MUTUNCI MADARA...

BABI NA HUƊU

by @fareedaabdallah

***

MUTUNCI MADARA...

©Fareeda Abdallah

Paid book ne. Kuɗin karanta labarin 1k kacal. Ki tura kuɗinki ta wannan account ɗin 7039080978, Opay, Farida Abdullahi, sai a tura min shaidar biya ta wannan numbern *** domin samun damar kasancewa a group ɗin da zan dinga posting ɗin littafin akan lokaci in sha Allahu.

4)

Shi zunubi duk sadda ya faru sunanshi zunubi, babu sabon zunubi babu tsoho. Duk sadda bawa ya aikata zunubi in dai akwai ɓurɓushin Imani ko ɗan kaɗan ne a tare da shi to fa lallai wannan bawa dole sai ya ji babu daɗi a zuciyarsa.

Irin haka ne ya faru da Kamal da Sakina. Duk da da haɗin kansu da son zuciyarsu komai ya faru, sai da komai ya kammala sai kuma suka afka cikin ƙunci, damuwa, da na sani.

Ba ma kamar Sakina, har tana kuka. Daƙyar Kamal ya rarrasheta da tausasan kalamai, yana sake jaddada mata lallai fa shi ne mijinta. Don haka ta kwantar da hankalinta, kayansa ne, halaliyarsa ne, mallakinsa ne yake amfana daga albarkatunsu.

Kawai dai kuskuren shi ne ɗan gajen haƙurin da yayi wajen jiran waɗannan kayayyaki nasa har zuwa sadda za'a mallaka mishi su. To amma kuma ya zaiyi? Lalura ce, da ƙaddarar sha'awar da ta taso mishi sanadiyyar shan lafiyayyen maganin sanyi wanda ke motsa duk wani lafiyayyen namiji.

Ya sake jaddada mata ta kwantar da hankalinta. Domin babu abinda zai hana shi aurenta sai dai idan mutuwa yayi. Da waɗannan zaƙaƙan kalaman ya shawo kanta ta daina kukan da take yi. Kamar miji da mata, haka ya ɗauke ta cak zuwa banɗaki ya gasa kayanshi, a gurin wankan ma sai da ya sake mammatseta, sannan da ƙyar ya barta tayi wankan tsarki ta fita, shi ma yayi.

A gurguje suka shirya ya ɗauketa a mota zuwa gidan Karima, lokacin ana ta kiraye-kirayen sallar azahar a masallatai.

Don haka yana sauketa suka wuce masallaci shi da Ma'aruf. Ita da Karima kuma suka ƙule can uwarɗakinta suna labarin bayan rabuwa. Kamar sun ɗauki watanni basu haɗu ba.

Kamar mafiyawa daga cikin amaren wannan zamani da basa iya riƙe sirrin mu'amalar auratayyarsu, haka Karima ta zage tana ta zuba ma Sakina labarin irin wahalar da ta sha a daren farko, da sauran dararen da suka biyo baya kafin ta zama ƴar gari. Da labarin irin tarairayar da Ma'aruf yake yi mata saboda tsananin gamsuwar da yake samu a tare da ita. Da yadda ita ma yanzu ta zama ƴar gari, ba ƙaramin daɗi da gamsuwa take samu a mu'amala da mijinta ba, musamman da ya kasance wayayye, kafin ya je mata kai tsaye sai ya gama isar mata da ƴan saƙonninsa ya kunna ƙwayayen lantarkinta gaba ɗaya...

Ita dai Sakina haka tai shiru tana sauraren Karima cike da shauƙi, gurin tsoro ta zazzare idanu kamar gaske bata san wahalar da ake sha ba. Gurin dariya tayi dariya, gurin shauƙi ta lumshe idanu. A zuciyarta babu abinda take hasashe sai ita da Kamal a irin wannan duniya da Karima take ba ta labari.

Duk da ita ma a yau ta tabbatar da wasu maganganun na Karima. Domin tabbas sadda Kamal ya zura hannu a cikin rigarta yana lugwuigwuitata tsakani da Allah ita ma ta ji wannan daɗin da Karima take magana. Musamman da ya kafa bakinshi a...

Dukan da Karima ta ɗaka mata a cinya shi ya dawo da ita duniyar tunanin da ta afka.

"Daɗina da ke wasu lokutan ke fa banza ce Sakina. Ina ta magana kin yi min shiru kina tunani, tunanin me kike yi?"

Karima ta tambayeta tana dariya.

"Uhmmm"

Sakina ta faɗa tana sosa inda Karima ta duke ta.

"Amma dai Wallahi ke muguwa ce Karishma. Wannan dukan ai sai ki ɗaye min fata"

A tare su biyun suka ƙyalƙyale da dariya. Sai kuma suka canja akalar hirar zuwa yadda aka ƙarƙare bikin ba tare da Sakina ba. Da yadda ƙawayensu suka rabe kuɗin sallamah ba tare da sun raba da Sakinan ba.

****

A ɓangaren Kamal da Ma'aruf, hirarsu ta fi ƙarfi ne akan zuzuta kyawun magungunan sanyi da na ƙarfin maza da abokinsu Mubarak yake saidawa. Ma'aruf cikin dariya da Annashuwa yake tabbatar ma da Kamal shi fa ya ga guri, domin ada can baya kafin yasha maganin shi a tsammaninsa ma bai da ƙarfin da zai iya kula mace duk bayan kwana biyu.

Sai ga shi sanadiyyar magungunan Mubarak jin sa yake gadagau, kamar ɗan saurayin doki majiyin ƙarfi. In banda tausayin Karima da yake ji a wasu lokutan ai shi zai iya shafe tsawon ko wane dare yana kashe arna bai gaji ba.

Taɓe baki Kamal yayi, alamun hirar ba wani ɗaɗa shi da ƙasa yayi ba. Kai tsaye ba wani kwana-kwana ya ce

"Ai kuwa dai Wallahi ka bi a hankali, don shi wannan rijiya da kake gani masana sun tabbatar da duk yadda kake ji da ƙarfin sukuwa baza ka taɓa iya ƙure zurfinsa ba. Kuma ko ba haka ba a Likitance ma yawan yin bai da wani amfani, musamman ma ace sai da taimakon magunguna ake samun ƙarfin yin. Amma ba a yanzu ne za ka fahimci haka ba, sai can gaba lokacin da kana ji kana gani ga fura da nono amma ba ka da ludayin sha..."

"Aniyarka ta bika. Bakinka ya sari ɗanyen kashi. Kada Allah ya nuna min wannan lokacin a rayuwata."

"To Amin. Amma fa lallai da gaske idan ba ka son ganin wannan lokacin ka daina amfani da magungunan ƙarfin nan, ka tsaya a iya halittar da Allah yayi maka."

"Kamal kenan! Mu bar wannan maganar kawai."

Ma'aruf ya faɗa yana dariya. Kafin Kamal yayi magana sai ya cigaba da cewa

"Na yi maka uzuri, tunda kai har yanzu kifin rijiya ne. Ka ga kuwa ƙauye bai san asirin birni ba. Muna nan da kai, bayan bikinku za mu maimaita wannan hirar."

Shi ma Kamal dariya yayi kawai. Bai cigaba da jan maganar ba domin ya fahimci Ma'aruf ya fara nisan da bazai ji kira a sauƙaƙe ba. Shi kuma jikinsa babu ƙarfi sosai. Don haka bai shirya ƙarasa jigatar da kansa akan gaddama da Ma'aruf ba.

******

Kwanaki huɗu tsakanin wannan ranar, Sakina ta fito daga gida za ta tafi Islamiyar da take zuwa can bayan layinsu. Kiran Kamal ya shiga cikin wayarta, ko da ta ɗauka irin numfarfashin da ta ji yana ja a wahalce kamar mai shirin mutuwa shi ya alamta mata halin da yake ciki.

Bata ce komai ba ta katse wayar. Amma maimakon ta ƙarasa Islamiya, sai ta tare keke napep ta wuce gidansa.

Ta je ta tarar da shi cikin mawuyacin hali, ai kuwa ba tare da damuwar komai ba ta cire hijabi ta fara bashi taimakon gaggawa kamar yadda ta saba.

Sai dai a wannan karon, abubuwa biyu masu muhimmanci sun faru a tsakaninsu. Abu na farko shi ne, duk mu'amalar auratayya da suka yi da duk wasannin da suka yi a yau, Kamal ya ɗauka Vidio a wayarsa. A cewarsa, duk sadda sha'awa da kewarta suka taso masa zai dinga kunna Vidiyoyin yana kalla har sai ya samu nutsuwa.

Abu na biyu da ya faru a tsakaninsu shi ne, ya tabbatar mata daga wannan ranar ko da sha'awa zai kashe shi bazai ƙara nemanta ba, har sai bayan sun yi aure. Don ba ya so ya gama shanye romon democraɗiyyarsa tun a waje.

Sun rabu daf da za'a tashe su islamiyya. Sun rabu zukatansu na farin ciki. Ba ma kamar Sakina, saboda a yau tabbas ta ji daɗin mu'amalarsu ba kaɗan ba. Sannan kuma ta ji daɗi da ya ce bazai ƙara nemanta ba sai bayan sun yi aure.

Tana shiga unguwarsu ta ga ƴan ajinsu na dawowa daga islamiya. Kawai itama sai ta fuske ta bi ayari, kamar dai itama daga makarantar take.

Kwanakin da suka biyo baya komai ya ci gaba da tafiya dai-dai tsakaninta da Kamal. Soyayyarsu ta cigaba da tafiya zam-zam fiye da baya. Yana bata kulawa, yana tarairayarta. Minti ɗaya biyu zai kira ta a waya don jin halin da take ciki. Dama a gidansu ya daɗe da zama ɗan gida, idan ya je hira har Falo yake shiga.

Ire-iren siyayyar da yake mata da kuɗaɗen da yake sakar mata kuwa kamar ba aurensu ne ya matso ba. Da waɗannan dalilan yasa ita ma sam ba ta ƙyashin yin duk abinda ta san zai faranta masa rai. Kamar misalin ƙirƙiran sabbin zaƙaƙan kalamai tana faɗa masa don faranta masa rai. Da yawan kiransa ko da bai kira ba.

Har wata ɗabi'a ta tsira wacce a baya sam ba halinta bane, wannan ɗabi'ar shi ne ɗaukar hoto ko vidiyon tsiraicinta tana tura ma Kamal. A tunaninta, ganin wannan zai ƙara kwantar masa da hankali daga lalurar da take damunsa.

Kuma a yadda ta fahimta sosai hakan da take yi ke faranta masa rai. Yana nuna mata jin daɗinsa a fili, shi yasa ita kuma ta zage ta cigaba da bin duk hanyar da ta san za ta faranta mishi.

Kwanakin bikinsu na ƙara matsowa, ko wane ɓangare su na cigaba da shirin bikinsu hankali kwance. Saboda tsananin son da yake mata duk siyayyar kayan lefen da yake yi sai ya tura mata a hotuna da vidio ta zaɓi wanda take so, sannan zai siya ya kaima mahaifiyarsa.

******

A ranar da bikinsu ya rage saura kwanaki goma sha bakwai cif! A ranar Sakina ta fara lura da wani irin sauyi da ya soma shiga tsakaninta da Kamal.

Sauyin da Sakina ta kasa fassara shi da farko, sai daga baya ta fahimta... Ba komai ta fahimta ba kuwa sai zargin ta da Kamal ya fara yi.

Suna hira ne a falonsu, wayarta na hannunta tana dannawa lokaci bayan lokaci, kawai sai saƙon Karima ya shigo mata, bata san hankalinta ya ɗauku a kan saƙon har tana karantawa da murmushi a fuskarta ba sai da ta ji ya ce

"Da wa kike chatting har kina irin wannan tattausan murmushin?”

Ta ɗaga idanu a hankali daga wayarta tana kallonshi da ɗan mamaki a fuskarta.

"Karima ce fa.”

Ta amsa mishi a taƙaice.

A maimakon ya yarda da abinda ta ce, sai kawai ya tamke fuska ya sake cewa

"Idan Karima ce me ya sa kika ɓoye wayar da na matso?”

Gabanta ya ɗan faɗi. Don ita bata ma san sadda ya matso ba balle har ta ɓoye wayar.

"Haba dai! Wani irin ɓoye waya kuma? Me zai sa in ɓoye waya?"

Ya miƙa mata hannu, har lokacin bai saki fuskarsa ba.

"Bani wayar in gani.”

Da farko ta yi zaton wasa yake yi. Amma da ta ga yadda fuskarsa ta ƙara haɗewa sai jikinta yayi sanyi sosai. Ta miƙa masa wayar.

Ai kuwa ga mamakinta sai ya karɓa, ya fara duba chats ɗinta ɗaya bayan ɗaya.

Ita kuwa sai kallonshi take yi da maɗaukakin mamaki yana binciken wayarta kamar wani ɗan sanda. Sai da ya gama dube-dubensa don kanshi ya mayar mata da wayar.

"Next time idan ina magana dake ki daina danna waya”

Sai ta ji maganar tasa ta yi mata wani banbaraƙwai a kunnuwanta. Ranta ya sosu ba kaɗan ba, amma duk da haka sai bata bari ɓacin ranta ya bayyana ba.

"Tam"

Ta amsa a gajarce.

Tun daga nan kuma sai hirar ta daina daɗi, daga bisani ma dole suka yi sallama duk zukatansu a jagule.

****

Tun daga wannan rana, sai Shaiɗan yayi ma zuciyar Kamal dabaibayi. A hankali zargin da yake ma Sakina ya fara yawa.

Idan yaje hira ta fito cikin kwalliya tayi kyau sosai sai ya ce

"Irin wannan kwalliya duk ni kaɗai? Ko dai kin yi ma wani ne kika tura masa a hoto ni kika fito min da saura?”

Idan ta ɗauki lokaci ba ta ɗaga wayarsa ba idan ya kira tana ɗauka zai ce

"Hala kina tare da wani ɗan iskan ne a waje?”

Idan ta yi posting hotonta ko magana a WhatsApp Status sai ya ce mata

"Wa kike son burgewa Sakina?”

Da farko ta ɗauka kishi ne kawai, ko kuma taƙaitaccen abu ne da zai wuce nan da nan. Amma sai ta ga abu ya fara miƙa, har an wuce sati ɗaya lamarin sai ƙara ƙamari yake yi.

Rashin yarda da ita ya fara girmama a zuciyar Kamal. Sauƙin abun dai bata taɓa biye mishi sun yi babu daɗi ba. Lallaɓa shi take yi sosai tana guje ma ɓacin ranshi.

A cikin kwanakin marasa daɗi wata rana suna hira ya ce mata

"Kin san wani abu?”

Ta kalle shi a hankali sannan ta amsa da.

"A'a sai ka faɗa”

Ya yi murmushin yaƙe. Kai tsaye ba wani ɓoye-ɓoye ya ce mata

"A cikin kwanakinnan na rasa dalilin da yasa zuciyata ta kasa yarda dake..."

Maganarsa ta sauka a kunnenta kamar saukan mari. Idanunta a warwaje ta dafe ƙirjinta da hannu bibiyu ta ce

"Kamal...?"

Ya katse ta da cewa

"Na riga ba sanki ciki da waje fa Sakina, kuma na lura ke ma fitinanniya ce ajin farko, a yanzu da ba komai da ke wani tabbaci nake da shi baza ki ba wani namijin kanki ba tunda ko kin bada ba ganewa zanyi ba...?”

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un"

Ta faɗa cikin masifaffen tashin hankali.

Lokaci ɗaya idanunta suka cicciko da hawaye

"Amma Kamal kai kanka ka san ni ba ƴar iska ba ce. Kai ne fa ka fara...”

Ya katse ta da sauri.

"Please kar ki fara maimaita min wannan al'amarin da yanzu ba na komai sai da na sanin afkuwarsa.”

Ya katse ta cikin fushi da masifa...

Littafin marubuciyar👇🏽

1)A DALILIN ƊA NAMIJI

2)BARA A KUFAI

3)DUNIYA SABUWA

4)INUWAR MUTUWATA

5)SANADIYYA

6)TSAKANINA DA MUTUWA

7)BILHAƘƘI

8)RABON AYI (KUSKURE NA, YOUTUBE)

9)TUBALIN TOKA...

10)LOKACI

11)RANAR NAKA...

12)GUDUN GARA...

13)ƘASAITACCIYAR MACE...

14)BA NI DA IKO...

15)MUTUNCI MADARA...

Bononza ga masu son karanta littattafaina gaba ɗaya su biya 3k. Har da wannan sabon da nake rubutawa a yanzu. A tura kuɗin a acc ɗina da ke saman page sai ayi min magana domin samun littattafan gaba ɗaya. Na gode.

Ina matan da suke fama da matsalar rashin haihuwa? Matsalar Sanyi? Ko Cancer ne matsalarki? Ko kuwa matsalar haihuwar daga gurin mijinki ne? To albishirinku, Muna da ingantaccen saiwoyin maganin rashin haihuwa, sanyi, da garukan magunguna Anti biotics masu kyau na ciwon Cancer. Magungunanmu tested and trusted ne. An gwada an dace ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba. Masu son magani da gaske su tuntuɓeni ta wannan number ***