MUTUNCI MADARA...

BABI NA BAKWAI

by @fareedaabdallah

MUTUNCI MADARA...

©Fareeda Abdallah

Paid book ne. Kuɗin karanta labarin 1k kacal. Ki tura kuɗinki ta wannan account ɗin 7039080978, Opay, Farida Abdullahi, sai a tura min shaidar biya ta wannan numbern *** domin samun damar kasancewa a group ɗin da zan dinga posting ɗin littafin akan lokaci in sha Allahu.

***

Littafin marubuciyar👇🏽

1)A DALILIN ƊA NAMIJI

2)BARA A KUFAI

3)DUNIYA SABUWA

4)INUWAR MUTUWATA

5)SANADIYYA

6)TSAKANINA DA MUTUWA

7)BILHAƘƘI

8)RABON AYI (KUSKURE NA, YOUTUBE)

9)TUBALIN TOKA...

10)LOKACI

11)RANAR NAKA...

12)GUDUN GARA...

13)ƘASAITACCIYAR MACE...

14)BA NI DA IKO...

15)MUTUNCI MADARA...

Bononza ga masu son karanta littattafaina gaba ɗaya su biya 3k. Har da wannan sabon da nake rubutawa a yanzu. A tura kuɗin a acc ɗina da ke saman page sai ayi min magana domin samun littattafan gaba ɗaya. Na gode.

Ina matan da suke fama da matsalar rashin haihuwa? Matsalar Sanyi? Ko Cancer ne matsalarki? Ko kuwa matsalar haihuwar daga gurin mijinki ne? To albishirinku, Muna da ingantaccen saiwoyin maganin rashin haihuwa, sanyi, da garukan magunguna Anti biotics masu kyau na ciwon Cancer. Magungunanmu tested and trusted ne. An gwada an dace ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba. Masu son magani da gaske su tuntuɓeni ta wannan number ***

7)

Washe gari misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe Sakina tayi ma gidan Mama mahaifiyar Kamal dirar mikiya.

Duk da yadda zuciyarta ke bugawa bata fasa jan duk addu'o'in da suka zo bakinta ba. Haka kawai tunda ta tashi da asubah ta ji har lokacin shawarar da ta yanke na ta je ta sanar da Mama matsalarta da Kamal na nan daram a ranta, kawai sai ta tafi. Tare da fatan ta dace da biyan buƙata.

Duk da bata san ta inda za ta fara faɗa mata ainahin tushen matsalar ba, sannan ba ta san yadda Mama za ta karɓi maganar ba, amma ta san abu ɗaya.

Wannan abu ɗayan shi ne bazai yiwu ta cigaba da rayuwa cikin wannan tsoro da firgicin da Kamal ya jefata a ciki ba. Za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin Kamal bai ci nasara a kanta ba.

Tana waɗannan saƙe-saƙen har aka yi mata iso gurin Mama. Da yake da niƙaf a fuskarta, shi yasa Mama bata gane ta ba sai da ta ɗage Niƙaf ɗin ta fara gaishe ta a kunyace. Mama tana zaune a falonta tana duba wasu takalma da aka kawo mata za ta zuba a cikin akwati.

Da mamaki sosai a fuskar Mama ta dinga bin Sakina da kallo har suka gama gaisawa.

"Sakina? Ke ce tafe da safennan? Lafiya kuwa?"

Mama ta tambayeta bayan ta kasa haƙurin jiran Sakinar ta faɗa mata abinda ya kawo ta gidan a irin wannan lokacin.

Da farko Sakina kasa magana tayi, hannayenta da suke dafe a ƙasa sai rawa suke yi. Muryarta na rawa, daga ƙarshe dai bayan ta tuna nuƙu-nuƙu da ɓoye-ɓoye bazai sama mata mafita ba kawai sai ta fara magana.

Muryarta ƙasa-ƙasa da matsananciyar kunya da tozarta ta fara ba Mama labarin ta inda suka fara aikata kuskuren ita da Kamal, har zuwa yanzu da Kamal yake yi mata barazana. Ba ta ɓoye mata komai ba, ba ta rage ba bata ƙara ba. Ta faɗi komai tsakaninta da Allah kamar yadda ya faru.

Da farkon labarin, Mama ta yi shiru ne kawai tana sauraren Sakina, girman mamakinta na ƙaruwa.

Amma da Sakina ta cigaba da magana, sai fuskarta ta fara canjawa har ta haɗe tai kirtiɓ! Lokacin da ta ji maganar vidiyoyi da barazana kuwa, sai ta miƙe tsaye hankalinta a tashe ta ce

"Subhanallahi! Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!"

Ita dai Sakina ta sunkuyar da kai tana ta hawaye bayan ta gama bata labarin.

"Amma Sakina kin bani mamaki kuma kin ɓata wayonki, ban taɓa tsammanin ke shashashar yarinya ba ce sai yau. Wace irin wawuyar yarinya ce ke? Wannan wane irin wauta da hauka ne kika aikata ma kanki?"

Mama ta jero mata tambayoyin cikin ɓacin rai.

"Ina hankalinki Sakina? Ina tarbiyyar da iyayenki suka ɓata tsawon shekaru suna baki? Ko kuwa za ki ce min da saninsu kika aikata wannan hauka da rashin hankalin?"

A wannan gaɓar duk yadda Sakina ta so daurewa ta kasa, sai da ta fashe da ƙaƙƙarfan kuka.

"A'a Mama."

Ta amsa da muryar kuka.

"To me ya kai ki gidan namiji ba tare da an ɗaura muku aure ba?"

Shiru Sakina tayi ta kasa amsawa, sai ƙara sunkuyar da kanta ƙasa da tayi kamar ƙasa ta tsage ta shige ciki don kunya da muzanta.

"Wace irin yarda da aminci ne ku ƴanmatan yanzu kuke ba samarin da ba tare aka haife ku ba?"

Nan ma shiru Sakina tayi bata amsa ba.

"Ke da kanki kin yarda sakarci da hauka kika aikata?"

"Na yarda Mama. Wallahi na yarda."

Sakina ta amsa da ƙyar cikin kuka.

Mama ta cigaba da yi mata faɗa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, ranta a ɓace.

"Ku ƴan matan yanzu kuna da abin ban haushi da ban mamaki. Idan kuka faɗa cikin soyayya sai ku dinga yi kamar a kanku aka fara... na rasa rawar kai ne ke damunku ko kuwa rashin sanin ciwon kai ne oho! Sai ku miƙa ma namiji yarda da soyayya ɗari bisa ɗari, bayan ko a addinance ma cewa aka yi kuyi so sama-sama kuyi ƙiyayya sama-sama. To bari ki ji in sake faɗa miki abu ɗaya, ba Kamal da yake ɗana ba, Da yawa daga cikin maza idan mace tayi kuskuren amincewa da su ta miƙa musu kanta kafin aure, to fa ko da sun cigaba da soyayya da ita wannan ƴa macen, kaso sittin daga cikin ɗari na so da yardan da suka yi mata zubewa yake yi. Ko yanzu wa gari ya wa ya?"

Sai da Mama ta yi mata faɗa sosai kamar za ta dake ta. Faɗan da ya fito daga ƙarƙashin zuciyarta, irin faɗannan da ko ƴar da ta haifa ne iyakar faɗan da za tayi mata kenan.

Sakina ta yi kuka, ta yi kuka, kamar za ta haɗiye ranta. Zuciyarta ta ƙara cika da matsanancin da na sani, har ma tana ji a ranta ina ma ace za a iya dawo da hannun agogo baya, to fa lallai da a guje za ta dawo da nata hannun agogon don gyara kuskuren da ta yi. Sai dai ina, lokaci ya riga ya ƙure mata.

Mama ta ƙarasa kusa da ita, a tausashe ta ɗago ta suka zauna a kan kujera. Ta kamo hannunta ta riƙe, karo na farko ta tausasa murya ta cigaba da magana

"Ki saurare ni Sakina. Ina yi miki faɗan nan ba don na tsane ki ko kuma don Kamal bai da laifi bane, kin gane?"

Sakina ta ɗaga kai a hankali.

Mama ta cigaba da cewa

"Ina yi miki faɗa ne a matsayina na uwa... Domin abin da kika aikata kuskure ne babba. Amma kuskure ba shi ne yake nufin ƙarshen rayuwa ba. Ni abinda na yarda da shi shi ne wata kyakkyawar rayuwar mai cike da jin daɗi da darasi tana farawa ne bayan aikata kuskure."

Sabbin hawaye suka zubo ma Sakina.

Mama ta cigaba da cewa

"Ki tuba ga Allah."

"Na tuba Mama."

Sakina ta amsa a hankali.

"Sannan ki dage da istigfari."

"In sha Allah Mama."

"Kuma ko da a gaba kada ki sake yarda wani namiji ya yaudare ki da sunan soyayya ya ci galaba a kanki."

"To Mama. Zan kiyaye in Allah ya yarda."

Mama ta ja numfashi mai nauyi ta sauke

"Yanzu dai da farko kafin in ɗauki ko wani mataki ina so in fara tabbatar da abu guda ɗaya."

Mama ta ɗaga waya ta kira direbanta da yake tsakar gida, ya ɗauke su ita da Sakina zuwa wani asibitin kuɗi mai kyau.

Suna shiga tasa aka yi ma Sakina duk wasu gwaje-gwajen da suka dace don tabbatar da ba ta ɗauke da ciki a jikinta.

Sakina ta ƙara shiga cikin mugun ɗimuwa da tashin hankali. Ita gaba ɗaya ma firgicin fasa aurenta da Kamal ya ce zaiyi yasa ta manta da zancen zai iya yiwuwa fa ta samu ciki a waɗannan mu'amalar da suka yi ita da Kamal. Duk da dai ko kusa bata ji wani canji a jikinta ba.

Lokacin zaman jiran fitowar sakamako sai suka zama wasu irin lokuta mafiya ƙunci da tsawo a rayuwarta. Numfarfashi take ta ja sama-sama, zuciyarta cike da fargaba da tunanin idan aka ce tana ɗauke da ciki ya za ta yi? Sai kuma tayi saurin kwaso addu'o'in da duk suka zo ranta taita maimaitawa a firgice. A ɗan zaman da suka yi shigarta bayi sau biyu saboda firgici.

Sai dai kuma abin farin ciki ga Mama da ita kanta Sakina shi ne bayan fitowar gwaje-gwaje Likita ya duba sakamakon, ya tabbatar ba ta ɗauke da ciki a mahaifarta.

"Alhamdulillah."

Ita da Mama suka furta cikin matsanancin farin cikin da sai da yasa Likitan bin su da kallo. Domin shi a tsammaninsa haihuwa suke nema ido rufe.

Basu tsaya yi ma Likita wani ƙarin bayani ba duk da yadda ya so hakan, Direba ya tuƙa su suka koma gida.

Tun a hanya daman Mama ta kira Kamal a waya ta ce ya bar duk abinda yake yi ya je tana nemansa da gaggawa. Da wannan dalilin yasa sun koma gida babu daɗewa shi ma Kamal ya isa gidan.

Yana shiga falon, bai lura da Sakina da take rakuɓe a can gefe ɗaya ba ya zube a ƙasa ya fara gaida Mama.

Sai dai bata amsa ba, a madadin ta amsa ma sai ta yafito shi da hannu

"Zo nan."

Kai tsaye ya rarrafa har kusa da ƙafafunta, ita kuma tana zaune a kan kujera. Ko da ya ɗaga idanu da nufin sake gaisheta a karo na biyu, sai ya lura da wani irin fushi da ɓacin rai a fuskarta da ya daɗe bai gani ba. Hankalinsa a ɗan tashe ya ce

"Mama lafiya...?"

Kafin ya rufe baki ta sauke mishi ƙaƙƙarfan mari a kuncinsa, ji kake tas!

A kiɗime ya dafe kuncinsa, bakinsa na rawa ya ce.

"Mama...!"

"Kar ka kuskura ka ce min Mama!"

Ta katse shi cikin fushi.

"Ashe rainon cikinka watanni goma da na yi ɗan iskan yaro na haifa ban sani ba?"

Ƙirjin Kamal ya buga daram! Ya kasa amsawa don bai san inda maganarta ya nufa ba.

A karo na biyu Mama ta sake gaura mishi mari a ɗaya ɓangaren kumatunsa lokaci ɗaya tana cewa

"Ashe rainon da na yi maka na tsawon shekaru na raini wanda zai yi amfani da sirrin ƴa mace ne ya dinga yi mata barazana?"

Sai a lokacin Kamal ya fara fahimtar inda maganganun Mama suka nufa. Hankalinsa a tashe ya rungumo ƙafafunta yana bata haƙuri.

Mama bata saurare shi ba sai da tayi mishi wankin babban bargo fiye da yadda tayi ma Sakina. Sannan ta rantse mishi da girman Allah in dai ita ta ɗauki cikinsa, ta haifesa, tayi rainonsa bai isa ya ce ya fasa auren Sakina ba.

"Ko da aurenta shi ne abu na ƙarshe da za ka gudanar a rayuwarka Wallahi sai ka aure ta."

"To Mama! Zan aure ta. Ko yanzu ma na amince a ɗaura auren in dai za kiyi haƙuri ki yafe min. Don Allah kiyi haƙuri Mama."

Ya cigaba da bata haƙuri, hankalinsa a tashe, domin tunda yake a rayuwarsa da wayonsa dai Mama bata taɓa marinsa ba. Sai ga shi yau ta mare shi har sau biyu, kuma ta faɗa mishi munanan kalaman da ko makamantansu bata taɓa faɗa mishi ba.

Bai samu ƴar nutsuwa ba sai da Mama ta amsa ta yi haƙuri, kuma ta yafe mishi. Ta kira Sakina ta zauna a can gefe ta ƙara yi musu nasiha gaba ɗaya.

Bayan doguwar nasihar da Mama ta yi musu. Kamal ya ɗauki alƙawarin bazai sake ce ma Sakina bazai aure ta ba. Har ya bata haƙurin ƙuntata mata da yayi a cikin kwanakin. Ita ma Sakinan ta bashi haƙuri akan irin abubuwan da suka faru.

Daga ƙarshe Mama ta umarci direba ya mayar da Sakina gida. Shi kuma Kamal bayan ya sake ba Mama haƙuri, ta tabbatar masa komai ya wuce, ya tafi ɓangarensa na gidan iyayensa ya kwanta zuciyarsa cike da tunani da damuwa.

Domin a zahirin gaskiya ya amince ne kawai saboda mahaifiyarsa.

Shi kaɗai ya san abin da ke cikin ransa. Abinda Sakina ta kasa ganewa shi ne yanzu duk wani so da yake mata ya sane a zuciyarshi.

A da idan aka ambaci ko da sunan Sakina ne, wani irin farin ciki ne yake cika zuciyarsa.

A da idan ta kira shi, ko cikin taro yake sai ya nemi hanyar amsa kiranta don baya son ɓata mata. A da idan yana tunaninta, yana hangen rayuwa mai tsawo da zai gudanar tare da ita.

Amma yanzu komai ya canja. Ba ya jin wannan farin cikin da yake ji idan yana tare da ita.

Ba ya jin wannan shauƙin da yake ji idan ya tuna da ita. Duk yadda Mama za ta sasanta su a yadda zuciyarsa ta ƙeƙashe ya san zaiyi wahala ya sake kallon Sakina da idon da yake kallonta a baya.

*****

Ko wane ɓangare suka cigaba da shirye-shirye. Kwanakin bikin suka ƙaraso kamar ƙiftawa da bismillah. Gidan su Sakina ya kaure da hayaniyar ƴan biki da suka zo daga sassa daban-daban.

Ƙawayenta na ta kai-ko-mo. Danginta na ta murna, Iyayenta kuwa da basu san sa toka sa katsin da aka taka kafin isowar wannan rana ba sai godiya ga Allah suke yi da ya nuna musu wannan rana mai muhimmanci.

Sakina ta sha gyaran jiki na ban mamaki daga isowar amaryar Babanta da matar Yayanta. Sai walwala take yi cikin ƙawaye da ƴan'uwa da abokan arziki, duk da Kamal ba ya kiranta sai dai ita ta kira shi, sam ba ta damuwa.

A ganinta ai komai ya wuce. Lokaci kaɗan za su koma kamar da, ko ma fiye da hakan. Ta yi zaton faɗan da Mama ta yi ma Kamal ya dawo da shi cikin hankalinsa.

Ta yi zaton ya gane kuskurensa. Ta yi zaton ya dawo yana sonta kamar da, kunyar irin cin mutuncin da yayi mata ne ya hana shi sakewa. Shi yasa ita take kiranshi don ta nuna mishi babu komai fa, komai ya wuce a zuciyarta.

Abinda Sakina ba ta sani ba shi ne akwai babban banbanci tsakanin mutum ya haƙura da abu, da kuma mutum ya yarda da abu daga ƙarƙashin zuciyarsa.

Ranar kamu ya yi armashi sosai. Washe gari aka ɗaura aure. Da la'asar aka yi walima. Ango da abokansa sun je, an ɗauki hotuna sosai. An yi wasa da dariya tsakanin ƙawaye da abokai. Daga ƙarshe aka yi addu'o'i.

Duk wanda ya ga Kamal a wurin bikin nan zai ce yana cikin farin ciki sosai. Fuskarsa a sake, yana aikata duk abin da ake tsammanin ango mai farin ciki ya yi.

Sai dai a cikin zuciyarsa sam ba ya farin ciki. Yana rayuwa ne kamar mutumin da aka ɗora wani ƙaton nauyi a zuciyarsa, kuma aka tilasta masa rayuwa da wannan nauyi.