BABI NA BIYAR
MUTUNCI MADARA...
©Fareeda Abdallah
Paid book ne. Kuɗin karanta labarin 1k kacal. Ki tura kuɗinki ta wannan account ɗin 7039080978, Opay, Farida Abdullahi, sai a tura min shaidar biya ta wannan numbern *** domin samun damar kasancewa a group ɗin da zan dinga posting ɗin littafin akan lokaci in sha Allahu.
***
5)
Tsawon wasu daƙiƙu Sakina ta zuba ma Kamal ido tana kallonshi da tsananin mamaki da matsanancin ɓacin rai a zuciyarta. Sai kuma hawaye suka fara zubo mata kamar an buɗe famfo.
"Kamal."
Ta kira sunanshi da muryarta da ke rawa.
"Wai yau Kamal ni ce kake faɗa wa ire-iren waɗannan maganganun?"
Abinku da namiji, kawai sai ya maze abinsa ya kawar da kai gefe ɗaya. Fuskarsa a ɗaure tamau kamar hadari.
Wannan kawar da kai da yayi shi ya ƙara karya mata zuciya
"Idan za ka yi min adalci kai da kanka ka san ko ni wacece Kamal. A tunanina za ka iya bada shaidan arziki a kaina ko da a bayan idanuna ne Kamal. Kai kanka ka san irin tarbiyyar da aka yi min. Ka san irin tsoron Allah da nake da shi. Ka san ban taɓa ba wani namiji dama kamar yadda na baka a rayuwata ba..."
Sai ta dakata da magana tana goge hawayenta.
Shiru ya mamaye tsakaninsu na wasu daƙiƙu. Daga maganganun da ta yi, tabbas Kamal ya ji wani abu ya soki zuciyarsa.
Duk maganganunta ya san gaskiya take faɗa, har ya ji kamar zai tausaya mata, amma sai wani sashe na shaiɗaniyar zuciyarsa ya ƙi yarda da hakan.
Wani irin zargi da tsana marar tushe ya cigana da azalzalar zuciyarsa.
Ta yunƙura da ƙyar ta miƙe tsaye, da ƙyar ta iya tsayawa da kyau saboda yadda jikinta yake rawa.
"Kamal."
A karo na barkatai ta sake kiran sunanshi.
"Ka bani mamaki. Na amince da kai fiye da kowa a duniyar nan. Na yarda da kai fiye da yadda na yarda da kaina..."
A wannan karon duk yadda ya so sharewa sai da kalamanta suka bugi zuciyarsa da ƙarfi. Sai kuma shaiɗan yayi saurin gogewa da watsar da duk wani ɓurɓushin tausayi nata da suke ta neman su ƙuƙƙulla kansu a zuciyarsa.
"Amma a yau kuma wai kai ne kake kallon cikin idanuna ka iya faɗa min waɗannan munanan kalaman. Babu komai Kamal, ba komai, na gode."
Sakina ta ƙarasa maganar tana kallonsa ido cikin ido. Na shi idanun a bushe ƙayau babu ko ɓurɓushin tausayi. Na ta idanun kaca-kaca da hawaye, duk kwalliyar da tayi mishi ya ɓaci da hawaye.
"Kin ga Sakina, duk waɗannan maganganun da kike yi don in tausaya miki idan zan faɗa miki gaskiya suna shiga ta kunnen dama ne su fita ta kunnen hagu. Don haka ina ganin a madadin duk wani tashin tashina mu kawo ƙarshen wannan al'amarin kawai..."
"Me kake nufi? Me yasa kake min haka?"
Ta katse shi da tambayoyin a ruɗe.
Ya ja dogon numfashi. Sai kuma ya kawar da kansa gefe kamar wanda ya ke jin nauyin abinda zai faɗa mata.
"Gaskiya Sakina bazan ɓoye miki ba..."
Maganar da ya fara ya yanke yasa ƙirjinta ya buga daram!.
"Me kake nufi?"
Ta sake tambayarsa a ruɗe.
Ya yi ɗan shiru kafin ya amsa mata da.
"Gara in faɗa miki gaskiya Sakina. Ni a yanzu tsakani da Allah ba na ganin zan iya auranki."
Kalamansa suka sauka a kunnenta kamar an buga mata ƙaton dutse a ƙahon zuci.
"Kamal...?"
Ta kira sunansa a firgice, idanunta a warwaje. Sai kuma bakinta yayi nauyi ta kasa cewa komai bayan kiran sunansa.
Shi kuwa ko a jikinsa ya cigaba da cewa
"Kar ki wani yi kamar baki gane me nake nufi ba Sakina..."
Hawayenta suka cigaba da zuba da ƙarfi, hankalinta a tashe. Da ƙyar ta laluba bayanta ta zauna daɓas akan kujera don kar ta faɗi a tsaye.
"Amma me na yi maka da zafi Kamal? Me nayi da za ka yanke min wannan ɗanyen hukuncin?"
Ya kalleta a wani wulaƙance. Sai kuma yayi dariya
"Me kika yi kike tambayata Sakina? Ko kin manta komai ne da ya faru a tsakaninmu?"
Ya miƙe tsaye, ya matsa kusa da ita. Hankalinsa a kwance ya cigaba da magana
"Wallahi Sakina a yanzu zuciyata sam ta ƙi bani haɗin kai wajen amince ma cigaba da tsara yadda zan zauna da ke mu rayu a matsayin ma'aurata. A cikin kwanaki biyun nan ko wane lokaci zuciyata na jefa min tambayar ta yaya zan auri macen da na riga na san komai na ta?"
A firgice ta buɗe baki za ta fasa ihu, sai kuma tayi saurin dafe baki bayan ta tuna a inda suke. Cikin rashin abin cewa ta ce
"Kamal! Don Allah..."
Ya ɗaga mata hannu da sauri ya katse ta.
"A'a Sakina, da gaske bazan iya ba. In don ta alƙawuran da nayi miki ne tuni na fara istigfari.. Ki saurare ni da kyau. Da gaske nake yi na fasa aurenki Sakina..."
"Amma fa Kamal kai ne ka fara jefa ni a wannan hanyar."
Ta faɗa daƙyar cikin kuka.
Shi ma ya katse ta da sauri.
"Ko da na fara jefa ki a hanyar, ai ban ce dole ki bi ni ba Sakina."
Wani irin kuka mai ciwo ya sake ƙwace mata.
"Kamal wannan zalunci da mummunar cin amana kake ƙoƙarin yi min..."
"Ko ma mene ne sunansa Sakina, wannan shi ne gaskiyar magana."
Ya ciro wayarsa daga aljihu, ya kunna, ya buɗe wani faifan vidiyo ya haska mata a fuska.
Nan take jikinta ya ƙara ɗaukar rawar sanyi.
"Kamal don Allah..."
"Ki adana magiyarki don a yanzu baza tayi miki amfani ba. Ki saurare ni da kyau Sakina. Ba na son hayaniya, kuma ba na son gardama. Don haka ki dakatar da maganar auren nan da kanki."
Idanunta suka zazzaro waje kamar mai shirin haukacewa.
"Me ne?"
"Eh! Na ce ki nemo hanyar da za ki sa a soke maganar aurennan"
Ya sake faɗa mata kai tsaye ba tare da ya damu da irin rikicewar da ta shiga ba.
"Ka...mal..?"
Ta kira sunanshi a rarrabe. Sai kuma ta sake fashewa da kuka. Tana kukan tana toshe baki don kar Mummynta ta jiyo ta a cikin gida.
"Don Allah... Don girman Allah kar ka yi min haka Kamal."
Da farko bai amsa ba ya yi banza da ita ya fara danna wayarsa, can kuma sai ya ɗaga idanu yana kallonta ya ce
"Idan kika ƙi aikata abinda na ce miki..."
Sai ya ɗaga wayar da ke hannunsa ya nuna mata vidionta tsirara haihuwar uwarta, tana tsaye a banɗaki tana wasa da al'aurarta cike da shauƙi da iskanci. Sai lumshe idanu take yi tana shushuta da baki tana lashe laɓɓa kamar tsohuwar maiya ta ci yaji.
"...Idan kika ƙi dakatar da auren nan Wallahi zan tura wa iyayenki wannan vidiyon, da ma sauran vidioyi da hotunan da suke danƙare a wayata."
Saboda tsananin tashin hankali lokaci ɗaya Sakina ta ji duniyar tana juya mata. Bata san sadda ta zame zuwa ƙasa ba hannayenta biyu ɗore akai tana kuka ta ce
"Kamal... Wallahi za ka kashe ni..."
"Ni ban ce zan kashe ki ba."
Ya katse ta tun kafin ta aje numfashi.
"Kawai dai aurenki ne bazan yi ba, kuma ba na so iyayena da iyayenki su ga laifina."
"Don Allah Kamal..."
"Keh dakata don Allah"
Ya katse ta da tsawa.
"Ni fa Wallahi idan na ga dama ko kuma kika ƙure ni zan iya sakin vidioyinmu a duniya uban kowa ma ya gani. Kar kiyi tunanin zan ji tsoron abin da mutane za su ce a kaina."
Ya taɓe baki cikin rashin damuwa, ya ɗage kafaɗu alamun ko oho!
"Ni namiji ne. Ko me namiji ya yi ado ne a gurin Mal Bahaushe."
Sai ya nuna ta da yatsarsa manuniya.
"Amma ke fa Sakina?""
Ya sakar mata murmushin da ya fi kama da na mugunta.
"Kin zubar da mutuncin kanki, kin zubar da mutuncin iyayenki. Sannan kuma duniya za ta daɗe tana terere da ke da abinda kika aikata. Kuma za a ɗauki lokaci mai tsawo kafin wani namijin mai rangwamen gata ya iya kwasarki. Don haka ruwanki ne ki dakatar da auren nan mu rabu a mutunce a sauƙaƙe. Ruwanki ne kiyi min taurin kai muyi rabuwar dutse da hannun riga."
Yana gama faɗin haka ya juya ya nufi ƙofar fita.
Har ya kama hannun ƙofar sai ya tsaya na ɗan lokaci ba tare da ya waiga ba ya ce,
"Ki yi tunani sosai Sakina. Ki yanke ma kanki shawarar da zai ɓulle da ke kafin lokaci ya ƙure miki."
Ya fita ya bar Sakina tana kuka, kamar wacce aka faɗa ma rasuwar iyayenta.
*******
"Idan ki ka ƙi dakatar da auren nan, Wallahi zan tura wa iyayenki wannan vidiyon..."
Kalaman da suke ta maimaituwa a kunnuwanta kenan suna ƙara haukatar da ita cikin maɗaukakin tashin hankali.
Baza ta ce ga a yadda ta shiga gida ba, sai da ta ji muryar Mummy da ke zaune a babban falo tana kallon talabijin tana ce mata
"Ke Sakina? Lafiya? Me yake faruwa?"
Sai a lokacin ta ɗan dawo cikin hankalinta. Da sauri ta kama gefen mayafinta tana goge hawaye wasu na sake bulbulowa. Sai ta ɗanyi murmushin yaƙe ta ce
"Lafiya lau Mummy."
Ganin irin kallon da Mummyn take mata alamun bata yarda da abinda ta ce yasa ta sake cewa
"Da gaske fa babu komai Mummy. Mun ɗan samu misunderstanding ne da Kamal, amma zan kira shi in bashi haƙuri."
Mummy ta ƙara bin ta da wani irin kallo kamar bata yarda ba. Don ƙara tabbatarwa yasa ta ce
"Kin tabbata?"
"Eh Mummy."
Ta amsa a gaggauce.
"To shi kenan! Amma lallai ki bi shi a hankali. Sannan kuma ko ke ce da gaskiya kar ki saka ma kanki girman kai lallai ki kira shi ki bashi haƙuri. Domin ke ce a ƙasa da shi. Kuma bayan haka ma a irin wannan lokacin da auranku yake daf aikin Shaiɗan ne yayi ta tunzura zukatanku don ya samu galaba a kanku. Irin haka ne idan ba'a yi sa'a ba sai ki ga maganar aure ya fara tangal-tangal. Masoya da yawa suna fama da irin wannan matsalar, don haka ki kiyaye. Kin gane ko?"
"Na gane Mummy. Zan kiyaye in sha Allah."
Ta amsa jikinta a sanyaye.
"Madallah! Shiga ciki ki huta."
Ai kuwa ta wuce ɗakinta da sauri.
Tana rufe ƙofar ta zube a ƙasa ta sake fashewa da kuka mai cin rai.
Kuka irin wanda yake fitowa daga can ƙarƙashin zuciya mai cike da matsanancin da na sani. Ta yi kuka har ta gaji. Ta yi kuka har idanunta sun kumbura.
Ta yi kuka har hawayen su da kansu suka ƙafe ba sa fitowa.
Kawai sai ta kwanta tana kallon silin ɗaki.
A karo na farko a rayuwarta, ta ji tsoron gobe, don bata san abinda goben za ta haifar ba. Ga tsoron abin kunya, ga tsoron ranar da iyayenta za su ga vidion abinda ta aikata. Ga tsoron irin kallon da za suyi mata.
Kamar a mafarki wayarta ta fara ringing, sai ta waiga tana kallon fuskar wayar da sauri. Kamal ne yake kiranta.
Haka kawai sai ta ƙi ɗauka, domin bata san me zai faɗa mata ba. A karo na biyu ya sake kira. Ta ƙi ɗauka. A karo na uku ya kira, nan ma ta ƙi ɗauka.
Kamar ya san tana kallon kiran ta ƙi ɗagawa sai ya tura mata saƙo. Ta buɗe message ɗin hannayenta na rawa.
"Kar ki tunzura ni Sakina. A ko wani lokaci ki dinga tuna sirrinki da yake hannuna..."
Ƙirjinta ya buga daram!
Ta yi jifa da wayar da sauri kamar wacce ta riƙe wuta. Mintuna kaɗan suka wuce sai ga wani saƙon ya sake shigowa. Kamar wacce aka yi ma dole haka ta sake rarumo wayar ta fara karanta saƙon da ya sake turo mata.
"Kina da kwanaki uku kacal Sakina. Ko dai ki nemo hanyar dakatar da maganar auren nan, Ko kuma ki jira abin da zai biyo baya daga gare ni."
Wayar ta suɓuce daga hannunta ta faɗa kan gado, ita kuwa ta ƙura ma wayar idanu kamar wacce take karanta wani abu daga jikinta.
A wannan dare ko abinci ta kasa ci. Ta kasa sakin jikinta balle har ta yi hira da Mummynta ko tayi kallo.
Da yake Mummyn ta yarda da maganar saɓani suka samu da Kamal sai bata matsa mata ba. Sai daga ƙarshe ne ma Mummyn ke ce mata idan ta bashi haƙurin ya ƙi haƙura ta bashi space zuwa safe ya huce.
*****
Washe gari tunda tayi sallar asubah bata iya tsinana komai ba. Tana zaune a kan dadduma, ita ba ta yi azkhar ba, ita bata yi Karatun Alƙur'ani ba. Sai tulin tunani da damuwa sunƙi-sunƙi da suke danƙare da zuciyarta ta rasa ta hanyar da za ta bi wajen fara warware su.
Daga ƙarshe ta miƙe ta fita ta kama ayyukan tsakar gida laƙaƙai-laƙaƙai kamar kazar da ƙwai ya fashe ma a ciki.
Da misalin ƙarfe goma na safe, wayarta tayi ƙara, kamar baza ta duba ba don a tsammaninta Kamal ne, sai kuma ta duba. Karima ce.
Da farko kamar baza ta ɗauka ba, sai kuma ta ɗaga.
"Amarsu ta Ango mai zaƙin miya!"
Karima ta fara faɗa cikin dariya.
Duk yadda Sakina ta so tayi dariya ko na yaƙe ne ta kasa. Da ƙyar ta iya cewa
"Uhmm"
"Dole ki ce Uhmm mana Amarya. Yarinya ta kusa shiga daga ciki duk ta ishi mutane da karaɗi a status..."
Maganganun Karima suka ƙara karya ma Sakina zuciya, aikuwa ta fashe da kuka.
"Subhanallahi! Sakina? Kuka kike yi? Me yake damunki?"
Karima ta tambayeta a ruɗe.
Da farko tayi shiru tana jan ajiyar zuciya. Can kuma sai wani abu ya motsa a zuciyarta.
A karo na farko tun da matsalar ta fara sai ta ji tana son faɗa ma wani.
Ta ji tana son samun wanda zai saurari kukanta ya bata shawara. Ta ji a ranta lallai tana son samun wanda zai taimaka mata.
"Karima."
Ta kira sunanta a hankali.
"Na'am?"
Karima ta amsa cikin damuwa da zaƙuwa.
Da ƙyar ta haɗiye wani ƙululun takaici da baƙin ciki ta ci gaba da magana da rawar murya
"Ina buƙatar ganinki Karima. Ina neman shawararki. Wallahi ina cikin babbar matsala."
Karima ta yi shiru cikin jimami, domin tunda take da Sakina bata taɓa jin muryarta cikin irin wannan yanayin ba.
"Ina roƙon Allah ya yaye miki damuwarki Sakina. Za ki zo ne ko ni in zo?"
Da sauri Sakina ta ce
"A'a kar ki zo. Domin ba na so Mummy ta san halin da ake ciki. Ni ina nan zuwa anjima."
A haka suka yi sallama da Karima, sun rabu zukatansu babu daɗi ko kaɗan.