BABI NA GOMA SHA HUƊU
MUTUNCI MADARA...
©Fareeda Abdallah
Paid book ne. Kuɗin karanta labarin 1k kacal. Ki tura kuɗinki ta wannan account ɗin 7039080978, Opay, Farida Abdullahi, sai a tura min shaidar biya ta wannan numbern *** domin samun damar kasancewa a group ɗin da zan dinga posting ɗin littafin akan lokaci in sha Allahu.
Ina kuke Ƙasaitattun mata ƴan gayu waɗanda basa ƙyashin cire kuɗi su gyara kicin ɗin su da jikinsu? Me kike buqatar siya a gurinmu Hajjaju? To ki dakata a nan, domin kayanki ya tsinke a bakin kaba💃🏽 Idan ma kuɗin ne kike ƙyashin cirewa a lokaci ɗaya muna adashen gata don sauƙaƙa ma abokan hulɗar mu🥰 Duk abinda kike son siya za mu baki dama ki tara kuɗinsa sannu a hankali bayan kin gama biya ki karɓa bisa gaskiya da amana 🤝 Idan kayan kicin kike so ga link ɗin group kiyi joining.
👇👇👇👇
***
Bayan kayan kicin muna sayar da ƙayatattun Laces, Shadda, Atamfa, Veil's, Shoes, bags. Abin burgewar kuma shi ne muna bada kayanmu akan farashi mai sauƙin gaske👌🏽👌🏽🥰 ku yi joining group ɗinmu ku kwashi garaɓasa Sisters💃🏽💃🏽
👇👇👇👇
***
Sannan kuma muna da Group da muke siyar da Lagos shoes, muna bada sari daga 6pcs akan farashi mai kama da kyauta🥰👌🏽Wannan dama ce ga masu son fara sana'a, da kuma waɗanda suke sana'ar💃🏽💃🏽
👇👇👇👇
***
14)
Sakina ba ta yi mintuna goma a zaune ba sai ga Firdausi da mahaifiyarta Amina. Da fara'a sosai a fuskar Sakina take yi musu maraba, ta janyo Firdausi zuwa jikinta ta rungume tana yi mata ƙorafin bata sake shiga gurinta ba.
Firdausi ta yi dariya da kyakkyawar fuskarta. Sai kuma ta fara yi ma Sakina bayanin sun koma makaranta ne, dama ko ranar monday da suka shiga gidan hutun Mid-term-break ake yi.
Da gamsuwa a fuskar Sakina ta ce
"Ma sha Allah Babyna. Ki maida hankali kiyi karatu sosai kin ji?"
"Tom Aunty Amarya."
Fiddausi ta amsa. Har ta yi shiru sai kuma ta sake cewa
"Aunty Amarya kin yi kyau sosai"
Sakina da Amina suka yi dariya.
"Na gode. Ke ma kin yi kyau Babyna."
Sakina ta amsa tana ɗan kama kumatun Firdausi a hankali.
Sai a lokacin Sakina suka gaisa da Amina. Sai kuma Sakina ta ɗan ɓata fuska tana cewa
"Aunty Amina ke ma sai yau?"
Amina tana murmushi ta ce
"Yi haƙuri Amarya, kin san ba abu bane mai kyau a cika zirga-zirga gidan Amare. Yanzu ma dawowarmu kenan har za mu shige gida na ce bari mu leƙo ko a gudu-gudu mu duba ki."
"To ai kuwa na gode Aunty. Amma ni dai don Allah ki dinga leƙowa, ko ke baki zo ba ki dinga turo min mutumiyata in dai tana free ta taya ni hira. Barin kawo muku ruwa."
"To in sha Allah in dai tana gida za ta dinga zuwa."
Amina ta amsa tana dariya.
Sakina ta shige kicin, can sai ga ta da gorunan lemu masu sanyi da ruwan gora. Ta ajiye a gabansu, ta sake komawa cikin kicin ɗin, sai ga ta da Cake a cikin farin leda mai kyau ta zubo, Karima ce ta je mata da cake ɗin.
Ta damƙa ledar a hannun Firdausi tana cewa
"Tunda na ji kin ce gudu-gudu kika shigo na san ba zama za kiyi ba Aunty. Wannan idan kun je gida sai ku ci. Sannan kafin ki tafi sai mu yi musayar number Aunty, idan na fara fita gidanki ne farkon inda zan ziyarta a unguwar nan in sha Allahu."
"Allah yasa."
Amina ta amsa.
Suka yi dariya gaba ɗaya.
Duk yadda Amina ta ce baza ta daɗe ba a gidan Sakina, a ƙallah sai da suka yi kusan mintuna ashirin da biyar. Saboda yadda Sakina ta sake jiki da ita, haka tai ta jan ta da hira kamar da ma can da sanayya a tsakaninsu.
Suka shiga cikin ɗaki Amina ta duba ɗinkin jikin Sakina, ta ga ya warke saura ƙiris, ta ƙara ba Sakinan shawarwarin yadda za ta kula da kanta ko da gaba. Sannan da ƙyar Amina ta yakice Firdausi suka fito a gidan Sakina, suka rabu da farin ciki kaman kar su rabu.
Har bakin Get Sakina ta raka su da mayafi a jikinta, tana tsaye tana ɗaga ma Firdausi hannu, ita ma Firdausi tana ɗaga mata har suka shige gida, sannan ita ma ta koma cikin gidanta. Zuciyarta cike da ganin girman Amina, da ƙaunar ƴarta Firdausi.
A falo ta zauna kan kujera tayi shiru, ganin tunani na neman rufe ta sai ta ɗauki wayarta da ke ajiye a gefenta ta kira Mummy. Kiran na gaf da tsinkewa Mummy ta ɗaga, ta gaisheta da girmamawa.
Bayan sun gaisa Mummy ta ce
"Sakina, Ni da Daddynku mun yi tunanin yau da aurenku ya cika sati ɗaya Kamal da abokansa za su zo gaisuwar iyaye da godiya kamar yadda ake yi a al'adance?"
Ƙirjin Sakina ya buga daram! Lokaci ɗaya ta ruɗe har sai da Mummy ta so ta fahimta.
"Lafiyarki kuwa? Ko akwai wata matsala ce?"
Mummy ta tambaye ta.
"A'a"
Ta amsa da sauri.
"Babu matsalar komai Mummy."
Ta sake faɗa tana ƙoƙarin daidaita rawar da muryarta ke yi.
"Dama... Dama.. Dama yau ɗin ba ya nan ne."
Ta ƙirƙiro ƙarya da ƙyar ta faɗa. Sai kuma tayi saurin ƙarin bayani don daidaita ƙaryar da ta yi
"Tun sassafe ya yi tafiya zuwa Kano. Amma idan ya dawo gobe in sha Allah yana nan zuwa Mummy. Dama mun yi maganar da shi... Za su zo! Ku yi haƙuri."
"To ba damuwa! Allah ya dawo da su lafiya."
Mummy ta yi addu'ar a fili, amma a zuciyarta tana jin ba gaskiya Sakina ta faɗa ba. To amma kuma a ganinta ba ta da hujjar tsananta bincike, za ta jira ta gani zuwa goben.
A sanyaye Sakina tayi ma Mummy sallama ta katse wayar.
Hankalinta a tashe ta buga tagumi tana tunanin hanyar da za ta bi wajen yi ma Kamal maganar zuwa gaida iyayenta ba tare da ya wulaƙanta ta ba. Duk iya tunaninta ta rasa hanyar da ya kamata ta bi mai sauƙi-sauƙi, don haka kawai sai ta lalubo number Mama ta danna mata kira.
Wayar tana fara ringing Mama ta ɗaga, da murya mai bayyana ƙauna da soyayya take amsa gaisuwar Sakina, ta ƙara da tambayarta babu wata matsala ko?
"Babu matsalar komai Mama."
Sakina ta faɗa a kunyace.
"To Alhamdulillah! Allah ya ƙara zaunar mana da ku lafiya. Ko ba yanzu ba idan akwai wata damuwa kafin ki tunkari kowa da ita ki fara faɗa min kin ji ko Sakina?"
"To Mama! In sha Allah! Na gode ƙwarai. Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana mai albarka."
"Amin thumma Amin."
Har Sakina ta yi shiru, sai kuma ta ce
"Ummm... dama Mama zan ce ne ki tuna mishi zuwa yi ma iyayen Amarya godiya da ake yi a al'ada bayan sati ɗaya da biki."
"To ba damuwa Sakina. Ai kuwa zan tuna mishi. Kin ga kuwa nima na manta, da tun safe da ya shigo na yi misho magana ai da sun je da yamman nan. Amma in sha Allahu gobe za su je."
"Allah ya kaimu da rai da lafiya. Na gode Mama! Na gode."
Suka rabu a wayar Sakina na ta farin ciki a fili. Yanayin da ya jefa matsanancin tausayinta a zuciyar Mama. Domin ko Sakina bata fito fili ta faɗa mata ba ita ta sani zaman haƙuri take yi da Kamal. Da wannan dalilin yasa kullum idan Kamal ya je gaishe su tana yawan yi mishi nasiha akan ya ji tsoron Allah, ya riƙe matarsa da Amana. Nauyinta da Allah ya ɗora masa lallai ya tabbatar yana ƙoƙarin saukewa.
A ɓangaren Sakina kuwa ba tare da damuwar komai ba ta buɗe Data don rage zaman kaɗaici, nan take saƙonni suka fara shigowa, mafi yawansu daga groups ɗin da take ciki ne, sai ɗaiɗaiku daga ƙawayenta, cikinsu har da Karima, saƙon ta fara buɗewa don ganin ko me ta ce, tunda basu daɗe da rabuwa ba
"Amarsu ta Ango, kin sha wannan maganin da na kawo miki kuwa?"
Ta yi murmushi kamar Karima na kallonta. A taƙaice ta mayar mata da amsar
"Na sha"
Har ta tura saƙon sai kuma ta sake cewa
"Ya kuka koma gida? Na gode, Allah ya bar zumunci."
Bayan ta tura ma Karima saƙon, ta bi ƙawaye da ƴan'uwansu da take da lambarsu ta tura musu saƙon ban gajiya da godiya, sannan ta rufe datan ta ajiye wayar.
Ta lumshe idanunta na wasu daƙiƙu. Sai kawai wani tunani ya faɗo mata a rai, wannan tunanin shi ne
'Tun da aka kawo ta gidan Kamal ba ta taɓa ganin ya dawo gida da wuri ba.'
Haka kawai sai ta ji kuma ranta ya sosu da rashin dawowar tashi. Can kuma sai ta yi ma kanta murmushin takaici.
A hankali ta yi magana a fili
"Ke ma dai wani lokacin kina da abin haushi Sakina. Yau kuma Kamal ɗin da kika fara koyon yadda za ki yakice shi a ranki shi ne kike damuwa da rashin dawowarsa kan lokaci?"
Sai ta ji wani abu ya soke ta a ƙirji. Ta sauke numfashi a hankali. Ta miƙe ta nufi ɗakinta. Tayi alwala tayi sallar magriba sannan ta sake gyara kwalliyarta.
Tana gyara kwalliyar take ce ma kanta
"Ba don kowa nake yin wannan kwalliyar ba, ina yi don kaina ne. Don in faranta ma raina ba don wani ya yaba ba."
Bayan ta gama kwalliyar ta sake fesa turare, sannan ta sake fita zuwa falo. Ta ɗauki remote ta kunna T.v, ko minti goma ba ta yi ba ta kashe, saboda ba ta jin daɗin kallon. Duk tashoshin da take so basa haska film mai kyau.
Sai ta ɗauko Alƙur'ani ta fara karantawa. Muryarta na fita a hankali. Karatun shi ya ɗauke mata hankali har aka kira sallar isha'i.
Sai a lokacin ne ta ɗan kalli agogo. Ƙarfe bakwai da mintuna hamsin da biyar. Ɗakinta ta shige tayi sallar isha'i tunda tana da alwala, maimakon ta koma Falo bayan ta idar, sai tayi zamanta a ɗaki.
****
A dai-dai lokacin shi kuma Kamal ya gama gararambarsa a gari ya koma gidan. E to gararamba mana, tunda shi kanshi ba shi da gurin zuwa, kuma yana ganin kiran Ma'aruf da Mubarak ya ƙi ɗagawa, don ya san abinda za su ce masa.
Maganar zuwa gaisuwa da godiya ga surukai ne da suka mishi jiya, ya ce sai yau. Yau ɗin ma kuma shi dai bazai ja ba, domin bai ga wani abu na musamman da aka mallaka mishi tare da Sakina ba da har zai je yi ma iyayenta godiya. A ƙarshe ma da su Ma'aruf suka ishe shi da kira, kawai sai ya kashe wayarsa.
Ya je ya kama ɗakin hotal mai kyau ya sha barcinshi, yini guda sur! Bai fito ba sai da aka idar da sallar magrib! Shi ne ya koma gidan yana ciccijewa.
Yana shiga falon kai tsaye idanunsa basu sauka a ko ina ba sai kan kujerar da ya saba ganin Sakina a zaune.
Yau sai ya ga bata a kan kujerar. A fakaice ya sake kallon lungu da saƙo na falon.
Ko ina a gyare Tsaf-tsaf, amma ba Sakina. Ba zato babu tsammani sai wani irin yanayi ya ratsa zuciyarsa, yanayin da ya kasa bashi fassara na kai tsaye.
A karo na farko tun bayan aurensu, sai ya ji kamar idanunsa suna kewar ganin Sakina...
Ranar litini in sha Allah za mu ƙarƙare Free pages. Gobe da jibi ina da biki. Kar in yi alƙawarin sabon page in kasa cika alƙawari. Ina godiya ga masu karatun labarin SAKINA a duk inda kuke a faɗin duniya. Ina maraba da sharhi, ƙorafi, shawarwari ta wannan number ***