MUTUNCI MADARA...

BABI NA GOMA SHA ƊAYA

by @fareedaabdallah

MUTUNCI MADARA...

©Fareeda Abdallah

Paid book ne. Kuɗin karanta labarin 1k kacal. Ki tura kuɗinki ta wannan account ɗin 7039080978, Opay, Farida Abdullahi, sai a tura min shaidar biya ta wannan numbern *** domin samun damar kasancewa a group ɗin da zan dinga posting ɗin littafin akan lokaci in sha Allahu.

Ina kuke Ƙasaitattun mata ƴan gayu waɗanda basa ƙyashin cire kuɗi su gyara kicin ɗin su da jikinsu? Me kike buqatar siya a gurinmu Hajjaju? To ki dakata a nan, domin kayanki ya tsinke a bakin kaba💃🏽 Idan ma kuɗin ne kike ƙyashin cirewa a lokaci ɗaya muna adashen gata don sauƙaƙa ma abokan hulɗar mu🥰 Duk abinda kike son siya za mu baki dama ki tara kuɗinsa sannu a hankali bayan kin gama biya ki karɓa bisa gaskiya da amana 🤝 Idan kayan kicin kike so ga link ɗin group kiyi joining.

👇👇👇👇

***

Bayan kayan kicin muna sayar da ƙayatattun Laces, Shadda, Atamfa, Veil's, Shoes, bags. Abin burgewar kuma shi ne muna bada kayanmu akan farashi mai sauƙin gaske👌🏽👌🏽🥰 ku yi joining group ɗinmu ku kwashi garaɓasa Sisters💃🏽💃🏽

👇👇👇👇

***

Sannan kuma muna da Group da muke siyar da Lagos shoes, muna bada sari daga 6pcs akan farashi mai kama da kyauta🥰👌🏽Wannan dama ce ga masu son fara sana'a, da kuma waɗanda suke sana'ar💃🏽💃🏽

👇👇👇👇

***

11)

'Kafin ya tafi ɗakin Sakina har ya aikata wannan abinda ya faru. Tun bayan fitarta daga ɗakinsa ta barshi cikin ƙunan zuciya, ya daɗe yana cika yana batsewa, zuciyarsa cike da takaicin yadda har ya bari ta fita bai kwak-kwasa mata mari ba. Da ƙyar ya fara ƙoƙarin yakice tunani da damuwarta daga zuciyarsa. A ƙoƙarinsa na mantawa da Sakina da matsalarta, ya ɗauki wayarsa ya kunna da nufin cigaba da kalle-kalle a social media domin ya ɗauke mishi hankali, sai dai abin ya ci tura.

Sai dai abin takaici duk page ɗin da ya shiga kamar aikin asiri sai ya ga fuskarta tana hawaye. Can kuma sai ya fara tuna yadda ta shigo ɗakin cikin sanyin murya tana kiran sunansa. Ya tuna yadda hawaye suka cika idanunta lokacin da ta ce, 'Don Allah ka tausaya min Kamal...'

Sai ya ja tsaki da ƙarfi. A fili ya ce, 'Munafuka kawai', Sai kuma wani sashe na zuciyarsa take ya musanta kalmar munafunci da ya jingina ma Sakina. Domin idan bai manta ba tun daga ranar da ya fara sonta, bai taɓa kama Sakina da laifin munafurci ba.

Kamar an tsungule shi sai ya miƙe ya fara sintiri a tsakar ɗakin. Can kuma sai ya tsaya a gaban madubi. A karo na barkatai fuskarta ta sake faɗo masa a rai...

A take kuma sai fuskarta ta ɓace, hoton irin vidiyoyin da tai ta tura mishi na tsiraici ba kunya ba tsoron Allah sukai ta hasko mishi a fuskarsa. Nan take tsanarta sabo fil ya dawo a zuciyarsa.

'Na tsaneki Sakina...'

Ya faɗa a fili zuciyarsa na ƙuna. Kamar a tv sai kuma aka hasko mishi yadda ta shiga ɗakinshi da shara-sharan rigar barcin jikinta, ya tuna yadda ta rungume shi ta baya tana goga mishi ƙirjinta. Ya runtse idanu da ƙarfi, jikinsa ya amsa masa da wani irin yanayi da ya daɗe bai shiga ba a dalilin Sakina.

Da sauri ya nufi bayi ya watsa ma jikinshi ruwa. Sai dai maimakon ya samu sauƙin lamarin sai ƙara hauhawa ya yi, ya kwanta a takure. Minti goma, ashirin, talatin, har lokacin barci ya ƙi ɗaukarsa. Tunanin Sakina kuma sam ya ƙi fita daga zuciyarsa.

Can kuma sai Shaiɗan ya fara yi mishi sabuwar saƙa da mugun zare, wannan saƙa ba komai bane dace tunzara shi ya je ya kusanci Sakina a wannan dare, to amma fa zai kusance ta ne ba don soyayya ba, zai kusance ta ne don ya ƙara tabbatar mata a yanzu ba ta da wani sauran daraja a gurinsa. Wani irin murmushin takaici da baƙin ciki ya suɓuce masa, nan take ya miƙe ya nufi ɗakin Sakina...'

******

Sakina ta ɗauki kusan awa ɗaya a kwance kamar yadda Kamal ya bar ta, ko ƙwaƙƙwaran motsi ba ta iya yi saboda tsananin jigatuwar da ta yi.

Wani irin yana yi take ji a zuciyarta, ba yanayin fushi ba, ba yanayin takaici ba. Wani irin yanayi ne take ciki mai kama da mutum ya ɗauki lokaci mai tsawo yana tafiya ɗauke da wani babban buri a zuciyarsa, yana daf da isa inda ya nufa, kwatsam! sai ya gano cewa tun farko hanyar da yake bi ba ita ce hanya madaidaiciya ba.

Abin haushin kuma shi ne har lokacin ta kasa fashewa da kuka. Ta runtse idanu da ƙarfi. Kalaman Kamal suna sake dawo mata a zuciya.

"Ba daɗi..."

"Babu wani sabon abu da ban sani ba a tare da ke Sakina..."

"Mutunci madara ne ke kuma kin daɗe da ɓarar da naki bazai taɓa kwasuwa ba..."

Kamar a lokacin yake faɗa mata kalaman, sai ta ji wani irin raɗaɗi mai zafi ya ratsa ta. A hankali ta miƙa hannuwa ta janyo bargon da yake yashe a gefen gadon ta lulluɓe jikinta gaba ɗaya.

Yau dai a karon farko, tun bayan da Kamal ya fara nesanta kan shi da ita, ta fara tunanin cewa wataƙila ba zai taɓa komawa irin Kamal ɗin da ta sani a baya ba.

Ko da ya canja tana rayuwa ne da shi da wani irin kyakkyawan fata. Fatan cewa wata rana zai fahimci kuskurensa. Fatan cewa wata rana zai fahimci irin matsanancin son da take masa. Fatan cewa wata rana zai daina kallonta a matsayin mai laifi.

Sai dai kuma abin da ya faru tsakaninsu da asubahin nan ya fara karya mata waɗannan fata-fatan ɗaya bayan ɗaya. Domin a yau ba kawai zarginta ko tsanarta Kamal yake yi ba.

Ya wulaƙanta ta. Ya tozarta ta. Ya kuma bayyana mata cewa ko da ya kusance ta, ba wai don yana sonta ba ne. Saboda haka me ya rage da bai nuna mata ba? Wace irin fata ce za ta ci gaba da ginawa a zuciyarta bayan wannan abinda ya gwada mata ganin idanunta??

Sai a wannan gaɓar ta ji wani zazzafan hawaye ya gangaro mata. Sai bata hana kanta kukan ba. Ta yi ta kuka mai tsuma zuciya. Kuka irin na wacce ta gaji. Kuka irin na wacce ta fara rasa ƙarfin zuciyar da take ɗauke da shi...

****

A can ɗakin Kamal kuwa, yana zaune a ɗaya daga cikin kujerun ɗakinsa. Har ya yi wanka, ya yi sallar da bai samu yi akan lokaci ba.

Sai dai kuma wani abu da ya rasa ganewa shi ne, maimakon bayan faruwar komai zuciyarsa ta samu sauƙi, sai kuma wani irin rashin natsuwar zuciya yake damunsa.

Ya ɗauki wayarsa, ya ajiye. Ya kunna Tv, ya kashe. Ya buɗe WhatsApp, ya sake fita. Ya buɗe face book, ya fita. Sai kuma ya aje wayar a gefe ɗaya ya lumshe idanu yana saƙe-saƙe.

Can kuma sai ya miƙe zumbur! Ya fara zagaye cikin ɗakin, minti ɗaya kuma ya koma ya zauna. Duk abin da yake yi ya kasa ɗauke masa tunani, wannan tunanin kuwa ba na kowa bane face Sakina.

Ya ja tsaki da ƙarfi, a fusace ya ce a fili

"Wai ma me yasa nake ta tunaninta?"

Nan take wani sashe na zuciyarsa ya amsa masa da cewa

"Saboda har yanzu kana son ta."

Da sauri ya dafe kansa yana cewa

"A'uzubillahi minashshaiɗanir rajim."

Domin ya tabbata wannan amsar ba daga kowa bane face Shaiɗan.

Nan take ya tuna matsiyatan vidiyoyin Sakina. Ya tuna hotunanta na banza da ita da kanta ta tura mishi. Ya tuna yadda take yi masa magana a cikin vidiyon da salon da yake ganin ba nata ba ne sam! Nan take wani irin fushi da tsanarta ya sake turnuƙe shi.

Ganin tunanin banza da wofi na neman hana shi kataɓus kawai sai ya ɗauki wayarsa, da makullin motarsa ya fice daga ɗakin.

Yana isa tsakar gida direban Mama na isa gidan da abincinsu, karɓan abincin yayi ya shiga da shi ciki ya aje a tsakiyar falo, sannan yayi ficewarsa a gidan, ba tare da tunanin ya shiga ɗakinta ya duba halin da take ciki ba.

******

A can cikin ɗakin Sakina kuwa har lokacin tana kwance, domin jikinta babu ƙarfi gaba ɗaya. Tana jin sadda aka buɗe get aka shigo, sannan aka fita da mota. Ta girgiza kai kawai, don ta san Kamal ne ya fice daga gidan.

A hankali ta fara ƙoƙarin yunƙurawa ko za ta iya miƙewa ko ba don komai ba don Sallar Asubah, da kuma wata matsananciyar yunwa da tun ɗazu ta ke nuƙurƙusarta.

Ta na ƙoƙarin miƙewa kawai sai ta ga ɗakin ya fara juyawa a idanunta. Ga wani azababben zafi da ya ratsa tsakankanin ƙafafunta, ai kuwa ba shiri ta koma ta kwanta tana cije baki da ƙwallah a idanunta.

Sai a lokacin ta tuna tun jiya da rana babu wani abincin kirki da ta ci.

Magungunan da Aunty Lubnah ta ba ta ne kawai suka cika cikinta.

Da ta tabbatar ba Sarki sai Allah kawai sai ta fara addu'a a zuciyarta tana fatan Allah ya jefo da wacce za ta iya taimaka mata.

Ta ɗauki tsawon lokaci a haka, har ta fara sarewa ta fitar da rai. Barcin da bata samu jiya ba na wahala ya fara ɗaukarta, kamar a mafarki kawai sai ta ji ana ƙwanƙwasa ƙofar ɗakinta, da muryar mace tana ta doka sallama.

Aikuwa da sauri cikin rawar murya ta wage baki tana amsa sallamar, lokaci ɗaya tana haɗawa da tambayar

"Wace ce?"

Bata jira an amsa ba ta sake wage murya tana bada umarnin a shiga, ƙofar ɗakin a buɗe take, zuciyarta cike da yaƙini da fatan duk wacce za ta je gidan a yanzu, to fa lallai Ubangiji ne ya karɓi addu'arta ya turo wacce za ta taimaka mata.

Sannu a hankali aka buɗe ƙofar, lokaci ɗaya ana cewa

"Amarya...? Kina ciki ne?"

"Eh! Ina.. kwa..na"

Sakina ta amsa da ƙyar, ganin baƙuwar fuskar matashiyar matar da bata taɓa gani ba a rayuwarta.

Ita kanta Matar sai ta ɗan tsaya turus! Ganin Sakina naɗe a kan gado. Sai kuma ta ɗan wayance da murmushi a fuskarta ta ce

"Lafiya ƙalau Amarya. Kiyi haƙuri, Sunana Amina. Da ga nan maƙwaftanku nake, gida na biyu a gaban naku. Wallahi tun jiya da yarinyata Firdausi ta biyo rububin yara suka shigo ganin ɗakin Amarya har kika basu dubulan ta ishe ni da maganar kina da kirki. Tun jiyan take ta min nacin in shigo mu gaisa na ƙi, yanzu ma tana ƙofar gida ta ga fitar Angonki shi ne ta shiga da gudu ta ishe ni da roƙon in shigo mu gaisa har da kukanta. To ashe ma ko tashi baki yi ba, kiyi haƙuri don Allah, bari in koma tunda mun gaisa, na dawo wani lokaci."

Har ta kama hannun ƙofar za ta murɗa ta fita, Sakina ta ga lallai fa idan ta bari Amina ta fita daga gidan ba lallai ta ƙara samun wacce za ta taimaka mata a kusa ba. Don haka ta buɗe baki a raunane, idanunta cike da hawaye ta ce

"Aunty Amina ɗan tsaya don Allah, ki taimaka min in miƙe zuwa bayi don Allah."

Da sauri Amina ta waiga tana kallon Sakina, ta ɗan tsaya jim! Sai kuma ta ce

"Ba damuwa Amarya."

Ta taka a nutse zuwa gurin gadon Sakina. Ba tare da tunanin komai ba Sakina na ƙoƙarin ƙanƙame bargon da take lulluɓe da shi Amina tasa hannu ta yaye bargon

"Subhanallahi!"

Ta furta da sauri sannan tayi gaggawar lulluɓa ma Sakina bargon. A kunyace da muzanta Sakina ta kawar da kanta gefe ɗaya.

Amina kamar baza ta ce komai ba, can kuma sai ta ce a hankali

"Lafiya kuwa Amarya?"

Kafin Sakina ta amsa sai ta sake cewa

"Ko dai daren farko ne?"

Sai da wasu zafafan hawaye suka gangaro ma Sakina sannan ta ɗaga kai a hankali. Zuciyarta cike da takaici da baƙin cikin wannan tozarci da Kamal ya ja mata, yanayin da ya kamata ya zama sirrinsu ita da shi amma sanadiyyar tozarcinsa yasa ta bayyana shi ga wacce bata taɓa saninta ba.

Kamar Amina ta san tunanin da take yi sai ta ce

"Ki kwantar da hankalinki Amarya. Ni ma'aikaciyar jinya ce. Don haka ki saka a ranki Angonki ne ya ɗauko ni in baki taimakon gaggawa ba don ba ya son ki ba. Kin fahimta?"

A karo na biyu Sakina ta sake ɗaga kai.

Nan take Amina ta cire hijabinta ta ajiye a gefe ɗaya. Kafin ta ɗaga Sakina sai da ta shiga banɗaki ta tara mata ruwa mai zafi, sannan ta je ta kamata a hankali tana lallaɓata kamar ƙanwarta na jini har suka isa banɗaki.

Amina ita ta taimaka ma Sakina ta gasa jikinta sosai, sannan ta haɗa mata ruwa ta ce tayi wanka ita kuma ta fita a bayin. Ko kafin Sakina ta fito har Amina ta gyare mata ɗakin ƙal.

Sannan ta fita zuwa teburin cin abinci ta haɗo mata Tea mai kauri, ta zubo mata dankalin turawa da ƙwai a flate. Sai a lokacin Amina ta tuna da ƴarta da suka je gidan tare. Tana zaune akan kujera tana game a wayar Mamanta. Dama ko da suka shiga basu tarar da Sakina a falo ba, ita yarinyar ce ta nuna mata ɗakin Sakina da cewa jiya nan ta ga Sakina ta shiga da manyan baƙinta.

Ce ma yarinyar tayi tana zuwa. Ta sake komawa ɗakin Sakina, sai ta tarar har ta lallaɓa ta fito daga bayi, ta zura doguwar riga tana sallah a zaune.

Tea da dankalin ta ajiye a gefenta ta ce

"Idan kin idar don Allah ki ci abinci. Bari in je gida in ɗauko miki magungunan da za ki sha, yanzu zan dawo."

Tana gama faɗin haka ta fice da sauri.

Amina ba ta koma gidan ba har sai da Sakina ta gama karyawa, ta lallaɓa ta fita falo ta kwanta akan doguwar kujera. Duk da ta ɗan shafa mai ta mutsuka Powder a fuskarta, kallo ɗaya za a yi ma Sakina a ga ramar da tayi a dare ɗaya. Idanunta gaba ɗaya sun zurma ciki saboda wahala.

Har ta fara gyangyaɗi sai ta ji muryar Amina tana tashinta, kama ta tayi a hankali suka koma ɗaki. Suna tafiya Amina ke ce ma Sakina

"Sai fa kin yi haƙuri ƙanwata, na ga ɓarnar da Ango yayi ba kaɗan bane, sai kin yi haƙuri ko ɗinki biyu na yi miki a ta gurin nan, idan ba haka ba kuwa za ki daɗe baki koma yadda ake so ba, idan ba sa'a aka yi ba ma kin buɗe kenan. Kin amince ayi ɗinkin ko?"

Da sanyin murya sosai Sakina ta amsa da

"Babu komai Aunty. Na amince a yi. Na gode da taimakonki, Allah ya biya ki da mafificin alkhairinsa."

"Amin ya rabb"

Amina ta amsa fuskarta cike da jin daɗin addu'ar da Sakina tayi mata.

Duk da ta yi ma Sakina allurar kashe zafi, ba ƙaramin wahala ta sha gurin yin ɗinkin nan ba. Amma ta yi matuƙar dauriya ƙwarai da gaske, saboda ta sa a zuciyarta baza ta taɓa bari son zuciyar Kamal ya lalata mata martabarta ta ɗiya mace ba.

Sai da aka gama ɗinkin, sannan Amina ta bata magunguna ta sha, da yake cikin magungunan har da na barci. Nan da nan nannauyan barci yayi awon gaba da Sakina.

A dole Amina ta bar Firdausi a falon Sakina, ta kunna mata MBC3 ta ce ta zauna tayi kallo, zuwa sadda Sakina za ta farka daga barci.