda wani ɗan riƙewa da mararta ke yi.

Bayan sun zauna Dr Kubrah ta ce "Mijinki ya gaya min abun da  ke damunki, amma ina son ji daga gareki"      ba don ta so ba ta yi bayanin,     shi dai Hamdan da ido kawai yake binta don kuwa wani abun  bai ma san tana yi ba.

Dr ta ɗan murmusa gami da cewa "Sannu da ƙoƙari Hajiya Hibba" Hibba ta gyaɗa kai ba tare da lura wai gatse ake mata ba.

Ɗan numfasawa Dr Kubrah ta yi kafin ta cigaba da cewa "Kin yi  Period ne wancan watan da ya wuce?, a taƙaice ma dai rabonki da shi tun yaushe?"    Wata sassanyar kunya ta ji ta lulluɓe ta,  ta kalli Hamdan sai ta ga ya juya mata ƙeya yana kallon wani  gurin kamar bai san suna yi ba,    ta ɗan yi ƙasa da kai sannan ta ce "Nayi amma  bai  zo min daidai yadda na saba ba,  kaɗan-kaɗan ya zo kuma na kwana biyu, da kuma ina yin uku ko huɗu"    Dr Kubrah ta ce "Ya zo miki da ciwo haka ko kuma ya zo ne kamar yadda yake yi a Da?"    "Eh na ɗan yi ciwo amma ba irin na da can ba, kawai Marata tana riƙewa ne ta yi min nauyi"      "Amma dai kina ciye-ciye abubuwa da yawa ko? musamman kayan zaƙi ko magungunan Mata?"      ɗan murmushi ne ya kufce mata, ta ɗan kalli Dr kafin ta maida kai ƙasa ta ce "Bana shan magunguna sosai amma dai ina shan zaƙi,  ina cin abubuwa da yawa".

  Dr Kubrah ta murmusa gami da kallon Hamdan ta ce "Matarka na ɗauke da juna biyu, Sati Bakwai kenan, amma idan ba ku kula  ba za ku Kashe ɗanku, don haka sai ka ƙara lura da ita"   Hamdan ya washe baki gami da cewa "Yawwa ni fa na ga abun ya wuce inda nayi zato, na daɗe da ganin ta canja amma na kasa gane meye matsalar,  gaskiya na gode Dr, in sha Allahu zan kula da ita sosai da sosai"    Dr ta ce "Ai ƙuruciya ce take damunku da kai da ita ɗin, shiyasa har ciki ya kusa haɗe Wata biyu baku san da shi ba"   "Gaskiya haka ne Anty, ai yanzu tun da na sani  zan kula da ita bakin rai bakin fama,   duk wani abunda ma ze iya jawo matsala idan ta ci,   zan kwashe shi in zubar kawai"     Dr ta jinjina kai sannan ta shiga ba su shawarwari.

    Hibba dai  ko kallonsu bata yi ba daga shi har Dr ɗin saboda farinciki da  walwalarta  sun yi tsalle sun  bar jikinta.
   Banda tsalle da sukuwa ba abinda zuciyarta ke yi, musamman in ta tsinkayi muryar Dr na jawabi akan  wani rai da ke cikinta.

    Kallonta Dr Kubrah tayi a karo na ba adadi, yanzu kam kasa jurewa tayi don haka ta ce "Amma Hibba ya naga mijinki yana ta murna ke kuma da alama ba kya yi?"    Ɗago idanunta da suke mata zugi tayi ta zubawa Dr kafin ta ce "Bana son haihuwa yanzu!, don Allah idan akwai abun da ake yi ba sai an haihu ba ina so"     da ɗan mamaki Dr Kubrah ta ce "To fa!, amma meye dalilinki?"    ɗan jim! tayi kafin ta ce "Duka fa Auren namu wata biyu ne da ƴan kwanaki ko wata uku be yi ba, gaskiya ni bana so!"     Hamdan ya ce "Dr Ina ganin mamaki kawai ta yi saboda cikin ya zo da wuri, amma ba damuwa ba ce,  nima dai na so in tambaya dama ana yin haka ne?,  a yadda na lissafa fa bai fi sati biyu da yin Auren ba aka samu juna biyu"

Dr ta ɗan murmusa  Kafin ta ce "Na lura dai kawai ku auren kuka yi baku nemi iliminsa  na yau da gobe ba,   a taƙaice dai amsarka ita ce eh,  hakan na faruwa sosai musamman a wannan zamanin,     kuma halittun Mata kala-kala ne, wata Allah yayi mata baiwar saurin ɗaukar ciki,  wasu da zarar sun haihu ma suna iya ƙara ɗaukar ciki koda kuwa a sati zuwa sati uku ne da haihuwa  indai har sun samu tarayya da Miji,     kuma in banda abunka rana ɗaya ma idan tsautsayi ya ratsa aka yiwa Mace fyaɗe ba ka ganin ana samun Ciki? bare kuma anyi rayuwa har tsayin kwanaki?"    Hamdan ya jinjina kai gami da cewa  "Na gane!,  abun dama ba wuya ai tunda Allah ke yin halittar a lokacin da ya so"        "To ka gani, don haka ki  kwantar da hankalinki Hibba, idan ma Tazarar haihuwa kuke so to fa da zarar kin haihu sai kiyi Planning, idan kika huta sai ki ƙara, amma yanzu  furcin ma bakya son cikin ba daidai ba ne, Allah ya riga yayi miki kyautarsa don haka ki karɓa hannu bibbiyu,  in kika ce za ki dakatar da haihuwa yanzu to kina nufin zubar da shi kenan" 
  
Miƙewa Hamdan yayi yana murmushi ya ce "Ƙyaleta Anty Likita, ni dai na gode miki,    zan lallaɓa ta  maybe kawai tsoro take ji"
Sallama suka yi  sannan suka fito, ita dai Hibba banda kuka ba abunda take yi.

   Koda suka iso wajen Mota sai ta ƙi shiga, ta jingina a jiki ta cigaba da kuka.
Sai da ya kwantar da Malika wadda tuni tayi bacci sannan ya zagayo wajenta, jikinsa duk yayi sanyi ƙalau,   cikin tattausar murya ya ce "Ki yi haƙuri Hibba!, ina ganin  abun farinciki ne ya same mu ba kuka ba"    girgiza kai tayi cikin nuna iyakar gaskiyarta ta ce "A'a, a gurinka zai iya zama farinciki amma ni tashin hankali ne, ba wai ba na so bane  amma kasan  ba ze taɓa yuwuwa in haihu in ƙara haihuwa ba tare da danginka sun sani ba,  ni ina da nawa dangin, amma abun da zan haifa dole yana buƙatar nasa, kaga kuwa maganin kar ayi kawai kar a fara"

   Hamdan ya ɗan murmusa kafin ya ce ''Wannan shi ya sa kika ƙi nuna farinciki da samun gudan jinina kenan?"      "Eh mana,  nasan ko na haihu ba zasu taɓa yarda ma ɗanka bane, kuma kana jin abunda Likita ta ce wasu suna iya ɗaukar ciki da wuri bayan haihuwa, gaskiya bana so Ƴaƴana su fuskanci wannan tozarcin!"  ta ƙarasa maganar cikin matsanancin kuka. "Hibba!, ki saurare ni kuma ki fahimce ni"  ya ɗan yi jim! kafin ya cigaba.........

*Aunty INDO*