SAWUN KEKE season 1

Sawun Keke

by @auntyindo



Gari na wayewa suka shirya suka nufi Makaranta tare da Zara. Husnee sai muzurai take yi sabida kunyarsu da take ji. Sheikh Auwal ya yi mamakin ganinta sosai sai dai ya yi shiru da bakinsa bai tambayi ba'asin zuwan nata ba don kar Akhiee ya zo ya tsefe masa gargasar jikinsa.

Ajin ya yi shiru ana tsaka da Addu'a gaf da za'a tashi wayarta da ke ɓoye a cikin jaka ta fara ƙara, zazzaro ido ta yi tana kallon Sheikh Auwal a matuƙar tsorace, Ta san doka ce zuwa da waya cikin Makaranta bare ma har ta yi ƙara a jita. Ta yi zaton zai yi mata hukunci kamar yadda ya saba yiwa kowa, ga mamakinta sai ta ji ya ce "Tashi ki je waje ki amsa." Kamar jira take yi, ta yi saurin miƙewa tana cewa "Na gode Malam!" har neman yin tuntuɓe take yi wajen fita waje.
Tana ɗagawa muryar Ahmad ta doki dodon kunnenta, "Husnee ki zo gida!" abinda ya furta kenan wanda ya sa hanjin cikinta suka ƙuƙƙulle lokaci ɗaya, haka kawai ta ji gabanta ya yanke ya faɗi, Zuciyarta ta shiga bugawa da sauri da sauri, "Lafiya kuwa Ya Ahmad?? na ji muryarka kamar ka yi kuka." shiru bai ce komai ba har na ɗan lokaci sannan ya ƙara danne Zuciyarsa ya ce "Ki zo dai, kowa ma na son ganinki, kuma yanzu-yanzu." daga haka ya katse wayar, jikinta ya yi matuƙar sanyi, yayin da tsoro da fargaba suka ɗarsu a Zuciyarta, kamar Kazar da ƙwai ya fashewa a ciki haka ta salallaɓa ta koma cikin Aji, wajen Sheikh Auwal ta nufa ta tsugunna sannan ta ce "Yayana ne ya kirani, ya ce ana son ganina a Gida yanzu-yanzu, don Allah Ya Sheikh a yi min uzuri in tafi." cikin kamilalliyar muryarsa ya ce "Kin tambayi Mijin naki??" girgiza kai ta yi gami da cewa "A'a amma zan gaya masa." ya gyaɗa kai tare da cewa "To, za ki iya tafiya." da sauri ta tashi tana cewa "Na gode!" 

Ta san Akhiee tsaf zai hanata zuwa gidan don haka ko ta kansa ba ta bi ba ta wuce.
Tin da ta ga taron Mutane a Ƙofar gidan Zuciyarta ta ƙara tsinkewa, a haka ta shiga cikin sanɗa tamkar wadda take shirin yin sata, gabaki ɗaya kallon da Mutane suke binta da shi duk sai ta ji ta ƙara tsorata, kuma abin mamakin ba maza ba mata, Muneeb ma da ta haɗu da shi ta yi masa magana ko kallon inda take bai yi ba sai ma tsaki da ya ja mata, gashi da alamu dai Mutuwa aka yi duba da yadda kowa yake a hautsine.
A Ɗakin Mommy ta tarar da ita tare da Ƙanwarta da Yayarta da Ƙannen Daddy da sauran mutane.
Kuka take yi sosai tana surutai suna bata haƙuri gami da tausarta duk da cewar su ma suna yin kukan.
Ba ta san lokacin da hawaye suka fara tsere akan kumatunta ba, bakinta na rawa ta ce "Mommy!! meke faruwa??? ya na ga hankalin kowa a tashe." wani mugun kukan kura Mommy ta yi ta janyo Hijab ɗin Husnee ta fara sharta mata wasu azababbun maruka, sannan ta rufeta da duka tamkar ba za ta barta da rai ba.
Sai da ƙyar suka ƙwaceta ta hanyar zame Hijab ɗinta suka barwa Mommy shi a hannunta,  
Duk da kuka take yi sai da lamarinsu ya ƙara ɗaure mata kai ganin sun yi sororo sun zuba mata ido suna binta da wani kallo me cike da manufofi kala daban-daban, su kuwa irin sittirar jikinta ce ta sa suka shagala wajen kallonta cike da mamaki da al'ajabi, Kayan saƙi ne damfara-damfara irin na Sarakunan Asali, ga wata dafkekiyar Sarƙa ta Gold a wuyanta wanda sabida tsayinta har ta kawo kan cikinta, faɗinta kuwa ya kusan cike faɗin Ƙirjin Husnee ɗin. 
Umma Hasiya ce ta kasa dannewa ta jinjina kai gami da cewa "Ma sha Allahu!, shi yasa fa Yarinya ta guji danginta ashe wata Duniyar kika samu, ke kuwa wane irin Ɗan Ta'adda kika Aura Husnee??, a dole ya kashe Muddassir don da alama ba ƙarami ba ne" Cikin shashshekar kuka Mommy ta ce "Shi ya sa nake son kashe shegiya in huta, ai ko me ya yi mana itace ta jawo mana, Muddassir shi kaɗai ne ya amince da auren nata sabida yana sonta, amma kin ga abinda suka saka masa da shi." "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! don Allah Mommy ki yi haƙuri kar ki kasheni, wallahi ƙarya aka yiwa Rislan ba zai iya kashe Ya Muddassir ba, Yayan ma bai mutu ba kuma na ganshi ma a cikin mutanen ƙofar gida." cikin kuka na tashin hankali take maganar tamkar wadda ta fara zaucewa, Ammy ce ta kawo mata mangara tana cewa "Ke dallah rufewa mutane baki!!, shegiya Ƴar daɗi miji, har mu za ki gayawa sharri aka yiwa mijinki??, kafin ki san Ɗan Iska ba mu kika sani ba dan ubanki??" girgiza kai kawai take yi, tana son yin magana amma ta kasa, sai wani irin kuka take yi tamkar za ta haɗiyi Zuciya.
"Ba zan yarda kai ne ka aikata ba AKhiee, na san ba za ka iya cutar da ɗan uwana ba" abinda take saƙawa a Zuciyarta kenan.
Su Umma Hasiya kuwa masifa suke yi tamkar za su ari baki, banda munanan kalamai ba abinda suke furtawa akan Akhiee har ita kanta Husnee ɗin ma wani abun da ita suke haɗawa, ita dai tana durƙushe a gefe hankalinta ma ya gama yin nisa ba komai take ji ba, Mutane kuwa sai leƙowa ake yi ana kallonta, duk wadda ta leƙo sai ta riƙe haɓa ta juya.

Kafin ka waiga ka waigo Gidan Mutuwa ya zama gidan tsegumi, ba maganar da ake yi sai ta Husnee da mijinta.
Husnee kuwa daga haka zazzafan zazzaɓi ya lulluɓeta, ta ɓungire a wajen tana rawar ɗari, amma ba wanda ya saurareta, daga baya ma sai kowa ya zare jiki ya bar mata ɗakin, sai mutane tsilli-tsilli da sukan shigo su zauna daga baya su tashi, da yawansu kuwa kallonta ne yake kawosu sai ka ce ba su taɓa ganinta ba.
Daga ita sai ubangijinta suka san irin azabar da take ji ga zafin zazzaɓi ga ciwon kai, ga Zuciyarta tana wani irin raɗaɗi da ƙuna, gashi ko abinda za ta lulluɓe jikinta ba wanda ya temaka mata da shi, Da haka wani wahaltaccen bacci ya yi awon gaba da ita.

Kamar a zahiri kamar a Mafarki ta ga Muneer ya na lulluɓeta da wani ƙaton bargo, ta buɗi baki tana son yi masa magana amma ta kasa muryarta ta ƙi fitowa, tana kallonsa har ya fice daga ɗakin.
Daga haka ba ta ƙara sanin inda kanta yake ba har sai da la'asar ta yi sannan ta farka daga yanayin da ta kasa bambance suma ne ko kuma bacci, a hankali ta buɗe idanunta da suke wani irin raɗaɗi da Azaba, daidai lokacin wata Mata ta zo ta ɗage labulen ɗakin tana leƙowa, da sauri ta ƙara rintse idanunta gami da sa hannu ta karesu sabida hasken da ya dokesu sai ta ji har tsakiyar kanta, Matar ta yi saurin sakin labulen ta juya tana cewa "Au ai ta tashi."   
Wani wahaltaccen kuka Husnee ta saki na tausayin kanta da kuma rashin Yayanta da ta yi.
Da ƙyar ta lallaɓa ta miƙe domin ɗauro Alwala ta gabatar da Sallah.

A wunin sai da ta fara nadamar zuwanta Duniya sabida ƙuncin da aka jefata, Mutane kowa tsoron ya raɓeta ko ta raɓeshi yake yi, da an ganta a wuri ba a zuwa haka in ita ta raɓi wuri sai a fashe, sai wani irin kallon tsoro da ake binta da shi, ga su Umma Hasiya sun sakota gaba da ɗibar albarka iri-iri.

Misalin Ƙarfe 10:00pm.....
   Ƙarar wayarta da ba ta san Duniyar da ta shiga ba ta dawo da ita hayyacinta, cikin yanayin na sanyi ƙalau da jikinta ya yi ta fara dube-dube; a ƙarƙashin gadon Mommy ta samota lokacin har kira na uku ya shigo, ɗagawa ta yi ƙirjinta tamkar zai buɗe sabida tsoron abinda za ta ji.
"Ban hana ki fita ba tare da izinina ba wai??, me yasa ba kya jin magana?" "Yayana ne fa ya mutu Akhiee." "Ko uban waye ba za ki sanar da ni ba?, kuma tin kafin ki san da Mutuwar ma uban waye ya ce ki je Makaranta?" "Allah ya baka haƙuri!" ta faɗa tana kuka, tsaki ya doka kafin ya ce "Maza ki bi Ɗan Bakwai ya mayar da ke gida, yana nan ya zo." "Akhiee a nan fa zan kwana, bai kamata na cewa iyayena zan tafi b......" katseta ya yi a fusace da cewa "Su ne da ke ko ni ne da ke??, ban amince ki kwana a gidan nan ba, in kuma ki ka yi mini gardama za ki ga abinda zai biyo baya." ya na kaiwa nan ya katse wayar, kukanta ne ya ƙara ƙarfi ta miƙe cikin sanyin jiki tana laluben Hijab ɗinta amma ba ta ga ko me kama da shi ba.
Ɗakin su ta nufa domin ɗakko na Khausar, anan ta yi katari da su Mommy wadda har yanzu kuka take yi. Duk da irin tsallen da Zuciyarta ke yi da cikinta da ke kukan tsoro hakan bai hanata daurewa ta nufesu ba. "Uban me ya biyo da ke nan kuma??" Ammy ce ta watsa mata tambayar cike da kyara da nuna ƙyama.
durƙusawa ta yi a gaban Mommy bakinta na rawa ta ce "Akhiee ne ya ce bai yarda na kwana ba, tafiya zan yi." "La'ilaha illallahu!!! Muhammadu Ɗan Abdullahi! eh!! lallai kin shahara yarinya, ko dan tinda ya hure miki kunne kika Aure shi ai wannan ba komai ba ne Husna." Umma Hasiya ce ta yi maganar cikin jinjina lamarin Husnee ɗin, Ammy da ta saki baki kamar sakatar sakarai, sai a lokacin ta jinjina kai sannan ta ce "Ah!! lallai, ana cewa in ka haifi Ɗa Namiji wata ka haifawa to ni yau na ga inda aka haifawa Wani namiji Ƴa Mace; Husna?? ya kashe yayanki amma sabida tsabar kema kin zama tantiriya har ki kalli tsabar idonmu ki gaya mana wai ya ce kar ki kwana tafiya za ki yi??" Umma Hasiya ta ce "Gane min hanya dai, ai wallahi in ni ce yadda Annabi ya bar Duniya ni ma na bar Aurenka kenan." cike da baƙin ciki da takaici Mommy ta kalleta sannan ta ce "Husna!! ki saurareni, muddin kika bar gidan nan yanzu to ko gawarki ban yarda a kawota gidan nan ba bare ki shigo da ƙafarki, Ni na haifeki ba shi ya haifeki ba don haka na ce ba za ki ƙara komawa gidansa ba." cikin shashshekar kuka ta ce "Don Allah Mommy ki barni na koma gobe zan dawo, wallahi tinda ya ce ba ya so idan na aikata zai yi abinda ba zai yiwa kowa daɗi ba." "Dan Ubanki akwai abinda zai yi mini wanda ya wuce kashe min Ɗa da ya yi??, iyeh???" girgiza kai ta yi tana cewa "A'a Mommy amma don Allah ki yafe mini, ki dena ganin laifina wallahi ba laifina ba ne, don Allah ki yi haƙuri, wallahi na san halinsa n...." kasa ƙarasa maganar ta yi sabida kukanta da ya ƙara tsananta, Ammy ta ce "Astagfirullah! yaya ki bar wannan Ƴa ta koma wajensa don na lura ta zama ba taki ba, Zuciyarta ta riga ta ƙeƙashe in kika hana ta ma sai su iya kasheki ita da Mijin nata." Mommy ta ƙara tattaɓe baki tana sakin wani sabon kukan gami da cewa "Haka ne wallahi, Husna ki koma gidan Mijinki, amma ina so ki sani ban yafe miki ba, baƙin cikin da kika sakani a rayuwa ke ma sai kin ga irinsa, kuma komai daren daɗewa in na Mutu ko kika Mutu to ki sani kin Mutu da fushina." "Don Allah! don Allah Mommy ki dubi rayuwata, kar ki bari na mutu da fushinki, don girman Allah ki yafe mini, wallahi tallahi ƙaddara ce ta kawo waɗannan abubuwan cikin rayuwata, ni ma ba a son raina suke faruwa ba, ki tausaya mini kar ki bari rayuwata ta ɗaiɗaice Mommy!!!." cikin wani irin masifaffen kuka take yin maganar, jikinta har karkarwa yake.
"Ba zan taɓa yafe miki ba har sai kin Kashe Mijinki!!, indai kika kashe shi kamar yadda ya kashe Ɗana to zan yafe miki, amma muddin ba ki kashe shi ba to fa ba ke ba yafiyata, ki tashi ki je na gaji da ganinki!!!." ta ƙarasa maganar tana ɗaga mata hannu.
"In kashe shi Mommy!?" Husnee ta tambaya idanunta a warwaje, "Ba za ki aikata ba ne??, ko kin fi son ran Mijinki akan yafiyar Uwarki??" Ammy ta tambayeta, da sauri ta girgiza kai tana cewa "Zan kashe shi, na gode Mommy!" ba wanda ya kulata a cikinsu, ta miƙe jikinta na tsuma ta ɗauko Hijab ɗin Khausar ta zura sannan ta fice.


Tin da ta dawo gidan ta kafa aradun kuka ba ji ba gani.Tana jin motsin shigowarsa ta yi saurin miƙewa ta nufeshi gadan-gadan ta na zuba masa idanunta da suka kumbura suntum sabida kuka "Akhiee! da gaske kai ne ka kashe mini Yayana??" ta jefa masa tambayar cikin tsananin ɓacin rai.
Cak!! ya tsaya da tafiya idanunsa na kanta, kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce "Ni ne!!" tassss!!! ta sharta masa wani haɗaɗɗen Mari, cikin ɗaga murya ta ce "Me ya yi maka??? abin naka ya wuce kan kowa ya dawo kaina ko?? meye abinda ya tare maka da ka kashe shi???, Duk gidanmu shi kaɗai ne ya amince da Aurenmu, amma sabida kai butulu ne shine ka kashe shi ko????" ta ƙarasa maganar ta na huci kamar za ta cinye shi sabida fusata.

Raɓewa ya yi ta kusa da ita ya wuce gami da cewa "Komai tsananin hukuncin da za ki yi min ba zan iya gaya miki abinda ya aikata mini ba" cikin sauri ta sha gabansa ta na cewa "To ka faɗa mana!! indai ba ƙarya kake yi ba ka faɗa mini abinda ya yi maka har ya cancani hukuncin kisa!!" Idanunsa da suka canja launi zuwa kalar Blue ya ɗago ya zuba mata kafin ya ce "Asma'u kin san ba na yi miki ƙarya, kuma magana ɗaya nake yi, na ce ba zan faɗa ba, in kina ra'ayi za ki iya kasheni ko kuma ki yi min duk hukuncin da zai sa Zuciyarki ta yi sanyi."
Murmushi me cike da takaici da baƙin ciki ta yi gami cewa "Hmm!! sabida ka san ka fi ƙarfina shi yasa ka ce haka??" Bai ce mata komai ba ya ƙarasa wajen bed site cikin nutsuwa. Dukkan zobukan hannunsa Guda tara ya zare ya zuba a kai sannan ya juyo ya na fuskantarta, fuskarsa ba alamar wasa ya ce "Yanzu za ki iya yi min komai; kar ki hukunta Zuciyarki a bisa laifin da ba naki ba, kawai ki hukunta ni Asma'u!!" ya yi maganar cikin wata irin murya me matuƙar karyar da Zuciyar me saurarenta, kasa cewa komai ta yi sai ma zubewa da ta yi a ƙasa ta rushe da wani wahalallen kuka.


Tuno waɗannan kalaman Na Mommy da Sharaɗinta da Husnee ta yi ya ƙara tashin hankalinta ainun, Zuciyarta ta shiga bugawa tamkar ana tseren doki da doki a cikinta.

 "Ya zan yi da rayuwata!!!? Me zan yi in samu salama? tabbas in na mutu da fushin iyayena zan gamu da Fushin Allah!!!! ta yaya kuma zan iya kashe Mijina da hannayena? Ta ya zan iya kashe Yardar da ya yi mini har in kashe shi??, Wayyo Allahna!!! Allah ka kawo mini mafita, ina cikin mawuyacin hali!!!"
Sambatun da take yi kenan cikin kukan nata ba tare da la'akari da cewar ya na jinta kuma ya na kallonta ba. "Ba ki da mafitar da ta wuce ki kasheni!, idan kuma ba ki yi hakan ba ni zan aikata da kaina!!" muryarsa ce ta karaɗe kunnuwanta, jin furucinsa na ƙarshe ya sa kukanta ya ɗauke cak! ta haɗiyi wani mugun ƙullutu da ya maƙale mata a maƙoshi, ta yi saurin miƙewa ta na gwalalo masa idanu cikin matsanancin tashin hankali da fargaba, ta sani sarai Zuciyarsa makauniyar Zuciya ce akan abinda ya so, aikata hakan gareshi ƙaramin aiki ne, ta buɗi baki za ta yi magana ta ga ya zare wata muguwar wuƙa daga ƙugunsa ya keta wuyansa..........

Wata muguwar ƙara ta ƙwalla tare da silalewa ta faɗi babu alamar numfashi a tare da ita..................