BABI NA ƊAYA
***
*MUTUNCI MADARA...*
©Fareeda Abdallah
*TSOKACIN LABARIN MUTUNCI MADARA NE, IDAN YA ZUBE BA YA TAƁA KWASUWA.*
_Wasu kura-kuran ba sa zuwa a siffar zunubi. Suna zuwa ne a siffar soyayya, murmushi, kulawa, daɗin baki, da alƙawarin aure. Sai mace ta buɗe zuciyarta tana tsammanin za ta shiga sabon babi na farin ciki... Ba tare da saninta ba ashe babin mummunan ƙaddararta ce aka buɗe da hannu bibiyu._
*1)*
"Sakina?"
Aisha da take tsaye a bakin ƙofa tana leƙa tsakar gidan ta kira Sakina. Kafin Sakina ta amsa ta cigaba da cewa
"Wai na ce kin ga Kamal kuwa? Wallahi ya fi ko wane abokin Ango haskawa a taron bikin nan. Ke ni fa in banda ma kar Amarya Karima ta ce na ci mata fuska ai Wallahi da sai in ce har Ango Ma'aruf wankansa da ƙyallin goshinsa bai kai na Kamal ɗin ki ba..."
Kofin da Amarya Karima ta ɗauka a fusace ta hurga ma Aisha yasa ta katse maganar da take yi tana dariya. Ta ɗaga hannuwa biyu sama alamun ta yi sorrender, tana dariya ta ce
"Allah ya huci zuciyarki Amaryarmu. Dama tsokanarki nake yi."
"Ai ke kam Aisha kin shiga uku! Na rantse da Allah sai yanzu na ƙara tabbatar da ba ƙaramin haƙuri Abdallah yake yi da ke ba. Shegiya da mijin aurenki a hannu amma ba ki da aiki sai yaba maza kyawawa! Allah ya shirye ki."
"To Amin. Tunda kyakkyawan addu'a kika yi. Amma fa kar ki wani ga laifina, domin gaskiya na faɗa. Kuma kyakkyawan namiji ai ba ni kaɗai na ke yabonshi ba, ko wacce a cikinmu nan bata ƙi a ce wanda za ta aura ya fi ko wane namiji kyau ba. A toh! Ko ke ma inda za ki faɗi gaskiya na san ba ki ƙi a ce Ma'aruf ɗin ki ya fi sauran maza kyau ba..."
Da gudu ta shige banɗakin da ke cikin falon ganin Karima na laluben abinda za ta jefe ta da shi.
Sauran ƙawayen amarya da ke zaune a ɗakin suka ƙyalƙyale da dariya. Ita kuwa Sakina da tun farko Aisha ta fara magana akan saurayinta Kamal murmushi kawai take ta yi, ita kaɗai take ta blushing, zuciyarta cike da jin daɗin yabon da Kamal ke sha a bakin ƙawayenta ko wane lokaci.
Har ta yi kamar za ta tashi ta leƙa, sai kuma ta taushi zuciyarta ta cigaba da zama tana jiran shigowarsu cikin falon. Domin ta san dole za su shigo, tunda sun shigo godiya ga iyaye ne bayan ɗaura aure da kuma gabatar da hotuna tsakanin Ango da Amarya.
Wata irin bugawa zuciyarta ke yi da matsananciyar son Kamal. Domin ba a kusa suka fara soyayya ba. Shekaru biyu cif suka kwashe suna zuba soyayya irinta bugawa a jarida. Shekaru biyu yana bibiyarta sau da ƙafa, har sai da ya tabbatar ya cike duk wani lungu da saƙo na zuciyarta da matsananciyar soyayyarshi. Ya tare gaba ya tare baya, ya hana ko wani namiji samun guri ko ɗan kaɗan a zuciyarta. Duk ƙawayenta da ƴan'uwanta sun san ta da Kamal, kamar yadda shi ma duk abokansa suka san shi da Sakina.
Sannan wani abu da ke ƙara kwantar mata da hankali yana hana ta yin da na sani a soyayyarsa shi ne, duk da irin matsananciyar son da take masa, to fa ba komai bane idan aka kwatanta da tsananin son da shi Kamal yake mata. Baya ga shaidar makusantansu akan son da yake mata ya fi wanda take masa, ita a karan kanta ta tabbatar son da yake mata ya ninka wanda take masa sau goma. Ko daga irin matsananciyar kulawa da tarairayar da yake mata ako wani lokaci, ita ta tabbatar Kamal yana son ta.
Kamal, kyakkyawan saurayi kalar Cakuleti, dogo mai faɗin ƙirji ƙirar ƙarfafan mazaje. Kyawawan idanunsa, ɗan madaidaicin bakinsa, dogon karan hancinsa su ne manyan abubuwa na farko da suke fara jan hankalin duk wata ƴa mace da ta ɗora ƙwayar idanunta a kansa. Kamal ya san wanka da gayu, wanka da gayu sun san Kamal, shi yasa suke bashi haɗin kai ɗari bisa ɗari.
Bayan duk waɗannan baiwa ta Kamal Allah ya huwace masa baiwar iya tsara magana. Kamal Irin mazan nan ne da idan suna magana da mace musamman wacce suke so ta kan ji kamar duk duniya ta fi ko wace mace dace da masoyi.
A yanzu haka da ake gudanar da bikin Abokin Kamal mai suna Ma'aruf, da Amaryarsa Karima wacce ta kasance ƙawar Sakina, watanni biyu Kacal ya rage a ɗaura auren Kamal da Sakina...
Shigowar abokan Ango cikin babban falon da Amarya da ƙawayenta suke ciki shi ya dawo da hankalin Sakina daga duniyar tunanin da ta afka. Bayan musayar gajeren gaisuwa tsakanin ƙawayen Amarya da abokan Ango, siririyar guɗa da dararraku ne suka kwashe da shi bayan Ango ya rungumi Amaryarsa a karon farko bayan ta zama halaliyarsa.
Mai ɗaukar hoto na tsaye da yaransa a gefe suna gudanar da ayyukansu cike da ƙwarewa. Bahaushe ya ce so-so ne amma son kai ya fi, duk tarin abokan Ango a idanun Amarya Karima Angonta Ma'aruf ya fi ko wanne abokinsa haɗuwa. Haka zalika a idanun Sakina Kamal ya fi ko wane namiji cinyewa a gurin. Su kuwa sauran ƙawayen ko wacce sai gwalli da laƙaiƙaita take yi ko za ta yi sabon kamu a cikin abokan Angon.
Haka dai suka gudanar da hotuna cikin farin ciki da Annashuwa. Daga ƙarshe dai suka fice bayan sun yi sallama da Amarya da ƙawayenta cewa sai an zo kwasarsu zuwa gurin Dinner da za'ayi da misalin ƙarfe takwas na dare.
****
_Northern Crown Royal Event Centre_
Tun daga bakin ƙofar shiga, ƙawaye da dangin Amarya suka ƙara fahimtar cewa lallai Ma'aruf ya shirya ma bikin nan. Shi yasa a komai baiyi harkar ƙaranta ba.
Katangar wurin an yi da wani irin farin dutse mai sheƙi, sannan aka maƙale manyan fitilun crystal na ta walƙiya a saman ƙofar shiga. A gefe biyu na hanyar shiga akwai jerin furanni fari da ruwan hoda, waɗanda aka kawata da ƙananan fitilu masu launin zinariya.
Babban hall ɗin yana da rufin sama mai tsawo, akwai chandelier guda uku manya da suke rataye suna zubar da haske kamar taurari. Kujerun baƙi an lulluɓe su da farin satin, an ɗaure musu ribbon na golden colour a baya. Tebura kuma an kawata su da furanni masu ƙamshi da fitilun gilashi masu walƙiya.
A tsakiyar hall ɗin akwai wani dogon jan carpet da ya taso daga ƙofar shiga har zuwa kujerun Ango da Amarya, waɗanda aka ɗora a kan wani ɗan mataki mai zagaye da furanni. A bayan kujerun kuma an rubuta.
"Ma'aruf ❤️ Karima"
Da manyan haruffan zinariya masu ɗaukar idanu. Ƙamshin turarukan wuta da na furanni ya gauraye a cikin hall ɗin, hakan yasa duk wanda ya shiga cikin gurin sai ya ji kamar ya shiga wata duniya ta daban.
A can wani ɓangare kuma ɗuma-ɗuman sipiku ne na zamani suke fitar da sautin waƙar Umar M. Sharif ta Babbar rana cikin ƙurewar sauti.
Abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne saman hall ɗin, inda aka rataye dubban ƙananan fitilu masu kyalli kamar taurari, sai suka ba wurin wani irin yanayi mai kama da sarauta da alfarma.
***
"Sakina?."
Kamal ya kira sunanta da wani irin yanayin da shi kaɗai ya isa ya saka ta manta da hayaniyar wajen.
Ta ɗaga idanu a hankali ta kalle shi. Tunda aka fara hidimar bikin basu samu keɓewa ita da shi kaɗai ba sai yanzu, ya yi kyau matuƙa a idanunta.
Ya canja shaddarsa ta ɗazu daga fara kar zuwa milk colour, aiki mai sauƙi aka yi a jikin shaddar, amma da yake a jikin Kamal ne sai tayi wani irin kyau da ƙayatuwa na gaske. Agogonsa sai walƙiya yake yi a hannunsa. Hular kansa ta dace ƙwarai da shaddar, sannan ta zauna cas! A ƙoƙon kansa. A jikinsa sai wani irin tattausan ƙamshi yake tashi kamar ya yi ɓarin turare.
"Na’am."
Ta amsa a hankali bayan ta kauda kanta daga kallon ƙurillar da take masa.
A hankali ya ɗan sake ƙure tazarar da ke tsakaninsu, fuskarsa a marairaice ya ce
"Kin yi kyau Nutsuwata. Ina ma ace wannan taron bikinmu ne ake yi?"
Ba ta ce komai ba sai ɗan murmushi da ta sakar masa, sai kuma ta ɗaga hannunta da yasha zanen lalle ta rufe gefen fuskarta a kunyace.
A marairaice ya sake cewa
"Ki ce wani abu mana Sakina..."
"To ni me zan ce?"
Ta tambaye shi da zazzaƙar muryarta.
Kafin ya amsa ta sake cewa
"Mu ma in sha Allah kamar gobe ne namu taron idan muna raye... An kusa fa."
"Haka ne."
Ya amsa a taƙaice.
Sai kuma ya ɗan yamutsa fuska, a hankali yasa hannunsa na dama ya dafe saitin mararsa. Ya ɗan lumshe idanu na wasu daƙiƙu yana ɗan cije gefen bakinsa.
Ita dai duk tana hankalce da shi. Ta buɗe baki da nufin tambayarshi ko baida lafiya ne sai ya riga ta cewa
"Pls Nutsuwata Zo mu je ki rakani wani wuri."
Ta ɗan waiga ta kalli hall ɗin taron da ake daf da farawa. Sai kuma ta sake kallonshi. Da ɗan yanayin damuwa a muryarta ganin yadda idanunsa suka canja lokaci ɗaya bayan ya buɗe su ta ce
"Me ke damun Mijin Sakina? Ba ka da lafiya ne?"
Ya sake cije baki a karo na barkatai, da rashin walwala a fuska da muryarsa ya ce
"Ina jin kamar ba ni da lafiya... Tun ɗazu da Mubarak ya bamu wani maganin sanyi muka sha ni da Ma'aruf nake ji na ba daidai ba... Amma yanzu ne nake ji yanayin ya fi tsananta min, zo mu je ki raka ni in karɓi magani daga can sai in aje ki a gida."
Tayi narai-narai da idanu kamar za ta saka kuka, wannan shi ne ga ƙoshi ga kwanan yunwa. Ga damuwa da halin da yake ciki, ga shi tana son ganin yadda Dinner zai kasance, musamman da ya kasance ita ce babbar ƙawar Amarya. To amma kuma ya za tayi? Lafiyarsa shi ne gaba da komai. Don haka ba tare da ta sake raba ɗaya biyu ba kawai ta shige cikin motarsa, dama suna tsaye a jikin motar ne.
Tana niyyar ta ɗauko wayarta ta kira Amarya don ta faɗa mata halin da ake ciki sai ta ji yana magana da Ma'aruf ɗin ta wayarsa. Har ma ya ce ya faɗa ma Karima tayi haƙuri ya wuce da ita, hankalinsa bazai kwanta ba idan ya barta a gurin ba tare da yana nan don kula da duk wani motsinta ba. Tana ji Ma'aruf na yi mishi tsiya, bai amsa ba dai ya katse wayar.
Suna tafe a hanya sakan ɗaya biyu take jera mishi sannu yana amsawa ganin yadda yake tuƙi da ƙyar yana ciccije baki. Bata ankara da inda suke tafiya ba sai da ta kalli gefe da gefen titi ta ga sam bata gane inda suka nufa ba.
A hankali ta kira sunanshi
"Kamal?"
"Uhmm?"
Ya amsa a taƙaice.
"Ina za mu je?"
Ta tambayeshi kai tsaye.
Ya kalleta a fisge, sai kuma ya ɗan sakar mata murmushin ƙarfin hali.
"Kin dai san bazan cutar da ke ba ko?"
"Na sani."
Ta amsa a taƙaice tana jin yadda ƙirjinta ya buga da ƙarfi.
"To ki kwantar da hankalinki. Gida za mu je in sha magani sai in mayar da ke gida."
"Tam"
Ta amsa, amma har lokacin zuciyarta na bugawa da ƙarfi.
*Ina matan da suke fama da matsalar rashin haihuwa? Matsalar Sanyi? Ko Cancer ne matsalarki? Ko kuwa matsalar haihuwar daga gurin mijinki ne? To albishirinku, Muna da ingantaccen saiwoyin maganin rashin haihuwa, sanyi, da garukan magunguna Anti biotics masu kyau na ciwon Cancer. Magungunanmu tested and trusted ne. An gwada an dace ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba, Alhamdulillah! Masu son magani da gaske su tuntuɓeni ta wannan number ****