GADAR GIWA... (Toro ke buga mata ganga)

Gadar giwa

by @auntyindo

"A gaskiyance ba Meeting ne kaɗai yasa na kawo ki nan ba, na gaji da ɓoye matsayina a gurinki, don haka yau Ki shirya Gaida Daddyna" ɗan tsahirtawa yayi kafin ya ƙara da cewa "Ba a Matsayin Uncle ba, a Matsayin Surikinki,,, a gurin kowa kuma ki karɓi girmanki, ki Amsa sunanki MATAR HAMDAN AHMAD MAI MATASA"    
Ya ƙarasa maganar cikin ƙwarin gwuiwa, bai jira abunda zata ce ba ya fice daga Motar, tuni daman ƴan rakonsa sun buɗe masa murfinta.

 "Innalillahi wa inna ilaihi raji'u! Ya Allah ga Baiwarka Marainiya!, banida wata dubara tawa har sai abunda ka bani ikon yi Ya Allah" abunda Hibba ta furta kenan tana lumshe idanunta gami da dafe cikinta dake motsawa...

    Buɗe murfin motar da akai ne ya sanyata buɗe idanunta, ta sauke su kan me buɗewar,,, Hamdan ne sam babu wata alama akan fuskarsa wadda zata nuna maka ainahin abunda yake ji a Zuciyarsa, hannu ya miƙo mata ba tare da yayi magana ba.


   Sanin ba yadda zatayi yasa ta ɗora nata hannun kan nasa sannan ta fito daga Motar tana ɗan cije leɓenta.

   Ƙin sakar mata hannun yayi ya shiga janta suna ratsa sassa da shafuka na cikin Kamfanin ba tare da damuwa da kallonsa da ake ba, har Manyan Ma'aikata duk sun bayyano don ganewa idanunsu abunda suka ji.

   Sai da suka dangana da wani ƙawataccen Office su wanda aka kashewa kuɗi wajen ƙawata shi, ya zaunar da ita kan Kujerar dake fuskantar wani dogon Table, sannan ya saki hannun nata ya tsaya a gefenta yana fuskantar Mutanen gurin, wanda suka bi layi akan nasu kujerun.

  Sai lokacin Hibba ta iya ɗago kai cikin nutsuwa ta ƙarewa Office ɗin kallo har kan Mutane da kujerun wajen, da ganin tsarin table da kujerun ko ba a faɗa ba tasan wannan kujera da take kai ta C.E.O ce Hamdan ya zo ya ɗora ta akai don ya jawo mata abun faɗe.

   Durƙusawa Hamdan yayi a gabanta ya damƙe hannunta don samun nutsuwarta, hakan da yayi mata ya bata damar sauke ajiyar zuciya sannan ta zuba masa ido.

    Fuskarsa ɗauke da murmushi yace "Baki ji ba mutane na miki magana?" tayi ƙasa da kai don bata jin zata iya amsawa, don kuwa wani a cikinsu ma yayi sa'an Mahaifinta wani ma ƙila ya girme shi.

   Hamdan ne ya katse mata tunanin... "Ko baki amsa ba yana da kyau ki nutsu kiyi abunda dukkansu zasuyi farinciki da wannan Taron, kin gani harda Mata duk ke suke jira, cikinmu kuwa wasu aciki ba ƴan Nigeria bane, daga wasu ƙasashen Africa suka zo, Mutum biyu daga ciki ma in kin lura da kyau, Indiawa ne, don haka ki samu nutsuwa bana son sai na ƙara wahalar dasu wajen sake wani taron, ina so ayi komai yau a wuce gurin"

  Ta ɗan ƙara kallon jama,ar sannan ta sauke ajiyar Zuciya ta gyaɗa kai alamar ta gamsu da abunda ya faɗa.

    Da kansa ya gabatar da ita sannan ya nemi guri ya zauna a kujera mafi kusa da tata.

     Sai da ƙyar Hibba ta fara iya sa baki cikin maganar, ta fara yin abunda ya kawota.

    A cikin Kamfani kuwa tuni magana ta karaɗe ko'ina cewar Hamdan ya shigo da Mace, Macen ma me ciki, abunda ba su taɓa gani ko yarinya ya shigo da ita ba, a zahirance ma hanyar aikin Mata daban ta Maza daban a tsarin Hamdan ɗin.

  Tuni magana ta fara zagayawa har wajen kamfani ba iya ciki ba.
***************************

     Sunyi nisa da Tattaunawar suka ji an hankaɗo ƙofa da ƙarfi ana ƙwallawa Hamdan kira.

   Yaya Marwan ne da wannan aikin, a fusace ya ƙaraso ya tsaya gaban Hamdan sannan ya ce "Da gaske dai bin Mata ka fara yi kenan?, wace Ƴar iskar ce ka shigo da Ita Kamfani a yau har kake ƙanƙamar hannunta?"    

  Ɓoyayyar ajiyar Zuciya Hamdan ya sauke kafin ya kalli Hibba, a dake yace "Ki fara gaishe da wannan Kafin Daddy ya zo!, shine Yayana Marwan!"   

   Sai a lokacin Marwan ya lura da Hibba... Tana tsaye tana rarraba ido, jikinta na ɓari zuciyarta tana bugawa da kata'in gudu.

    Sai da kan Marwan ya kusa yin tsawa saboda ganin abunda be taɓa tsammani ba.
  Cikin tsananin fushi da rufewar ido ya kaftawa Hamdan wani azababben Mari.

  Da sauri ya kawar da fuskarsa gefe gami da runtse idanunsa yana sauraren azabar da ta ratsa ƙwaƙwalwarsa.

   Wasu daga cikin Mutanen gurin suka tashi suna ƙoƙarin janye Marwan,,, Hamdan ya dakatar dasu ta hanyar ɗaga musu hannu.

  Be damu da barbarar bakin da Marwan ɗin yake ba ya sake kallon Hibba a karo na biyu yace "Baki ji me nace ba ne?"     
 da sauri ta ɗan Matso, ta rusuna tace "Ina wuni!" Bai amsa ba sai a fuskar Hamdan , wani Marin ya ƙara tafka masa ya cigaba da tuhumarsa cikin tsawa da ƙaraji irin na Fusataccen Namiji "Wacece wannan Dan Ubanka!, ba zaka bani amsa ba sai na kakkarya ka??!"'     

  Banza Hamdan yayi masa, shi kuwa ya cigaba da zabga masa Mari yana balbalin bala'i.....

    Kuka sosai Hibba ke yi tana bashi haƙuri amma ko kallonta yaƙi yi bare tausayinta yasa ya dena.

  Sai da yaga taurin kan Hamdan yafi ƙarfinsa sannan ya dena kai masa hannu, ya koma kan Hibba da faɗa da zagi yana Tambayarta alaƙarta da Hamdan, harda wai Uban wa yayi mata Ciki...

     Kai kawai take iya Girgizawa, ta kasa magana saboda matsanancin kukan da takeyi.

 Wata Muguwar tsawa Marwan ya doka mata gami da ɗaga hannu zai yarfa mata Zaratan yatsunsa a Fuska...

 Ta runtse ido da ƙarfi tare da sallamawa ta shiga jiran saukar Marin.

    Tsawa Hamdan ya doka masa hakan ya dakatar da Ƙudurin nasa don kuwa yayi bala'in girgiza, tunda yake be taɓa jin Furcin Hamdan cikin mummunan ɓacin rai irin wannan ba, ba akan shi da yake Yayansa ba ko akan Ƙannensa hakan bata taɓa faruwa ba.

    Hamdan ya zuba masa idanunsa da sukayi murtuk! da zallar Ɓacin rai da zafin Zuciya, cikin kakkausar Murya da sigar kashedi yace "Kar ka kuskura hannunka ya taɓa ta koda da sunan Wasa ne bare kuma Duka!, zaka iya yi min komai na jure amma in kayi wannan sai ka kasance kana nadama har Bayan ranka!"  

   Nan a take Bugun zucuyar Marwan ya sauya salo, bai san lokacin da idanunsa suka zazzare kansu ba kamar wanda aka saita Ƙahon Zuciyarsa da Mashi.

    Shirunsa ne ya bawa Hamdan damar cigaba da magana cikin fusatacciyar murya, "Ita Mace ko Baiwa ce ba abar Wulaƙantawa ba ce!, bare wannan da ta kasance Mafi Tsada a Duniyata!,,, koda bayan raina Kuskure ne dukanta, ba ma akan Idona ba!"  

   yana gama faɗen haka ya matsa gaban Hibba, hannu yasa ya tallafo haɓarta sannan yace "Ki rufe min baki, ko tari ban ce ki ƙara yi ba balle kuka!"    
  Da sauri ta gyaɗa kai tana ƙoƙarin tsaida kukan nata, don kuwa tsananin fushin da ta ganshi a ciki yayi bala'in rikita tunaninta, bata taɓa zaton yana da irin wannan tsanin fushin ba sai yau da ta gani da idonta...

     Ba wani Ɓata lokaci ta tsayar da kukan, ta shiga jan numfashi da sauke ajiyar zuciya.

   Sassauta murya Hamdan yayi yace "So yake yaji wacec ce ke! duk da cewar yasan asalinki, don haka ki faɗa masa matsayinki Gareni ba, ba sai kin bashi dogon tarihi ba!"    
  Wurga ido tayi kan Marwan da jikinsa yake kyarmar mamaki da tsananin Fusata, da sauri ta maida idonta kan Hamdan saboda kwarjinin da yayi mata, nan ɗin ma sai ta ga ba masaka tsinke, don haka bata da zaɓin da ya wuce yin abunda yace.

   Sai da ta sauke Nannauyar ajiyar zuciya sannan ta ce "Ni Matar Hamdan ce!" Duk da Marwan yayi tunanin hakan amma da yaji tabbaci sai da hantar cikinsa ta juya, don kuwa kasa gazgatawa yayi don matuƙar haƙurin Hamdan, be yi zaton hakan zata iya faruwa ba.     

Hamdan ne ya katse masa tunanin da cewa "Kuma cikin jikinta Nawa ne!" ..... Wani ƙullutun baƙinciki Marwan ya haɗiye yana bin Hibba da kallo, tunanin abunda yaji akanta ya shiga yi,,, indai kuwa abunda ta faɗa yanzu gaske ne to fa lallai an gama kaishi Birnin Shashashai.

     Jinjina kai yayi yana ƙara girmama lamarin, ya ɗan sassauta murya yace "Kenan da aka ce Kinyi Aure, wannan Yaron kika Aura?" yayi maganar yana nuni da Hamdan, gyaɗa masa kai tayi cikin sauri don gudun ya ƙara kawo mata duka...........


*Aunty INDO*