MUTUNCI MADARA...

BABI NA BIYU

by @fareedaabdallah

***

MUTUNCI MADARA...

©Fareeda Abdallah

Paid book ne. Kuɗin karanta labarin 1k kacal. Ki tura kuɗinki ta wannan account ɗin 7039080978, Opay, Farida Abdullahi, sai a tura min shaidar biya ta wannan numbern *** domin samun damar kasancewa a group ɗin da zan dinga posting ɗin littafin akan lokaci in sha Allahu.

2)

Daga waɗannan maganganun basu sake magana ba har ya isa ɗan madaidaicin gidansa mai kyau da ya gina kuma ya zuba komai na ciki da nufin idan Allah ya nufi aurensa da ita a nan za su zauna.

Har ya gama daidaita fakin ɗin motar a tsakar gidan bata dawo cikin nutsuwarta ba. Da wannan dalilin yasa ko da ya nemi ta shiga cikin gidan taso tayi mishi musu, amma da ya tafi luuu kamar zai kife a gurin bata san sadda ta fita da sauri ta riƙo gefen rigarsa ba. Duk da haka bata iya riƙe shi ba sai da ya kama ƙofar mota da sauri sannan ya hana kansa faɗuwa.

Ta cigaba da kallonshi da idanu masu cike da firgici.

"Kamal ba ka da lafiya... Mu je ciki ka sha magani ni ko baza ka iya mayar da ni ba sai in tari keke napep."

Bai iya amsawa ba, saboda wani irin rawa da jikinsa ya kama yi kar! kar!! kar!!! kamar ana kaɗa mishi ganga.

Yana damƙe da hannunta da ƙarfi har suka isa cikin falo, suka wuce ɗaya daga cikin ɗakunan barci uku da suke flat ɗin.

A falon ma ta so turjewa amma ya ƙi sakin hannunta. Suna shiga cikin ɗakin ya maida ƙofa ya rufe, sannan ya zube yaraf a ƙasa daidai ƙafafunta.

Idanunsa ciccike da hawaye ya haɗe hannayensa biyu alamar roƙo da magiya ya ce

"Don girman Allah Sakina..."

A kiɗime ta ja da baya tana kallonshi, don ita sam bata fahimci roƙon me yake yi mata ba. Da rawar murya ta ce

"In...in... ina maganin yake in ɗauko maka...?"

"Babu wani magani a gidannan sai ke Sakina..."

Ya faɗa a raunane, lokaci ɗaya hawayensa suka zubo sharrrr!! Abinda bata taɓa gani ba a tare da Kamal.

Idanunta a warwaje take kallonsa da matsanancin tashin hankali a fuskarta.

Shi kuma a wahalce ya cigaba da magana

"Wallahi ba na cikin hayyacina ko kaɗan. Babu abinda nake buƙata a yanzu sai ke Sakina... Idan ban same ki ba Wallahi Tallahi zan iya mutuwa... Don girman Allah ki taimaka min..."

A ruɗe, a kiɗime, kamar wacce bata fahimci maganganunsa ba ta ce

"Kamal mu tafi gida."

Ya ja gwuiyawunsa a gigice ya matsa kusa da ita. Cikin kuka ya cigaba da magana lokaci ɗaya yana sake damƙe mararsa.

"Wallahi Tallahi zan aure ki Sakina. Bazan taɓa fasa aurenki ba... Don Allah ki taimaka min.”

Hankalinta a tashe ta fisge ƙafafunta tace

"Kamal..."

Ya katse ta da sauri.

"Kar ki manta na kai kayan aure gidanku Sakina. Har Sadaki na daɗe da biya. Tun da na biya ko hannunki na taɓa riƙewa da gangar? Ko kuwa na taɓa nuna miki ba auranki zan yi ba?"

Ya jera mata tambayoyin hawayensa na ƙara ƙarfin sauka a kumatunsa.

"Abu ɗaya ne kawai ya rage a tsakanina da ke Sakina, wannan abun ba komai bane sai shafa fatiha."

Ya rarrafa ya sake damƙo ƙafafunta da ta tsaida su cak guri ɗaya, saboda maganganunsa sun fara karya mata jiki.

Cikin rawar murya ya cigaba da magana

"Wallahi kina raina Sakina. Duk duniya bayan mahaifiyata ke kaɗaice macen dana fi so fiye da komai. Ki taimaka min... Sau ɗaya kawai... Sau ɗaya kawai Nutsuwata..."

Numfashinta ya soma nauyi. Ta fara jan shi da ƙyar! A rarrabe ta ce

"Kar ka min haka Kamal... Kar ka sa na saɓa ma Mahalicci na..."

Wata irin ajiyar zuciya ya sauke a fisge. Kamar wanda yake shirin sumewa ya ce

"Sakina... ki taimake ni don Allah..."

Sai ta ji kalmar 'Don Allah' da ya faɗa mata a yanzu kamar an saka mata ita kai tsaye a zuciyarta. A wannan lokacin, sai shaiɗan ya samu nasarar rufe mata idanu, ba ta ganin komai sai soyayyar Kamal da irin kulawarsa a gare ta.

Shaiɗan bai bari ta sake tuna tsoron Allah yadda ya kamata ba. Ba ta tuna kyakkyawar tarbiyyar da iyayenta suka shafe shekaru ashirin da uku suna gina ta a kai ba. Ba ta tuna me zai je ya zo gobe ba.

Abin da kawai take gani a idanunta kuma take tunawa a zuciyarta shi ne. Mutumin da zai zama mijinta a kwanaki kaɗan masu zuwa.

Mutumin da take so fiye da yadda take son kanta.

"Kamal... Please..."

Muryarta ta fito a sanyaye.

Bai ce komai ba, sai ƙara rungume ƙafafunta da yayi sosai jikinsa na ƙara ɗaukar rawa.

Hawaye suka ciko a idanunta. Wani sashe na zuciyarta na faɗa mata kada ta yarda.

Amma soyayyarta na jan ta zuwa ga amincema buƙatar Kamal.

Dama a wasu lokutan, idan soyayya ta haɗu da amana... mace kan miƙa komai nata domin tana tsammanin an ba ta kariya. Ba tare da tuna wasu mazan, da zarar sun samu abin da suke nema, wani ɓangare na darajar macen kan mutu a idanunsu ba.

A hankali da zuciya mai cike da taraddadi Sakina ta buɗe baki da ƙyar ta ce

"Na amince... Amma sai ka ɗaukar min alƙawari baza ka taɓa fasa aurena ba..."

"Wallahi Tallahi ni Kamal bazan taɓa fasa auren Sakina ba. Ya Allah ka zama shaida."

Ya ƙarasa shan alwashin yana aika mata wani irin kallo...

Kallon da ya haɗu da sha’awa, da son mallakarta, da mayen maganin da ke yawo a jikinsa.

Ya miƙe tsaye da sauri. Za ta ja baya yayi saurin kamo hannunta ya manna a ƙirjinsa.

Ta ji yadda zuciyarsa ke bugawa da ƙarfi.

"Kin ji yadda zuciyata ke bugawa da matsanancin SO da SHA'AWARKI ko?"

Hawaye suka zubo mata.

"Ni tsoro nake ji..."

Bai bari ta ƙarasa magana ba ya rungumeta.

"Zan bi komai a hankali Sakina. Kamal bazai taɓa cutar da wacce ta kasance Nutsuwarsa ba."

Bata sake cewa komai ba. Ya ɗauki daƙiƙu yana shafa bayanta cikin rarrashi. Can kuma sai ya sumbaci goshinta. Ya cigaba da furta mata kalaman soyayya cikin raɗa. Lokaci ɗaya yana raba ta da kayan jikinta..

Sannu a hankali jikinta ya ƙara sanyi. Kuma a hankali ta fara rasa ƙarfin ture shi.

A wajen Kamal kuwa, dama sha’awa ta riga ta rinjayi hankalinsa.

Musamman idan ya tuna cewa nan da kwana kaɗan ma ai Sakina matarsa ce.

Shi ya sa bai ga girman abin da yake shirin aikatawa ba.

A wannan daren, Sakina tana ji tana gani tayi ma Kamal kyautar abin da ya fi kowace kyauta tsada a rayuwar ƴa mace. Ta yi mishi kyautar ne da zuciya ɗaya, zuciyar da ke cike da soyayya. Da amana. Da tabbacin cewa,

"Kamal bazai taɓa wulaƙanta ta ba.”

***

Bayan komai ya faru a tsakaninsu. Ɗakin yayi shiru cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara... Shiru mai cike da tunani, damuwa, taraddadi.

Sakina tana zaune a gefen gadon, hannayenta harɗe a ƙirjinta. Ta matse cinyoyinta kamar mai jin fitsari. A fili idanunta kallon ƙasa suke yi, amma sam ba ta ganin komai. Tunaninta ya yi nisa sosai fiye da inda take zaune.

Kamal kuwa na tsaye kusa da windon ɗakin. Ya zura hannu cikin aljihun wandonsa yana kallon duhun daren da ya fara mamaye unguwar. Wai don ma unguwar ta masu hannu da shuni ne, kusan ko wani gida da hasken Soler.

An ɗauki tsawon lokaci babu wanda ya yi magana a tsakaninsu.

Ba wanda ya san kalmar da ta dace ya fara furtawa ɗan'uwansa.

A hankali Sakina ta ɗaga hannunta ta goge wani hawayen da ya zubo mata ba tare da ta sani ba. Motsinta yasa Kamal ya waigo da sauri. Da sassarfa ya taka zuwa gare ta.

A tausashe, da wata irin kulawa ta musamman a muryarsa ya ce

"Sakina? Kuka kike yi?"

Bata ce mishi komai ba. A hankali ya zauna kusa da ita ya sake cewa

"Kiyi haƙuri... Don Allah kada ki yi kuka."

Sai a lokacin ta girgiza kai.

"Ba kuka nake yi ba."

Ta faɗa, amma muryarta ta bayyana akasin abinda bakinta ya faɗa. Muryarta na rawa, sannan akan idanunsa hawaye ya ɗiga ɗis akan kafet ɗin da ke shimfiɗe a gaban gadon.

Ya kamo hannunta da sauri.

"Haba nutsuwata. Wallahi babu abin da zai canja don wannan abun da ya faru a tsakaninmu. Ki kwantar da hankalinki pls!"

Sai a lokacin ta iya ɗaga idanu ta kalle shi.

Da ƙyar ta ce,

"Da gaske?"

"Da gaske mana."

Ya matse hannunta kaɗan alamun tabbatarwa.

"Har yanzu ke ce matar da zan aura. Har yanzu ke ce Nutsuwata. Har yanzu ke kaɗai ce ƴa macen da zuciyata ta amince ma inyi rayuwar aure da ita"

Wani sashe na zuciyarta ya so ya kwanta. Sai dai wani sashe ya ƙi kwanciya.

Saboda wani irin nauyi da ta ke ji a zuciyarta.

Nauyin da ba ta taɓa ji ba a rayuwarta.

"Kamal?"

"Na'am?"

Ya amsa da kulawa.

"Abin da muka yi..."

Da sauri ya katse ta.

"Kar ki sake tunani a kai."

Ta yi shiru tana sauke numfashi.

Sai ya cigaba da cewa,

"Wallahi ko da yau aka ce za a ɗaura mana aure zan yi farin ciki fiye da zatonki Sakina."

Maganarsa ya sa ta ɗan murmusa. Amma murmushin bai kai zuci ba.

Can wajen ƙarfe goma na dare ya mayar da ita gida. Tun kafin motar ta tsaya a ƙofar gida ta hango motar Yayanta a harabar gidan.

Ƙirjinta ya buga daram! Sai a lokacin ta tuna Dinner na auren Karima.

"Sauke ni a nan in shiga ciki."

Ta faɗa da sauri.

Kamal ya yi murmushi.

"Haba dai, a nan? Kamar wacce ta aikata wani laifi."

A karo na barkatai zuciyarta ta sake bugawa daram! Gaba ɗaya a tsarge take, gani take kamar kowa zai iya ganin abinda ta aikata a fuskarta.

Ba ta amsa maganarsa ba, a maimakon tayi magana ma sai ta buɗe ƙofar motar ta fita. Ta ɗaga ƙafa za ta wuce ya kira sunanta a tausashe.

"Sakina?"

Ta waiga a ɗan firgice tana kallonsa.

Ya haske ta da murmushi, sannan ya ɗaga mata hannunsa alamun bye bye.

"Na gode. Allah yayi miki albarka. Ki yi barci lafiya. Sannan don Allah ki daina damuwa."

Ta mayar masa da martanin murmushinsa cikin ƙarfin hali.

"Allah ya tashe mu lafiya."

"Amin ya Allah Nutsuwata, Matar Kamal har a Aljannah in sha Allahu."

A karo na biyu ta sake yi masa murmushi. Ta juya ta shiga gida da zuciya mai cike da ruɗani. Tun daga bakin ƙofar falon gidan ta fara jiyo hayaniyar ƴaƴan yayanta Sudais da Shuraim.

Matar Yayanta Lubnah ce ta fara hango shigowarta.

"Kun ga ƴar Halak da ta ƙi ambato. Ga ta nan ta dawo."

Nan take Mamanta, Yayanta Ibrahim, da yaran suka waiga suna kallonta. Yaran suka tafi da gudu suna yi mata oyoyo. Manyan suka bi ta da wani irin kallo da ya ƙara jefa ta a firgici, amma tayi iya ƙoƙarinta gurin fuskewa don kar ta tona ma kanta asiri.

"Sakina? Ina kika shiga ne? Daga ina kike?"

Yayanta ya tambayeta da fuska mara walwala.

Ta haɗiye yawu mai kauri, daƙyar ta ƙaƙalo murmushi ta ɗora a fuskarta sannan ta amsa da

"Laaa Ya Khalil Mummy bata faɗa maka ba? Yau ne auren Karima fa, mun je Dinner ne... Yanzu ma ba'a tashi ba Kamal ya ce in zo ya dawo da ni gida..."

"Ya kyauta kuwa, domin dare ya fara yi. Yanzu dai je ki canja kaya ki zo mu gaisa. Dama mun tsaya jiran ganin dawowarki ne kafin mu wuce gida."

Aunty Lubnah matar Ibrahim ta katse tuhumar da yake niyyar yi ma Sakina.

A fakaice, ba tare da ta bari kowa ya lura ba ta sauke nannauyar ajiyar zuciya. Ta amsa ma Aunty Lubnah da murmushi a fuskarta, sannan ta kalli mahaifiyarsu a tausashe ta ce

"Mummy barka da hutawa."

Mummy ta amsa mata cikin kulawa. Ta shafa kan yaran, da murmushi a fuskarta ta ce musu tana zuwa. A nutsenta kamar yadda ta saba tafiya a hankali ta nufi hanyar da zai sada ta da ɗakinta. Sai da ta tabbatar ta ɓace ma ganinsu sannan ta ɓata fuska, ta cije baki, tana jin tsananin zafi a ƙasanta saboda abinda ya faru da ita, ga shi kuma bata samu wadataccen lokacin yin gashi yadda ya kamata ba.

Ko da ta shiga ɗakinta, hurgi tayi da jakanta a kan gado, kai tsaye ta wuce bayi. Ruwa mai zafi-zafi ta tara a baho ta shiga ciki, tsananin zafi yasa ta runtse idanu tana gumtse baki don kar ta kwarma ihu. Mintuna kaɗan tayi a cikin ruwan ta zubar, ta tara wani ruwan tayi wanka a gurguje, sannan ta fita daga cikin bayin. Bata ɓata lokaci ba ta fice zuwa gurin Yayanta da matarsa, wacce suke tsananin shiri kamar ita ce ƴar'uwarta ba Ibrahim ba.

****

A wannan daren, duk yadda Sakina taso barci ya ɗauketa ya gagara. Da ta runtse idanu babu abinda take gani sai abinda ya faru tsakaninta da Kamal.

A karo na farko cikin rayuwarta, ta ji tsoro, sai tunani take wataƙila ta aikata kuskuren da ba za ta iya gyarawa ba.

Amma a can wani sashe na zuciyarta, yana ta maimaita mata waɗannan kalaman.

"Kamal yana son ki. Kamal zai aure ki.

Kamal ba zai taɓa cutar da ke ba."

Waɗannan kalaman su kaɗai ke ƙwarara mata gwuiwa, har ta ji hankalinta ya kwanta kaɗan.

Ina matan da suke fama da matsalar rashin haihuwa? Matsalar Sanyi? Ko Cancer ne matsalarki? Ko kuwa matsalar haihuwar daga gurin mijinki ne? To albishirinku, Muna da ingantaccen saiwoyin maganin rashin haihuwa, sanyi, da garukan magunguna Anti biotics masu kyau na ciwon Cancer. Magungunanmu tested and trusted ne. An gwada an dace ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba. Masu son magani da gaske su tuntuɓeni ta wannan number ***