BABI NA GOMA SHA BIYU
MUTUNCI MADARA...
©Fareeda Abdallah
Paid book ne. Kuɗin karanta labarin 1k kacal. Ki tura kuɗinki ta wannan account ɗin 7039080978, Opay, Farida Abdullahi, sai a tura min shaidar biya ta wannan numbern *** domin samun damar kasancewa a group ɗin da zan dinga posting ɗin littafin akan lokaci in sha Allahu.
Ina kuke Ƙasaitattun mata ƴan gayu waɗanda basa ƙyashin cire kuɗi su gyara kicin ɗin su da jikinsu? Me kike buqatar siya a gurinmu Hajjaju? To ki dakata a nan, domin kayanki ya tsinke a bakin kaba💃🏽 Idan ma kuɗin ne kike ƙyashin cirewa a lokaci ɗaya muna adashen gata don sauƙaƙa ma abokan hulɗar mu🥰 Duk abinda kike son siya za mu baki dama ki tara kuɗinsa sannu a hankali bayan kin gama biya ki karɓa bisa gaskiya da amana 🤝 Idan kayan kicin kike so ga link ɗin group kiyi joining.
👇👇👇👇
***
Bayan kayan kicin muna sayar da ƙayatattun Laces, Shadda, Atamfa, Veil's, Shoes, bags. Abin burgewar kuma shi ne muna bada kayanmu akan farashi mai sauƙin gaske👌🏽👌🏽🥰 ku yi joining group ɗinmu ku kwashi garaɓasa Sisters💃🏽💃🏽
👇👇👇👇
***
Sannan kuma muna da Group da muke siyar da Lagos shoes, muna bada sari daga 6pcs akan farashi mai kama da kyauta🥰👌🏽Wannan dama ce ga masu son fara sana'a, da kuma waɗanda suke sana'ar💃🏽💃🏽
👇👇👇👇
***
12)
Duk da barcin da Sakina take yi tana yi ne da taimakon magunguna, sam barcin bai yi kama da na wacce take cikin nutsuwar zuciya ba. Magungunan da Amina ta bata sun yi tasiri gurin tsawaita barcinta ne kawai, amma damuwa da ƙuncin da take ciki yana nan danƙare a zuciyarta.
Wannan dalilin yasa lokaci bayan lokaci take motsawa cikin barcin a ɗan firgice, can kuma sai ta ɗan haɗe gira kamar wacce take fama da wani azababben mafarki.
A lokacin, Amina har ta sake komawa gidan. Tana zaune a Kujera ɗaya na ɗakin Sakina tana kallonta lokaci bayan lokaci. Babban burinta Sakina ta farka, idan ta ga a yanayin da ta farka da sauƙi sosai sai ta ɗauki Fiddausi su tafi.
Haka kawai, wani irin tausayin Sakina ya lulluɓe zuciyarta. Ga shi dai bata taɓa sanin Sakinan ba sai yau, amma haka nan halin da ta same ta a ciki ya tsaya mata a zuciya ba kaɗan ba, kuma ya jefa ta a tunani.
Ba abu bane mai sauƙi sannan abin mamaki da damuwa ne sosai Ango yai yaga-yaga da Amarya a darensu na farko, sannan kuma ya tsallaketa ba tare da damuwa ko bata kulawa a halin da take ciki ba kawai yai tafiyarsa.
Kuma a ce har ana neman a yini bai koma gidan ba, bai kira ta waya ya dinga nuna mata kulawa ba. Tabbas wannan abin mamaki ne da tsayawa a zuciya sosai.
A matsayinta na ma'aikaciyar jinya, ta ga mata da yawa da suka shiga wahala iri-iri sanadiyyar mazajensu. Ta ga matan da mazajensu suke cin zarafinsu har a asibiti. Ta ga waɗanda suka fuskanci cin amanar aure, sanadiyyar haka suka kamu da mummunan cuta har suka ƙulla abota da zirga-zirgar asibiti. Ta ga matan da mazajensu ke jibgarsu, mari kuwa wannan ba komai bane tsakaninsu da matansu.
Amma fa ganin Amaryar da Miji ya tara da ita a darensu na farko, kuma ya wulaƙantata irin wannan mafi munin wulaƙanci abu ne da ba kasafai ta cika samun case a kai ba.
Kallon fuskar Sakina kawai da ta yi ya isa ya sanar da ita cewa akwai wani abu da yake damunta wanda ya fi munin wulaƙantata da mijinta ya yi. Wani abu take gani mai zurfi. Wani abu da ya karya zuciyar Sakina.
A hankali Amina ta ja nannauyar ajiyar zuciya ta sauke. A dai-dai lokacin Firdausi ta shigo ɗakin da sauri, muryarta ƙasa-ƙasa ta ce
"Mama."
Amina ta ɗaga kai tana kallonta da sauri, don ta zaci wani muhimmin abu ne.
Buɗar bakin Fiddausi sai cewa ta yi
"Mama kin ga Aunty Amarya tana da kyau sosai ko?"
Sai da Amina ta yi murmushi sannan ta ce
"Na ganta tana da kyau sosai Fiddausi. Me ya faru?"
Firdausi ta matsa kusa da Mamanta tana yi tana leƙa fuskar Sakina.
"Wallahi Mama ba komai, ni dai haka kawai Aunty Amarya take burgeni tunda ta bani dubulan jiya. Ina son ta"
Amina ta yi dariya.
"Ni ma ina sonta tunda kina sonta Fiddausi."
Wani abu da Amina da Fiddausi basu sani ba shi ne, Sakina tana jin duk maganganunsu. Tana barci ne, amma maganganun kai tsaye suke shiga kunnuwanta kamar tana mafarki. A hankali wani zazzafan hawaye ya silalo daga gefen idonta na hagu.
Tun da suka yi aure Mijinta bai ce yana sonta ba. Ko kaɗan bai nuna mata kulawar da ta dace a matsayinta na Amaryarsa ba. Sai ga shi wata ƙaramar yarinya da mahaifiyarta da suke matsayin baƙi a rayuwarta suna yi mata abin da ya kamata ta samu daga miji da take aure.
****
A can Ofishin Kamal, tunda ya je ya kasa tsinana wani abin arziki. A teburin gabansa akwai files da ya kamata a ce tun safe ya duba, ya shigar da bayanai a Laptop ɗin da ke gabansa, Amma ko ɗaya baiyi ba. Yana zaman ɗumama kujera ne kawai tun safe, sallar azahar ma a cikin Ofis ɗin ya yi.
Misalin ƙarfe biyu da rabi na rana, akwai taron ganawar da aka gudanar da ma'aikatan gurin gaba ɗaya, amma sam Kamal ya kasa shiga, sai uzurin rashin lafiya ya bada.
Wani saƙon Email da Oganshi ya ce ya tura mishi ya duba, sau takwas yana karantawa amma sam bai fahimci komai ba.
Zuciyarsa gaba ɗaya a ƙuntace take, ya rasa me damunsa, ya kuma rasa abinda yake yi masa daɗi. Daga ƙarshe a fusace ya matsar da Laptop ɗin da ke gabansa gefe ɗaya.
A karo na barkatai fuskar Sakina ta sake baiyana a cikin idanunsa. Sai dai kuma a yanzu ba fuskar jiya ba ce da take ta roƙonsa a marairaice da hawaye cike da idanunta. Ba fuskar lokacin da take dariya ba ne sadda suke cikin jin daɗi da tsananin son juna. Ba fuskar shauƙi irin na lokacin da take turo masa vidiyoyin tsiraicinta ba.
Fuskar da ya bari a tare da ita da safiyar yau ne, fuskar da ta yi jajur saboda ɓacin rai amma babu hawaye. Fuskar da babu komai a cikinta sai ƙunci da bayyana alamun ciwon da ke danƙare a zuciyarta.
Nan take ya miƙe tsaye, ya dafe goshinsa a fili ya ce
"Damuwar Sakina ko kuma wani hali da na bar ta a ciki wannan fa ba matsalata ba ce."
Sai dai kuma zuciyarsa ta ƙi amincewa da zancen bakinsa. Nan take wani sashe na zuciyar ya jefa masa tambayar
'Idan ba matsalarka bace me yasa tun safe ka kasa kataɓus sai tunaninta?'
Shi kanshi ba shi da amsar wannan tambayar. Kawai sai ya ɗauki wayarsa da makullin motarsa ya fice daga Ofishin. Yana isa inda suke Packing ɗin motocinsu kawai sai yayi kiciɓus da abokan aikinsa Muhammad da Nura, da alamun fita za su yi, kuma a motar mutum ɗaya za su fita.
Har sun fara mishi tsiyar Ango Ango ka sha ƙamshi sai suka ga fuskarsa ba walwala.
"Wai jikin naka ne har yanzu?"
Nura ya tambaye shi.
"To ko dai sai ka dangana da asibiti ne?"
Muhammad ya faɗa kafin Kamal ya amsa tambayar da Nura ya fara yi mishi.
Ya ɗan yamutsa fuska, sai kuma ya kore tambayoyinsu ta hanyar cewa
"Ina za ku je ne haka na ga kuna haramar fita?"
"Wallahi wani sabon ɗan ƙaramin gurin cin abinci ne aka buɗe a can Tudun wada. A yawace-yawacen Nura ya gano mana gurin, to fa tunda muka ɗanɗana abincinsu Wallahi yanzu ba ma iya cin abincin rana a ko ina sai can."
Muhammad ya amsa yana dariya.
"Ni fa ka ga ɗazunnan Madam ta aiko min da abinci, amma ɗan tsakura kawai nayi yanzu na fito zan je can gurin Hajiya Adama in ci Sinasir. Matar ta san hannunta ne ina faɗa maka, ko tuwon shinkafa, ko sakwara, ko waina, ko sinasir, ko Alale duk wanda ka ɗanɗana ƙarshen haɗuwa kenan. Wani farfesun nama da take yi da daddawa kuwa..."
Ya haɗiye miyau muƙut! Sannan ya ƙarasa da
"...Ba a ba yaro mai ƙwuiya."
Suka yi dariya gaba ɗaya har da Kamal.
"Ko za mu je ka gwada abincin ne Ango.?"
Muhammad ya tambayi Kamal yana kashe mishi ido ɗaya.
"Haba! Haba rufa mana asiri Muhammad. Kana ganin shi sabon Ango ai kai ka san lafiyayyen haɗaɗɗen girkin Amarya na can na jiranshi. Yawon gidan abinci ai sai mu da muka kwana biyu da shiga daga ciki."
Nura ya faɗa yana dariya tun kafin Kamal ya bada amsar tambayar da aka yi mishi.
Wannan maganar da Nura yayi na cewa bazai iya zuwa gidan cin abinci ba saboda Sakina kawai sai ya ji a ranshi gara ya je ɗin, ko don ya ƙara ƙuntata mata. Da wannan tunanin yasa shi cewa
"Mu je ka ji Muhammad. Ka ƙyale Nura da sharrin shi."
Suka yi dariya. Da farko duk sun zaci da wasa yake yi, sai da suka ga ya buɗe motar Muhammad da suke tsaye a jikinta ya shiga ciki sai suka yadda da gaske yake yi zai bi su.
Bayan duk sun shiga Muhammad ya tayar da motar, shi kuma Nura cikin dariya da salon tsokana ya ce
"Ni dai Wallahi babu ruwana idan Amarya ta ji labari."
Har suka isa gidan abincin suna ta hira da dararraku a tsakaninsu. Wannan hira da suka yi shi yasa zuciyar Kamal ta ɗan saki, ya kawar da damuwa ya cigaba da Walwala a cikinsu.
Cikin ƙanƙanin lokaci suka isa, ashe ma babu wani nisa mai yawa tsakanin gurin abincin da ma'aikatarsu. Kamar yadda suka ce mishi ƙaramin gurin cin abinci ne, sai dai matar da take da gurin cin abincin da alamun ta ɗauki sana'ar da muhimmanci. Kuma tana da tsafta, don ko ina ƙal-ƙal yake yana fitar da daddaɗan ƙamshi.
Daga yadda ya ga su Nura suna wasa da matar da suke kira Hajjaju ya tabbatar mishi da a ɗan zuwan da suke yi har sun saba da ita. Gurin abincin yana da sassauƙan tsari, za ka iya zuwa ɓangaren da Hajiya da ma'aikatanta suke ka saka Order da kanka, sannan kuma za ka iya zama a ɓangaren cin abinci, yaran shago za su biyo ka su tambayi abinda za a kawo maka.
Da yake bai san kan gurin ba, biye yake da su Nura har suka ƙarasa gurin wani ɗan kanta da aka rufe da shara-sharan labule, kai tsaye suka yaye labulen, sai ga Hajiyar zaune a kan wani babban kujera, a gefe da gefenta kuma ƴan matan shagon ne, sun sha T.shet da skeirt iri ɗaya.
A can gefe guda kuma wata yarinya ce sanye da zumbulelen hijabi zaune akan kujera, da casbaha a hannunta tana ja tana ta motsi da baki. Kai tsaye idanun Kamal a kan yarinyar suka sauka, duk da kuwa gefen fuskarta fari sol kawai yake gani daga inda yake tsaye. Ya kalle ta na wasu daƙiƙu sai ya ɗauke kansa, ya mayar kan Hajiyar da suke gaisawa da su Muhammad cikin barkwanci.
"Hajjaju yau babban baƙo muka kawo miki, kin ganshi nan Ango ne sabo fil a leda. Kwana biyu da auren shi muka ce lallai ya kamata yau ɗaya dai ya biyo mu ya ɗanɗana haɗaɗɗen girkin Hajjaju mai barazanar tsinke kunne."
In ji Nura sarkin karaɗi ne yake wannan ƙarin bayanin.
Shi dai Kamal sai murmushi yake yi, da yanayin kunya a fuskarsa. A kan idanunsa ya ga wannan farar yarinyar da take riƙe da casbaha ta juyo da fuskarta gaba ɗaya tana kallonsa. Dara-daran manyan fararen idanunta da suka sha kwalli rangaɗaɗau ta zuba a fuskarsa, tsawon daƙiƙu talatin sai kuma ta kawar da kanta daga gare shi ta cigaba da abinda take yi.
A hankali Kamal ya sauke ajiyar zuciya, lokaci ɗaya sanyin jiki daga inda bai sani ba ya lulluɓe shi. Da ƙyar ya mayar da hankalinsa kan Hajjaju suka gaisa, ta tambayi me za a kawo mishi? Ya ce Sinasir da farfesun naman Rago.
Su Nura ma kowa ya saka order abinda yake so sannan suka wuce zuwa inda aka tanada don zaman cin abinci.
Idanun Kamal yana kan wayarsa yana daddanawa, sai jin wani tattausan ƙamshin turare yayi yana shiga hancinsa, ko da ya ɗaga ido, sai ya ga wannan farar yarinyar mai sanye da zumbulelen hijabi ce ta kawo mishi abincin da ya saka Order.
Nura da Muhammad kuma sauran ƴanmatan shagon ne suka kai musu nasu abincin.
"Ustaza Maryamu manyan ƙasa, ganinki sai an cika Foma-fomai ba ma form ɗaya ba. Yau kuma ke da kanki ne kika kawo abincin ke da sam ba kya son matsawa daga kusa da Hajiya?"
Nura yayi maganar da mamaki yana kallon yarinya mai hijabi.
A kan idanun Kamal, ya ga ta saki wani ƙayataccen murmushi. Bata ce komai ba ta ɗan tattare hijabinta da ke jan ƙasa gefen hijabin har yana taɓa jikin rigar Kamal tayi wucewarta.
*****
Misalin ƙarfe huɗu na yamma Sakina ta farka daga nannauya kuma wahalallen barcin da ta yini tana yi. A hankali ta buɗe idanunta, wacce ta gani a zaune a ƙasa kusa da gadonta tana wasa da Teddy Firdausi ce.
Kamar an ce Firdausi ta kalli Sakina, kawai sai ta ga idanun Sakina a buɗe. Ai kuwa sai ta fara dariya tana murna ta ce ma Sakina
"Aunty Amarya kin tashi? Yanzu me yake miki ciwo?"
Sakina ta kasa hana kanta yin murmushi, sai kallon yarinyar take yi da idanun burgewa. A hankali ta miƙa hannu ta shafo kan Firdausi sannan ta amsa da
"Na tashi Baby, ke ce Firdausi?"
Kai yarinyar ta ɗaga, sannan ta amsa
"Eh! ni ce."
Kafin Sakina ta sake cewa wani abu Firdausi ta miƙe da sauri tayi hanyar ƙofa tana cewa
"Bari in kira Mamana ta baki magani, dama ta ce min kina farkawa in kira ta"
Ko kafin Sakina ta amsa har ta fice da gudu.
Sakina ta bita da kallo a ranta tana cewa
"Ƙuruciya mai daɗi."
Ta yunƙura a hankali ta miƙe zaune, cikin hukuncin Allah sai ta ji jikinta da sauƙi, ba kamar da safe ba. A hankali ta sauka ta taka har zuwa bayi, ta tara ruwan zafi ta sake gasa jikinta sosai, sannan ta ƙara yin wanka.
Ko da Amina ta koma gidan ta tarar da ita har ta shirya ta gama ramakon sallah, tana zaune akan dadduma tana tasbihi.
"Alhamdulillahi! Lallai Aunty Amarya jiki da sauƙi, to Allah ya ƙara lafiya."
"Amin Aunty. Ina dai sake miki godiya, Allah ya saka miki da mafificin alkhairi ya raya zuri'a."
"Amin thumma Amin."
Amina ta amsa da murmushi a fuskarta.
Shiru ya ɗan ratsa tsakaninsu na daƙiƙu. Sakina ce ta karya shirun da cewa
"Yanzu Aunty kuɗin Treatment ɗin da kika min gaba ɗaya ya kama nawa kenan? Sai ki bani account number in tura miki..."
"Haba haba Allah ya kiyaye. Ni na yi miki komai ne saboda Allah Sakina. Fatana dai Allah ya baki lafiya. Roƙona a gare ki shi ne don Allah ki daure ki cigaba da gasa jikinki da ruwan zafi, sannan kuma ki dinga shan magungunanki akan lokaci. Idan kika daure kika yi komai yadda na ce miki in Allah ya yarda za kiyi mamakin yadda za ki warke cikin ƙanƙanin lokaci."
"Zan kiyaye in sha Allahu Aunty. Na gode ƙwarai."
Amina ta miƙe tsaye tana gyara zaman hijabin hijinta.
"To ni dai na tafi. Sai kuma idan na samu lokaci na sake shigowa."
"To Aunty. Na gode."
Sakina ta faɗa, sannan ta miƙe a hankali don taka ma Amina, har sun kai falo sai ta dakatar da Amina cewa tana zuwa.
Kicin ɗinta ta shiga, ta samu babban leda ta zuba ma Amina kayan gara dangin su dubulan, cincin, alkaki. Sai dai ko da ta kai ma Aminan daƙyar ta magiyar Allah da Annabi sannan ta karɓa.
A cewarta ita ta taimaki Sakina saboda Allah ne. Ita ma Sakinan ta dage ta ba ta saboda Allah ne. A dole dai Amina ta karɓi ledan ba don ranta yana so ba.
Har ta kama hannun ƙofar ta buɗe za ta fita harabar gidan, sai ta waiga ta ce ma Sakina
"Aunty Amarya lallai fa ki ba Ango haƙuri ki rarrashe shi ya ɗaga miki ƙafa har ki warke. Domin gurin nan akwai miki sosai, idan ya ce zai sake bi ta gurin lallai duk aikin da aka miki zai lalace."
A kunyace Sakina tasa tafukan hannayenta biyu ta rufe fuskarta. Da ƙyar ta iya buɗe baki ta ce
"To Aunty. Za mu kiyaye in sha Allahu"
Saura pages uku mu gama free pages, kin biya kuɗin karatunki kuwa?