BABI NA TARA
MUTUNCI MADARA...
©Fareeda Abdallah
Paid book ne. Kuɗin karanta labarin 1k kacal. Ki tura kuɗinki ta wannan account ɗin 7039080978, Opay, Farida Abdullahi, sai a tura min shaidar biya ta wannan numbern *** domin samun damar kasancewa a group ɗin da zan dinga posting ɗin littafin akan lokaci in sha Allahu.
Ina matan da suke fama da matsalar rashin haihuwa? Matsalar Sanyi? Ko Cancer ne matsalarki? Ko kuwa matsalar haihuwar daga gurin mijinki ne? To albishirinku, Muna da ingantaccen saiwoyin maganin rashin haihuwa, sanyi, da garukan magunguna Anti biotics masu kyau na ciwon Cancer. Magungunanmu tested and trusted ne. An gwada an dace ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba. Masu son magani da gaske su tuntuɓeni ta wannan number ***
***
9)
Sakina ta daɗe a tsaye a gurin da Kamal ya bar ta. Wasu daga cikin baƙaƙen maganganunsa suna ta maimaita kansu a cikin kunnuwanta,
"Ina taya ki murnar samun cikan burinki na aurena Sakina... Kin ci galaba a kaina... Ba na jin ko ɓurɓushin soyayyarki a cikin zuciyata..."
Ta runtse idanunta da ƙarfi, saboda yadda tuno baƙaƙen maganganun kaɗai ke ƙara ƙona mata zuciya.
Sabbin hawaye suka sake ɓalle mata.
Daƙyar ta taka zuwa gefen gado saboda yadda ƙafafunta suka yi sanyi ta zauna a hankali. Sai kuma ta ji zaman bai mata daɗi ba, ta sake miƙewa tsaye, sai kuma ta fara safa da marwa a cikin ɗakin.
A iya tsawon rayuwarta bata taɓa tunanin ranar da ta daɗe tana mafarkin gani za ta zo mata a cikin irin wannan yanayin ba.
Tun tana yarinya take mafarkin kyakkyawan rayuwar aurenta. Mafarkin zama matar mutumin da take masifar so. Mafarkin ranar da za a raka ta gidan mijinta cikin farin ciki.
Amma sai ga shi yau Allah ya nuna mata ranar, sai dai farin cikinta bai cika ba. A taƙaice ma kamar babu ɗaya daga cikin mafarkanta da za su tabbata a wannan dare.
A hankali ta zauna a ƙasa, ta jingina da gefen gadon. Ta yi tagumi da hannu bibiyu. Sai kuma ta cire tagumin ta ɗaka kai da tafukan hannayenta biyu ta fara addu'a.
"Ya Allah..."
Ta faɗa da ƙyar, bakinta har wani ɗaci-ɗaci yake mata.
"Na gode maka da ka nuna min wannan rana mai albarka. Amma ya Allah kana ji kana ganin cakwakiyar da na fara cin karo da shi tun a ranar farko... Ina roƙon ka ka sauƙaƙa min ya rabbi"
A karo na ba adadi hawaye masu zafi suka sake zubo mata a kumatu.
Tana cikin wannan halin bata san sadda Kamal ya buɗe ƙofar ɗakinta ba sai ganinshi tayi tsaye a kanta, har lokacin fuskar nan tasa babu walwala ko kaɗan. Bai ce mata komai ba, sai wayarsa ya miƙa mata.
Jikinta a sanyaye tasa hannu biyu ta karɓa, tana kallonsa da idanun neman ƙarin bayani. Da ƙyar ya iya dannar zuciyarsa ya ce mata a tausashe,
"Mama ce za kuyi magana. Ta nemi numbarki bata samu ba. Ina wayarki?"
Kafin Sakina ta amsa sai ta ji muryar Mama tana cewa
"Sakina? Ƴar albarka kina ji na?"
Sai a lokacin Sakina ta fahimci dalilin Kamal na yi mata magana a tausashe, ashe Mama tana jinsa ne. Watsar da tunanin komai tayi ta saisaita muryarta ta fara gaida Maman a ladabce.
Bayan musayar gaisuwa cike da nuna ƙauna a tsakaninsu, da tambayar yadda taro ya watse a ko wane ɓangare, Mama ta daidaita muryarta ta fara faɗa ma Sakina dalilin kiransu a wannan dare.
"Sakina yanzu ina sauraren tambaya mabuɗin ilimi na ji Malam Daurawa ya bada fatawar cewa idan mu'amalar aure ya shiga tsakanin saurayi da budurwa, dole sai ita budurwar ta yi istibra'i don tabbatar da ba ta da ciki kafin a ɗaura mata aure. Wannan istibra'i kuwa jini ɗaya ne, domin a tabbatar da mahaifar mace a tsarkake take. To kin ga duk da mun je asibiti an yi miki gwaje-gwaje an tabbatar ba ki da ciki yana da kyau mu bi tsarin addininmu ya zo da shi, tunda mu musulmai ne."
"Gaskiya ne Mama."
Sakina ta faɗa da sanyin murya.
"Amma kamar yadda aka yi gwaji ba ni da komai Mama. A ranar da na zo gidanki na fara period, yau da safe nayi wankan tsarki. Kin ga bayan wancan gwajin na asibiti jini ɗayan da ake buƙata ma na yi. Ba ni da komai."
"Kin tabbata kin yi jinin ko Sakina?"
Mama ta tambayeta don ƙara tabbatarwa, duk da ba ta tunanin Sakina za ta yi mata ƙarya.
"Wallahi da gaske na yi Mama. Kin san bazan miki ƙarya ba."
"Na sani Sakina, na sani. Allah yayi miki albarka."
"Amin Mama."
Sakina ta amsa.
Da farin ciki bayyananne a muryar Mama ta cigaba da jero musu kyawawan addu'o'i
"Allah ya baku zaman lafiya, da zuri'a masu albarka."
"Amin ya Allah Mama."
Sakina ta amsa a kunyace.
Suka rabu a wayar Mama tana ta farin ciki na gaske, ita kuma Sakina tana ta murmushin yaƙe, ga kunya, da takaicin wannan tambari na abin kunya da ta bar ma kanta.
Duk wayar da Mama ke yi da Sakina Kamal yana tsaye ƙiƙam yana ji, sai dai ko a fuska baza a fahimci yanayin da yake ciki ba. Mama tana katse waya kamar ana yaƙi ya fisge wayarshi ba tare da jiran ta miƙo mishi ba.
Uffan bai ce mata ba ya fice daga ɗakin, ita kuma ta raka shi da kallo. Ko bayan fitarsa ta daɗe tana tunani da saƙe-saƙe, bata tashi a gurin ba har sai da ta ji idanunta suna mata zafi sosai. Ta yunƙura ta tashi da ƙyar, ta shige bayi ta ɗauro alwala.
Sallar isha'in da bata yi ba ta fara yi, tayi shafa'i da wuturi, Sannan ta yi addu'a mai tsawo. Addu'ar da mafi yawancinta kuka ne da tuba ga Allah kan kuskuren da ta aikata, kuskuren da har yanzu yake bibiyarta.
Daga ƙarshe ta shafa addu'ar ta miƙe tsaye. Ko kayan jikinta bata samu sararin canjawa ba ta kwanta. Sai dai barcin ma ya ƙi zuwa.
Lokaci zuwa lokaci sai ta waiga ta kalli ƙofar ɗakin, zuciyarta cike da tunanin ko Kamal zai dawo? Ko zai tuna wannan daren shi ne darennan da suka sha ɗauka mishi alwashin irin kulawa da tarairayar da za su yi ma junansu?
Sai dai har zuwa lokacin da wani wahalallen barci ya ɗauke ta, Kamal bai dawo ba.
******
A kan kunnenta daga wani masallaci can nesa Ladan ya ƙwala kiran sallar farko. Daman barcin nata raba da rabi ne, don haka ta tashi ba tare da wani magagin barci ba. Bayan ta yi alwala ta raka'atanil fijr, sai ta buɗe App ɗin Alƙur'ani a wayarta tai ta karatu, har aka kira sallah na biyu ta yi sallar Asubah, tana Azkhar a nan kan Sallaya barci ya sake ɗauke ta.
Karfe takwas na safe ta farka daga barci, da farko kamar ta manta a inda take. Saboda a yanzu ta samu nutsattsen barci ba kamar barcin da ta yi cikin dare ba. Sannu a hankali kuma sai komai ya dawo mata.
Daren farko na ranar aurenta. Maganganun Kamal. Kukan da tayi na tsawon lokaci. Duk suka dawo mata lokaci ɗaya. Ta miƙe a hankali.
Wanka ta fara yi, ta gargasa jikinta da ruwa mai zafi-zafi saboda gajiya, sannan ta shirya cikin wata kyakkyawar doguwar riga na atamfa.
Duk da halin da take ciki bai hana ta tsantsara kwalliya ba, ta yi kyau sosai. Sai ta fito a amarya sak! Babu wanda zai kalle ta ya ce tana cikin wata damuwa.
Duk da ɗakin baiyi wani datti ba ta sake gyarawa ƙal! Ta fito a hanlali zuwa falo, sai a lokacin ta ga ledar Kazar da ya ce mata Ma'aruf ne ya siya mata. Ɗaukar ledar tayi ta nufi kicin.
Ta ɗauki tsawon lokaci tana yaba kyau da tsaruwar da kicin ɗinta ya yi, a fili ta gode ma Iyayenta sannan ta yi musu addu'ar ƙarin buɗi da tsawon kwana mai albarka. Cikin nutsuwa ta fara ƙoƙarin haɗa musu sassauƙan abin kari, tana aikin tana rarrashin zuciyarta akan Kamal.
'Shi ne fa wannan Kamal ɗin da muka ɗauki tsawon shekara biyu da ƴan watanni muna soyayya... ya sha faɗa min bazai taɓa iya daddaɗan rayuwa ba tare da ni a cikinta ba... Na san lokaci kawai yake buƙata... Zai huce. Ba dai an riga anyi mai wahalar tunda an ɗaura mana aure ba? Komai zai wuce in sha Allah.. Za mu daidaita. Za mu koma kamar da, ko ma fiye da da. Bakin da ya furta so, ko ya ce baya so ƙarya yake yi. Komai zai wuce.'
Da wannan tunane-tunanen ta cigaba da aikace-aikacenta. Tana daf da gamawa sai ga abin kari daga can gidan Mama ta aiko musu da shi.
Sai a lokacin kuma shi ma Kamal sai ga shi ya fito, a yanzu ma yana sanye da jallabiya mai ruwan toka. Fuskarshi babu walwala ko kaɗan.
Babu wani alamar farin ciki irin na sabon ango a tare da shi. Ko kallonta bai yi ba. Kai tsaye ya nufi dining table ya zauna.
Sakina da take kallonshi daga ƙofar kicin a hankali ta ƙarasa gurin teburin cin abincin ta zauna a kujerar kusa da shi. Da murmushin da ta ƙaƙalo ta ɗora ma fuskarta ta ce
"Good morning Sweet heart. Ka tashi lafiya?"
Sai da ya aika mata da wani muzantaccen kallo sannan ya amsa a shaƙe
"Alhamdulillah."
Shiru ya ratsa tsakaninsu na wasu daƙiƙu. Can kuma sai ya miƙa hannu zai ɗauki saving spoon don zuba ma kanshi abinci da sauri ta riga shi.
Lafiyayyar waina ce da tayi mugun kyau a ido da miyar taushe, sai kuma farfesun naman rago da yayi ruwa-ruwa sosai, sai ruwan tea da ya ji kayan ƙamshi. Sune kayan karin da Mama ta aika musu da shi.
Wainar ta fara zuba mishi ɗan daidai, ta sa mishi miya a gefe. Ta zuba mishi farfesun a wani ɗan bowl daban, ta buɗe flask za ta zuba mishi ruwan tea ɗin ya ce a cuccushe
"Is Ok!"
Bai kalleta ba ya fara cin abincin, da alamun yunwa yake ji. Domin wanda ta zuba mishi sai da ya cinye tas, ya ɗauki goran ruwa ya sha. Sannan ya miƙe tsaye.
A lokacin ne Sakina ta kasa haƙuri ta ce cikin sanyin murya
"Sweet heart don Allah ka yi haƙuri ka yafe min... A tunanina tunda har muka kai wannan matakin za ka yi watsi da komai mu zauna lafiya..."
"A tunaninki kika ce ko?"
Ya katse ta da tambayar.
Shiru tayi mishi bata amsa ba, domin ƴan maganganun da ta tsara sadda yake cin abinci da nufin za ta faɗa mishi lokaci ɗaya suka tarwatse a cikin kwakwalwarta.
"Wai ke me yasa har yanzu daƙiƙiyar zuciyarki ta kasa yarda na tsane ki Sakina?"
Kalmar daƙiƙiya ta sauka a zuciyarta kamar bugun guduma.
Ta kasa magana, ko ƙwaƙƙwaran motsi ta kasa motsi. Kawai tana zaune kamar mutum-mutumi tana kallonsa.
Shi kuwa ya ja mata dogon tsaki kamar mace, sannan ya juya ya fice daga ɓangaren cin abincin.
Ta daɗe tana kallon gu ɗaya, can kuma da ƙyar ta ɗaga hannu ta dafe kanta da ta ji lokaci ɗaya ya fara yi mata wani irin ciwo kamar zai faɗo daga jikinta. Ashe irin ciwon da ake ji kenan idan wanda kake so ya fara nuna maka ba ka da wani matsayi a wurinsa?
Ta lumshe idanunta. A zuciyarta take ta ƙoƙarin lalubo wancan Kamal ɗin mai tsananin son ta. Wancan Kamal ɗin da idan ta yi rashin lafiya baya iya kwantar da hankalinsa sai ta sami sauƙi. Wancan kamal ɗin da yake kiranta a waya fiye da sau goma a rana. Wancan Kamal ɗin da yake cewa ita ce farin cikinsa, ita ce nutsuwarsa.
Da ƙyar ta miƙe tsaye, bayan ta yi iyakar ƙoƙarinta ta hana kanta yin kuka. Ta share gumin da ya ɓata mata fuska. A maimakon ta zauna ta cigaba da tunani ko kuma ta kwanta kawai sai ta cigaba da gyaran falon.
Tana aikin tana jaddada ma kanta abu ɗaya, wannan abun kuwa shi ne, za ta yi iya ƙoƙarinta wajen ganin bata bari wannan auren ya rushe ba. Ko da kuwa ita kaɗai ce za ta yi ta bada gudummuwa wajen ɗorewar zaman auren.
Yinin ranar haka Sakina tayi ta fama da baƙin ƴan'uwa da abokan arziki. Daga ɓangarenta da na su Kamal, zuwan baƙin shi ya taka muhimmiyar rawa gurin tilasta mata yin watsi da damuwar komai ta koma cikin walwalarta.