47
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️-----47
tare suka fito suka nufi cikin gidan zeenah na zaune a valcony ta kasa dauke idanunta daga kansu yayin da wani irin kishi ya cika mata zuciya
ganin yadda suka taho Suhail sai zuba murmushi yake basu lura da ita ba har sai suka matso dap da ita
tuni idanunta suka chanza kala kallon da take wa Suhail sai da yaji jikin sa yayi sanyi lokaci guda ya hango kwanciyar hawaye a idanun zeenah wanda suke ƙoƙarin zubowa ita kanta iman sai da jikin ta yayi sanyi
ba tare da sun kula taba suka shiga ciki Mami na zaune kan kujera a falon ƙasa tana kallon wani shiri
Da sallama suka shiga Mami ta amsa tana kallonsu
Idanunta suka ɗan tsaya kan Iman
a gefe guda ta samu waje ta zauna
ta gaishe da mami ta amsa ba yaɓo ba fallasa
Suhail ma ya gaishe ta
Shiru sukayi babu wanda ya kara magana
mami ta ce"Suhail daman inaso nayi wata magana da kai"
gaba daya ya maido hankalinsa ga mami
"ya kamata ace nima na samu jika daga bangare ka ga kanan da mata har biyu amman har yanzu shiru ba amo ba labari"
take iman taji zuciyatar ta buga bata taɓa tsanmanin Wannan Maganar daga bakin Mami ba da mutuwa da haihuwa ai na Allah ne shi ke bada a sanda yaso ya kuma amsa a duk sanda yaso
Idanun Suhail suka ƙada lokaci guda
Ya kalli Mami na wasu sakanni ya ce"
Mutuwa da haihuwa duk suna hannun Allah, Mami Mu bayi ne kawai ba mu da ikon tilasta abin da Allah bai ƙaddara ba
Idan Allah bai ba mu a yau ba, muna fatan gobe zai bamu Don Allah Mami, a bar wannan maganar
Iman ta kasa ɗaga kanta
Mami ma ta ɗan yi mamakin yadda ya faɗi maganar
amman ba Abinda mamaki bane a wajen ta kullum tunanin iyayen iman sunyi ma Suhail asiri sun raba ta dashi
zeenah dake tsaye bakin kofa taji wani abu ya tokare mata a wuya
ganin yadda Suhail ke kokarin kare iman a gaban mami
Iman ko a ranta take ji Suhail ba iya miji bane kadai a wajenta
Mutum ne da yake ƙoƙarin tsayawa a bayanta lokacin da duniya take son ta karya mata zuciya
suhail ya taka wani matsayi a rayuwa wanda take jin duk duniya bayan Malan da Ammi babu wanda take jinsa a ranta Suhail
mami ta ce"nidai na fadi Abinda ke raina"
ta miƙe da kyar ta koma sama
iman da har lokacin kanta ke ƙasa
Kalaman Mami sun shiga zuciyarta yanzu kenan har an soma yi mata gorin haihuwa idan akwai wanda jinkirin
haihuwa ke damu ai bayan ita da Suhail ne amman Mami ta kasa fahimta har ta fara jefar su da kalaman da suka fi rashin haihuwa ciwo
Suhail ya kalli Iman
Tun daga yadda ta sunkuyar da kai ya fahimci maganar ta taɓa ta
“Iman"
A hankali ta ɗago kai
“Kada ki bari maganar kowa ta dame ki kuma nayi alƙawarin zama dake Ko da Allah bai ba mu yara yanzu ba, bazaki taba ganin canji daga gare ni ba Iman"
nauyin dake kan Zuciyarta taji ya ragu
daidai lokacin zeenah na shigowa falon
mikewa yayi ya ce"ki hada kayan ki zamu tafi"
"okay" kawai ta ce
Suhail ya kama hannun iman ya ce"muje ki gaisa da Abba naga motar sa parking space"
Ba tare da ta musa ba ta bi bayan sa
Zeenah ta tsaya tana kallonsu har suka nufi part ɗin Abba
Abba na zaune yana karanta jarida
Da ya ɗago ya gansu, murmushi ya yi
“Ah, Barrister nawa Har kun dawo kenan?"
Suhail ya ƙarasa ya gaisheshi cikin girmamawa
Iman ma ta gaida shi,Abba ya amsa cikin fara’a
Abba ya ce"ya kika baro su malan din"
"lafiya qlau Abba"
abba ya dubi Suhail ya ce"hala ba tare kuka zo da dayar matar taka ba"
mamakin Maganar abba yayi ya ce"tare muka zo ai a Wajen mami ma ta kwana"
jinjina kai abba yayi
mamakin da yayi yadda zeenah ta kwana a gidan batazo ta gaishe da abba kuma mami bata ce tazo ba
"Abba bari na kira ta"
hannu Abba ya daga masa ya ce"ka barta kawai Suhail"
nasiha ya kara masu tare da jan kunne wanda duk sanda suka zo haka yake masu
gyara zama Abba yayi ya ce"Allah ya kara hada kanku ya baku zuriah ta gari masu albarka"
"Amin" suka amsa a tare .
A wannan karon idanun Iman suka cika da ƙwalla
Suhail ya lura da hakan amma bai ce komai ba
Sai dai a ransa ya ƙara yanke shawarar kare ta daga duk wani abu da zai ƙara mata ciwo
Bayan sun yi sallama suka fito
zasu koma part din mami ta roki alfarmar ya barta taje ta gaishe da aunty Fauziya
Iman na shirin juya wa ta nufi part ɗin Aunty Fauziya.
Sai ta hango Zeenah tsaye daga can gefe
Tun lokacin da suka fito daga wajen Abba take tsaye tana kallonsu
Wani irin raɗaɗi ya cika mata zuciya
A baya ita ce take mafarkin wannan rana
Ita ce take mafarkin Suhail zai riƙa tafiya da ita yana gabatar da ita ga iyalansa'
Amma yau tana tsaye ne tana kallon yana yi wa wata
Da sauri ta kau da kai kada su ga ƙwallar da ta cika mata ido
Suhail ya lura da yanayin fuskarta
ya nufi wajen ta
hannun ta ya kama zeenah "are You fine"
kai ta girgiza masa yayin da take ƙoƙarin share hawayen ta
Iman na shiga ɗakin aunty Fauziya ta same ta akan kujera bayan dun gaisa aunty Fauziya ta ce"shine jiya kika gudu ai nayi tunanin nan zaki kwana"
murmushi kawai iman tayi ta ce"dama nazo na maki sallama zamu tafi"
Aunty Fauziya ta ce"da wuri haka na dauka zaku kwana biyu"
har baƙin kofa ta taro ka tare da addu'ar sauka lafiya
a daren ranar suka kama Hanyar Abuja
har suka isa ba wanda ya ce wa kowa ƙala
koda suka isa jennifer ta fito ta tarbi zeenah tare da amsar mata jakar hannun ta
kowa ya nufi sashen sa daren Ranar iman kwana tayi tana sallah tana rokon Allah ya basu yara nagari har tafi Suhail shiga damuwa
Iman ta share hawayenta bayan ta gama sallah
A karo na farko tun bayan aurensu, ta fara jin tsoron kada jinkirin samun haihuwa ya zama wata babbar jarabawa a rayuwar auren su.
washe gari
Suhail ya fito cikin shirin sa na zuwa office ko breakfast fast bai tsaya yayi ba kasancewar ya bar mutane suna jiran sa
like
share
comment