MUTUNCI MADARA...

BABI NA GOMA SHA UKU

by @fareedaabdallah

MUTUNCI MADARA...

©Fareeda Abdallah

Paid book ne. Kuɗin karanta labarin 1k kacal. Ki tura kuɗinki ta wannan account ɗin 7039080978, Opay, Farida Abdullahi, sai a tura min shaidar biya ta wannan numbern *** domin samun damar kasancewa a group ɗin da zan dinga posting ɗin littafin akan lokaci in sha Allahu.

Ina kuke Ƙasaitattun mata ƴan gayu waɗanda basa ƙyashin cire kuɗi su gyara kicin ɗin su da jikinsu? Me kike buqatar siya a gurinmu Hajjaju? To ki dakata a nan, domin kayanki ya tsinke a bakin kaba💃🏽 Idan ma kuɗin ne kike ƙyashin cirewa a lokaci ɗaya muna adashen gata don sauƙaƙa ma abokan hulɗar mu🥰 Duk abinda kike son siya za mu baki dama ki tara kuɗinsa sannu a hankali bayan kin gama biya ki karɓa bisa gaskiya da amana 🤝 Idan kayan kicin kike so ga link ɗin group kiyi joining.

👇👇👇👇

***

Bayan kayan kicin muna sayar da ƙayatattun Laces, Shadda, Atamfa, Veil's, Shoes, bags. Abin burgewar kuma shi ne muna bada kayanmu akan farashi mai sauƙin gaske👌🏽👌🏽🥰 ku yi joining group ɗinmu ku kwashi garaɓasa Sisters💃🏽💃🏽

👇👇👇👇

***

Sannan kuma muna da Group da muke siyar da Lagos shoes, muna bada sari daga 6pcs akan farashi mai kama da kyauta🥰👌🏽Wannan dama ce ga masu son fara sana'a, da kuma waɗanda suke sana'ar💃🏽💃🏽

👇👇👇👇

***

13)

Tun bayan fitar Amina daga gidan Sakina, sai gidan yayi mata shiru sosai, irin shirun nan wanda yake saka mutum yai ta saƙe-saƙe yana tuna abubuwan da suke damun rayuwarsa.

A hankali Sakina ta zame gadon bayanta, ta jingina sosai akan kujerar da take zaune. Tana wannan saƙe-saƙen tunanin kwatam sai idanunta suka sauka akan ƙofar ɗakin Kamal.

Duk da bata je ta murɗa hannun ƙofar ɗakin ba ta yi tunanin ƙofar a rufe take. Kuma duk da ta yini tana barci tana da tabbacin tun da ya fita da safe bai koma gidan ba. Domin da ace ya koma, da Firdausi ko Mamanta sun faɗa mata.

Haka kawai ba ta san me yasa ba, daga kallon ƙofar ɗakinsa da tuna shi sai zuciyarta ta yi mata wani irin rauni sosai. Duk da mu'amalar tozarcin da yayi mata. Duk da munanan kalaman da ya faɗa mata. Duk da azabar da ya gana mata kamar ya samu dabba. Da rashin adalci irinna zuciya kawai sai ta ji kamar tana kewarsa.

Sai take ayyanawa a ranta ina ma ace zai dawo gidan yanzu, ya nufo ta da fuska mai nuna tsantsar nadama, ya kalle ta a tausashe ya ce mata

'Ki yi haƙuri Sakina.'

Sai dai ita da kanta ta san wannan hasashen nata zai tafi a tunani ne kawai, hakan bazai taɓa faruwa a gaske ba sai dai a cikin mafarki, ko a tunani irin wannan.

Tana wannan tunane-tunanen sai jin kiran sallar magriba ta yi a masallacin nesa da su. Ta miƙe tsaye sannu a hankali, ta shige ɗakinta don sauke farali.

Ko da tayi alwala ta fito, har ta saka Hijab za ta yi sallah a cikin ɗaki kawai sai ta fita falo. Ta yi sallah a nutse, bayan ta idar ta yi azkhar sai ta ɗauko Alƙur'ani ta fara karantawa. A fili take karatun, da murya mai sanyi da tsayawa a zuciyar mai saurare.

Mintuna goma sha biyar tayi tana karatu sannan ta yi addu'a ta shafa. Ta mayar da Alƙur'ani da Hijabinta cikin ɗaki, ta sake komawa falo ta zauna. A yanzu bata bari tunani ya dame ta ba, sai ta kunna T.v, ta saka tashar MBC 2 tana kallon Film ɗin da suke haskawa.

Saboda kallo ya ɗauke mata hankali har bata ji buɗe get da shiga da mota cikin gidan ba, sai buɗe ƙofar falon kawai ta ji. Tana waigawa karaf! idanunta suka faɗa cikin na Kamal.

Suka yi musayar kallo na daƙiƙu ashirin, shi ne ya fara kawar da kansa yana ƙara tamke fuska. Kawai Ita ma sai ta mayar da fuskarta kan T.v tana taɓe baki.

Taɓe bakin da tayi kuwa akan idanun Kamal da ya waiga don ƙara kallon fuskarta. Abin sai ya ɗan ba shi mamaki kaɗan. Abinda ya saka shi mamaki shi ne tun da suka yi aure, duk lokacin da za suyi katarin haɗa idanu da ita, yana ganin kallo mai cike da ƙauna a ƙwayoyin idanunta. Amma a yanzu sai bai ga wannan ƙaunar ba, ko da ya sake waigawa don tabbatar da ba kallon ƙauna take mishi ba kawai sai ya ga ta taɓe baki.

Kamar zai yi magana, sai yayi shiru bai tanka ba. Karo na farko tun bayan da suka yi aure maimakon ya wuce cikin ɗakinsa kamar yadda ya saba, sai ya nemi guri ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun falon.

Shiru ya ratsa tsakaninsu. Ba a jin ƙarar komai a falon sai na T.v da Sakina take kallo. Kamal yana ta saka ran Sakina za ta yi mishi sannu da zuwa, ko kuma oyoyo kamar yadda tayi mishi jiya. Sai ta ƙaryata tunaninsa, kallon arziki ma bai samu ba balle har ta buɗe baki tayi mishi magana. Gaba ɗaya hankalinta yana kan kallon da take yi, kamar ma bata san akwai wata halitta mai numfashi bayan ita a cikin falon ba.

Kawai sai ya miƙe ya nufi hanyar ɗakinsa, yana ta ɗan waigen ko za ta biyo shi. Sai ya ga bata biyo shi ba. Sai da ya kusa isa ƙofar ɗakinsa ta kalle shi sheƙeƙe, babu wata tausasawa ko lanƙwasa a muryarta ta ce

"Ga abincinka can a kan dining."

Tana gama faɗin haka ta miƙe tsam! Ta nufi ɗakinta, Kamal ya bi bayanta da kallo. Har ta ɓace masa da gani bai daina kallon hanyar da ta bi ba. Abin mamaki, sai yadda ta share shi ya ɗan tsaya masa a rai.

Tun da ta shiga ɗakinta bata fito ba ta tsaya waya da ƙawayensu har aka kira sallar Isha'i. Da yake tana da alwala, sai ta kuskure baki ta shimfiɗa dadduma, ta tayar da sallah.

Ko da ta idar da sallah, ita da kanta ta daɗe tana tunanin irin tarbar da tayi ma Kamal. A ɗazu ne ta yanke shawarar sauya akalar zamansu, daga salon da take kai na cusa kai inda babu kwarjini, zuwa sabon fage irin na idan so cuta ne, haƙuri magani ne.

Tana zaune akan sallaya tana ta saƙe-saƙe, ta ƙura ma ƙasa idanu, zuciyarta sai zafi take yi. Ta ja nannauyan ajiyar zuciya ta sauke. Can kuma sai ta ɗaga hannayenta sama, da murya mai bayyana rauni da karaya ta fara addu'a muryarta a sanyaye.

"Ya Allah..."

Nan take idanunta suka ciccika da hawaye.

"Ya Allah idan da alkhairi ko misƙala zarrah tsakanina da Kamal ina roƙonka ka sassauta zuciyarsa, ka ƙara min haƙuri da juriya wajen zama da shi."

Ta yi shiru tana mayar da numfashi, hawayen da suka cika idanunta suka gangaro. A hankali ta cigaba da cewa

"Allah idan babu alkhairi a cikin zamana tare da shi kada ka bar ni in wahala, duk yadda nake son zaman ka saka min haƙurin rabuwa da shi."

A wannan gaɓar sai muryarta ta ƙarasa karyewa gaba ɗaya, tana kuka sosai ta cigaba da addu'ar cikin rawar murya.

"Ya Allah ka cire min wannan matsanancin son da nake masa. Ka bani ƙarfin zuciyar jure zama da shi ko babu soyayya idan da alkhairi a tsakaninmu. Ka bani ƙarfin zuciyar jure zafi da raɗaɗin rabuwa da shi idan babu alkhairi a tsakaninmu."

Ta shafa addu'ar hannayenta na ta rawa. Sai ta durƙusar da kanta tana ta kuka gwanin ban tausayi. Allah ya sani duk yadda ta daɗe tana hasashen rayuwar aurenta ita da Kamal ba haka ya zo mata ba.

Abin mamaki, a karon farko wai yau ita ce ba addu'arta Kamal ya ƙara son ta ba. Ba addu'arta ya dawo da son da yake mata a baya ba. A yau, addu'ar da ta fi yi shi ne Allah ya sauƙaƙa mata irin matsanancin son da take ma masa.

Ta ɗauki tsawon lokaci tana kuka, daga bisani ita da kanta ta rarrashi kanta ta share hawayenta. Ta miƙe ta naɗe daddumar, ko hijabin bata cire ba ta haye gado ta kwanta. Daga wannan kwanciyar sai barci ya ɗauketa.

******

"Malam na samo shi."

Ta faɗa da karaɗin murna a muryarta.

Dattijon da ta kira da Malam ya fashe da ƙaƙƙarfan dariya. Sai da ya ɗauki tsawon lokaci yana ɓaɓɓaka dariyan sannan ya tsagaita ya ce

"Ai dama na faɗa miki, yau Litini, rana ce mai tsananin sa'a a ɓangaren taurarinki. Shi yasa na ce ki fita a yau, tabbas za ki same shi. To amma ya kika gan shi?"

"Wallahi Malam ya haɗu, ya haɗu iya haɗuwa. Kyakkyawan matashi ne mai ƙirar ƙarfi, ta ko ina ya kai irin mijin da nake so ɗari bisa ɗari."

Ta ƙarasa maganar tana lumshe idanu cike da shauƙi.

"Amma fa wani hanzari ba gudu ba Malam! Akwai wata matsala guda ɗaya..."

Hankali da nutsuwarshi ya ƙara tattarawa gaba ɗaya zuwa gare ta sannan ya tambayeta

"Toh fa! Wace matsala ce Mairo?"

Ta yi ɗan shiru tana tunani, sai kuma ta ce

"A maganganun da na ji daga bakin abokansa sun ce Ango ne, kwanaki biyu kenan da aurensa. Kana ganin nawa al'amarin zai yiwu?"

Da yanayin yarda da kai ya amsa mata da

"Ƙwarai kuwa! Me zai hana naki al'amarin ya yiwu? Kin taɓa ganin inda bikin magaji ya hana na magajiya?"

"A'a Malam"

Ta amsa tana dariya.

"To kin gani? Yanzu dai ki kwantar da hankalinki kamar tsumma a randa. Ki je gida, ki manta da shi da al'amarinshi. Ki cigaba da harkokinki kawai, shi da kanshi zai dawo da ƙafafunshi ranar wata laraba mai zuwa. Amma fa ni da kaina bazan ce miki ga takamaimai ranar larabar ba, abin da na sani kawai ranar da zai dawo ta kasance Laraba ce.

Don haka kafin ranar Larabar da zai zo gare ki, duk ranar talata ki dinga zuwa kina karɓan lallen da za ki dinga ƙunsawa a tafukan hannu da ƙafafunki, kar ki taɓa bari lallen ya koɗe ba tare da kin maida wani lallen ba har zuwa larabar da Allah zai dawo da shi gare ki. Daga wannan ranar larabar da kuka haɗu... An gama kawai. Sai mu jira ranar shafa fatiha."

A tare ita da Malam suka kwashe da dariya. Zuciyarta cike da matsanancin farin cikin samun cikan burinta a nan kusa, ba tare da an ɗauki dogon lokaci ba kamar yadda ta yi tsammani da farko.

******

Duk wanda ya ce cire So a zuciya kamar cire riga ne tabbas ya yi ƙarya. Amma fa da gaskiya a cikin salon maganar nan ta Mal Bahaushe da ya ce

"Idan so cuta ne, to tabbas haƙuri magani ne."

A rayuwar duniya duk yadda mutane za su kai ga matsawa domin son canja halaye da ɗabi'un wani ɗan Adam, to fa lallai bazai taɓa canjawa ba in dai ba shi ne a karan kanshi ya so ya canja ba.

Da gaske Sakina ta so canjawa akan salon zamantakewarta da Kamal, sai ga shi cikin hukuncin Allah da taimakonsa da saka ma ranta da tayi, sannu a hankali ta fara canjawa.

A baya idan ta zauna akan dadduma za ta yi addu'a, kusan fiye da rabin addu'o'inta a kan Kamal ne. Ba ta gajiya da yin addu'ar Allah ya ƙara masa sonta. Da suka fara samun matsala sai mafiyawan addu'o'inta ke tafiya kan Allah ya huci zuciyarsa ya yafe mata ya dawo da matsanancin son da yake mata a baya. Da suka yi aure sai take addu'ar Allah ya ƙara haɗa zukatansu. Allah ya ƙara masa arziki da yalwa.

Amma a yanzu da ta ɗaura aniyar canjawa. Idan ta ɗaga hannu za tayi addu'a ba sunansa take fara kira a farko ba. Iyayenta take aika ma da kyawawan addu'o'i, da mahaifiyarsa, wacce ba don ita da jajurcewar da ta yi wajen tsayawa har aka yi wannan auren ba da bata san irin ɗaiɗaicewar da za ta yi ba.

Bayan nan kuma sai ta sako na ta rayuwar. Ta roƙi Allah ya cigaba da tsare mutuncinta. Ya ƙara mata natsuwa da kwanciyar hankali. Ubangiji ya ƙara mata kusanci da shi, da miƙa al'amarinta gaba ɗaya zuwa gare shi. A ƙarshe kuma sai ta roƙi ya cire mata matsanancin son Kamal ya zaɓa mata mafi alkhairi a rayuwar aurenta.

Yau kwanaki huɗu kenan da faruwan al'amarin da ya zama sanadiyyar buɗewar idanunta. Jikinta yana ta sauƙi ƙwarai da gaske, da yake tun asali ita ba ta da ƙan jiki, ita da kanta ta san ta ji sauƙi. Kuma da yake tun wancan ranar Kamal bai ƙara yunƙurin neman ya kusanceta ba, sai sauƙin nata ya zo a gaggauce.

A tsakaninta da Kamal, ta kame kanta tsaf, duk da dai wasu lokutan zuciyarta na fin ƙarfinta wajen yi mishi azarɓaɓi, amma fa kaso sittin cikin ɗari yanzu ta daina mishi shisshigi, ta nutsu sosai, ta kawo idanu ta zuba ma sarautar Allah tana jiran saukar hukuncinsa.

Duk wasu nauye-nauye da suke kanta matsayinta na matar gida tana saukewa, kamar misalin haɗa mishi abinci, gyara gida, da makwancinsa idan ya fita, yi mishi sannu da zuwa a taƙaice idan ya dawo tana falo, da sauran ƙananun abinda baza a rasa ba.

Amma fa bayan wannan babu komai a tsakaninsu, idan ma ba ta fito falo bane sai ta kwana ta yini bata ganshi ba.

A ɓangaren Kamal tun yana mamaki da al'ajabin sauyin Sakina har ya daina. Duk da a wasu lokutan yana jin kamar babu daɗi a yanayin da ta tsira, amma kuma girman kai da jiji da kai ya hana shi ya tambayeta dalilin canjin nata.

Sai kawai ya saka ma zuciyarsa ai hakan ma ya yi daidai, dama tuntuni layin da yake so ta ɗauka kenan amma ta ƙi. Tunda yanzu ta ɗauka, normal ne. Soyayyarta ne dai ba ya yi, ya daina, na baya ma idan ya tuna har mamakin kansa yake yi. Kawai shi ma sai ya cigaba da zama da ita zuwa taƙaitaccen lokacin da ya tsara zai roƙi Mama ta bashi dama ya sauwaƙe mata.

Ranar asabar da ya kama sati ɗaya da bikin Sakina da Kamal. Tun da wuri take ta fama da baƙi, ƙawaye da dangi daga ɓangarenta da na Kamal, haka tayi ta ɗorawa da saukewa tana tarban baƙi har zuwa ƙarfe biyar na yamma.

Lokacin ne ta samu kanta, da yake kafin Karima da sauran ƙawayensu su tafi sun gyara mata gidan tas sun yi wanke-wanke. Bayan tafiyarsu sai ta yi wanka, ta tsala kwalliya na gaske ta zauna a falo, sai ta yi kamar Amaryar da ta ɗau wanka tana jiran dawowar Angonta.