MUTUNCI MADARA...

BABI NA UKU

by @fareedaabdallah

***

MUTUNCI MADARA...

©Fareeda Abdallah

Paid book ne. Kuɗin karanta labarin 1k kacal. Ki tura kuɗinki ta wannan account ɗin 7039080978, Opay, Farida Abdullahi, sai a tura min shaidar biya ta wannan numbern *** domin samun damar kasancewa a group ɗin da zan dinga posting ɗin littafin akan lokaci in sha Allahu.

3)

Washe gari duk da ya kasance lahadi, da sassafe Sakina ta fito ta fara aikace-aikacen gidan kafin kowa ya fito. Ba don ta samu wadataccen barci a nutse ba, sai don kasa samun lafiyayyen barci na tsawon daren da ta yi. Duk yadda ta so yakice tunanin al'amarin a ranta ta kasa. Kaso mai yawa na tunaninta da na sani ne, wanda bahaushe ya kira da ƙeya.

Amma ta san bata isa goge abinda ya faru ba. Wanda wani sashe na zuciyarta ke ɗauka a mummunan ƙaddara.

Abin da ya faru ya riga ya faru. Kuma ba za a iya mayar da hannun agogo baya ba. Don haka sai dai kawai a kiyaye gaba.

Ta ja nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, ta cigaba da ayyukanta tana yi tana Istigfari. Zuwa ƙarfe bakwai da minti arba'in da biyar na safe ta gama komai, hatta abinda za su karya da shi ta gama ta jera akan teburin cin abinci. Sannan ta wuce ɗakinta don yin wanka.

Tana fitowa wanka daga can cikin falon gidan ta dinga jiyo muryar mahaifiyarta tana magana da wata mata. A nutse ta shirya, sannan ta fita falon, tana tafe a hankali.

Da sallama a bakinta ta shiga cikin falon. Mummy ta amsa tana kallonta.

"Himma ba ta ga rago Autana. Ina can ina barci ashe har kin tashi kin yi ayyukan gidan?"

"Eh Mummy."

Ta amsa a hankali.

A karo na farko, iya tsawon rayuwarta ta ji kunyar haɗa idanu da Mummynta. Ba kuma wai don Mummy za ta fahimci wani abu ya faru da ita ba, saboda tsawon daren da ta ɓata tana tunani akai-akai take shiga banɗaki tana gasa jikinta da ruwan zafi. Shi yasa hatta tafiyarta yanzu ya koma normal yadda take yi.

Ta ji kunyar haɗa idanu da Mummynta ne saboda ita a karan kanta ta san ta ci amanan irin kyakkyawan tarbiyar da suka yi mata. Ba ma kamar ita Mummyn da ko wane lokaci tana tare da ita. Domin Abbansu yana aiki ne a Abuja, duk ƙarshen sati yake dawowa yayi musu hutu.

"Ina kwana Mummy? Maman Haidar ina kwana?"

Ta katse tunanin da take yi ta hanyar gaida Mummy da baƙuwar maƙwafciyarsu da ta tarar a falon.

Suka amsa mata da kulawa, Mummy ta ƙara da tambayarta

"Ba ki da lafiya ne?"

Da sauri Sakina ta girgiza kai.

"Lafiyata ƙalau Mummy. Me kika gani?"

Mummy ta ƙara kallonta na wasu sakanni, sai kuma ta ce

"Gani nayi kin yi wani iri haka. Ko duk gajiyar bikin ne?"

"Gajiyar ma akwai ta Mummy."

Tayi saurin fakewa tunda ta samu mafaka.

Sai kuma ta bar gurin da sauri don ma kar Mummy ta sake turketa da wani zancen. Kai tsaye ta nufi ɗakin Mummy ta nufa don duba ko su Sudais sun tashi, cikin sa'a kuwa tana shiga sai ta tarar da su sun tashi suna miƙa. Suna haɗa idanu da ita suka washe baki suna yi mata oyoyo, ta ƙarasa gurinsu da dariya.

Sai kuma ta saki ranta ta manta da tunanin komai ta kama hidimar yaran, cikin ƙanƙanin lokaci ta ware gaba ɗaya. Yini tayi cikin yaran suna wasa da dariya.

Ko gidansu Karima da ya kamata ace ta koma saboda yau za a kai Amarya gidanta ƙin komawa tayi, ta fake da cewar ba ta da lafiya, kanta na ciwo sosai baza ta iya da hayaniya ba. A dole Mummy ta ƙyale ta ita ta tafi gidansu Kariman, ta bar Sakina da yaran a gida.

****

A wannan rana, ita da kanta baza ta iya ƙayyade yawan kiran da Kamal yayi mata ba. Domin ko daga sassafe da ta bar wayarta a ɗaki zuwa ƙarfe goma sha ɗaya na safe Misscalls ɗinsa goma sha tara ta taras.

A lokacin, riƙe wayar a hannunta tayi tai shiru ta ƙura ma lambarsa idanu. A zuciyarta take kallon abinda ya faru jiya tsakaninta da Kamal. Wayar na riƙe a hannunta kiransa ya sake shigowa.

Kamar baza ta ɗaga ba, sai kuma ta ɗauka, jikinta a sanyaye. Kafin ta ce komai ya fara yi mata magana da damuwa da kulawa a muryarsa.

"Nutsuwata... Kina lafiya? Allah yasa ba ciwo kike yi ba har kika kasa ɗaukar wayata? Na damu... Wallahi na damu da halin da kike ciki... Dama jira nake yi idan sha biyun rana tayi baki ɗauka ba zan zo gidan da kaina in duba lafiyarki. Ya jikinki? Hope dai babu inda yake yi miki ciwo? Kiyi haƙuri Babe. Ga lokacin da ya dace in tarairayeki amma ya zo mana a wani irin yanayi... Kiyi haƙuri... Ki yafe..."

"Ya jikinka?"

Ta katse jerin maganganu da tambayoyin da yake mata hankalinsa a tashe.

"Jikina da sauƙi Nutsuwata. Na ji sauƙi sosai. Abinda ke damuna a yanzu kawai damuwar halin da kike ciki ne..."

"Ka kwantar da hankalinka. Nima lafiyata kalau. Babu abinda yake damuna. Ka yi ta kira ban ɗauka bane saboda na bar wayata a ɗaki, ni kuma ina falo da su Sudais."

"Alhamdulillah! Tunda lafiya kike Alhamdulillah, babu komai Sakina. Dama damuwata ace rashin lafiya ce ta hana ki ɗaukar wayar."

Hira ya cigaba da janta da shi, ita kuma tana amsa mishi a taƙaice. A dole dai ya katse wayar bayan sun ɗauki mintuna suna hiran da mafiyawancin maganganun shi yake yi.

Tun daga wannan wayar kuma kusan duk bayan awa ɗaya sai wayarsa ta shigo mata. Idan ta ɗauka kuma babu wata ƙwaƙƙwarar magana sai zallar kulawa da tarairaya da yake nuna mata.

"Wane hali kike ciki?"

"Kin ci abinci?"

"Kin yi barci?"

"Har yanzu kina fushi da ni ne?"

Da farko amsoshinta a taƙaice ne, jikinta a sanyaye. Daga baya kuma a hankali ta fara sakewa. Tana amsa mishi da walwalarta.

Ko da yamma tayi, ta ce mishi baza ta koma gidansu Karima don kai amarya ba kai tsaye ya goya mata baya, har ma ya ce mata shi ma ya fasa zuwa. Duk da kuwa a lokacin Ango na ta kiransa yana uzzura masa akan duk abokan sun haɗu shi kaɗai ake jira.

"Me yasa baza ka je ba?"

Sakina ta tambayeshi cikin sanyin murya.

"Saboda ke ma baza ki je Nutsuwata."

Ya amsa mata kai tsaye.

Kafin tayi magana ya sake cewa

"Kin taɓa ganin gangar jiki cikin kwanciyar hankali alhali babu nutsuwarsa a tare da shi?"

"A'a!"

Ta amsa tana murmushi.

"To kamar haka ne kike a tare da ni Sakina. Ke nutsuwata ce. Bazan taɓa samun kwanciyar hankali ba idan ba kya nan a inda ya kamata a ce muna tare. Don haka dole Ma'aruf yayi haƙuri. Bazan sami zuwa ɗaukar Amaryarsa ba..."

"To idan ya kira ka me za ka ce mishi?"

Ta katse shi da tambaya, duk da kuwa a zuciyarta daɗi ne take ji matsananci saboda tsananin soyayyar da yake nuna wa akanta da duk abinda take so.

"Kai tsaye zan faɗa masa bazan sami zuwa ba. Saboda bakya jin daɗi..."

"Ni dai a'a!"

Ta katse shi a shagwaɓe.

"Don Allah ka je. Na yarje maka ka je, ka ga ni da kai ne manyan aminan Amarya da Ango. Da wannan dalilin kuwa bai kamata a ce ni da kai duk ba ma nan ba. Don Allah ka je, ka ji mijin Sakina?"

Yai shiru, kamar bazai amsa mata ba. Can kuma sai ya ce da murya ƙasa-ƙasa.

"Ni dai Allah ya sani ba na son zuwa..."

"Ka yi haƙuri... Ai domin ni za ka je. Ko ba ka son ka faranta min...?"

"Ina so Wallahi."

Ya amsa da sauri. Ya cigaba da magana.

"Zan je, tunda kina so. Bari ma in shirya in tafi."

Tana dariya ta amsa da

"Yauwa Mijin Sakina. Allah ya nuna mana ranar aurenmu."

"Amin thumma Amin."

Ya amsa da farin ciki sosai a fuska da muryarsa.

Suka yi sallama. Suka rabu suna farin ciki.

****

Ko da ya je can bai manta da ita ba. A kai-akai yake kiranta, har zuwa can dare, misalin sha ɗaya da minti biyar. Lokacin ne ya koma gida, bayan sun damƙa Ango a hannun Amaryarsa.

Har ta kwanta ya tura mata saƙon message

"Wallahi ina sonki fiye da komai Sakina."

Haka tayi ta karanta saƙon tana jin daɗi, a zuciyarta take sake jaddada ma kanta ba komai fa. Abinda ya faru ba komai bane. Babu abinda zai canja a tsakaninsu. Domin da zai canja, da tun yau ya fara canjawa. Babu komai. Abinda ya faru a tsakaninsu abu ne da yake yawan faruwa a tsakanin masoya guda biyu. Ba komai bane, in Allah ya yarda.

******

Kwanaki suka cigaba da tafiya kamar komai bai faru ba. Rayuwa ta koma yadda take ako wani ɓangare. Komai na tafiya daidai. Soyayya tsakanin Sakina da Kamal ya ci uban na da.

Domin kulawar Kamal akanta ya ninka na da.

Soyayyar da yake nuna mata ta ƙaru sosai.

Wannan dalilin ne ya sa a hankali ta watsar da damuwar komai da ya taɓa faruwa a tsakaninsu.

Wata ranar juma'a, da ya kama kwanaki ashirin cif da faruwar komai a tsakaninta da Kamal, misalin ƙarfe goma sha biyu da kwata na dare. A daren ya je gurinta sun daɗe suna hira, sun rabu lafiya kalau cikin farin ciki da dariya da soyayya.

Tana tsakiyar barci kamar a mafarki sama-sama ta dinga jin vibrating ɗin wayarta. Idanunta a rufe tasa hannu ta lalubo wayar a gefenta, ta ɗaga kiran, ba tare da duba suna ko lambar da ke kiranta ba.

"Helloooo..."

Ta faɗa ƙasa-ƙasa da magagin barci a muryarta.

"Sak...ki...naaaa... zan mutu..."

Ta ji muryar Kamal yana faɗa mata haka da ƙyar cikin shaƙewar murya.

Kamar wacce aka sheƙa ma ruwan ƙanƙara aikuwa a firgice ta wartsake tana jan salati da sallallami.

"Kkkkaakamal? Menene? Me yake faruwa? Me yake damunka?"

Ta jero mishi tambayoyin a kiɗime.

Bai amsa ba sai katse wayar da yayi. Hankalinta a tashe kuma tayi ta kiranshi bai ɗauka ba, sai da ta kira sau huɗu ba amsa. Izuwa lokacin hankalinta ya kai ƙololuwa gurin tashi.

Tana niyyar danna mishi kira na biyar sai ga shi ya kira ta, amma kiran Vidio. A kiɗime ta ɗaga, ta ma manta yanayin da take ciki na daga ita sai ƴar rigar barci saboda tashin hankali.

Kwance akan katifa, yayi ruf da ciki. Hannayensa duk biyu suna ƙasan mararsa. A jikinsa daga vest fara kar sai gajeren wando, idanunsa da ya ƙure ta da kallo sun kaɗa sun yi jajur, a cikin kwarmin idanunsa har da wasu kwantattun hawaye. Laɓɓansa ma sun yi jajur, saboda yadda yake ta tsotse su yana ɗan taune su saboda tashin hankali da ciwon da yake ciki.

"Kamal? Menene? Me yake damunka?"

Ta sake jera mishi tambayoyin a kiɗime.

"Sha'awar nan baza ta barni ba Sakina..."

Ya faɗa mata a hankali.

Wasu ƙananun hawaye suka gangaro a gefe da gefen idanunsa. Ya cije laɓensa na ƙasa, a hankali da murya mai bayyana matsananciyar jin ciwo ya cigaba da cewa

"Tun a wancan lokacin da na sha maganin nan na Mubarak ba tare da sanina ba ashe sai masu aure suke shan maganin, Wallahi ni kaɗai na san wahalar da nake sha kafin in iya yin barci ako wane dare... Ko bayan da abinnan ya faru a tsakaninmu, sauƙin na daren kawai na samu... Kullum wahala kawai nake sha Sakina... Ba na faɗa miki ne saboda ba na so in ɗaga miki hankali... Ko yau ma da na faɗa miki lamarin ya fi ƙarfina ne... ina ga... ina ga mutuwa kawai zan yi Sakina..."

"In sha Allahu baza ka mutu ka barni ba Kamal. Baza ka mutu ba in Allah ya yarda."

Ta amsa cikin kuka.

Bai ce komai ba sai runtse idanu da yayi da ƙarfi, can kuma tana kallonsa sai ya fara juye-juye yana ƙara damƙe mararsa. Da yake ya ajiye wayar a fuskar gadon ne, shi yasa take kallon duk abinda yake yi, akan idanunta yai ta malelekuwa akan gadon cikin tsananin ciwon mara.

Tana ta kuka tana jera mishi sannu, sai da ciwon ya ɗan sassuta mishi sannan ta ce ko zai je ya jiƙa Lipton da lemun tsami? Wata kila ciwon ya lafa mishi gaba ɗaya.

Wayar ya ɗaga ya nuna mata kofunan da yasha Lipton har guda biyu, sannan ya nuna mata wani sachet ɗin magani da ya je asibiti Likita ya bashi, duk ya sha basu yi mishi amfani ba. Yana yi mata wannan bayanin ɗif! Kiran ya katse.

Da sauri ta bi bayan kiran, sai ta ji bai shiga ba. Ko da ta kira shi normal call kuma sai na'ura ta faɗa mata wayar a kashe take. Hankalinta idan yai dubu duk sun tashi. A taƙaice ta yi mishi kira ya fi sau talatin ana sanar da ita wayar a kashe take.

Ga damuwa ga takaici, da tashin hankali yayi mata yawa kawai sai ta dungurar da wayar ta fashe da kuka. Zuciyarta cike taf da tausayin Kamal, da tunanin halin da yake ciki. Kashe waya haka kawai lafiya kalau ba tare da ƙwaƙƙwarar dalili ba ba ɗabi'arsa bace.

Shi yasa yanzu ko da ta ji wayar a kashe tasa a ranta kawai ciwo ne yasa shi kashe wayar. A yadda take ji kamar tayi tsuntsuwa ko kuma ta rufe idanu ta buɗe ta ganta a kusa da shi.

Ta daɗe tana kuka, da ƙyar ta rarrashi kanta, ta ɗauko wayar ta sake danna mishi kira, har lokacin wayar a kashe. Jikinta a sanyaye ta ajiye wayar ta kwanta, nannaɗe jikinta tayi a bargo tayi shiru tana tunanin halin da yake ciki. Ta daɗe sosai kafin raba da rabin barci ya ɗauketa daf da Ladan zai ƙwala kiran sallar farko.

Rashin samun barci shi yasa ta makara, ƙarfe shida saura ta farka. Saboda da tunanin Kamal ta kwana har tana mafarkinsa shi yasa kafin ta je bayi ta ɗauro alwala sai da ta kira lambarsa, sai dai abin takaici da ƙarin damuwa a gare ta shi ne har lokacin wayarsa a kashe.

Jikinta sanyi ƙalau ta je bayi tayi alwala, tayi sallah. Sannan ta fita tsakar gida ta kama aikace-aikacenta. Komai tana yi ne cikin sanyin jiki da rashin ƙarfi, shi yasa ta daɗe bata gama ba.

Da yake tun jiya ta faɗa ma Mummy yau za ta je gidan Karima ta duba ta, domin tun da aka kai Amarya bata je ba. Tun Kariman tana roƙon ta zo har ta gaji ma tayi fushi, sai yau tayi niyyar zuwa duba ta.

Da wannan dalilin yasa ta shirya da wuri. Ƙarfe goma da kwata tayi sallama da Mummynta ta tafi. Sai dai ko ta fita, a maimakon ta wuce gidan Karima kai tsaye, sai kawai ta wuce gidan Kamal.

Ai kuwa kamar yadda ta zata, ta tarar da shi cikin rashin lafiya. Har lokacin mararshi na ciwo, amma kuma a lokacin zazzaɓi ya fi damunshi.

Da farko yana zaune ne a gefenta kan doguwar kujera. Daga baya kuma sai ya zame ya kwantar da kanshi a kafaɗunta, da yaga bata hana shi ba, sai kawai ya kwantar da kanshi a cinyarta yana jan numfarfashi sama-sama.

Sakina dai tana jin shi. Bata iya hana shi ba saboda tausayinshi take ji. Zuciyarta cike take da matsananciyar tausayinsa. Kuma ko ba ma haka ba Kamal ɗinta ne fa? Wanda ya kai komai na aure gidansu. Shafa fatiha kawai ya rage a tsakaninsu.

Bayan duk wannan ma ai mu'amala ta riga ta shiga tsakaninsu, to me ya rage? Me za ta ɓoye mishi? Tana wannan tunanin kawai sai ji tayi ya cusa hannunsa a cikin rigarta yana laluben na shanunta da suka cika gaban riga taf! A tare ita da shi suka sauke nannauyar ajiyar zuciya.

Daga haka dai Sakina baza ta ce ga abinda ya faru ba. Da haɗin kanta da na Kamal, da sharrin shaiɗan, a karo na biyu Mu'amalar auratayya ya sake shiga tsakaninta da Kamal.

*****

Littafin marubuciyar👇🏽

1)A DALILIN ƊA NAMIJI

2)BARA A KUFAI

3)DUNIYA SABUWA

4)INUWAR MUTUWATA

5)SANADIYYA

6)TSAKANINA DA MUTUWA

7)BILHAƘƘI

8)RABON AYI (KUSKURE NA, YOUTUBE)

9)TUBALIN TOKA...

10)LOKACI

11)RANAR NAKA...

12)GUDUN GARA...

13)ƘASAITACCIYAR MACE...

14)BA NI DA IKO...

15)MUTUNCI MADARA...

Bononza ga masu son karanta littattafaina gaba ɗaya su biya 3k. Har da wannan sabon da nake rubutawa a yanzu. A tura kuɗin a acc ɗina da ke saman page sai ayi min magana domin samun littattafan gaba ɗaya. Na gode.

Ina matan da suke fama da matsalar rashin haihuwa? Matsalar Sanyi? Ko Cancer ne matsalarki? Ko kuwa matsalar haihuwar daga gurin mijinki ne? To albishirinku, Muna da ingantaccen saiwoyin maganin rashin haihuwa, sanyi, da garukan magunguna Anti biotics masu kyau na ciwon Cancer. Magungunanmu tested and trusted ne. An gwada an dace ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba. Masu son magani da gaske su tuntuɓeni ta wannan number ***