Girl from the desert 🏜️
by @zahrabmrs02
Zafin ranar hamada mai haɗe da ƙurar da iskar gabas ke kaɗowa ta bugi kyakkyawar fuskar Tadala. Tana tsaye a tsakar gidan laka na mahaifinta dake birnin Agadez na ƙasar Nijar, sanye da tsohon material shuɗi wanda ya yi mata daidai da jikinta.
Duk da talaucin gidan nasu, Tadala tana da irin kyawun da ke sa mutane su juya su sake kallonta. Doguwa ce mai siririn kugu da cikar surar da ta dace da juna. Fatar jikinta fara ce mai ɗaukar hasken rana, yayin da idanunta manya masu zurfi wanda suke da asalin kwalli ko ba a shafa musu ba..”
Ta kai kusan shekaru huɗu kenan da gama sakandare (Lycée). A cikin shekarun nan, da ƙyar ta ci gaba da karatu har ta sami Diploma a fannin Accounting a jami’ar Nijar. Amma daga nan komai ya tsaya cak saboda rashin kuɗin ci gaba.
Ta daɗe tana tura wa cousin ɗinta, Sadiya, takardun Diploma ɗinta ta hanyar amfani da wayar Mansoor, tana fatan samun gurbin Direct Entry a Najeriya. Sai dai shiru kake ji. A hankali ta cire rai, ta rungumi ƙaddarar rayuwa.
Rayuwar a gidansu cike take da matsi da gwagwarmaya.
Mahaifinta, Malam Attaher, tsohon Buzu ne wanda kullum yake fita kasuwar dabba neman abin da za su ci, amma sam al’amura ba sa tafiya yadda yake so.
Mahaifiyarta, Hajjo, ita ma tana taya shi da ɗan tallan mai da nono domin su ciyar da yaran.
Su huɗu ne a wajen iyayensu.
Babban yayansu namiji, Moussa, mai shekaru talatin, wanda yake raka motocin dakon kaya da shanun ’yan kasuwa ta cikin hamada zuwa kan iyakar Najeriya domin ya samo musu abincin yau da kullum.
Sai Fiza, wacce ta riga ta yi aure a cikin Agadez. sai ita Tadala sai kuma auta, Aghali.
Wani lokacin idan Moussa ya dawo daga tafiya jikinsa cike da ƙurar hamada, amma hannunsa babu komai, sai Tadala ta shige ɗaki ta yi kuka a ɓoye.
Burinta guda ɗaya ne a rayuwa:Ta yi karatu.Ta sami aiki.Ta fitar da iyayenta daga wannan rayuwar.
A cikin shekarun nan huɗu, babu wanda Tadala ke kira idan ba cousin ɗinta ba, Sadiya.Mahaifiyar Sadiya, Hajiya Adiza, yayar Hajjo ce uwa ɗaya uba ɗaya.Sadiya ta tashi ne a Najeriya saboda mahaifinta ɗan Najeriya ne, kuma ta yi katari ta auri shahararren billionaire, Alhaji Kamal Usman Kibiya.Lokacin suna yara, Sadiya tana yawan zuwa hutu Nijar wajen su Hajjo. Ko bayan ta yi aure ma ta taɓa zuwa sau biyu saboda gyaran jiki da Hajjo ta yi mata.Amma daga nan…Ta yi ɗif.Ta manta da su.
Kullum Tadala tana maƙale da tsohuwar wayarta tana kiranta.“Anty Sadiya, don Allah kiyi mini magana da Alhaji Kamal ya taimaka mini na zo jami’a a Najeriya. Rayuwar nan tamu tana cikin matsi.”
Sadiya mace ce mai ji da kai da taƙama.Kullum sai ta yi mata alkawarin bogi.Har Tadala ta cire rai gaba ɗaya.ranar wata Alhamis da yamma, Tadala na zaune a kan tabarma a tsakar gida tana tsefe dogon gashinta dake zube a bayanta, sai wayarta ta soma ruri.
Ta dubi screen.
Anty Sadiya Abuja.Ta saba ganin sunan.
Amma ba ta saba jin labari mai daɗi daga gare ta ba Cikin sanyin jiki ta ɗaga.
“Hello Anty…”
“Tadala! Kina jina?”
Ta zauna da kyau.
“Eh Anty.”
“Maza ki shirya kayanki na sawa baki ɗaya. na samar miki admission a Base University dake Abuja. Za ki fara Direct Entry a 300-Level, Accounting.”Tadala ta daskare.Sadiya ta ci gaba.
“Next week jirgi zai tashi da ke daga Niamey zuwa Najeriya. Na tura wa Moussa kuɗin mota ya kawo ki babban birni.”Comb ɗin hannun Tadala ya faɗi ƙasa.Ta kasa magana.idanunta suka cika da hawaye.Shekaru biyu kenan tana tura mata takardu.Shekaru biyu tana roƙo.
Sai yau Allah ya taɓa zuciyar Sadiya.
“Anty… da gaske?”
“Eh mana! Yanzu dai ki fara shiri.”
Tadala ta fashe da kuka.Amma wannan karon…Kukan farin ciki ne.“umaaaaa!”
Ta mike da gudu.
“Moussa! papa!”
Mahaifiyarta ta fito a gigice.
“Lafiya?”
“Zan tafi Najeriya!”
Alhamduillah !”
Cikin daƙiƙu kaɗan, gidan ya kaure da murna.Har Malam Attaher da ba ya yawan nuna farin ciki sai da ya share hawayen idanunsa.A daren nan, babu wanda ya yi barci da wuri a gidan.
Tadala kuwa…Ta kwanta a kan katifarta da murmushi a fuskarta.
Ta dinga kallon saman ɗakin laka.Ta yi mafarkin jami’a.Ta yi mafarkin aiki.
Ta yi mafarkin ranar da za ta dawo ta ce:
“papa umaa … wahala ta ƙare.”
ABUJA GIDADON KATSINA MANSION
A cikin unguwar Maitama ta Abuja, wani katafaren gida ne mai kama da fadar sarauta.
Gidadon Katsina.
Gidan hamshaƙin attajiri, Alhaji Kamal Usman Kibiya.Mutum ne da idan sunansa ya fito a kafafen yaɗa labarai, hatta gwamnoni kan ɗaga waya su gaishe shi.
Duk da maƙudan kuɗinsa, yana da wata irin nutsuwa da kwarjini da ke sa mutane su girmama shi kafin ma ya yi magana.
Alhaji Kamal kyakkyawan Bafulatani ne mai shekaru hamsin da biyu .Baƙi ne, dogo .fuskar sa cike take da kamala.Gemunsa mai gaurayen furfura da baƙin gashi ya ƙara masa annuri.Kasuwancinsa ya shafi harkar Oil & Gas da kuma gine-ginen zamani.
Matansa na aure uku
Dr. Mariya. gynecologist ce yaranta hudu (ameenatu24 ,khalifa 22 amal 19,yusra16 )
Hajiya Falmata. tana aiki a NNPC yaranta biyu (maimuna(kuna23) Zahra20
Sai amaryarsa, Sadiya. interior decorator ce yaranta uku (safa da marwa 19 sai Ahmad17 )
Sadiya tana zaune a bedroom din alhaji kamal , yayin da yake duba wasu takardu.
Ta ajiye wayarta ta saki tsaki.“Kai… Tadala akwai naci. Shekara biyu tana bina da maganar zuwa Najeriya.”Alhaji Kamal ya ɗago. gira a ɗage.
Shekara biyu?
Eh.
Haba Maman Twins… shine baki taɓa faɗa mini ba?”Sadiya ta ɗan turo baki.Ban so na takura maka da matsalolin dangina ne .Alhaji Kamal ya girgiza kai.Amfanin arziki shi ne ka taimaki ’yan uwanka. Nina ce miki nauyin da ke kaina ya yi yawa?Ya ajiye takardunsa.
Allah ya kyauta,Amma tunda kin riga kin nema mata admission ɗin, hakan ya yi kyau.”
da daddare gabadaya iyalin gidan suna zaune a babban dining table ,bayan an gama cin abinci, aka koma falo a nan ne Sadiya ta gyara murya.
Dr. Mariya, Maman Kuna… daga mako mai zuwa za mu sami baƙuwa a gidan nan, kowa ya dago ya kalleta.
Yar uwata ce daga Nijar. Sunanta Tadala. Ta samu admission a Base University kuma a nan gidan za ta zauna. Masha Allah, Umma ta ce,Allah ya kawo ta lafiya,Falmata ta ɗan kurɓi shayi.ta yi murmushin manya.Allah ya kaimu. Ai gidan na kowa ne.
Sai dai a cikin zuciyoyinsu…Kowacce na da nata tunani.
Ameenatu ta bi dr mariya ɗaki umma, wai me Maman Twins take nufi da kawo mana wata daga Nijar?Umma ta yi murmushin takaici,gasa mana kin san daddynku ya biyawa sisters dina tution fee zuwa Qatar shine ita ma zata sa alhaji ya dauki nauyin cousin dinta
wai umma maman twins bazata dena gasa da ke ba ?duk abinda kikayi sai tayi ?naga ma su anty shahida baa gidan nan zasu zauna ba ,kyaleta ameenatu a jura zuwa rafii nema waje ki zauna gaki da tsohon ciki tsayawar da kika yi is not good for the baby ,A daya ɓangaren kuma…Kuna ta dubi mahaifiyarta,Momy, wai da gaske Mami za ta kawo wata ta zauna a gidan nan? Falmata ta ɗan yi dariya.yeah haka tace momy ta amsa cikin ko in kula
Zara ta ce Kuma Dad fa ba ya son cinkoso ,baki sai da suzo suyi weeks su tafi baya son hada mu da bare Falmata ta yi murmushi,Ku ƙyale ta. Idan dai Sadiya ce… ba za su rabu lafiya da wannan cousin ɗin nata ba.”mu bar maganar sadiya haka kun san ban son ana maganar mutane a ɗakin Sadiya kuwa Safa ta marairace fuska. Mami, me zai sa ta zo nan gidan?Ta zauna hostel mana.Sadiya ta juya da sauri.Ta watsa musu kallo Ba za ku gane ba.”Ta yi murmushi mai cike da isa.I am trying to prove a point. Ta ɗaga kanta sama.
da zarar Tadala ta shigo gidan nan da zama, kowa zai gane cewa ni daban nake a wajen Hubbi. Za su fahimci cewa akwai abubuwan da nake nema daga gare shi kuma ba ya taɓa cewa a’a.”biki ga so called favorite dinsa ba falmata jikin ta dik yayi sanyi?(a duniyar social media hajiya falmata ce favorite din gidadon katsina sabida yadda ake yawan ganinsu tare a ko wani event sometimes har da matching color oufits, basu san cewa falmata har media team gareta wanda take biya a boye,a duk sanda zasu taro da alhaji kamal takan fada masu suje wajan ma kafin ta iso har lakabi aka mata da zinariyar gidadon katsina
Agadez…
Tadala ta lumshe idanunta cikin farin ciki.
Ba ta san cewa a cikin Gidadon Katsina akwai mutanen da suka riga suka fara jin haushinta ba…