GADAR GIWA... (Toro ke buga mata ganga)

Gadar giwa

by @auntyindo

Murmushin takaici Hamdan ya yi kafin ya ce "Ashe kai ma Bibiyarta ɗin kake yi!, ashsha! na ji maka takaici, don ka Manta cewa in kai a tafe kake,,,, Wani a can ya Kwana!" 
 
 Wani mugun kallo ya zubawa Hamdan yana jin wani matsanancin ɗaci na turnuƙo masa!, ƙwafa yayi kafin yace "Wallahi sai ka san da ni kake yi!, kuma wannan Auren da kake ikirari mu bamu san da zamansa ba!, don haka wajibi ne rabuwarka da wannan Me kama da Kuliyar Mayun!" Yana kaiwa nan ya fice fuuu! kamar me shirin yin dambe da iska.

Hibba dai gefe ta koma ta tsaya tsam! tana fuskantar wasu hargitsatstsum tunani masu kama da mafarki...

   Haƙuri Hamdan ya bawa kowa tare da ɗaga Taron zuwa wani lokacin dan kuwa ba a cimma matsaya ba, sai da kowa ya fice daga Office ɗin sauran su biyu sannan Hamdan ya dawo inda take....

   "Ni da shan duka ke da yin Kuka?, wannan tsohon Azanci ne irin na Mutan Da, don haka ki dena" yayi maganar cikin sigar zolaya.
 Zirr!! zirr!!! hawaye suka shiga tsiyayo mata, cikin muryarta da ta gama yin tuɓis! tace "Wannan fa ba abun wasa bane, babban tashin hankali ne, me yasa zakayi haka a wannan lokacin?, ko so kake a raba mu ai sai ka bari sai na haihu cikin salama sannan!" "Kash!! Hibbana!, Faɗen Marwan fa ba faɗen Allah bane, ni har yanzu ban hango wata barazana tashi da zata iya rabani dake ba, yanzu dai bar wannan maganar, mu tafi ne ko zaki jira Daddy ya zo ku gaisa?" da sauri tace "Bana fatan ƙara ko Minti a Kamfanin nan, kuma in sha Allah har Abada ba zan ƙar....." hannusa ya ɗora akan bakinta yana cewa "Kar kiyiwa kanki Alƙawarin da ba zaki iya cikawa ba, ke Matar Hamdan ce, abinda ya shafe shi ya shafeki"   
   Ture hannun nasa tayi cikin kuka tace "Don Allah mu tafi, ka kaini Gidan Maama, ba zan koma wannan Gidan ba a yau, ina tsoron..." katse ta yayi da cewa "Kar ki ji tsoron kowa sai Allah, kuma ni ban yarda da wannan baɗi ba ran naki ba!, tare nake so mu kasance na tsawon lokacin da ban yiwa iyaka ba!".
*********************************

       Cikin ƙanƙanin lokaci gabakiɗaya Gidan Alhaji Ahmad ya yamutse kowane ɓangare ba zancen da ake sai na Hamdan.

Daddy tun yana iya zazzaga masifa har ya ja baki yayi shiru saboda tsananin baƙin ciki da ɓacin rai, musamman yadda wasu daga cikin ƴaƴan nasa suke ta karta masa magana a baibaice.

  Ammy kuwa tashin hankali da mamakinta yafi gaban misali, ta rasa tsugun, da ta zauna sai ta miƙe ta hau sagaraftu.

    Haka aka wuni a Gidan tsabar son Ayi duk ba wanda ya je ko ina, Aunty Fauzah ma da ba damuwa tayi da zuwa gidan ba, tuni yau ta zo don ayi da ita.
    Haka suka wuni suna zuba idon ganin Hamdan amma shiru, an kira duk layikansa a kashe, gashi ba wanda yasan inda yayi aure ya tare.

          Hamdan kuwa yana can tare da Hibba ko a jikinsa, bai damu ba sannan ya hana ta damuwa ita ma, da ya ga ta ɗan yi zugum zata fara tunane tunane kokuma ta tsirko masa maganar sai ya ɗaure fuska tamau, dole ta bi shi da yadda yake so.

 Sai Ƙarfe taran dare ya buɗe wayarsa ba don ƴan gidansu ba sai don Jama'arsa da Abokan cinikayyarsa.

     Ai kuwa yana buɗeta gamo da Kasawa sai ga kiran Daddy, wanda har yanzu ya kasa ɗaura laifin akan Hamdan har sai yaji daga gareshi.

    Ƙin ɗauka Hamdan yayi sai da Hibba ta fara hawaye tana masa magiya sannan ya ɗauka, murya ba yabo ba fallasa yayi sallama.

 a ɗayan ɓangaren kuwa Daddy be amsa ba ya fara da cewa "Hamdan! duk inda kake kuma ko me kakeyi ka ajiye shi ka zo ina nemanka, sannan ka tawo da amsoshin da zaka bani in na tambayeka" "Okay" Hamdan ya ce a taƙaice, har Daddy ze tsinke kiran sai ya fasa, ya ƙara da cewa "Umarni na baka ba shawartarka nake ba, kuma bani da lokacin ɓatawa" yana gama cewa haka ya yanke kiran.

   Hamdan ya numfasa gami da zubawa Hibba ido sannan yace "Maza ki shirya mu je Gida" ido ta zazzaro gami da girgiza kai, hawaye ya fara ziraro mata, gabakiɗaya ta ma rasa abunda zata ce masa.

   Miƙewa yayi cikin ko in kula yace "Idan kina iyawa ki je gurin Mota kafin in fito, in kuma ƙafarki ba zata iya zuwa ba zan kaiki da kaina"
   Ba zata iya yi masa musu ba, haka babu wani inkari da zata iya kawowa a yanzu, don haka ta shiga salati da sallallami a cikin Zuciyarta.
***********************************

      A babban Falon gidan Alhaji Ahmad kuwa kowa na gidan ya hallara sai zuba ido suke cike da zaƙuwa da son kallon Dramar da ake shirin haska musu.

    Dukkanninsu babu wanda zaka kalli fuskarsa ka iya faɗen abunda ke Zuciyarsa kai tsaye, don kuwa yawanci abunda suke nunawa a zahiri ba shine a ɓoye ba.

  Hairan da Sabran kuwa su ne ganiyar abun, duk sun cukune fuska kamar dare, sai dai kowannensu abunda ke tashi Zuciyar daban.

 Hairaan shi kansa ba ze iya cewa ga abunda Zuciyarsa take raya masa, sai dai yana jin tayi masa wani bala'in nauyi, ga ƙunci dake ƙara mamayarta.

  Suna kan haka Hamdan ya shigo fuskarsa ɗauke da fara'a yana ɗan magana ƙasa-ƙasa, da alama dai shi da Hibba ne.

  Ita kuwa jinta take tamkar an jefa ta a wuta sannan aka hana ta ihu, rarraba idanunta dake cike da mararin zubar da hawaye kawai takeyi, yayin da bugun Zuciyarta ke ƙara tsananta.

   Wanda basu yarda da tabbacin da Marwan ya basu ba yanzu kam sun yarda sun gazgata.

   Zubewa Ammy tayi ta shiga ɓarza kuka da gaske! tana ikirarin Hibba da Uwarta sun yiwa ɗanta asiri sun raba ta dashi.
 
   Ai kuwa Daddy ya rufa da faɗa ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, haka ma Marwan, shi kuwa harda duka ya haɗa masa bayan zagi na cin mutunci da suke bin Hibba dashi.

     Kafin ka ce me gurin ya kacame kowa na faɗen albarkacin bakinsa har da wanda basu kai su faɗa ba.

   Shi dai Hamdan ya musu kunnen uwar shegu, Hibba kuwa aikinta kuka ne da bada haƙuri sai dai hakan baya aiki, duk ta firgice ta fita daga hayyacinta.

   Hairaan ji yayi Zuciyarsa tamkar zatayi tsawa ta fashe, don haka ya tarkata i nasa i nasa ya bar wajen.

Sabran kuwa yayi gingirim a zaune sai ido kawai yake rarraba musu.
*********************************

    Sai da suka gaji sannan suka tsagaita wuta sai wuci da harar-harare.

   Daddy ya nemi guri ya zauna, ya sarara sannan yace "Tun da girma da arziki ina Umartarka ka saketa ko kuma da kai da ita in nuna muku duk a ƙarƙashin ƙafata kuke"    
Ammy ta karɓe da cewa "Wallahi nima abunda ya faɗa haka ne a gurina, ka saketa tun kafin in nuna maka tsantsar fushina!, kuma anan gurin zaka saketa ba sai an je ko ina ba"

   Haɗiye yawu Hamdan yayi sannan yace "Ina matuƙar son bin Umarninku, amma don Allah akan wannan kuyi min sassauci, hukuncin yayi min tsauri da yawa"   
  A hasale Marwan yace "Wai yaushe ka raina mutane ne?? har ana cewa ga yadda zakayi kana yiwa mutane gardama?, to ko itace shugabar Mayu shugabar Ƙwalamammu yau se ka sake ta anan gurin"

Aunty Fauzah ta ce "Ya kamata dai ka san inda ke maka ciwo Hamdan!, ko ana Aure ba tare da sanin iyaye ba ai ana duba cancanta ko?, to gaskiya ka dena ɓatawa iyayenmu rai abun ya isa haka wallahi"

   Arman yace "Ai ganganci kayi Yaya Hamdan, ni ban san me ya shiga ƙwaƙwalwarka ma har kayi wannan aikin ba, da hankalinka"  

 Hamdan ya ɗan murmusa Yace "Haukacewa nayi Arman! ai gwara ka faɗa yadda kowa ze gane" 

  Ammy ta mammatso hawaye ta fyace sannan tace "Asiri sukai masa wallahi, Hamdan ɗina ba ze taɓa aikata hakan da gangan ba"

   Daddy kuwa gyara zama yayi yana ƙara murtuke fuska, babu alamun wasa ko sassauci yace "Hamdan! akan wannan fa babu sassauci, sannan ba sani ba sabo, na shirya karɓar Suruka ta, da kuma jikana amma ban shirya haɗa Alaƙa da wannan ba" ya ƙarashe maganar yana nuna Hibba, ya ɗan huta sannan ya cigaba da cewa "Muddin ka haifu kuma ka shaida kai ɗana ne, to ina so kafin nan da Minti Biyar ka furta sakin wannan Yarinya, sannan takarda ta biyo baya!, wajibi ne kayi hakan!"

    Gefen leɓensa ya kama ya cije da ƙarfi tare da runtse idanunsa saboda wata muguwar sarawa da kansa ke yi ga wani duhu-duhu da ya fara mamayar ganinsa.

 Da lalube ya nemi gurin zama akan Sofa, har lokacin idanunsa a runtse suke, baki ɗaya ƙwaƙwalwa da Zuciyarsa sun hargitse ya fara rasa ina kansa yake, furcin Daddy yana da girma , da kuma matuƙar tsanani gareshi...........


   Shiru ne ya ratsa wajen kamar ruwa ya cinye kowa, duk jiran motsin da Hamdan ze yi suke yi.

  Tsawa Marwan ya buga masa da cewar yana ɓata musu lokaci, kuma ga mintunan suna neman cika be cika Umarnin ba.

    A hankali ya ɗago idanunsa da suke masa zugin azaba tamkar an watsa musu dakakken barkono ya bi kowa da kallo har ya kawo kan Hibba dake ta famar shashshekar kuka.....

  Ƙuri yayi mata da ido kamar yana shirin narkar da ita don kallo, sai kuma ya lumshe idon gami da numfasawa, ya haɗiye wani ƙululu da yayi kakagida a maƙoshinsa.

Gyaran Murya yayi, ya ƙara buɗe idonsa akanta sannan ya buɗi bakinsa da yayi masa wani mugun nauyi tamkar be taɓa furta ko kalma ɗaya dashi ba....................... Ya ce "Na..................................................