Episode 3
SAUYIN KADDARA
.................................................................
Writing by hauwau armayau 🥰
(Jidder 💘 💘)
Episode 3
Kallonsa Bilal ya komayi yace Farooq Amman ya kamata mu fara bincike tunkan abunda muke ma kallon Karamin Abu zai iya zama zama babba,
girgiza Kai Farooq yayi yace Bilal ta ina zan fara da wani Ido zan kalleta ta ina zan fara wa da wa zan tuhuma da wa zan fara shiru ya danyi kafin ya tashi ya bar office din,
kallon tausayi Bilal ya bishi da shi sannan ya girgiza Kai,
Sosai TAHAREEQ ya Maida hankali akan aikinsa domin kwata kwata baya son mamy tana fushi da shi koma yasan in ba aikin nan yasa a gaba ya cigaba da kula da shiba hankalinta bazai taba kwanciya ba
Saidai yakai karshen maganarsa kafin daddy ya dago yana kallon Farooq Wanda ya gama masa bayani,
to wai Farooq in tambayeka ni na haifeka ko Kai ka haifani,
Kaine cewan Farooq to da yau umarni nake baka ba shawari ba ka cire hannunka a cikin magana tun ban saba maka ba mutumin banza mutumin a wofi sai an taroka tanan ka Kara bu tsarewa ya karasa maganar cikin fada,
mamy ne ta shigo dakin hannunta rike da kofin shayi kallon Farooq tayi tace ga shi ka sha,
girgiza wa mamy Kai yace na gode mamy Amman na koshi sake kallonshi tayi sannan ta karasa kusa da shi tareda rike hannunshi ta daura masa shayin Bai Kuma mata garddamaba ya dauka ya fara sha cigaba da kallonshi mamy tayi Yana Shan shayin cikin nutsuwa duk da Yana cikin damuwa saidai ya shaye shayin tass ya ajiye kofin tareda daura kansa a cinyan Mami ita kowa sai shafa masa sumar kansa takeyi,
duk abunda sukeyi daddy na kallonsu Bai kulasuba karshe ma tashi yayi ya basu guri,
Yau ma kamar kullum ta shirya cikin uniform din makaranta ta,
fitowa tayi daga dakinsu hannunta rike da safa da takalmin makarantanta,
shanza Dake zaune bakin kofan dakin tace har kin shiryane,
eh anty shanza bazaki Karaya bane eh na koshi yanzuma na kusan late,ina ga na tsaya karyawa Alisha Dake ta bayanta tace ungo yar autamu,
juyawa tayi ta kalle abunda take Bata naira Dari biyarne girgiza Kai tayi tace aa anty Alisha bazan karba na gode,
kara Miko mata tayi sannan tace ki karba kije ki sai wani Abu ki karya Dan bayadda za'a yi ki fita Baki karyaba,
Allah bazan karba Ina ganifa jiya yadda ki kayi alawanki madara baba ya karba yaba wai an Yan iskan Yaran nan Bai Baki kudiba ta ta karasa maganar cikin sigan tausayi,
kar ki damu Alisha ungo wannan auta ta mika mata Dari biyu tace karba kiyi Maza ki tafi kar ki tsaya wasa cewan shanza, tsayawa kallonsu tayi daya daya tukunna tasa hannu ta karba Dari biyu da shanza ke Bata tareda sumbatan hannunta juyawa tayi ta rungume Alisha kafin ta saketa cikin soyyaya anty Alisha saina dawo anty shanza saina dawo zan muku tsaraba,
dukkansu murmushi sukayi sannan suka ce sai kin dawo auta Kara daga musu hannu tayi tareda ficewa,
ajiyan zuciya sukayi a tare kafin ko wacce ta fara aikin gabanta a gidan su biyune kawai masuyi aikin gida duk yawan yammata gid