MUTUNCI MADARA...

BABI NA GOMA

by @fareedaabdallah

MUTUNCI MADARA...

©Fareeda Abdallah

Paid book ne. Kuɗin karanta labarin 1k kacal. Ki tura kuɗinki ta wannan account ɗin 7039080978, Opay, Farida Abdullahi, sai a tura min shaidar biya ta wannan numbern *** domin samun damar kasancewa a group ɗin da zan dinga posting ɗin littafin akan lokaci in sha Allahu.

Ina matan da suke fama da matsalar rashin haihuwa? Matsalar Sanyi? Ko Cancer ne matsalarki? Ko kuwa matsalar haihuwar daga gurin mijinki ne? To albishirinku, Muna da ingantaccen saiwoyin maganin rashin haihuwa, sanyi, da garukan magunguna Anti biotics masu kyau na ciwon Cancer. Magungunanmu tested and trusted ne. An gwada an dace ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba. Masu son magani da gaske su tuntuɓeni ta wannan number ***

***

10)

Tun da Kamal ya fita gidan da safe, har misalin ƙarfe tara da mintuna arba'in na dare bai koma gidan ba. Zuwa lokacin duk baƙin da suka yini zuwa ganin ɗakin Amarya sun tafi. Sakina ta sake gyara gidan ƙal kamar bata yini cikin baƙi ba. Hatta ɗakinsa ta gyara, ta baza turaren wuta mai ƙamshin daɗi a ko wani lungu da saƙo na gidan. Sannan ta ɗanɗasa wanka, ta yi kwalliya cikin wata ƴar mitsitsiyar riga da wani ɗan guntun skeirt iya cinyoyinta. Ta yi kyau ba kaɗan ba, sai ta fito cas da ita kamar Priyanka Chopra a film ɗin Koi mil Gaya.

Bayan shawarar da ta yanke ma kanta na bada duk gudumuwar da ya kamata don ɗorewar rayuwar aurenta. Ta ƙara yanke shawarar zamowa mace mai riƙe sirrin aurenta ɗari bisa ɗari, shi yasa ko da Karima ta je gidan a yau ta yini mata, ko a fuska bata nuna mata alamar tana cikin wata damuwa ba. Ta faɗa mata komai yana tafiya lami lafiya ƙalau tsakaninta da Kamal, bata fuskanci matsalar canja fuska, harara, balle uwa uba gori ba tsakaninta da Kamal a darensu na farko ba. Ta ce mata sun gudanar da mu'amalar auratayya cikin shauƙi da soyayyar juna.

A ƙoƙarinta na nuna ma Karima komai na tafiya mata daidai, har wayar ƙarya tai ta yi lokaci bayan lokaci, tana ta zuba kalaman soyayya a waya alhalin Kamal bai kira ta ba. Ita ce tai ta kiran shi bai ɗauka ba, a ƙarshe ma da ta dame shi da kira, sai ya jefa lambarta a black list, yadda ko ta kira shi baza ta same shi ba.

Wannan labari na ƙarya da ta ɗora Karima a kai, shi ya cire Karimar daga cikin fargabar da ta kwana da shi tana tunanin Sakinar. Labarin da ya jefa ta cikin farin ciki, minti ɗaya biyu sai ta ce Alhamdulillahi Sakina.

"Wallahi ki ƙara gode ma Allah da ni'imar da yayi miki Sakina. Domin ba ko wace ƴa mace bane take biye ma namiji suyi mu'amala kafin aure, sannan bayan sun yi aure ya cigaba da ganin kima da mutuncinta ɗari bisa ɗari. Da yawan matan da irin wannan ƙaddarar ta afka musu, in dai za su bada labari za ki ji sun ce sun fuskanci canji da wulaƙanci daga mazajensu, har ma ki ji suna da na sanin aikata kuskuren a karon farko."

"Haka ne kam Karima. Alhamdulillah"

Sakina ta amsa da ƙyar, tana ƙoƙarin ɓoye tashin hankalinta.

Wannan magana da Karima ta faɗa sai ya zama kamar sukar kibiya a zuciyar Sakina, a zuciyarta take ta ƙara jero Istigfari da Da na sani. Domin tabbas wannan matsala da Karima take faɗe ita ganau ce ba jiyau ba.

Karima da bata fahimci halin da Sakina take ciki ba, haka tai ta yi ma Sakina murna. Bayan ta gama murnar kuma ta ƙara ba Sakina sirrika da dama na janyo hankalin ɗa namiji zuwa ga matarsa, ko da kuwa yana fushi da ita ne.

Sakina ta buɗe kunne tana ɗaukar darasin da dukkan nutsuwarta. Har ma a zuciyarta take ayyana za ta fara gwada shawarwarin Karima a yau, wata kila ita ma ta samu nasarar janyo hankalin Kamal ya dawo kanta kamar yadda suke a baya.

Ita kuwa matar Yayanta Aunty Lubnah wasu Emergencyn kyawawan magungunan mata ta ƙara kai mata, bayan waɗanda aka bata kafin bikin da wanda ta sha jiya ranar ɗaura aure.

"Tunda dai yanzu kun zama ɗaya ke da shi waɗannan magungunan ba ƙaramin taimaka miki za suyi ba. Suna da saurin saukar da ni'ima da gigita rayuwar ɗa namiji ya dinga miki ƙananun kukakkaki. Don da ganin idanun Kamal bazai haƙuri da matarsa a shimfiɗa ba. Bari in fara dama miki waɗannan, idan kuka gauraya anjima za ki kira ni kina godiya."

Sakina dai ba baka sai kunne, sai sunkwui da kanta ƙasa take yi cikin kunya tana ta murmushin da bai kai ciki ba. Haka dai ta daure ba don ranta yana so ba ta shanye magunguna cikin babban kofi da Aunty Lubnah ta dama mata, yayi kirtiɓ da madara.

Waɗannan magunguna da ta sha su suka taru suka ƙulle mata mara tsam! Kamar wacce take jin fitsari, amma kuma ko ta je banɗaki sam ba ta iya yin wani fitsarin azo a gani, haka dai tai ta daurewa tayi ayyukan gyaran gidan har zuwa dare, duk ta ƙosa Kamal ya dawo, kamar ma dai ta manta irin sa toka sa katsin da suke ciki.

Ko abincin dare da Hajiya ta aika musu da shi kaɗan ta tsakura ta kwanta a kan doguwar kujera. Idanunta biyu, jikinta duk a sanyaye. Tana ta rarraba ido tsakanin agogo da T.vn falon har zuwa sadda ta ji an buɗe get ɗin gidan.

Ta yunƙura da ƙyar ta miƙe ta zauna, idanunta akan ƙofar falon ya murɗa hannun ƙofar ya buɗe ya shiga cikin falon, bakinsa ɗauke da sallama ciki-ciki kamar an yi masa dole.

Da yake idanunta akan fuskarsa yake, shi yasa ta ga alamun sallamar da ya yi. Ta amsa da sassanyar muryarta, muryar da a da, Kamal ke cewa tana saukar masa da nutsuwa ba kaɗan ba.

Amma a yanzu sai ya ƙara tsuke fuska kamar ta nuna shi da bakin wuta. Ita kuwa fuskarta yalwace da murmushi, kamar bata ga ɗaurewar da yayi ba ta miƙe tsaye da ƴar sassarfa mai haɗe da yanga ta nufo shi da niyyar rungume shi. Lokaci ɗaya tana cewa

"Barka da dawowa Annurin zuciyar Sakina..."

Tana gaf da isa gare shi ya lura da abinda take niyyar yi, ai kuwa da saurin gaske ya goce ta rungumi iska. Ta tsaya turus, jikinta a sanyaye tana kallonshi.

Shi kuwa ya aika mata da wani kakkausan kallo mai tafe da gargaɗi, ya ja mata tsaki, sannan yai wucewarsa zuwa ɗakinshi.

Bai san tana biye da shi a baya ba sai da ya ji muryarta tana cewa

"Yau dai Ango ya yi ma Amarya wahalar gani. Kuma Babe nayi ta kiranka baka ɗauka ba? Allah yasa dai ka yini lafiya?"

Banza yayi da ita bai tanka ba.

Bata gaji ba ta sake cewa

"Allah ya huci zuciyarka ranka ya daɗe."

Nan ma yai mata shiru.

"Uhmm! Kamaluna kenan. Yanzu dai don Allah ka faɗa min, ruwan sanyi da abinci zan fara shirya maka a dining table? ko kuwa in kawo maka ruwan ka sha idan kayi wanka sai ka ci abincin?"

"Sakina?"

Ya kira sunanta a kausashe.

"Na'am Habibee"

Ta amsa a sanyaye da murmushi, kamar duk abinda yayi bai ɓata mata rai ba.

"Amma na faɗa miki ki bani lokaci ko ban faɗa miki ba?"

Ya tambayeta yana kallon cikin idanunta.

Ta ƙifƙifta idanu sau biyu, sai kuma ta marairaice ta ce

"Allah sarki Kamal, ai na zaci isasshen lokacin da na baka jiya daren farkonmu ya isa ka manta da komai. Don Allah kayi haƙuri mana..."

Kafin ta rufe baki ya damƙi tsintsiyar hannunta, yana janta tana turjewa har sai da ya fita da ita daga cikin ɗakin sannan ya yarfar da hannunta da ƙarfin da ya saka ta runtse idanu tana cije baki.

"Da gaske na tsane ki, ba na ko son ganinki. Kina rayuwa a gidannan ne kawai albarkin Mama. Ki fita daga harka ta, idan ba haka ba Wallahi sai na yi mugun saɓa miki."

Yana gama faɗin haka ya shige cikin ɗakinsa da sauri sannan ya rufe ƙofar da ƙarfi.

Ta daɗe a tsaye inda ya barta, sai murza inda ya damƙa a hannunta take yi saboda zafin da yake mata. Daga ƙarshe ta ja ƙafafunta a sanyaye ta koma cikin falon ta zauna akan kujera. Can kuma sai ta tashi ta wuce ɗakinta ta shiga bayi, fitsari take ji.

Sai dai ko da ta zauna a toilet fitsarin bai fito ba sai ƴar kaɗan. Mararta ya sake ƙullewa sosai. A dudduƙe ta fita daga bayin ta kwanta ta dunƙule jikinta a kan gado, can kuma sai ta janyo filo ta kifa mararta a kai. Zuciyarta cike da tunanin sabuwar hanyar da za ta ɓullo ma Kamal...

******

Misalin ƙarfe goma sha biyu da rabi na dare, ciwon mara ya ishi Sakina, tun tana dauriya tana haƙuri bata san sa'adda ta fara hawaye ba. Da yake ita ba yarinya bace, ta san me ke damunta kai tsaye, sha'awa ce ta motsa mata sanadiyyar magungunan mata masu kyau da ƙarfi da ta sha a ranar.

Ganin ciwon mara na neman yayi ajalinta ita ba gwauruwa ba tana da miji, kawai sai ta yanke shawarar tunkarar Kamal komai ta fanjama-fanjam.

Daga ita sai ƴar yaloluwar rigar barci da bai ɓoye komai na halittar jikinta ba ta nufi ɗakinsa, zuciyarta cike da addu'ar Allah yasa ƙofarsa a buɗe take. Cikin tsananin sa'a kuwa tana murɗa hannun ƙofar ta buɗe, saboda tsananin farin ciki bata san sadda ta sauke ajiyar zuciya ba.

Ta shiga ɗakin da siririyar sallama a bakinta. Da yake akwai haske irin mai ɗan duhun nan kunne a cikin ɗakin kai tsaye idanunta ya sauka a kan Kamal. Yana kwance akan gado babu riga a jikinsa, ta haɗiye wani miyau muƙut!

Da alamun idanunsa biyu, domin ta hangi hasken wayarsa riƙe a hannunsa yana dannawa. Yana jin shigowarta ya juyo da sauri yana kallonta, daƙiƙu talatin ya ɗauka yana ƙare mata kallo, sai kuma ya kawar da kansa da sauri yana ƙoƙarin korar wani sabon tunani da yake neman bijiro mishi.

"Me ya kawo ki ɗakina a irin wannan lokacin na tsakiyar dare?"

Ya tambayeta da kaurin murya.

Bata amsa ba, a madadin ta amsa sai ta taka da sassarfa ta rungume shi ta baya. Da yake bai ji tahowarta ba sai rungumar da tayi masa ya ji, duk yadda ya so hana kansa ya kasa, sai da ya ja ajiyar zuciya ya sauke a firgice.

Yai ɗan shiru na wasu daƙiƙu, ita kuma ta yi amfani da wannan damar ta dinga goga mishi ƙirjinta a bayanshi da wani irin salo na jan hankali. Ko me ya tuna sai ya juya da sauri yana fuskantarta, ganin tana neman sake rungume shi cikin ficewar hayyaci yasa shi riƙe kafaɗunta da ƙarfi ya jijjigata.

"Ke Sakina"

Ya kira sunanta a tsawace.

A karo na biyu ya sake wujijjiga kafaɗunta sannan ya sake cewa

"Wai ke wace irin sakaryar yarinya ce? Me yasa ba ki da ganewa ne? Me yake damunki ne?"

"Kamal.."

Ta kira shi a raunane.

"Don Allah kayi haƙuri... Cikina da marata ciwo suke min kamar zan mutu. Ka tausaya min don Allah..."

Ta ƙarasa maganar cikin hawaye.

Kamar ta watsa ma Kamal wuta da kalamanta, sai ya miƙe tsaye zumbur! yana yi mata wani irin kallo mai kama da na zargi.

"Ke da uban waye kuke chatting ɗin banza da musayar Vidiyoyin banza har ya tayar miki da sha'awa?"

Ya jefa mata tambayar cike da hargagi a muryarsa.

Duk da halin da take ciki, sai da ta ɗaga idanu a firgice tana kallonsa.

"Kamal?"

Ta kira sunanshi a tsorace.

"Zargina kake yi?"

Ta tambaye shi bakinta na rawa.

Kafin ya amsa mata sai da ya ɗauki wayarsa ya buɗo mata wani vidiyon tsiraicinta da ta tura mishi na ƙarshe-ƙarshe gab da zai ce ya fasa aurenta.

A vidiyon tana zaune ne a tsakiyar gadonta, ta kafe camera a gabanta tana ta fari da idanu, hannayenta duk biyu suna tallabe da tsayayyun manyan na shanunta tana ta lugwuigwuitasu tana yamutsa su, kawunansu a tsaye cir kamar za su tsokane ma mai kallonsu idanu, tana yamutsa su lokaci ɗaya tana raira waƙar

"Suna kewa... Suna kewar masoyinsu... suna kewa... suna kewar abin ƙauna..."

Sai kuma ta daina waƙar ta cuno mishi kawunansu tana cewa

"Ka gansu Yayana... mararin yamutsar tausasan hannunka suke yi, za ka sha? Za ka sha? Za ka sha?"

Sai kuma ta ƙyalƙyale da dariya sannan vidion ya ɗauke ɗif.

Yayi hurgi da wayar a kan gado, sannan ya fincikota ya shaƙo wuyanta da ƙarfi, idanunsa sun kaɗa sun yi jajur.

"Tunda kika turo min wannan vidiyon, kuma kika kira ni da Yayanki alhalin ba kasafai kike ce min haka ba, na gano kin samu wani ɗan iskan da kike tura mishi hotunan tsiraicinki don ki burge shi... Abinda baki sani ba tunda na gano hakan na fara tsanarki. Duk da na san ni fara keta alfarmarki waɗannan ƴan iskan lalatattun vidiyoyin da kika yi ta turo min ba a gurina kika koya ba. Kuma ko rantsuwa nayi babu kaffara ba ni kaɗai kike tura ma irin waɗannan vidiyoyin ba. Don haka ki ja tsumman jikinki ki bar min ɗaki tun kafin in yi ajalinki Sakina, na tsane ki. Babu wani sura naki ko wani abu da zai sake jan hankalina zuwa gare ki. Fita ki bar min ɗaki tun kafin inyi Ball da ke"

Ya ƙarasa maganar cikin tsawa, sannan ya wancakalar da ita akan gadon.

Ai kuwa saboda tsananin tashin hankali da tsoro da firgici da rarrafe Sakina ta bar ɗakin Kamal.

*****

Faɗin irin tashin hankalin da Sakina ta shiga a wannan dare ɓata lokaci ne. Ashe akwai tashin hankalin da ya fi ƙarfin ayi masa kuka? Domin kuwa idanunta soyewa suka ƙamas! Duk yadda ta so ta fashe da kuka ko ɗigon hawaye ya ƙi fitowa.

Saboda tsananin tashin hankali sha'awar da take ji ma nemanta tayi ta rasa. Da ƙyar ta iya jan sanyayan ƙafafunta ta je bayi tayi wanka ta gargasa wuyanta da tawul saboda zafin da yake mata.

Ko da ta fito daga bayin, bata iya saka komai a jikinta ba ta shige cikin bargo ta lulluɓa har kanta. Wasu irin tunanuka ne a zuciyarta, tunanika mabanbanta a kan Kamal da sabbin halayensa. A yau, a wannan dare, Kamal ya goge mata hadda gaba ɗaya. Kamal ya bata mamaki. Kamal ya ɗaure mata kai.

"Ashe vidiyoyin da take yi na tsiraicinta take tura mishi duk don ta faranta mishi, sannan ta sauƙaƙa mishi halin da yake ciki, kuma yake nuna mata yana jin daɗi duk ƙarya yake yi mata? Ashe shi duk a banza yake kallonta? Ashe tana zubar ma da kanta mutunci ne a gurinsa bata sani ba? Ashe shi zarginta ma yake yi amma shi ne bai taɓa faɗa mata ta daina ba? Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!"

Ta runtse idanunta da ƙarfi, zuciyarta sai suya take mata, kuma duk iya daren ta kasa barci, ko gyangyaɗi ta kasa yi saboda tsananin ƙunci da damuwar da take ciki.

Sai da aka fara kiraye-kirayen sallar farko sannan wani nannauyan barci ya fara yunƙurin awon gaba da ita.

Can a cikin barci kamar tana mafarki ta ji an fincike bargon da ta lulluɓa da shi. Ko kafin tayi wani yunƙuri, ta ji an afko kan jikinta. Da ƙyar ta buɗe idanunta suka shiga cikin na Kamal, sai dai kafin tayi wani yunƙuri ya sakar mata nauyinsa gaba ɗaya cike da salon mugunta da son zuciya.

Duk yadda ta so tayi yunƙurin ture shi ta kasa ko ƙwaƙƙwaran motsi, shi kuwa yayi amfani da damarsa ya fara mu'amalantarta a wulaƙance cike da mugunta kamar mara galihu.

Babu wani tausasawa balle aika ɗan saƙo kamar yadda addini yayi umarni. Har aka kira sallah na biyu, aka tada iƙama, aka idar, bai sarara mata ba. Da yake ko kusa shi ma babu wani shauƙin al'amarin a tare da shi.

Zallar mugunta ce kawai da kuma niyyar koya mata hankali da yayi. Ai kuwa sai da yayi yaga-yaga da ita, ya yayyaƙusheta, ya ciccije mata kan nashanunta saboda tsananin mugunta, sai da gari ya fara washewa sannan ya ɗaga ta a wulaƙance.

Zuwa wannan lokacin Sakina ta kai matuƙa gurin galabaita, ko ɗan yatsarta da ƙyar take iya ɗagawa, idanunta sun yi jajur, har lokacin ta kasa yin kukan idanu sai na zuci.

"Ba daɗi... Ba wani shauƙi... Babu wani sabon abu wanda ban sani ba a tare da ke Sakina... Ko da yake daman wani dare ne jemage bai gani ba? Ai sai dai daren mutuwarsa. Mutunci madara ne... Ke kam kin daɗe da ɓarar da naki a idanuna kuma bazai taɓa kwasuwa ba."

Ya ja mata wani dogon tsaki sannan ya fice daga ɗakin...

Saura pages biyar in sha Allah in gama Free pages. Kin biya kuɗin karatun labarin kuwa? Wannan littafin sabuwar tafiya ce mai cike da sabon salon da zai ilmantar da ku, ya faɗakar, sannan ya nishaɗantar da ku in sha Allahu.