GADAR GIWA... (Toro ke buga mata ganga)
Gadar giwa
by @auntyindo
"Mai Matasa!" da sauri ya ɗago ido yana kallon fuskarta, kawar da kai tayi gami da sauke wani gwaurin numfashi sannan ta ce... "Na haɗu da Ƙaninka!"
Zabura yayi ya tashi zaune tamkar ta soka masa mashi a Ƙirji, idanunsa a warwaje ya ce "Ni kuma? Wanne Ƙanin nawa??"'
Ta girgiza kai tana faɗin "Ban san shi" "Amma yana matuƙar kama da kai, Yana da tsayi da faɗi haka sannan ya fika Farar fata, kuma irin Miskilan nan ne"
"Hasbunallah!" ya faɗa gami da runtse Idanunsa, a hankali ya furta "HAIRAN!" sai kuma ya zabura ya riƙo hannunta gam! yana faɗin "Me ya ce Miki?, a ya kuka haɗu da shi?" ganin ya rikice lokaci guda yasa ta sakin murmushi ta ce "Kawai tambayata yay...." Katseta yayi da cewa "Ta wace sigar ya Tambayeki?, kar kiyi min Ƙarya Hibba!" Lumshe ido ta yi tare da tafiya tunanin abunda ya faru, dandanan komai ya fara dawo mata sabo fil tamkar yanzu yake faruwa, bata san lokacin da ta fara zayyana masa ba.
"Ban lura da shi ba, kawai sai ji nayi ya riƙo hannuna tamau, kuma ya ƙanƙameni a cikin Ƙirjinsa, sannan ya tambayeni cikin Miskilar Muryar nan tashi, 'A ina kike Rayuwa?' Duk da naji matuƙar tsoro, Zuciyata tana ta bugawa sai na ba shi amsa, 'A Gidan Mijina' ban san me yasa yayi yayi shiru ba, amma Tabbas bugun Zuciyarsa ya sauya a lokacin da nayi wannan furcin, sai daga baya ya ƙara Tambayata 'Waye Shi?!' a lokacin ƙwaƙƙwarar bugawar da Zuciyata tayi yasa na kasa bashi amsa sai na fara ƙoƙarin ƙwatar kaina jikina na karkarwa, a lokacin na ƙara jin muryarsa yana maimaita min tambayar, 'Mijina Sirrina ne!, Ba wajibi bane sai na sanar da kai Dukkan rayuwata' haka na gaya masa , kuma ba tsarawa nayi ba kawai maganar fitowa tayi kai tsaye!"
Buɗe idanunta tayi akan Hannun Hamdan wanda ke riƙe da nata, tana shirin ƙara magana Hamdan ya katseta da cewa "Sai me ya faru?" ta ɗan numfasa sannan ta ce "Daga haka sai na bangaje shi kawai na wuce" da sauri Hamdan ya katse ta da cewa "Faɗa min gaskiyar dai, nasan zaki iya bangaje shi, amma ba lallai ko motsawa yayi ba bare har ki samu hanyar wucewa, karki ɓoye min duk abunda ya faru, Please!"
Ɗan jim! tayi sannan tace "Kawai na samu Jarumtaka ne, nayi masa magana cikin fushi 'Idan kai baka san Darajar Aure ba ni na sani!, don haka ka sake ni don ni ba muharramarka ba ce!' nayi sa'a ya cireni daga matsar da yayi min, amma hannunsa na damƙe da nawa, kuma yana zuba min idanunsa irin naka, ni kuma sai na zambaɗa masa harara na ja tsaki, hakan be sa ya sake ni ba, kuma bai dena kallona ba, sannan bai ce ko uffan ba, ban san me yake tunani ba, sai daga baya ya sakar min hannun, kuma ya cigaba da zuba min Idanu, ni kuwa na firgita sosai ban siyi abunda zan siya ba na fice daga super market ɗin, saboda ina tsoron kar ya bibiyeni ma ban dawo gidan nan ba, haka ban nufi gidan Maama ba, sai na nufin Gidan su Raihana". ɗan shiru tayi kafin ta ƙara cewa "Wannan ita ce iya gaskiyata, sannan kafin muyi Aure ma na taɓa haɗuwa dashi, lokacin na raka Raihana, sai dai ranar kawai bibiyata ya dinga yi shi da Abokansa, bai zo kusa dani ba bare magana ta haɗa mu".
Sakin hannunta Hamdan yayi ya gyara zamansa ya zuba wani mugun tagumi ba tare da ya bata amsar komai ba.
Jin shirun yana neman yin yawa yasa ta cewa "Amma ya akai ka karanci yanayin Ƙaninka har haka?, kuma me yasa naga ka shiga Damuwa sosai?" wani gwauron numfashi ya sauke sannan ya ɗan murmusa ya ce "Hairan, yana ɗaya daga cikin ƙannena da nafi Matuƙar So, hakan yasa nake matuƙar ɗora hankali akan lamuransa, amma ba damuwa nake ba Matuƙar shakkar Yaron nake, musamman a kanki"
"Amma meye na shakka akansa?, ina ganin wannan ba ma abun damuwa bane ai"
Murmushi me ciwo Hamdan ya saki kafin yace "Ke kawai ganinsa kika yi, ni kuma na san halin kayana, ki bar ganinsa Yaro wanna sai yayi miki abunda ni da kike gani Babban ba zan iya yi miki ba, kuma kullum a shirye yake don samun damar da zai ɓata min rai, na tabbata da bakinki ya furta sunana a yau da yanzu bana tare da ke!"
Yanzu kam Hibba ta rasa bakin magana, Zuciyarta sai aikin tsalle da sukuwa take yi, lallai ta ɗaukarwa kanta Dala ba Gammo, kuma ta tari babbar Kasadar da ka iya zama wuƙar yanke farincikinta a rayuwa, kokuma ta kai ga tsinke rayuwar tata ma baki ɗaya.
Lallausar Muryarsa ce ta katse mata tunanin "Hibba!, bana son hanaki zuwa Aiki, amma ki ƙara ninka tsaro fiye da Da, ki kula min da kanki sosai, sannan ki koma saka liƙaf idan zaki fita, Hairan kuma ki barni da shi" cikin sanyin jiki ta gyaɗa kai ba tare da ta ce komai ba.
_______________________________
Bayan ƴan Watanni.....
Hibba na zaune tana mammatsa ƙafafunta da suka ɗan fara kumbura, saboda nauyin da tayi, fuskarta sam babu alamun walwala sai alamun tarin damuwar da ke addabarta.
Malika ce ta katse mata tunaninta da cewa "Mamma! yau Abbu be dawo ba" ɗan kallonta Hibba tayi ta kawar da kai, ta ɗan numfasa sannan ta ce "Ba lallai ya zo ba ma, don har Tara ta wuce yanzu" ƙarfin hali kawai tayi ta danne zafin dake mamayar zuciyarta, banda haka da kuka kawai zata fashe dashi a memakon bada amsa.
Malika ta rausayar da kai kafin ta canja wata tambayar, "Naji kin ce Azumi ya kusa ko? nima zanyi Azumi Talatin" Hibba ta ɗan murmusa gami da cewa "Malika!" ta ɗan yi shiru kafin ta cigaba da cewa "Azumin fa ba wasan yara bane, ki kwantar da hankalinki ke ma naki lokacin zai zo, har sai kin gaji da yi ba me hana ki"
Malika ta ɗan murmusa tace "To zanyi goma sha Takwas" Hibba tace "Malika barni da abunda ya dameni don Allah ki bar zancen azumin nan"
"Me yake damunki?" Malika ta tambaya cikin sauri.
Hibba na shirin bata amsa Sallamar Hamdan ta dakatar da ita, ɗago idanunta da suka ɗan kukkumbura tayi ta zuba masa har ya ƙaraso ya zauna kusa da ita, shima kallonta yakeyi yayin da Ƙauna da Tausayinta ke karaɗa dukka kafofin Zuciya da gangar jikinsa.
"Sannu Matar Hamdan" ya faɗa cikin tattausar Murya, gyaɗa kai tayi tana murmushi sannan ta gaishe shi gami da tambayar lafiyarsa da kasuwarsa.
Malika tana karɓar ƴar tsarabarta ta kayan zaƙi ta wuce ɗaki don bacci.
Shiru ne ya ratsa gurin na ƴan Mintuna kafin Hamdan ya katse shirun da cewa "Ban dawo da wuri ba..." kafin ya kawo uzurin nasa Hibba ta katse shi da cewa "Ba komai ai yau da gobe sai Allah!" zazzafar iska ya furzar gami da cire hularsa ya ajiye gefe, yana shirin yin wata maganar Hibba ta ce "In haɗa maka Abinci ko?" ya ɗan girgiza kai, kamar ba zai magantu ba sai kuma yayi maganar cikin ɗan nauyi-nauyi "Yau sauri nake yi sosai, ina da uzuri a tare da Daddy, kiyi haƙuri sai gobe, zan fito da wuri"
Tsam! Hibba ta tsaya tana saurarensa ko motsi bata samu ikon yi ba har ya gama maganar, ta ɗan kalle shi ta sauke kai ƙasa tayi murmushin yaƙe wanda yafi kuka ciwo, "Ka gaishe min da su, duk da nasan ba zasu amsa ba" ido kawai ya zuba mata ba tare da bata amsa ba.
Bayan shuɗewar ƴan mintuna Hibba ta ɗan dube shi ta ce "Har yanzu dai baka zama nawa ba!, gashi a yanzu ne nake matuƙar buƙatarka a kusa dani, sai dai kuma kullum ƙara nesanta muke da juna" ware idonsa yayi tas! akanta, maganar tayi bala'in motsa Zuciyarsa,,, sauke idonsa yayi akan madaidaicin cikinta, duk da ba wani girma na azo a kalla yayi ba, amma duk wanda yasan macen da ta kusa Haihuwa to fa da kallo ɗaya zai sa Hibba a cikin jerinsu.
Nan take zuciyarsa ta ƙara karyewa, ya sauke wani gwauron nishi, cikin murya me cike da damuwa yace "Gaskiya kam bana kyauta wa kaina, amma kiyi Haƙuri in sha Allah gyara ya fara daga yanzu" "Kamar dai?" Hibba ta faɗa a taƙaice, sai kuma ta ƙara da cewa "Ba fa nayi magana ne don ka shiga damuwa ba, kawai rigimata ce"
"Rigimar taki ma tana da muhimmanci a gurina, don haka na zubar da duk wani uzuri bayan naki, bari in watsa ruwa in na fito sai in ci Abinci" ya faɗa tare da miƙewa, "Daddy zau jiraka fa, gwara ka tafi abunka ai gobe tana nan da yardar Allah" "Anan zan kwana!"' ya faɗa a taƙaice be jira amsarta ba ya cigaba da tafiya.
Zazzaro ido tayi tana bin bayansa da kallo Zuciyarta na bugawa, a gaskiyance tana matuƙar son kwanan nasa a gidan, sai dai tsoron da take wa tashin hankalin da ze biyo baya yafi ƙarfi a Zuciyarta.
___________________________
Washegari...
Bai koma gidan ba sai da rana gatse-gatse, nan ya iske ɓacin ran Ammy, ta zaunar da Yaya Marwan da Arman ta zana musu Hamdan ya dena ganin mutuncinta kuma yaƙi bin Umarninta.
Arman dai be wani damu ba, a cewarsa ita ta jawo wa kanta, da can Hamdan ɗin take so su kuma sun zama Ƴan kallo, ba ze yuwu yanzu tazo ta ce haka shi kuma ya hau kai ya zauna ba.
Shi kuwa Yaya Marwan daman jiran abunda ze haɗa shi da Hamdan yake yi, hakan ne ma yasa yaƙi barin gidan har sai da ya ga Shigowarsa.
Yau dai Ammy runtse ido tayi ta nuna masa matuƙar ɓacin ranta akan abinda ya shafi son zuciyarta wato Auren Farida.
Yaya Marwan kuwa me neman kuka ne aka jefa da kashin Awaki, maganganu iri-iri ba wanda be gayawa Hamdan ba harda kai masa duka.
Shi dai Hamdan bai maida martani ba kuma be yi ƙoƙarin kare kansa ba, don kuwa zafi da raɗaɗin da zuciyarsa take yi ba ze bashi wannan damar ba.
_____________________________
Bayan ƴan Kwanaki...
_____________________________
Hamdan
Kullum cikin Matsi yake a Gidansu, Ammy da Yaya Marwan sun haɗe kai a dole sai ya Auri Farida, a gefe guda kuwa Marwan sai yaudarar Inayah yake da daɗin baki, wai dole ze sa Hamdan ya so ta.
A ɓangaren Daddy kuwa a yanzu ba abunda yasa gaba irin Kasuwancinsa, don haka nashi matsin lambar a fannin Kasuwanci ne, musamman yanzu da Hamdan yayi ƙwaƙƙwaran motsi wajen saka hannun Jari a wani kasuwancin.
_____________________________
YAU
Da safiyar Allah Hamdan ya zo wa Hibba da maganar zuwa Kamfanin Daddynsa don tattaunawa da Abokan cinikayyarsa.
A cewarsa Ita ta kawo sabon tsarin, don haka ita ce zata yiwa kowa bayani yadda ze fahimta don shi kansa ma ya lura tana fin shi kaifin basira a wani ɓangaren.
Tunda yayi maganar gabanta ya faɗi, nan take jikinta ya hau tsuma, ta fara ƙoƙarin zille masa, sai dai fir! yaƙi. Har da magiya da kuka ta haɗa masa amma yaƙi Yarda.
Dolenta ta shirya cikin Shadda irin tasa kamar yadda ya Umarceta.
suka yi Anko ras! dasu, ta saka rangaɗeɗen Hijab ɗinta me ɗan matsakaicin girma, shi kuma ya ya ɗora tsadaddiyar Hularsa.
Sai da suka biya Gidan Maama suka ajiye Malika sannan suka wuce.
Adadin kusantar Kamfanin da suke adadin ƙaruwar bugun Zuciyarta, shiru kawai ke aiki a Motar, kowa ya lula Duniyar tunani, musamman Hibba da take jin kamar tai ta kurma Ihu.
Sai da aka buɗe wangamemen gate ɗin kamfanin sannan hankalin Hibba ya dawo jikinta, ta shiga rarraba ido tana kallon yadda ake miƙowa Hamdan Gaisuwa cikin Murna da girmamawa, hakan ya ƙara tabbatar mata irin Ƙaunar da ake masa Musamman Matasa wanda tun kafin ya shigo kamfanin suke tararsa a waje da tasu gaisuwar, lallai fa ya amsa sunansa (Mai Matasa).
Tunanin da ta tafi yi kenan hakan yasa bata damu da buɗe Gilashin Motar duka da yayi ba, ana kallonta shi ma ana kallonsa, har suka ƙarasa parking space ya ajiye motar sanna ya ce "Mu je ko?"
Zuciyarta ta ƙara bada rasss!!, ƙara ɗago ido tayi saboda ƴar hayaniya da take ji, gani tayi Mutane kamar ƙaruwa suke suna binsu, kuma da alama ita suke kallo.
Lumshe ido tayi tare da ambaton sunan Allah.
A hankali ta buɗe idanun nata ta dube shi cikin muryar da take bayyana irin tashin hankalin da take ciki tace "Ka temaka min ka maidani Gida don Allah!" bbbn"Saboda me?" ya tambaya a taƙaice, "Kawai bana so ne a samu matsala, ka ga na kusa haihuwa, ko ba komai yana da kyau in haihu cikin rufin Asirina, ina matuƙar tsoro, sai nake jin kamar wani aun ze faru dani ne!" ta ƙarasa maganar cikin matuƙar karaya, idanunta sun cicciko taf! da ƙwalla.
Tunda ta fara maganar idanunsa dake isar da saƙon zuciyarsa suke kanta har ta kai ƙarshe kafin yayi wani ɗan murmushi sannan yace............
*Aunty Indon aiii✍️😍*