BABI NA TAKWAS
MUTUNCI MADARA...
©Fareeda Abdallah
Paid book ne. Kuɗin karanta labarin 1k kacal. Ki tura kuɗinki ta wannan account ɗin 7039080978, Opay, Farida Abdullahi, sai a tura min shaidar biya ta wannan numbern *** domin samun damar kasancewa a group ɗin da zan dinga posting ɗin littafin akan lokaci in sha Allahu.
*Sisters na ce ba? Wai kuwa Kuna da labarin shahararriyar mai sayar da kayan yara da kayan kicin ɗinnan akan farashi mai sauƙin gaske fiye da kasuwa? Na san dai ko ban faɗi sunanta ba da yawanku kun santa, amma dai duk da haka bari in faɗa muku sunanta. Imzeed Enterprises LTD, ta shahara gurin siyar da kayan yara da kayan kicin kala daban-daban akan farashi mai sauƙin gaske. Sauƙaƙawarta bai tsaya a nan ba, tana yin adashin kayan kicin weekly da monthly ga ƴan'uwa masu niyyar siyan kaya amma basu da dunƙulallen kuɗin a lokaci ɗaya. Abin burgewar shi ne tana da branch a Jihar Kano da jihar Filato (Jos), sannan tana aika kaya cikin ƙanƙanin lokaci a faɗin Nigeria da Nijer. Ku tuntuɓeta a kan wannan lambar wayar domin ku kwashi garaɓasa...07077532253. Muna maraba da masu sayen ɗai-ɗai ko sari.*
***
8)
A guri ɗaya da Kamal ya turje har ya so dasa ma Ma'aruf tunanin wani abu shi ne gurin Dinner. Ba tare da sanin Kamal ba ashe bisa jagorancin Ma'aruf da sauran abokansu sun shirya mishi ƙayataccen Dinner, za ayi a daren ranar ɗaurin aure.
Hatta ɗinkin da za su saka a gurin Dinner Ma'aruf yai mishi. Sai dai ko da suka je mishi da zancen Dinner kai tsaye ya ce baza ayi ba. Da farko sun zaci wasa yake yi, sai daga baya suka gane da gaske yake yi. Har yana haɗa musu da rantsuwar baza shi ba, sannan Sakina ma in dai shi ne mijinta baza ta ba.
"Me kake nufi Kamal?"
Ma'aruf ya tambaye shi da ɓacin rai a fuskarsa.
"Na zaci tun kafin wannan ranar ni da kai muke ta plan kan yadda za'a tsara Dinnern bikinku? Ko kuma don mun yi maka suprise ni da sauran abokanmu shi ne kake jin ba daɗi?"
Kamal yai shiru baiyi magana ba, a madadin yayi magana ma kawai sai ya ɗauki wayarsa ya fara dannawa. Fuskarsa a ɗaure tamau.
Mubarak da shi ma lamarin ya fara bashi haushi a fusace ya ce
"Yanzu dai ka faɗa mana me kake nufi? Asara kake so mu yi ko me..?"
"Dama na sa ku haɗa min wani Dinner ne?"
Kamal ya tambaye su ranshi a ɗugunzume. Kafin su amsa ya cigaba da magana
"Tunda ban saka ku ba sai ku je kuyi ku da ƙawayen Amarya da danginta. Amma ni kam babu inda zan je, kuma Sakina ma ban yarda ta je ba. Faƙat!"
Yana gama faɗin haka ya fice daga cikin ɗakin hotel ɗin da suke.
Da mamakinsa cike da zukatansu suka cigaba da tattauna al'amarin, gaba ɗaya zukatansu babu daɗi. To amma ya za suyi? Duk da maƙudan kuɗaɗen da suka kashe dole suka yi cancel ɗin Dinner, tunda dai bazai yiwu su yi babu Ango da Amarya ba.
***
Da Yamma liƙis aka fara shirye-shiryen kai amarya Sakina ɗakin mijinta Kamal. Ƙarfe bakwai na dare rantsattsun jerin gwanon motocin Abokan Ango suka cika ƙofar gidan su Sakina don kwasan Amarya da tawagarta.
Sakina tana zaune a cikin ɗakinta, ta sake yin wanka da ruwan turaruka masu taushin ƙamshi ƴan gaske. A cikin ƴan kwanakin da aka taso ta da zazzafan gyaran jikin Amarya ƙamshi ya kama jikinta sosai. Da yake Amaryar Daddynsu ƴar Maiduguri ce, ba tare da ƙyashi ba kuwa ta baje baiwarta ta yi ma Sakina gyaran jiki na kere ma sa'a.
An shirya Sakina cikin wata Lafaya mai masifar kyau, ya amshi jikinta ƙwarai da gaske. Sai ta ƙara fitowa a Amarya ɗanya sharaf ga ƙuruciya, fuskarta ta yi sumul, kuma ta yi haske sosai kamar wacce aka wanko ta a inji. A taƙaice dai ta yi kyau matuƙa.
Sai dai duk da tarin farin cikin da ke danƙare a zuciyarta, lokaci bayan lokaci tana ɗan tuna irin cakwakiyar da suka tsallako kafin isowarsu wannan matakin. Tana tuna dararen da ta kwashe tana kuka.
Tana tuna lokacin da Kamal ya kalli tsakiyar idanunta ya ce ba zai aure ta ba. Tana tuna irin mugun tashin hankalin da ta shiga saboda Vidiyoyinta na tsiraici da ke wayar hannunsa.
"Ko ya goge vidiyoyinma? Oho!"
Ta ɗage kafaɗunta alamun ko oho!
Ko babu komai dai bayan tsananin jajurcewa, juriya da haƙuri yau ga shi komai ya wuce. Allah ya kawo mata mafita cikin sauƙi. Ta lumshe idanunta tana murmushi. A fili ta ce
"Alhamdulillah."
"Amarya... Tunanin me kike yi?"
Karima da ta fito daga banɗaki ta tambayeta.
"Uhmmm! Karima tunani ya zama dole ai. Amma dai Alhamdulillahi, kin ga bayan jajurcewa komai ya wuce ko?"
"Haka ne Sakina. Sai mu cigaba da addu'ar Allah ya bada zaman lafiya da zuri'a masu albarka."
"Amin ya Allah."
Karima ta buɗe baki za tayi magana sai ga Aunty's ɗin Sakina sun shigo tafiya da ita gurin iyayenta suyi mata faɗa. Daga can za a wuce da ita gidan Mijinta. A dole Karima ta tsuke bakinta.
Gurin Iyayenta aka fara kai ta, suka yi mata nasiha sosai. Sannan aka wuce da ita gurin Gwaggwaninta da duk waɗanda suka kamata, kowa dai nasiha yake yi mata. Mafiyawancin kalmar da ake jaddada mata kuma shi ne
"Haƙuri... Ta yi haƙuri... Sai ta yi haƙuri in dai har tana son cin ribar zamantakewar aure..."
Bayan duk wata nasiha aka ɗauki Amarya, ƙawayenta, ƴan'uwa da abokan arziki zuwa gidan mijinta. Bayan gama ganin gidan Amarya da saka albarka abokai suka sake jigilar mutane aka mayar da su gidan su Mummy.
Saboda haushin da Kamal ya basu ko neman shi basu sake yi ba, suka sallami ƙawayen Amarya, kowa ya kama gabanshi.
******
A daidai wannan lokacin da aka kai Amarya, Kamal yana can gidansu ɓoye a ɗakinshi na samartaka. Gaba ɗaya hankalinshi a tashe yake. Tun ɗazu shi kaɗai yake ta saƙawa yana kwancewa amma har yanzu bai samu matsaya ba.
A hankali ya sauke nannauyar ajiyar zuciya. Ya miƙa hannu ya ɗauko wayarsa, ya shiga ɓangaren musayar saƙonni, ya lalubo lambar Sakina ya shiga ciki. Tsofaffin saƙonnin da suka taɓa musaya a tsakaninsu yake ta kallo yana maimaita karantawa.
Sai dai abin takaici a gare shi shi ne, ga shi dai saƙonnin na soyayya ne, da alƙawurran gatanta rayuwar juna da suka saba yi a tsakaninsu. Saƙonnin da a wancan lokacin da yake rubutawa suke fitowa daga can ƙarƙashin zuciyarsa. Sai dai a yanzu basu da wani armashi ko shauƙi na musamman a yayin karanta su, a taƙaice ma sai wani haushi da ɓacin rai ne suka ƙara turnuƙe shi.
Ya girgiza kai kawai. Duk da wani ɓangare na zuciyarsa na gaya masa a irin wannan rana bai kamata ya kasance a cikin wannan yanayin ba. Sai dai kuma ya zai yi?
Kasancewa a cikin wannan yanayin kamar dole ne a gare shi, tunda dai shi yanzu ya riga ya gama yin ittifaki ba ya son Sakina. Ba ya son kasancewa tare da ita a matsayin matarsa, amma ya san bakin alƙalami ya riga ya bushe, kasancewa tare da ita dolen-dole ne a gare shi tunda dai har mahaifiyarsa ta gindaya mishi sharaɗin haka.
Ya miƙa wayar zai ajiye kira ya shigo masa, ko da ya duba sai yaga Ma'aruf ne. Kamar bazai ɗaga ba, sai kuma ya ɗauka bayan ya kalli agogon fuskar wayar ya ga ƙarfe goma da minti arba'in da biyar na dare.
"Kana ina?"
Ma'aruf ya tambaye shi.
Yayi ɗan shiru, sai kuma ya ce
"Ga ni a gidan Mama..."
"Abokanmu duk sun wuce. Ka shirya ga ni nan zuwa in ɗauke ka zuwa gurin Amaryarka."
"Ok"
Ya amsa a taƙaice, sannan ya aje wayar.
Babu wani shiri da yayi har Ma'aruf ya kira shi yana jiransa a ƙofar gida. Babbar rigarsa kawai da hula sai wayarsa ya ɗauka ya fice daga ɗakin. Bai biya ta cikin gida ba, saboda dama Mama bata san yana gidan ba.
Suna hanyar tafiya, Ma'aruf ya kawar da ɓacin ransa yake tambayar Kamal ko akwai abinda aka yi mishi ne ya ɓata masa rai a sha'anin bikin?
"Ba komai."
Ya amsa a taƙaice.
Ma'aruf bai zurfafa mishi tambayoyi ba kawai sai ya juya akalar maganganunsa zuwa nasiha, jan hankali, da muhimmancin haƙuri a cikin rayuwar aure.
"Kai fa banza ne Ma'aruf, duka-duka yaushe kayi auren da har za ka dinga yi min wani nasiha?"
Kamal ya katse Ma'aruf yana jifar shi da hararar wasa.
"Wanda ya riga ka kwana dole ya riga ka tashi Yaro. Ko da ace jiya nayi aure dole akwai wani ilimi da na sani wanda kai baka sani ba, don haka ka buɗe kunnuwanka da kyau ka kwashi ilimi..."
Suka yi dariya gaba ɗaya.
Haka suka cigaba da wasa da dariya har suka ƙarasa gidan Amarya Sakina. Kamal ya so Ma'aruf ya shiga, amma ya bashi uzurin dare ya yi. Kujeran baya na motar ya buɗe ya ɗauko ledar da aka naɗe lafiyayyiyar kaza gashin taraba ya miƙa ma Kamal. Sai kuma ya sake ɗauko wani babban leda cike da gorukan magani ya sake miƙa ma Kamal ɗin.
"Wancan ledar kazar siyan bakin Amarya ne. Wannan kuma saƙon Mubarak ne ya ce a baka, a jikin gorar akwai bayanin yadda za ka sha ko wanne magani. Asha amarci lafiya..."
Suka sake yin dariya haɗe da cafkewa irinna tsaffin Aminai. Kamal yana tsaye a tsakar gidan yana kallon Ma'aruf har ya shiga cikin mota, ya tayar, sai ya kuma ya yafito Kamal ɗin da hannu.
Ko da ya zura kanshi ta cikin motar kamar zai faɗa mishi abin arziki sai cewa ya yi
"Kai tsohon tuzuru... Ka tabbata ka bi ƴar mutane sannu a hankali..."
A guje ya figi motar yai ribas ya fice daga gidan yana dariyar ganin yadda Kamal ya dunƙule hannu zai kai mishi naushi.
*****
Sakina tana zaune ita kaɗai tsuruuu a cikin ɗakin da aka ajiyeta, ɗakin ya yi tsit. Tana zaune a gefen gado, zuciyarta sai bugawa take yi da sauri.
Kamar kowace sabuwar amarya, Sakina tana cike da jin kunya, haɗe da tsoro, a gefe ɗaya kuma tana jin matsanancin farin ciki. Sai dai kuma tun tana zaman arziki ita kaɗai ƙwallin ƙwal kamar mayya har ta fara gajiya da zaman. Da farko ta ja kan lafayarta ta rufe har fuskarta, da zama yai zama ita da kanta tasa hannu ta yaye rufar ta buɗe fuska.
A taƙaice ta ƙare ma ɗakin da take ciki kallo, sai taga ɗaki ne na daban a cikin ɗakunan gidan, ba wancan ɗakin da ta sani bane inda suka saba shan shagalinsu ita da Kamal. Ta kalli agogon fuskar wayarta, sai ta ga goma da minti talatin da biyar, a fili ta ce
"Na san duk inda yake Kamal suna hanyar tahowa shi da abokansa, bari in rufe fuska da kyau, don kar su zo a ga amarya fuska sake a fasa siyan baki da daraja."
Ta ƙarasa maganar tana murmushi.
Bata san iya tsawon lokacin da ta ɗauka tana saƙe-saƙe ba, sai ji tayi ana buɗe get ɗin gidan, can kuma ta ji an rufe, a hankali ta ƙara gyara zama ta sunkuyar da kanta ƙasa sosai.
Duk da ta san abokai sun sallami ƙawayen Amarya, bata yi tunani Kamal shi ɗaya gayanshi zai je gidan ba.
Bayan kamar mintuna goma sha biyar da rufe ƙofar get ɗin gidan ta ji an murɗa ƙofar ɗakinta an shiga ciki. Ta ƙasan lafaya ta ɗan ɗaga kai tana hangenshi. Ya na sanye cikin farar jallabiya, ya yi kyau sosai.
Sai dai kuma fuskarsa babu walwala, babu murmushi ko misƙala zarrah. A taƙaice ma dai babu wani alamun farin ciki irin na sabon ango a tare da shi. Ya kalleta na daƙiƙu uku, sai kuma ya nemi guri ya zauna a kujera ɗaya da ke cikin ɗakin.
Yai shiru. Sakina tai ta jira ta ji ko zai yi magana. Amma bai yi ba. Aka ɗauki minti ɗaya, minti biyu, har aka doshi mintuna biyar, babu wanda ya yi magana a tsakaninsu.
Jikin Sakina yayi sanyi ƙalau, a hankali ta ja rufar fuskarta baya kaɗan, ta ɗaga kai ta kalle shi. Karaf, suka haɗa idanu. Sai ta ga ya ƙara haɗe fuska, ya taɓe baki, sannan ya kawar da kai gefe ɗaya.
Ƙirjinta ya buga daram!Tun lokacin da Hajiyarsa ta sasantasu, basu ƙara haɗuwa ido da ido ba sai yau da aka ɗaura musu aure. Ganin kuma yadda yake ta murmushi a can gidansu har yana ɗan rungumeta aka yi musu hotuna sai tayi tsammanin komai ya daɗe da wucewa a zuciyarsa.
Sai dai abinda ya sanyayar mata da jiki a yanzu shi ne, maimakon ta ga alamun soyayya da farin ciki irin wanda ta gani a ɗazu tare da shi, sai ta ga saɓanin haka. Wani irin yanayi da ba ta saba gani a tare da shi ba sadda suke cikin soyayya...
Kamal ya katse mata tunani ta hanyar yin gyaran murya. Dama idanunta a kansa yake tana karantar shi, sai kawai ta sake ƙure shi da manyan idanunta.
Da cusasshiyar murya ya kira sunanta
"Sakina?"
"Na'am!"
Ta amsa da sauri.
Ya yi ɗan shiru na wasu daƙiƙu, sai kuma ya ce,
"A iya taƙaitaccen lokacin zaman auren da zan yi da ke zan yi iya ƙoƙarina in danne zuciyata in sauke haƙƙoƙinki da suke kaina..."
"Uhmmm!"
Sakina ta faɗa da ƙyar, tana jujjuya maganganunsa a cikin ƙwaƙwalwarta. Bata fahimci inda ya nufa ba har ya cigaba da cewa
"Zan yi iya ƙoƙarina in haƙurƙurtar da zuciyata in zauna da ke kamar yadda Mama ta umarce ni Sakina, amma gaskiya sai kin bani lokaci..."
Ya ja numfashi ya sauke, sannan ya cigaba da magana
"...saboda a yanzu ko rantsuwa nayi miki babu kaffara ba na jin ko ɓurɓushin soyayyarki a cikin zuciyata..."
A wannan karon, wani irin mugun bugawa da ƙirjin Sakina ya yi sai da ta kai hannuwa biyu ta dafe ƙirjinta. Da rawar murya tayi saurin katse shi ta hanyar jefa masa tambayar
"Ba ka so na Kamal?"
Ya gyaɗa mata kai alamar Eh! Ya ƙara da cewa
"Kin san ni ban iya munafurci ko ɓoye-ɓoye ba. Ko da na faɗa miki a kwanakin can na daina son ki, Wallahi da gaske nake yi. Amma duk da haka kika nace sai da kika aure ni."
Ya yi ƙwafa. Sannan ya miƙe tsaye ya cigaba da magana.
"Ina taya ki murnar samun cikan burinki na Aure na Sakina. Kin ci galaba a kaina, amma..."
Sai ya girgiza kai kawai. A karo na biyu ya sake yin ƙwafa. Sai kuma yayi wani murmushi da Sakina ta kasa banbance murmushin yaƙe ne? Ko murmushin takaici? Ko murmushin baƙin ciki ne?
Tunaninta ya katse sadda ya cigaba da magana.
"Kazar Amarcinki da Ma'aruf ya siya yana can ajiye a falo. Ki huta lafiya Amaryar Kamal."
Yana gama faɗin haka ya fice daga ɗakin ba tare da ya jira ko za ta ce wani abu ba. Ita kuwa tana tsaye ƙyam! ta bi hanyar da ya fita da kallo kamar an daskarar da ita a tsaye.
Sai kuma a hankali hawaye suka fara tsattsafowa suna taruwa a idanunta, duk yadda ta so hana hawayen zubowa ta kasa, sai da suka sauko kan kumatunta...
Wancan link ɗin da ke cikin posting ɗin baya shi ne group ɗin Comment akan littafin nan, ku shiga ciki domin samun damar musayar ra'ayi da ni marubuciyar labarin, da sauran masu karatu. Ina maraba da gyara, ƙorafi, shawarwari. Amma fa maraba ta musamman ina yi ga waɗanda suka sayi littafin ne don nuna min ƙauna da ƙarfafa gwuiwa❤️. Don Allah ku zo ku sayi littafina❤️❤️😂 One love masu karanta littattafaina a duk inda kuke🥰