ALIYU HAYDAR

Chapter 12

by @nieemartullah

A departure lounge ya sami HAYDAR ya hade girar sama da ta qasa shi ala dole anyi mai laifi,shi dariya ma ya bashi sai kawai ya fisge yayi kaman ma bai gan shi ba,suna zaune kowa yana danna wayar shi babu mai cewa dan uwan sa ci kan ka,ganin fa dagaske Zannur ya manna masa hauka ya sa shi yin tsuka yana qara hade rai,tsukar da yayi ne yayi drawing attention din few people dake wurin,ji yayi an zauna a gefen shi kuma yana da tabbacin ba Zannur bane,inda Zannur ya zauna ya kalla ya ganshi zaune yana kallon direction din shi yana qoqarin danne dariya kaman mai jin tsoron wani abu ya juya kanshi don ganin me Zannur yake ma dariyar,tsabar shock besan lokacin da ya bude baki ba yana kallon yarinyar dake zaune gefen shi tana ta kallon shi kamar ta samu TV,sai da taga ya juyo yana kallonta yasa tace masa Good morning Handsome tsabar baqin ciki da takaici har wani duhu duhu yake gani a cikin idon shi,bata damu da rashin amsa gaisuwar da tayi masa ba ta dora da fadin  seems like baka gane ni ba ko?Ta fada cikin sigar tambaya mun taba haduwa da kai a Bococho beach almost two weeks ago,ta fadi hakan tana murmushi nan ma ko arziqin kallo bata samu ba hakan kuma bai dame ta ba ta cigaba da maganarta would you mind sharing your digits with me? gani ma yake yi kamar yarinyar nada tabin hankali shiyasa cikin dan daga murya yace leave this place before i lose my cool jin muryar shi da ta daki dodon kunnen ta yasa ta saurin ja da baya tana zare ido don ba qaramin tsorata tayi ba, yaga alamun kamar ma bata hayyacinta shiyasa ya qara jan wata tsukar ya tashi fuuuuu kamar wata kububuwa ya wuce..........................................
Tana shiga office dinta inda ta aje handbag dinta ta wuce ta fiddo da wayar ta three miss calls ta gani kuma duk na mom ne sai a lokacin ta tuna bata fada ma mom za suyi theatre ba kar taga ta dade,bin bayan kiran ta yi yana fara ringing ta daga sallama tayi mata ta amsa kafin tace ina kika shiga haka JAY kin daga min hankali,haquri ta shiga bata kafin ta fada mata dalilin rashin dawowarta akan lokaci sai a lokacin mom ta sauke ajiyar zuciya JAY ce ta qara cewa mom kin san yau wa na sake gani bayan na cire rai da qara ganinta?cikin sanyin murya mom tace Maimunatu kika gani JAY? Kamar tana gabanta ta shiga gyada mata kai kafin ta bude baki tace ita na gani mom,bayan wasu shekaru mom yau gani ga Munarh murmushin jin dadi tayi tace gani nan zuwa asibitin,tohm shikenan mom amma kisa aunty Naja ta hada musu abinci ki taho da su,babu kowa a tare da su kuma suna da buqatar abincin,toh shikenan bari na fada mata kafin na shirya nima.....................
Bayan sun gama waya da Hafsat dakinta ta wuce ta fada kan gado tana jin lokacin da aka bude gate mota  ta shigo amma bata ko motsa ba don bata yi tunanin shi ne ya dawo ba,bayan kusan minti biyu taji an bude qofar dakinta,juyawa tayi don ganin wanda zai shigo,miqewa zaune tayi don ganin wanda bata yi tsammanin gani ba,shigowa yayi ya zauna a bakin gadon,ganin da tayi shi din ne dagaske bawai hallucination ba yasa ta matsowa kusa da shi tace Raj amma ba ka ce man fita zaka yi ba?ta fada tana jin tsoran amsar da zai bata,eh harma na fita amma sai ma manta inda zanje shiyasa na dawo,ji tayi wani abu mai nauyi da ya tsaya mata a qirji tun lokacin da yace mata zai qara aure ya wuce,sosai taji duk wani nauyi da qirjinta ke mata ya dena,murmushin ta me kyau tayi masa tace gara da ka dawo ai,miqewa yayi riqe da hannunta a cikin nasa hannun suka fito parlour,ledar da ya aje lokacin da ya shigo ya nuna mata yace mata ta dauka nata ne rungume shi tayi tana masa godiya tana jin wani irin farin ciki a cikin zuciyar ta.......................................
Mintuna talatin tsakani ta kira JAY tace mata gata a premises din asibitin,lokacin tana office dinta a kwance kan daya daga cikin sofas din dake cikin office din na company B&B Italian sofa,tashi tayi daga kwancen da take ta zura takalmanta dake gefen ta ta fito zuwa premises din asibitin,jagora tayi ma mom har zuwa dakin da suke,a zaune suka tarar dasu suna dan yin hira saboda su basu wani ji ciwo ba,dan buguwa ne kawai suka yi sai tsorata da suka yi wanda shine dalilin da yasa suka zama unconscious,tana ganin mom ta sakko daga kan gadon da saurinta ta fada jikinta ta saki kuka mai cin rai,kana ganin yadda take kukan kasan daga qasan zuciyarta take yin shi,abubuwan da suka faru suka fara ringing a qwaqwalwarta,qara qanqame mom tayi kaman za'a qwace ta,nayi kewar ki sosai mom, hawaye ne ya kawo idon mom tayi saurin mayar da shi because she needs to be strong,dan patting bayan ta take yi tace nima nayi kewarki sosai daughter,ya jikin naki?naji sauqi mom ta fada tana jan hannun mom zuwa wajen gadonta,sai bayan ta zauna ta juya ta kalli Ummi tace sannu Hajiya,ya jikin?da yake Ummi itama wayayyar yar boko ce bata da duhun kai tace ai jiki da sauqi alhamdulillah,toh Allah ya qara lafiya ya kuma kare gaba,ameen ya Allah,sai a wannan lokacin Ummi ta kalli JAY tace doctor ko zamu iya ganin jikin Mu'azzam gane wanda Ummi ke nufi yasa tace eh zaku iya ganin shi dama na bari ne ku qara jin qarfin jikin ku sai ku je ku ganshi,tun lokacin da aka gama theatre ya farfado sai muka qara yi mashi alluran bacci don ya qara samun hutu,ai sai muje mu ganshi ko?ta juya akalar tambayar ta wurin Maimunatu,gyada mata kai tayi tana qoqarin tashi mom taimaka mata ta miqe,fita suka yi daga dakin JAY na gaba suna binta a baya suka bar mom ita daya a dakin....................................
Yau tunda safiyya ta tashi ta gama duk ayyukan da ta dorawa kanta na aikin gida a yan kwanakin na dakinta ta wuce tayi wanka ta shirya cikin wata Lace trimmed slit abaya ta fesa turarukanta ta nemi bakin gado ta zauna tana jiran taji fitar HAYDAR daga gidan don tana da tabbacin yau zai koma wurin aiki,tana jin lokacin da ya fita ba'a dau lokaci ba taji ya dawo ya zauna a parlour,bai fi minti goma ba taji ya qara,har bayan tsawon lokaci bai dawo ba,hakan ya tabbatar mata da ya tafi,makullin motarta da wayarta kadai ta dauka ta fito,kitchen ta shiga ta fita ta qofar baya inda zai kaita har part din da masu aikin gidan suke,for the first time zata je bangaren masu aiki cikin shekaru shiddan da tayi a gida,a qofar part din ta tsaya ta saka a kira mata barira,jiki na rawa ta fito kar tayi laifi duk da taga sauyi sosai wurin saffiyan amma dai tana gudun tayi laifi,tana fitowa ta duqa har kasa tana gaishe da ita,duk da haka takeyi idan zata gaishe amma yau sai taji wani iri,sai tace ki dena duqawa idan zaki gaishe dani don Allah,dan jinjina kai tayi tace in shaa Allah za'a kiyaye,yawwa kafin tace dama zan fita anguwa ne and ina son gidan ya zama under your watch har na dawo and maganar girki kuma ku dafa iya abinda zaku ci kafin na dawo zan iya kaiwa dare,addu'ar dawowa lafiya tayi mata kafin ta wuce tana yin hanyar compound din gidan ta shiga motarta ta bar gidan,tafiyar minti arba'in ce ta kaita cikin suleja, bayan ta shiga cikin suleja din shima tafiya ce tayi mai dan nisa kafin tayi parking a dai-dai wata bukka wacce babu gida gaba babu gida baya,tun da ta bude motarta ta fito taji atmosphere din wurin ya canja baki daya da wani irin wari kaman an jefar da mushe ji tayi kaman ma ta koma amma dai wannan ce kadai damar da take da ita wurin gyara abinda ta bata, hakan yasa kawai ta nufi hanyar shiga cikin bukkar tana qara kusanta wurin,tana qara jin wari har sai da ta daga dan labulen da ya rufe bukkar,gawar bokan da tarar ne ya firgitata har tana neman faduwa,sosai ta tsorata ganin irin yanayin data same shi a ciki sam babu kyan gani,hardewa qafafunta suke yi tana ganin duhu duhu a cikin kanta,da qyar da taimakon Allah ta kawo kanta inda tayi parking motarta,tana zuwa wurin ta fara kwarara amai,kamar gaba daya kayan cikinta ta amaiyar,ta galabaita sosai da qyar ta iya sa hannu ta dakko ruwa acikin mota ta dauraye bakinta ta kuma wanke fuskarta,sai da taji ta dan samu nutsuwa kafin ta shiga motarta tayi reverse ta bar wurin........................................................
Lokacin da suka sauka a MM international airport already driver din HAYDAR yana jiran su don yasan da zuwan nasu yana tsaye lokacin da jirgin su yayi landing,yana nan tsaye har suka fito daga cikin jirgi, Zannur ne ya fara hango shi,hakan yasa yayi hanyar inda yake hango shi,bin inda Zannur yabi da kallo yayi sai a lokacin yaga driver din shi da yazo daukar su,bayan shi yabi yana zuwa ya tarar har ya zauan a gidan baya hakan yasa shi jan tsuka ya bude front seat ya zauna,abin yayi mugun bawa Zannur dariya, har driver ya ja mota suka bar airport din yana dariya,sosai dariyar ta qular da HAYDAR yace kaga mallam idan mu aje aka psychiatric hospital ne sai mu sani,ka saka mutane gaba kana ta dariya,ko kallon inda yake be yiba bare ya nuna yasan da shi yake hakan kuwa ya qara qular da shi har aka aje su a office yana ta jan tsuka.............................................
Wani ikon Allah ne kawai ya kawo ta har gidan shema'u,mai gadi na bude mata gate ko parking din kirki bata iya tsayawa yi ba ta bude motar ta fito duhu kawai take gani cikin kanta,tana tafiya tana hada hanya har ta iso qofar parlour tayi knocking ba'a dauki lokaci mai aikinta ta bude ganin itace yasa ta bata wuri ta shigo tana gaishe da ita hannu kawai ta iya daga mata ta shige ciki,tana zuwa kuwa tayi sa'a tana gidan bata fita ba ko Ina ba, kan gadon shema'u kawai ta kwanta bata ma lura da ba shema'un bace kadai a dakin,bacci take son tayi ko zata samu yar nutsuwar yin tunani,shema'u kuwa tunda ta ganta cikin wannan halin hankalinta yayi mugun tashi don tasan halin safiyyah na shegen taurin kai zata iya yin duk abinda tayi niyyah sai safa da marwa take yi ta rasa wani irin tunani ma zata yi, ganin da tayi tana bata lokacin ta yasa kawai ta nemi wuri ta zauna tana jiran lokacin da safiyyah zata tashi daga baccin taji abinda yake faruwa ..................
Jinin sa yana da qarfi hakan yasa allurar da aka yi masa bata wani jima ba ta sake shi,lokacin da suka shiga dakin ya farka amma dai yana kwance idanun shi ne kawai a bude,bakin gadon suka tsaya gaba dayan su Ummi tayi masa ya jiki yace mata da sauqi Maimunatu ma ta mai ya jiki ya amsa,sai kuma ya fara qoqarin miqewa zaune,kafadarshi Maimunatu ta riqe ta taimaka mashi ya zauna ta saka mashi pillow daga bayan shi,sannu ta qara yi mashi ya jinjina mata kai,JAY ce ta tambaye shi yanda yake ji yanxu ya bata amsa da baya jin komai sai jikin shi da yake dan yi masa ciwo nodding kanta tayi masa tace shima zai dena sai kuma tacema su Ummi idan sun duba shi su bashi wuri ya qara hutawa,da toh suka amsa mata ta fice daga dakin baki daya tana komawa dakin da mom take, tana shiga dakin ta tarar da mom a tsaye alamun ita take jira,tana ganinta tace JAY zan tafi gida i have a guess to attend to,we will talk when you come back, gyada mata kai tayi suna fitowa daga dakinta mom tayi hanyar entrance din asibitin ita kuma ta nufi office dinta...........................
Jinta take kamar an saka ta a aljanna bata taba tunanin zata samu kan Sooraj har haka ba sai gashi kamar wasa tana ta ganin sauyi daga bangaren shi daga dawowar shi zuwa yanxu,duk wani abu da ta saka shi yana yi mata shi babu musu yake yi mata wasu abubuwan idan a da ne ko giyar wake tasha tasan bama zata yi gigin cewa yayi ba amma sai gashi yau yana yi mata su,lokacin da ya fita sallar isha'i ta dauki waya ta dokawa Hafsat kira tana dagawa bata tsaya ko sallama ba tace albishirin ki daga dayan bangaren Hafsat tace goro ina jinki shaqa min meke faruwa guda ta saki tace I'm over the moon baby girl i can't  express how i'm feeling right now,RAJ is now under my control,kar kiso kiga yadda yake wani nan nan da ni kamar zai maida ni ciki,shewa Hafsat ta saki tace shegiya qawata kice ke kam kina cikin alkhairi, fadi ki qara qawata ai sai yanxu na fahimci abinda kike qoqarin fahimtar da ni a baya,ai da gani kike kamar zan cutar dake ne ko na kaiki na baro kike ta biyema Meenah,ita fa cewa zata yi ki kwantar da kai har ki samu abinda kike so wata qila kafin lokacin ya qara auren shi zuciyar ki ta buga ki mutu a banxa shi baya da asara wata matar zai qara aurowa ta maye masa gurbin ki ,baki ga yanda take ma wannan shegen saurayin nata biyayya ba kamar qanin ubanta ni fah haushi take bani duk irin manyan mutanen dake cewa suna sonta amma ta liqe ma wannan yaron dan gidan matsiyata shine fah kadai Allah ya bawa arziqi,Laylah dake ita duk irin wannan zantuttukan basu dame ta ba ta tabe baki tace ki kyaleta taga zata iya ne shiyasa to be sincere bashi da wani aibu da za'a ce bai kai ta kula shi ba and arziqi na Allah ne ai,tsaki Hafsat taja tace au na ma manta da wa nake magana ai kema ba ciwon kan ki kika sani ba,in banda rashin sanin ciwon kai me ake da talaka kinga sai anjima kar kiyi spoiling mood dina,ta kashe wayar,yar dariya tayi tana girgiza kai tace Allah ya shirye ki..............................................
Bayan sun duba abinda zasu duba a office suka qara fitowa don komawa gida babu wanda yace da dan uwansa kanzil har suka iso qofar gidan Zannur,ya bude qofa ya fito har ya juya zai wuce ya shiga gidan shi yaji baxe iya tafiya inda HAYDAR yake yayi knocking glass din motar kawai ya sauke ya zuba masa idanun sa masu kaifi,kawar da kai yayi daga kallon da yake jifan shi da shi yace fito muyi magana cikin lallami,yanayin yadda yayi maganar ne yasa HAYDAR bude motar ya fito,tsaye yayi jikin motar shi yaqi kallon inda yake,hakan bai dameshi ba yace HAYDAR ina lura dakai tunda muka je abuja kana cikin damuwa,ina son ka sani dorawa kanka damuwa ba shine solution ba,kaje ka fuskance ta,abinda ya faru a baya ya riga da ya wuce ku nema wa kanku mafita,idan kuma kana ganin nesantar junan ku shine matakin da ka dauka shikenan bazan hana ka ba,amma dole ka cire duk wata damuwa ka fuskanci sabuwar rayuwa nayi niyyar fada ma Mamy amma sai naga zan shiga rayuwar ka dayawa ni kuma bana son kaga na yi maka rashin kyautatawa sunkuyar da kanshi yayi saboda tabbas abinda Zannur ya fada gaskiya ne amma bazai iya tunkarar ta ba ko kuma ya cire ta a cikin zuciyar shi,dagowa yayi ya kalli Zannur da idanun shi da suka fara sauya Launi daga fari zuwa ja ya bude baki zai yi magana amma ya rasa mema zai ce sai kawai ya girgiza masa kai ya bude motar ya shiga,Zannur dama yasan hakan zata iya faruwa sai kawai ya girgiza kai cikin matsanancin tausayin abokin nasa.......................................................
Ahankali take bude idanunta har ta gama bude su baki daya akan p.o.p din dakin,kalle kalle ta fara don ta gane a ina take,sai da ta rufe idanun ta kafin ta tuna abinda ya faru bayan zuwan ta gidan bokan su da abinda ta gani har zuwan ta gidan shema'u,bude qofar da shema'u tayi ne yasa ta dawowa daga duniyar tunanin da ta fada,juyawa tayi ta kalleta da niyyar fada mata abinda ta gani sai dai bakin ta taji yayi mata nauyi ta kasa fada sai binta takeyi da ido har ta zauna a gefen ta tace sannu sophie har kin tashi gyada mata kai kawai tayi ba tare da tace uffan ba,gyara zamanta tayi tace kin daga man hankali sosai,ki fada man meyafaru?wani abun yayi maki?ko dukan ki yayi?ko kuma sakin ki yayi?ta jero mata tambayoyin lokaci guda kuri tayi mata da ido sai kuma ta girgiza mata kai tana rufe ido wata ajiyar zuciya ta sauke tana jin sanyi a cikin ranta,tashi to muje ki ci abinci duk kinyi wani iri kamar mara lafiya,bata ce mata komai ba ta miqe don tana buqatar abincin dama bata ko tsaya tayi breakfast ba ta fito amma da ta zauna cin abincin sai ta kasa ci tana ta jagwalgwala shi ganin hakan yasa shema'u cewa wai safiyyah menene matsalar ki ne ko anyi maki wani abun ne,sai yanxu ta bude baki tace kar ki sa damuwar komai a ranki shema wani mafarki ne nayi ya tsoratar dani sosai amma babu komai,tsuka tayi tace wallahi muguwa ce ke safiyyah tsakani na dake Allah ya isa kin san irin tashin hankalin da kika saka ni na dauka ma wani mummunan abin ne ya faru na ganki cikin tashin hankali nayi zaryar zuwa bandaki yafi biyar,duk da tana cikin tashin hankali amma sai da maganganun shema'u suka saka ta tayi dariya ganin yadda ta taqarqare tana bala'i,miqewa tayi daga dining din tayi hanyar dakin ta tana ta yin hamdala a cikin ranta don kwata kwata bata fatan auren safiyyah da HAYDAR ya lalace bata cimma abinda take son cimmawa ba