MUTUNCI MADARA...

BABI NA SHIDA

by @fareedaabdallah

***

MUTUNCI MADARA...

©Fareeda Abdallah

Paid book ne. Kuɗin karanta labarin 1k kacal. Ki tura kuɗinki ta wannan account ɗin 7039080978, Opay, Farida Abdullahi, sai a tura min shaidar biya ta wannan numbern *** domin samun damar kasancewa a group ɗin da zan dinga posting ɗin littafin akan lokaci in sha Allahu.

6)

Tun da ta yanke shawarar sanar ma Karima halin da take ciki, ta zauna a gefen gadonta tana kallon kwalliyar da aka ƙawata bangon ɗakinta da shi.

Domin tunaninta ne ya kasu gida biyu.

Wani sashe na zuciyarta na ƙara ƙarfafarta akan ta gaya wa Karima komai da yake damunta. Wani sashe kuma na cewa kar ta faɗa mata, saboda idan ta faɗa mata gaskiyar abinda yake damunta, kenan Karimar za ta san abin da ya faru tsakaninta da Kamal. Kuma idan Karima ta sani, to tabbas akwai yiwuwar Ma'aruf ma ya sani. Idan Ma'aruf ya sani, to akwai yiwuwar kowa ma ya sani. Domin sirri yana a matsayin sirri ne a lokacin da mutum ya binne wannan sirrin a cikinshi shi ɗaya. Daga sadda wani ya sani, to fa wannan al'amari ya tashi a matsayin sirri.

Ta runtse idanu da ƙarfi,

ta sake jin kanta na sarawa kamar zai rabe gida biyu. Haka ta cigaba da tunani har rana ta rasa tsayayyar shawara tsakanin ta faɗa ma Karima ko kar ta faɗa mata.

***

Da misalin ƙarfe huɗu na yamma ta isa gidan Karima. Suna ƙule a uwar ɗakin Karima da take ta bin ta da wani irin kallo mai bayyana damuwa da tausayawa.

Domin a kallon farko da Karima tayi mata, ta gane lallai Sakina na cikin matsananciyar damuwa. Don ba wannan Sakinar da ta sani ba ce, wannan da ke zaune a gabanta wata Sakina ce can daban da damuwa ya sukurkutata. Duk gayun nan nata babu, ga idanunta sun kumbura suntum! Kuma sun yi ƙozai-ƙozai babu kwalli babu alamun kwalli a cikinsu.

Har wata ƙwarya-ƙwaryan rama tayi kamar wacce tayi jinyar wata guda. Wancan kyakkyawan murmushin da ba ya rabo a fuskarta yanzu ko ta yi niyyar yin murmushin ma ba ya fitowa.

Bayan tsawon daƙiƙun da Karima ta shafe tana kallon Sakina bata ce komai ba, sai

ta kamo hannunta ta riƙe a cikin nata. Muryarta a raunane ta kira sunanta

"Sakina.?"

Nan take idanun Sakina suka cicciko da hawaye.

Karima ta ƙara damƙe hannunta. A hankali ta sake cewa

"Me yake damunki Ƴar'uwata?"

Daƙiƙu sittin suka wuc Sakina ta kasa magana. Can kuma ta buɗe baki kamar za tayi magana sai kawai wani irin kuka mai cin rai ya ƙwace mata. Ta sunkuyar da kai tana rera kuka kamar wacce aka sanar da ita rasuwar iyayenta.

Wannan kuka da take rusawa shi ya ƙara ɗaga hankalin Karima. Lokaci ɗaya itama idanunta suka cicciko da hawaye, domin tsakani da Allah akwai ƙauna da aminci mai girma tsakaninta da Sakina. Muryarta na rawa ta ce

"Sakina don Allah kiyi haƙuri kiyi shiru."

Ta matse ƴar tazarar da ke tsakaninta da Sakina tana matsa hannuwanta alamun rarrashi.

"A tarihin duniya kuka bai taɓa zama maganin damuwa ba Sakina. Don Allah ki faɗa min me yake damunki don mu san ta inda za mu ɓullo ma al'amarin."

Sakina dai ta kasa magana, sai da ta yi kuka mai isarta sannan ta goge hawayenta. Ta ɗaga kai a hankali tana kallon Aminiyar tata. Domin a yanzu ta yanke shawarar sanar da Karima halin da take ciki, idan bata faɗa ba tana jin mutuwa za tayi. Nauyin damuwar zai iya saka zuciyarta ta buga lokaci ɗaya ta mace, ba tare da an san menene yayi ajalinta ba.

"Karima..."

Ta kira sunan Karima muryarta na rawa, kafin ta amsa sai ta sake cewa.

"Idan mutum ya yi kuskure..."

Ta haɗiye wani dunƙulallen abu da ya tsaya mata a maƙoshi sannan ta cigaba da magana

"...kuma wannan kuskuren ya fara bibiyarsa me ya kamata ya yi?"

A nutse Karima ta ce,

"Sai ya tuba ga Allah. Tuba taubatun nasuha. Tare da alƙawarin bazai sake aikata wannan kuskuren ba."

Wasu sabbin hawaye suka sake ɓalle ma Sakina. Laɓɓanta na rawa ta sake cewa

"To idan kuma akwai wani bawa da yake amfani da wannan kuskuren don ya hallaka rayuwar wacce ta aikata kuskuren fa?"

Karima ta ɗan yamutsa fuska. A ƙagare ta ce

"Ban gane ba Sakina."

Har ta yi shiru sai ta sake cewa

"Sai a kai ƙarar wannan mugun bawan gurin Allah. Domin babu wanda ya fi ƙarfin kuskure kuma ya tuba, a sadda wani ke neman shiga tsakanin bawa da Ubangiji ta hanyar hana wannan tubar ai sai a kai ƙararsa gurin Allah yai maganinsa."

Shiru ya ratsa tsakaninsu bayan maganganun Karima.

A hankali Sakina take sauke ajiyar zuciya. Da ɗacin zuciya ta buɗe baki ta ce

"Kamal ya ce ba zai aure ni ba Karima..."

Idanun Karima a warwaje ta ce

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Wannan wace irin magana ce Sakina? Me kika ce?"

"Kamal ya ce ba zai aure ni ba."

Sakina ta sake maimaita mata.

A firgice Karima ta miƙe tsaye, hannayenta biyu ɗore a kai. Da rawar murya ta ce

"Auren da ya rage saura kwanaki shida, shi ne zai ce bazai aure ki ba? Me ya faru? Me kika yi mishi da zafi haka?"

Sakina ta girgiza kai, sai kuma ta sake fashewa da kuka. Sai da ta ɗauki tsawon lokaci tana kuka kafin ta ce.

"Kuskure ne dukkanmu muka aikata, amma daga ƙarshe sai yake neman zamewa ya bar ni a ciki..."

Kanta yana ƙasa ta fara kora ma Karima labarin duk abinda ya faru, tun daga ranar bikin su Kariman.

Yadda Kamal ya kai ta gidansa.Yadda ya yaudare ta ya biya buƙatarsa da ita. Yadda ya ci gaba da amfani da ita da salon daɗin bakinsa. Yadda ya ɗauki vidiyoyin mu'amalarsu da hotunan tsiraicinta. Yadda ta zama sakarya wajen cigaba da tura mishi tsiraicinta duk don ta faranta masa. Yadda yake nema ya ci amanarta a yanzu, da kuma yadda yake yi mata barazana da cewa zai tura ma iyayenta da duniya vidiyoyinta da suke wajensa.

Saboda tsananin tashin hankali da firgici da farko Karima kasa magana ta yi. Tayi zaman ƴan bori a ƙasa kawai tana kallon Sakina kamar ta samu T.V. Can kuma kamar wacce aka watsa wa ruwan sanyi da ƙarfi ta ce

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Allahumma ajirnee fee musibati, wa akhlifnee khairan minha."

Daga haka bata sake cewa komai ba, ɗakin ya yi tsit. Babu abinda ke tashi sai sautin kukan Sakina.

A karo na farko wasu zafafan hawaye suka zubo daga idanun Karima. Muryarta a raunane ta ce

"Bayan duk waɗannan abubuwan da kika aikata a kansa yanzu shi Kamal ɗin ne yake miki barazanar bazai aure ki ba?"

Sakina ta gyaɗa kai kawai, ta kasa magana.

Karima ta miƙe tsaye a hankali, zuciyarta sai raɗaɗi take yi. A yadda take ji a ranta Wallahi da ace Kamal yana gabanta a wannan lokacin, da sai ya gane akwai bambanci tsakanin haƙuri da fushi.

"Wallahi bai isa ba. Kamal yayi kaɗan ya ce bazai aure ki ba Sakina. Bari Ma'aruf ya dawo."

Sakina ta yi saurin girgiza mata kai. Muryarta a ɗashe ta ce

"A'a Karima. Don Allah kada ki faɗa ma Ma'aruf."

"Me yasa?"

Karima ta tambayeta da mamaki.

"Kar dai ki ce min har yanzu kina ƙoƙarin kare Kamal da rufa asirinsa?"

Sakina ta girgiza kai.

"Ba kare shi ko ƙoƙarin rufa asirinsa nake yi ba Karima. Kawai dai ina tsoron abin da zai biyo baya ne idan maganar nan ta fita. Kar ki manta a matsayina na ƴa mace duk inda aka je aka dawo ni ce al'umma za su jingina ma kaso casa'in da biyar na laifin nan."

Karima gyaɗa kai alamun ta gamsu. Ta nemi guri kusa da Sakina ta zauna, tayi shiru cikin tunani. Can kuma sai ta ce

"Ki saurare ni Sakina. Akwai abu ɗaya da ya kamata ki sani."

"Mene ne shi?"

Karima ta kalleta ido cikin ido ta ce.

"Duk mutumin da zai iya yin amfani da wani sirri naki da ke hannunsa don ya tsoratar da ke, ko kuma ya tilasta miki yin wani abu da bakya so, to fa lallai wannan mutumin ba masoyinki bane. I'm sorry to say a yadda na fahimta da gaske Kamal ya daina son ki..."

Kalaman suka sauka a zuciyar Sakina kamar bugawar guduma. Amma kuma ita kanta ta sani gaskiya Karima take faɗa.

Karima ta ci gaba da magana.

"Duk Mutumin da yake shirye da ya lalata rayuwarki don ya tsira da tasa rayuwar, ba masoyi ba ne Sakina."

Sai ta kama hannun Sakinar ta cigaba da cewa

"Ni ina ga me zai hana ki faɗa ma su Mummy kin haƙura da auren Kamal? Domin a irin wannan yanayin ina tabbatar miki ko aurensa kika yi idan ba wani ikon Allah ba baza ki taɓa yin daraja ba Sakina... Da sai muyi ta addu'a, Allah sai ya dube ki ya kawo miki mijin da ya fi shi alkhairi Sakina."

Sakina ta yi shiru, a zuciyarta take ta jujjuya maganganu da shawarwarin Karima. Ta daɗe tana tufkawa tana warwarewa, daga ƙarshe dai suka rabu da Karima akan cewa ta bata lokaci tayi tunani da addu'a. Duk shawarar da ta yanke za ta kira ta faɗa mata zuwa washe gari da yamma.

*******

Har tsakiyar daren ranar, zuciyar Sakina cike take da nauyi da damuwa fiye da ko wani lokaci. Kalaman Karima ne suke ta yawo a cikin kunnuwanta, har zuwa lokacin ta kasa yanke shawarar amincewa da maganar Karima ko akasin haka.

"Duk Mutumin da yake shirye da ya lalata rayuwarki don ya tsira da tasa rayuwar, ba masoyi ba ne Sakina."

A da, idan wani ya gaya mata haka game da Kamal, za ta ƙaryata, har ma ta iya rantsewa cewa Kamal ba zai taɓa aikata mata haka ba.

Amma sai ga shi a yau, cikin ƙanƙanin lokaci da idanunta take kallon komai. Yau ita da kanta ta fahimci wannan karin maganar da mata ke cewa Namiji ƙanin ajali ne.

To amma me ya faru ne a cikin ƙananun kwanaki haka? Ashe bakin da ya furta so yana zuwa ya furta ƙi cikin ƙanƙanin lokaci? Ko dai da gaske ne da ake cewa so tsuntsu ne, yana tashi daga wannan bishiyar zuwa wancan? Yanzu Kamal ya daina son ta gaba ɗaya kenan? Yana nufin har ya gama cin moriyar ganga zai yada ƙyauronta kenan?

Ta ja nannauyar numfashi ta sauke. Yanzu idan ta amince da shawarar Karima na fasa auren Kamal, bayan duk abinda ya faru na kek-keta alfarmarta da ya yi, ya ci banza kenan?

Ta girgiza kanta da sauri. Tana hawaye take shan alwashi a fili

"Wallahi Tallahi bazai yiwu ba. Kamal baka isa ka lalata min rayuwa sannan ka tafi a banza ba. Ko za ka mutu sai ka aure ni, idan ya so ka aure ni yau ka sake ni washe gari. Da mu rabu ina matsayin budurwar da ta rasa budurcinta a hanyar banza gara mu rabu ina matsayin ƙaramar bazawara. Ko babu komai alfarmar auren da na taɓa yi bazai dasa ma mijin da zan sake aura zargina a zuciyarshi ba."

Tayi shiru tana matsar ƙwallah, tana cikin wannan halin ne ta tuna wata magana da Malamar Islamiyyarsu ta taɓa faɗa musu

"Duk lokacin da mutane ababen halitta suka rufe muku ƙofofi, to fa lallai ku tuna ƙofar Allah ko da yaushe a buɗe take."

Nan take wani sabon kuka ya ƙwace mata. Sai dai a wannan lokacin ba kukan damuwar Kamal ba ne. Ba kukan Vidiyoyin tsiraicinta da suke wajensa ba ne.

Ba kukan aurenta da yake ƙoƙarin rushewa ba ne. Kuka take yi na tsoron Allah. Kuka take yi saboda kuskuren da ta aikata a rayuwarta.

Jikinta na tsuma ta sauko daga kan gadon, ta shiga bayi da sauri ta ɗauro cikakkiyar alwala. Tana fitowa ta zura zumbulelen hijabi sannan ta shimfiɗa sallaya ta fuskanci gabas. Ta tsaya gaban Ubangijinta. Tun tana ƙoƙarin daurewa kar ta sake yin kuka, tun tana ƙoƙarin hana kukan fitowa, sai dai tana ɗaga hannu ta ce,

"Allahu Akbar."

Duk wani jarumta nata ya kau, muryarta ta karye. Da ƙyar ta iya karanta Fatiha cikin rawar murya. Da ƙyar ta iya karanta suratul Ikhlas, tayi ruku'u, tana saka goshinta a ƙasa gurin Sujuda kawai sai ta fashe da kuka.

"Ya Allah..."

Ta furta cikin kuka da murya mai rauni irin wacce take fitowa daga ƙarƙashin zuciya.

"Na zalunci kaina... Na saɓa maka Ya Rabb. Na ci amanar iyayena. Amma Ya Allah na san kai ne mai gafara ne kuma mai jin ƙai. Ina roƙon ka yafe min, ka kawo min daidaito da sauƙi cikin al'amurana."

Ta daɗe cikin Sujuda tana addu'a tana kuka. Sannan ta ɗago ta cigaba da sallah har tayi sallama. Ko da ta idar addu'a ta cigaba da yi tana haɗawa da Istigfari.

Sai da dare ya yi nisa sosai tana kan dadduma. Domin bayan addu'o'in Karatun Alƙur'ani tayi mai tsawo irin wanda ta daɗe bata yi ba.

A karo na farko cikin kwanakin tashin hankalin, ta ji a zuciyarta ta samu sauƙin damuwar da take ciki. Duk da ba matsalarta ne ta warware ba, amma ta koma ga Mahaliccinta, tana da yaƙinin zai kawo mata ɗauki ta inda bata taɓa zata ba.

Aka kwana aka wuni Sakina tana cigaba da ibada da istigfari. Ta cigaba da addu'a sosai.

Ko Kamal ya kira ta ba ta ɗagawa. Idan ya turo mata saƙo ba ta amsawa.

A daren ranar bayan ta ɗauki tsawon lokaci tana ibada, tana zaune tana kallon ƙasan dadduma, zuciyarta cike da tunani. Amma tunani take yi na nutsuwa ba irin kwanakin baya da take a ruɗe ba. Nazari take yi cikin neman mafita.

Can kawai sai wata dabara ta faɗo mata a rai. Ta ɗaga kai da sauri. Ƙirjinta ya ɗan buga bayan ta sake jujjuya shawarar da ya zo mata a rai.

A hankali ta ce a fili

"Mama..."

Mama, asalin sunanta Hajiya Balaraba. Ita ce mahaifiyar Kamal. Mace mai mutunci da sanin ya kamata. Matar da tun ranar Farko da Allah ya haɗa su da Sakina ta ce ta samu ƴa macen da Allah bai bata ba.

Sakina tayi shiru tana sake jujjuya shawarar da ke ta ƙara ƙarfi a zuciyarta. An ya za ta iya kuwa? Za ta iya zuwa ta gaya ma mahaifiyar Kamal komai da ya faru tsakaninta da ɗanta?

Zuciyarta ta cigaba da bugawa da ƙarfi. Kamar hakan bai kamata ba. Amma kuma shawarar na ta samun ƙarfi a zuciyarta. Kawai sai ta gyara zama ta ƙara fuskantar gabas, ta ɗaga hannuwa biyu sama tayi addu'a mai tsawo, bayan ta gama ta shafa a fuskarta.

Ta kwanta barci da nufin idan ta tashi da asubah ta ji har lokacin shawarar nan na amsa kuwwa a zuciyarta, to fa lallai za ta yi amfani da wannan shawarar. Wata kila mafitar da take ta roƙa ne Allah ya kawo mata a sauƙaƙe.

*****