GADAR GIWA... (Toro ke buga mata ganga)
Gadar giwa
by @auntyindo
Wata muguwar wawura ta kawo masa tana wani irin ihu da ƙaraji tamkar zautacciya kokuma wadda cutar iska ta kama, da ƙyar ya tsallake cafkar tata ya zura da gudu, bai zame ko ina ba sai cikin gidan, ya garƙame ƙofa sannan ya faɗi ƙasa warwas yana burgimar murna.
GIDAN ALHAJI AHMAD
Hamdan yana zuwa ya jefar da motar ko kashewa beyi ba ya fito ya fara bugun Ƙofa yana ƙwallawa Ammy kira cikin ɗaga murya.
Da gudu me gadi ya fito da Gorarsa a hannu ya ɗaga murya yana tambayar waye.
"Hamdan ne, ina Ammy take?, ina Daddy? wallahi ka ce su fito min da Hibba tun kafin na shigo!"
Jiki na rawa Mai gadi ya buɗe ƙofar sannan yayi saurin matsawa gefe don yadda yaji bugun da kuma karsashi a tare da Hamdan ze iya yin awon gaba dashi don ƙarfi ke aiki a jikinsa.
da sauri Me gadi ya fiddo keypad ɗinsa ya latso lambar Sabran ya tura kira, yayi sa'a Sabran ya ɗaga da wuri, sannan ya sanar masa ga fa Hamdan nan a buɗe masa ƙofar falo don ze iya karya ta.
Cikin sauri Sabran ya fito ya buɗe ƙofar, aikuwa Hamdan ya wancakalar dashi ya wuce ciki yana ƙara sakin murya tare da kiran Ammy!....
Kafin ka ce Kobo Jama'ar gida sun taru akan Hamdan, Daddy sai farinciki yake yana ƙoƙarin kwantarwa Hamdan hankali.
Shi kuwa faɗi yake "Ko a fito min da Hibba ko ayi bala'i a gidan nan! ku nuna min inda Ammy ta shiga ta ɓuya wallahi sai ta dawo min da Hibba, dama kun tsaneta ba kwa sonta! to ko kasheta kukayi sai kun bani Gawarta yanzun nan! kuma sai na kashe kowa da kowa!"
Riƙo hannunsa Daddy yayi yana cewa "Na ce ka nutsu zan gaya maka abunda ke faruw...." kafin ya rufe baki Hamdan ya bangazar dashi gefe ya fizge hannunsa yana cewa "Na ce a fito min da Hibbaa!" cikin ihu yayi maganar har saida wasu daga ciki suka runtse ido musamman Mata.
Daddy ya jinjina kai cikin matuƙar sanyin jiki yanzu ya fahimci Hamdan fa ya dena gane kowa sam ba a hayyacinsa yake ba, don ya tabbata indai Hamdan ɗin da ya sani ne to fa ko be saurari wasu daga ciki ba ze saurari wasu, wani lokacin yana da faɗa amma baya yinsa a rufa ido duk laifin da akai masa, komai nasa a tsanaki yake yinsa.
Kan kujera Daddy ya koma ya zauna ya dafe kai sannan ya fashe da wani azababben kuka yana faɗin "Kaicona! na cuci kaina na cuci Zuri'ata! nayi kuskure wayyo Allah na shiga uku!"
Arman ne ya ƙaraso kusa dashi cikin tausayawa yace "Don Allah ka dena kukan nan Dad!, ka yi masa magana a nutse ze fahimce ka"
Daddy ya ɗago kai da nufin yin magana idonsa ya saka akan Hamdan wanda yayi wani wawan tsalle ya faɗi ƙasa gabaki ɗayansa jikake rim!!!! zabura Daddy yayi ya miƙe tsaye yana ƙwallawa Hamdan kira.
Su Fauzan da Sabran ma kansa suka yi cikin kaɗuwa da tashin hankali.
Burgima ya shiga yi yana ihun kuka yana cewa "Wallahi ku fito min da Hibba, wallahi zan kashe kowa indai baku kawo min ita ba, ni a bani Hibba!" Wani maraitaccen kuka Mamy ta saki tare da zubewa a wajen tana salati, "Shikenan Bango ya faɗi!, wallahi mun zalumci Yaron nan gashi zalumcin ya dawo kanmu!, shi kenan kun rasa Gatanku Ƴaƴan nan! " surutan da Mamy ta shiga jerawa kenan don ta tabbata Hamdan tamkar Bango yake ga kowane Ɗa a gidan, ba ma iya Ƴaƴa ba har su kansu iyayen, yanzu gashi an wayi gari yana wannan abu da ta tabbatar ƙwaƙwalwarsa ba ƙalau take ba.
Rirriƙe shi Fauzan da Sabran da Arman suka yi suna gaya masa Hibba tana nan zata zo gobe da safe yayi haƙuri, be ma san suna yi ba kwata-kwata don baya fahimtar komai, burinsa bai wuce ya ga Hibba a gabansa ba.
Ƙaraji da ihu ya ƙara yi ya watsar dasu ya miƙe ya falla da gudu yaje ya daki bango ya faɗi ƙasa rim!, kafin su iso gurin ya ƙara miƙewa yana dukan bangon gami da bubbuga kansa, har i yanzu zancensa ɗaya ne a kawo masa Hibbansa.
Ƙara baje ƙarfi su Arman suka yi suka riƙe shi katamau da tunanin ba ze ƙwace ba, sai dai yana yin girgiza ɗaya ya watsar dasu ya ƙara yin tsalle ya faɗi ƙasa tim!!!.
Yanzu kam kowa ya fahimci abunda yake faruwa, sun tabbata ya riga ya zauce.
Kuka su Ammarah suka shiga rusawa, su suna yi Mamy da Daddy na yi.
Su Sabran ma saida suka matse tasu ƴar ƙwallar don ma basa son sakin kuka da ba abunda ze hana su yi.
Abu kamar ƙarami sai gashi ya zama babba sai kokawa suke famar yi da Hamdan sai sun riƙe shi ram! sun zaunar dashi sai ya girgije ya tashi, duk ya jiwa kansa raunuka.
Sun ɓata lokaci me tsayi suna fama kafin su fara shawarar neman igiyar ɗaure shi don abun yaci tura, mai gadi ne ya shiga ya fita ya samo ta ya kawo igiyar, suka karɓa suka ɗaure shi tamau! sannan suka koma suka zauna me tagumi yayi me matse ƙwalla na yi. A hakan ma sai kici-kicin kwancewa yake yi yana turje-turje.
Mai gadi yace "To ni dai ga shawara idan ba zata ɓata muku rai ba" ido suka gwalalo masa don kuwa a yanzu shawara indai sun san ba ta cutarwa ba ce ɗauka zasuyi. "Wannan ciwo nasa dai yafi kama da na iska, don haka nake bada shawara kar a zauna yi masa kuka a fara yi masa addu'a, tunda kuna da yawa kowa yayi abunda Allah ya bashi na ilimin addu'o'i masu nafiloli ma suyi" da sauri Daddy yace "Shakka babu hakan za ayi, wallahi hankalina ne ya tashi shiyasa na manta da hakan"
Murmushin takaici Sabran yayi, tare da kallon Daddy, ya goge ƙwalla sannan yace "Ai matsalar kenan! a gidan nan babu wanda alkairi ko akasinsa ze faɗo masa kuma ya tuna da ubangiji kai tsaye, wannan matsalar ita ce ma ta kawo mu ga wannan baƙin yanayin da muke ciki" "Haka ne ɗan nan ai yanzu se mu gyara, na so a ce Madina da Marwan sun ga wannan tashin hankalin ko Zuciyarsu zata dawo irin ta musulmi, amma koda hakan ma ba komai na kira shi Marwan tun ɗazu na gaya masa ƙarfe ukun dare na yi yaje ya ɗauko uwar tashi ya dawo da ita, asubar farko tayi musu a gidan nan" shiru Sabran yayi bai bada amsa ba, hakan yasa Daddy ya tashi ya nufi toilet don ɗaura Alwala, zuciyarsa a cunkushe da tunane-tunane.
Marwan...
Duk da bai ga irin tashin hankalin da ake ciki ba kasa bacci yayi sai ƴan juye-juye, hankalinsa ya kai ƙoluluwa wajen tashi.
Asbaha tana yi ya fice ya nufi gidan Yaya Fatima ya ɗauki Ammy suka wuce, duku-dukun safiya a gidan tayi musu.
Shi dai Marwan tunda ya zuba ido ya ga halin da Hamdan yake ciki sai ya koma gefe ya zauna ya doka uban tagumi, wani irin zafi da ƙuna haɗe da tausayi yake ji a Zuciyarsa wadda take ta famar tuhumarsa da alhakin abun da ke faruwa, ji yake tamkar ya tsage da kuka amma ya kasa sai na zuci, lokaci guda jikinsa ya ɗauki wani mugun zafi yayi laƙwas tamkar an zare masa laka.
Ammy kuwa kuka me ƙuna da raɗaɗi take sharɓawa duk wannan ɓaɓatu da surutun da take in abu ya sameta yau ta kasa don abun ya fi gaban nan.
Bayan Daddy ya gama bincikar duk wasu manyan Likitoci nasa har daga Abokansa, bayan ya samu wanda hankalinsa yafi kwanciya dashi sannan ya ce a taitayi Hamdan su nufi Asibiti.
Koda suka je nan take aka shiga aikin bincikar lafiyar Hamdan gami da ba shi agajin gaggawa.
Haka sukai ta famar kaikomo cikin matuƙar damuwa da tashin hankali, ko abinci babu wanda ya iya nema wuni guda har rana ta koma ga ubangijinta.
Abu kamar wasa har aka ƙara yin dare rana ta ƙara bayyana babu wani sabon cigaba da aka samu a lafiyar Hamdan, sai allurai na bacci da kashe jiki kawai ake ɗirka masa, su ma basa daɗewa a jikinsa tasirinsu yake karyewa, da zarar ya buɗi ido kuwa a Kawo masa Hibbansa shine abunda yake furtawa, ya dena gane kowa har ita kanta Ammy ba ganeta yake ba, hasali ma baya son ta raɓe shi kwata-kwata.
Daga bisani dai Doctors suka bawa Daddy shawara gwara kawai a bi shi da Addu'a don abun ya wuce duk inda ake zato, haukan nasa ba hauka ne wanda zai ji magani ba sai dai Allah ya yaye kawai.
________________________________
A ɓangaren su Hibba kuwa haka kawai take jinta tamkar mara lafiya duk jikinta a sanyaye yake.
Tana cikin wannan yanayin yau Isma'il ya dawo mata gida cikin tsananin damuwa, koda ta tambayi abunda ke faruwa sai ya ce mata ba komai kawai.
Ba don ta yarda ba ta ƙyale zancen, sai dai hankalinta ya gama tashi duk nutsuwarta ta ƙare kawai dannewa take, gabanta sai faɗuwa yake akai-akai sai dai ta haƙura ta dinga ambaton sunan Allah a duk lokacin da zuciya ta fara raya mata abunda bata san da zamansa ba.
2:43Am Hibba ta farka daga baccin da ta samu ya kwasheta bayan ta sha wuya kafin ya zo.
Tashi tayi zaune tana ɗan lullumshe ido, nan take damuwarta ta ƙara dawowa sabuwa, da sauri ta juya inda Isma'il yake kwance sai ta ga babu shi a wajen Zuciyarta ta ƙara bugawa da ƙarfi, tunani ɗaya ne ya zo mata kodai wani nata ne ba lafiya, duk da cewar sun yi waya da Maama da safe amma tayi tunanin ko wani abu ne ya faru da ita daga baya.
Tashi tayi da sauri ta fito Falo tana rarraba ido, yayin da zuciyarta ke bugawa a ɗari da tamanin.
A falon ta ci karo dashi zaune kan darduma ya haɗe kai da gwiwa sai rusa kuka yake tamkar wanda aka yiwa wata jinjinar Mutuwa.
Da sauri ta ƙarasa ta zube a gabansa jikinta na karkarwa, cikin rawar murya irin ta mai shirin fashewa da kuka ta ce "Me yake faruwa? Dan Allah ka faɗa min gaskiya! kodai Maam....." kasa ƙarasa maganar tayi saboda kuka ya danne harshen nata, ta goge ƙwallar da ta shararo kana ta zuba masa ido cikin jiran amsar shi.
Da ƙyar ya iya rarrashin zuciyarsa ya tsagaita kukan yana sauke ajiyar zuciya, ɗagowa yayi ya zuba mata idanu yana binta da wani kallo me karya Zuciya, cikin sarƙaƙƙiyar murya ya ce "Ba komai!, me yasa kika tashi?" da sauri ta girgiza kai ta ce "A'a! idan babu komai me zai sa ka dinga kuka haka? don Allah ka gaya min in sha Allahu zan yi haƙuri da ko menene" ta ƙarasa maganar tana sakin wani marayan kuka.
Kansa ya ɗaga sama yana cije gefen leɓensa, ya kwashe ƴan sakanni a haka kafin ya kalleta cikin raunin murya ya ce "Da gaske za ki iya jura kuma kiyi haƙuri da duk abunda zai biyo baya daga gareni?"
Sosai maganar ta tsorata ta kuma ta jefata cikin sanyin jiki gami da ruɗani..... sanin babu yadda ta iya da ƙaddararta ya sa ta gyaɗa kai ta ce "Zan jure indai hakan zai sa ka farin ciki!"
Runtse idonsa yayi da ƙarfi........
by Anti Indo