GADAR GIWA... (Toro ke buga mata ganga)

Gadar giwa

by @auntyindo

"Ko ƴaƴa Goma kike haifa duk Shekara ni ina son kayana, kuma ba zan bari rayuwarsu ta wulaƙanta ba, a taƙaice ma ko Babu raina Ƴaƴana ba zasu tozarta ba da izinin Allah, ba na so in ƙara jin wannan maganar a bakinki, ki raini Ɗanki da kulawa, kuma ki nuna masa ƙauna, kar ki bari wannan ragon tunanin yasa ki barranta kanki da ɗanki Hibbah!" 

  Shiru ya ɗan yi kafin ya cigaba da cewa "Rayuwata rayuwata ce, ba zan bari wani ya lalata min ita ba!, duk abin da kika ga ya faru to kawai Allah ne ya hukunta, ba wai gazawata ba, idan kin yarda da ni sai ki shiga mota mu koma Gida, in kuma ba ki yarda ba ki yanke hukunci daidai ra'ayinki" bai jira amsarta ba ya shige Mota.

  Ganin yana ƙoƙarin ja ya tafi yasa tayi wuf ta shige.
Yanzu kam kukan nata ya gaji ya dena zuwa, sai ta yi lamo! tana tunane-tunane.

    Washegari....
Tun sassafe ta kira shi ta sanar masa ita fa yau sai wajen Maama ba za ta zauna a gidan ba, ba ja ya amince mata don ya lura gabaki ɗaya a rikice take.
Kafin ma ya ce zai kaita da kansa ta sanar masa ita fa ba jiransa za tayi ba.

      Koda ta gayawa Maama abunda ke tare da ita sai ta ga Maama sai murna take yi tana cewa "Ikon Allah ashe rabon zuwan wani ran duniya ne ya ratso mu kuma muke ta ƙoƙarin hanawa!"        
Shiru Hibba ta yi ta bar Maama tana ta washe baki gami da bin su da addu,o,i, ita dai ji take tamkar taita tsala ihu.

Sai da Maama ta saka alamar tambaya akanta sannan ta gaya mata ita fa bata son haihuwar nan, ai kuwa Maama ta saka ta gaba da faɗa da nasihu masu ratsa jiki.
Sosai jikinta yayi sanyi, sai yanzu ma take ganin wautarta don kuwa banda sun yi hakan da Maama da sai ta nemo silar zubewar cikin.

   Sai dare Hamdan ya zo ya ɗauketa suka koma gidansu, shi ma ya ƙara mata da nasa nasihun.
______________________________

         Haka rayuwa ta cigaba da tafiya ana kwana ana tashi.

 Hibba... tana samun kulawa sosai a gurin Hamdan, ko me yake yi hankalinsa na kanta, duk wata nutsuwarsa ya ɗiba ya zuba akanta, hakan yasa a ɓangaren gidansu duk aka rasa gane kansa.

 Hibba kuwa zuwa yanzu so da ƙauna ya shiga tsakaninta da gudan jininta, yanzu take jin duk irin shauki da tausayin da mahaifiya take ji a yayin da take rainon ɗanta tun daga ciki, a duk lokacin da ta ji motsinsa duk tara nutsuwarta take akansa tare da binsa da addu,a. 
     Hamdan ya so ta dena zuwa Aiki sai dai ta nace dole ya barta, sai dai yanzu ita kanta bata yiwa kanta abunda zata wahala, taƙaita komai takeyi.

       *Ismail, Hajja Halima*

 Hira sukeyi irin ta Ɗa da Uwa cike da kulawa gami da walwala... 
Hajja Halima ganin Ismail cikin yanayin farinciki yasa ta ɗauko maganar da take ta son yi masa tun ba yau ba "Ismail! yanzu to sai yaushe za ka yi Aure ne?" da sauri ya kalleta sai kuma yayi ƙas da kai, sai da ya numfasa sannan ya ce "Ba yanzu ba, sai na samu wadda nake so take sona, yanzu dai Ɗanki yayi kwantai Ummi!, don Allah kawai a bar zancen Auren nan" ya ƙarasa maganar yana ƴar dariya cike da son mayar da maganar ta koma wasa.

 Murmusawa tayi kafin ta ce "Wannan dai zance ne inji magana, ta ya zaka tabbatar kayi kwantai bayan ba ka kasa a faranti ka yi talla ba?" ita ma tayi maganar cikin sigar zolaya, ƴar dariya yayi ba tare da ya bada amsa ba, hakan ya bata damar cewa "Ƙanwarka Khadija! tana matuƙar sonka, kuma nima ina sonta, na yaba da hankali da nutsuwarta da kuma mutuncinta, ina ganin ita ce mafi dacewa da kai Ismail" shiru yayi zuciyarsa na wata muguwar sassarfa.

Sai da ƴan mintuna suka shuɗe kafin ya iya ɗago idanunsa da suka cika taf da damuwa gami da ruɗanin zuciya ya zubawa Ummi sannan ya ce "Nima Khadija tana burgeni, sannan ina son duk wadda kike so Ummi!, amma zuciyata tana cike da ruɗani, ba wai don bana sonta bane, kawai Auren ne bana son yi a yanzu" Ummi ta zuba masa ido na ƴan sakanni kafin ta sauke nannauyan numfashi sannan ta ce "Ba komai, Allah yai mana me kyau, ya kuma zaɓa mafi alkairi, amma ka sani ba zan bada Ƙofar Khadija ta Auri wani ba, dani da ita muna zaman jiran amsarka" ya jinjina kai ba tare da ya ce komai ba.

     *Gidan Alhaji Ahmad*

"Ya kamata ka shiga maganar nan Abu Hamdan, yaro duk ya canja kamar ba shi ba? yanzu ko zama ya saurare ni in zanyi masa magana me muhimmanci baya yi" Ammy ce ke maganar cike da takaicin abunda Hamdan yake mata a kwanan nan.

 Cikin lallami Daddy ya ce "Hamdan! ka san dai kai ba Yaro bane, musamman tunda ƙannenka sun taso, yana da kyau ka fara yin Auren nan su ma ka basu ƙofa, kuma shi Aure ai martaba ne, da zarar ka yi shi ko a idon ƙannenka ma zaka ƙara girma" Hamdan ya ɗan murmusa kafin ya ce "Ba fa Aure ne bana so ba, kawai lokacinsa ne banida shi, kokuma in ce ba zan iya kula da haƙƙinsa a yanzu ba, kuma ba ƙin zaɓin Ammy nayi ba, kawai nace a bani lokaci ne, yanzu kun sani ina cikin yanayin da lamurra sun min yawa"

   Ɗan shiru yayi kafin ya cigaba "Daddy kai dama kawai Gudan jinina kake son gani ko?, to ka kwantar da hankalinka za ka gani in sha Allah, rana ɗaya zaka buɗe ido ka ga Jikanka, haka ya yi ko?" Daddy ya saki murmushi cike da jin daɗin kalaman Hamdan ya ce "Ai ni hakan nake so, hakan yayi, kawai yanzu kayi ƙoƙarin cika burin nan nawa shine ya rage" 

Ammy ta buntsire baki kafin ta ce "Yanzu fa shikenan har ka yarda ko?, ni ba hakan ne yafi damuna ba, har yanzu fa be taɓa ce min eh zai Auri Farida ba, kuma gashi Daddynta yana son Aurar da ita, me zan ce musu kenan?" "Ki ce musu kina kamu kawai ya wadatar, amma fa Aure ba yanzu ba, Ammy shekaru ma fa kamar ƴan kwanaki ne yanzu, kafin ki gama shiryawa ma sai ki ga lokacin ya zo, don haka ki kwantar da hankalinki" "To shikenan amma banda saɓa alƙawari, sannan kuma ka ragewa kanka wannan hidimomin ka tsaida hankalinka guri ɗaya, yanzu gabakiɗaya baka da lokacin kanka bare namu" "In sha Allah!, Komai zeyi daidai Ammy" Hamdan ya faɗa tare da miƙewa don barin Sashin Daddyn.

________Kwana yayi cikin tunane-tunane ya tufka wancan ya warware wancan, sosai yake nazarin ta yadda ze iya kufcewa Faɗawa tarkon Ammy da ƙawarta, sai dai duk ta inda yayi tunanin shiga sai yaga ƙofa ta kulle ya rasa mafita face kawai ya miƙawa Allah lamarin, don kuwa sai yadda hali yayi. Wani sashin kuwa tunanin ranar da zai nuna Hibba garesu a matsayin Matarsa yake, ko me zai faru?, shin Daddy ze goyi bayansa kodan kasancewar Hibba Ƴar Ƙanwarsa?, yaya rayuwar zata kasance idan suka ce sai sun raba shi da ita?. Tunani kala-kala yake yi amma ya kasa ɗaukar ko ɗaya, bai san me zai iya faruwa ba, don kuwa Daddy ma ba sauƙi gareshi ba indai akan ra'ayinsa ne, bare kuma Ammy wadda ta yarda ta danne Wani don Ita ta tashi. Haka ya yi ta tufka da warwara, gabakiɗaya baccin ya ƙi yi masa daɗi.

     Yau ...........
Hamdan na kwance kan doguwar Kujera ya tada kai da cinyar Hibba yana ɗan danne-danne a Laptop ɗinsa, yana yi yana bata labari gami da neman shawararta akan abunda ya shafi Kasuwancinsa. 
 Tuni sun saba hakan ta zama me bashi Shawara daga cikin gida, don kuwa tana da ƙwarewa sosai wajen iya sarrafa Kasuwanci gami da nazarin abun da ke kawo cigaba, hakanne ma yasa Gidauniyarsu take matuƙar Alfahari da ita kuma ba sa so ta nesanta dasu ko kaɗan. Yana matuƙar ganin cigaba daga shigowarta cikin lamuran nasa.

Yau dai yana lure da ita gabakiɗaya hankalinta baya kansa, bai san me take tunani ba amma sai ya ƙyaleta yake ɗan yi mata hirar kaɗan-kaɗan, daga baya ma sai yayi magana sau uku ba ta tanka ba, don haka ya ja nasa bakin ya tsuke.

    A hankali ta ɗora hannunta akansa ta fara wasa da sumarsa, magana take son yi amma nauyin da zuciyarta tayi ya ƙi bata damar hakan.

  Sai da ƙyar ta iya runtse ido sannan ta furta "................

*Aunty INDO*