Crossed borders
by @zahrabmrs02
Ƙamshin daddadan turaren wuta na Khumra da dilke na asali ya gauraye cikin ƙaramin shagon gyaran jiki na Hajiya Sidiya dake tsakiyar birnin Agadez. Tadala na zaune a kan ƙaramar kujera, sanye da tsohuwar rigar gidanta da ta ɗan tsage a gwiwar hannu, tana taya wata kwastoma shafa man gashi.
Shekaru huɗu kenan da gama sakandare. Ban da zama a gida, wannan shagon ne wurin da Tadala ke rage zafin lissafin rayuwa da radadin kasa ci gaba da karatu. Tana taya Hajiya Sidiya aiki domin ta sami ɗan abin da za ta taimaki iyayenta, duk da kuɗin ba masu yawa ba ne.
A nan ne ta koya sirrin gyaran fata, haɗa mayuka, da kuma zafafan turaren da matan Buzu ke amfani da su domin kula da kansu da kuma riƙe aure.
Tana cikin aikin ne ta ji ƙarar wata tsohuwar motar Peugeot 406 ta tsaya a ƙofar shagon tana fidda hayaƙi.
Ba sai ta duba ba, ta san Mansoor ne.Mansoor matashi ne ɗan shekaru ashirin da takwas, mai sanyin hali da haƙuri. Yana sana’ar saye da sayar da yadudduka a kasuwar Agadez. Shi kaɗai ne a gidansu mai ɗan rufin asiri, kuma shi ne babban masoyin Tadala wanda ke burin aurenta idan abubuwa suka daidaita.
Ya shigo da sallama.
“Barka da yamma, Hajiya Sidiya.”
“Lafiya lau, Mansoor. Ya kasuwa?” ta amsa.
“Alhamdulillah.”
Daga nan ya juya ya kalli Tadala.
“Tadala, na fito daga kasuwa ne. Tunda kika ce yau zaki je gidan Fiza kuyi sallama, nace bari na zo na kai ki da kaina.Tadala ta ɗaga kai ta kalle shi.Ba tare da tayi magana ba ta miƙe ta shiga ƙaramin changing room na shagon. Ta canza zuwa wata atamfa mai kyau, amma daga gani ta ɗan yi mata ƙanƙanta saboda yadda jikinta ya cika.
Da ta fito, Hajiya Sidiya ta yi mata murmushi.“Allah ya kai ki lafiya”
Ta ɗauko wata ƙaramar kwalbar turare da wata yar ƙaramar leda.
gashi nan. Turaren matan Buzu ne. Idan kika isa Najeriya ki riƙa amfani da shi. Idanun Tadala suka cika da ƙwalla.
“Merci, Hajiya… Nagode sosai.”
Suka yi sallama suka fita.ta kalli tsohuwar motar Mansoor sai ta ɗan turo baki.iskar hamada mai zafi ta bugi fuskokinsu saboda motar babu A.C.Tadala ta saki tsaki.
“Ah, mon Dieu! (Ya Allah!) Wai Mansoor, shekaru nawa kana wannan kasuwancin amma ka kasa canza wannan motar taka? Gaba ɗaya zafi ya isheni .”
Mansoor ya yi murmushin .haba Tadala, kiyi haƙuri mana. Kin san halin da ake ciki a gida. Kwanan nan ma na biya wa ƙanwata Hindatu kuɗin makarantar Computer School. Ita ma ta sami mafita,Tadala ta juya ta kalli taga.
‘Aiki kenan! Kullum gidansu ke gaba da rayuwarsa. Idan na zauna a Agadez, wannan soyayyar ba za ta kai mu ko’ina ba sai talauci.ta ayyana a ranta
Bayan ɗan lokaci suka isa gidan Fiza.Ƙaramin gida ne da bangon laka da ya fara fashewa a wasu wurare.
Mansoor ya kashe motar.Ki shiga kiyi sallama. Zan jiraki.Ta ɗan ji tausayinsa a ranta.
Fiza ta tarar a tsakar gida tana hura wutar itace. Fuskar ta sha hayaƙi, hannayenta sun yi baƙi saboda aiki.
“Tadala!” Fiza ta faɗa cikin murna.
Suka rungume juna tadala ta sanar da ita cewa ta samu admission a Base University kuma mako mai zuwa za ta tafi Najeriya.
Nan take fuskar Fiza ta sauya.tadala, zan faɗa miki gaskiya. Ban goyi bayan tafiyarki ba.“Pourquoi? (Me yasa?)
kowa ya san Sadiya ba mai sauƙin hali ba ce. Tun tana zuwa hutu nan tana kallonmu kamar ba kowa ba Yanzu kuma kina son ki je gidan mijinta ki zauna?”Tadala ta ɗaure fuska.Non, ma sœur. (A’a yayata.)
cWannan ita ce damata
Ta numfasa.Ke kanki dubi rayuwarki, Fiza. Kin yi aure amma wahala ta canza ki. Kamar kin shekara arba’in.”
Fiza ta yi murmushin takaici.tadala ta ci gaba.mutane suna cewa wai mu matan Buzu ba ma auren talaka saboda kyawunmu. Amma ke yanzu, a wane hali kike?”
Fiza ta yi shiru.
“Shin me kika samu a wannan auren? Kalaman suka ɗan taɓa zuciyar Fiza.Ta sauke numfashi.
“Allah ya kyauta. Amma ni dai naga Mansoor yana da rufin asiri.Tadala ta girgiza kai.Wane rufin asiri? Wannan motar ce? Duk kuɗin da ya samu a gidansu yake ƙarewa. Har Moussa ya masa maganar ya fito ya aure ni, ya ce bai shirya ba.”Ta ɗan yi shiru.Nifa fafutuka nake yi saboda ku. Ba zai yiwu talauci ya ci gaba da mana rashe a rayuwa ba.”
Fiza ta zuba mata ido.A karo na farko ta ga irin girman burin da ƙanwarta take da shi.Tadala ta ciro wasu kuɗi kaɗan.Ga wannan ki riƙe. Kuɗin sallama ne da Hajiya Sidiya ta bani. Ta miƙa mata biscuit.Kuma idan Hafsa ta dawo, ki ce mata Anty Tadala zata yi kewarta. Ki ce mata ina sonta sosai. Fiza ta yi murmushi.Kowa ya san irin ƙaunar da Tadala take yi wa Hafsa, ɗiyarta tilo.Da kyar suka rabu.
Bayan sun fito, Mansoor ya kai ta gidan aminiyarta Kubra,tana zaune a ƙofar gida..
tadala
Suka rungume juna.Kubra ta fashe da kuka,ashe da gaske ne zaki tafi ki banni? Waye zai riƙa taya ni hira? Waye zai saurare ni?idanun Tadala suka cika da ƙwalla,ta kama hannunta Ne pleure pas, ma chérie. (Kada ki yi kuka, masoyiyata.)Karatun nan shi ne mafitata. Zan riƙa kiranki. Kar ki manta da ni.kubra ta share hawaye tana gyada kai.
Bayan sun isa gida, kafin Tadala ta fito daga motar, Mansoor ya kashe engine.Ya juyo ya kalle ta idonsa cike suke da damuwa ya ciro wasu kuɗin CFA dake naɗe.… gashi nan. Ki yi guzurin hanya ,Ta dubi kuɗin.
Amma Mansoor
“Ki karɓa.”Ya haɗiye yawu.Abu ɗaya nake roƙonki. Kin san ina sonki. Idan kika je babban birni, zaki ga maza masu kuɗi da motoci. Kar arzikin birni ya sa ki manta da masoyinki na hamada.”
Tadala ta kalli fuskarsa.
Wani irin tausayinsa ya ratsa ta.
Ta karɓi kuɗin.
Merci beaucoup, Mansoor. (Nagode sosai.)”
Ta yi murmushi,Zan kiyaye ta shige gida.Mansoor ya ci gaba da kallon bayanta har ta ɓace daga gani.
A tsakar gidan kuwa, ta tarar da Hajjo zaune kan tabarma Idanunta sun kumbura saboda kuka, tafi son tadala a cikin yaranta.
Ta gama shirya mata wata kulli na musamman mai ɗauke da tsabar daka da man shanu na asali.
Malam Attaher ya gyara zamansa.
Tadala.
Oui, papa? (Eh baba?)”
Gashi zaki tafi Najeriya. Abu ɗaya nake umartarki da shi: ki yi wa Sadiya biyayya. Ki yi karatunki cikin mutunci. Kada ki jawo mana abin magana.”
“Oui, papa.”
Hajjo ta miƙa mata kullin.
“Wannan ki kai wa Sadiya. Wannan kuma ki kai wa yayata Adiza. Ki ce musu ina gaishe su.”
Tadala ta karɓa.
Ta sunkuyar da kanta.
“Oui, Uma… Insha Allah.”
Malam Attaher ya sanya mata albarka,Aghali ya shigo yana kuka ya rungume ta.Da wannan ta kwana cikin fargaba da ɗokin sabuwar rayuwa.
Washegari, Moussa ya ɗauki akwatin ta ya kai ta Niamey.Daga can ta hau jirgin sama zuwa Abuja.
A filin jirgin saman Abuja, mutane da dama sun tsaya suna kallonta.
Tadala ta fito sanye da ainihin kayan matan Buzu.Doguwar riga mai launin shuɗi, da ƙaton mayafi na mutanen hamada,Gashinta mai tsayi ya fito ta ƙarƙashin mayafin.
Idanunta masu kama da an shafa musu kwalli na asali suna haskawa.
Kyan fuskarta da yadda take tafiya ya sa mutane bin ta da kallo.
Malam Awaisu, direban gidan Alhaji Kamal, ya gane ta cikin sauƙi.
“Ke ce Tadala?”
“Oui.”
Ya karɓi akwatin ta cikin girmamawa.
Lokacin da motar ta shiga ƙatoton gate ɗin gidan Alhaji Kamal a Maitama, Tadala ta kusa suma.Ta kalli mansion ɗin,Ta kalli lambuna.
Ta kalli motocin alfarma.
Wani irin zafi ya turnuke zuciyarta.
“C’est incroyable! (Abin mamaki )
Anty Sadiya muguwa ce! Tana zaune cikin wannan daular, ta bar mu a Nijar muna fama da yunwa da ƙurar hamada! Ta ayyana a ranta
“Shekara biyu ina roƙonta…
muryar awaisu ne ya dawo da ita ya mata jagora har falo
sannu da zuwa, Tadala.”
“Merci, Anty.”
Safa da Marwa kuwa suna gefe suna kallonta ,Da suka ga yadda take kalle-kallen falon cikin rashin sabo, sai suka kalli juna suka ƙunshe dariya.
Mami ta ce:“twins … ku kai mata kayan ɗakinta.”
biyo mu, Cousin din mami suna aka buɗe mata ƙofar ɗakin, Tadala ta tsaya cak Babban gado,A.C.
Wardrobe,Madubi,L-shaped sofa.
Ta rasa me za ta ce.Ta taɓa gadon a hankali.
“Mon Dieu… c’est magnifique! (Ya Ubangiji… wannan ya yi kyau sosai!) Safa da Marwa suka yi murmushi.
“Ki huta. Bintalo zata kawo miki abinci. suka fita suka sake ƙunshe dariya.
Bayan ta yi wanka, aka kawo mata fried rice da chicken. ta kai loma ta farko baki…ƙwalla ta cika mata ido.Ta tuna uma da papa .Ta tuna tuwon hatsi..da suke chi tana cin abincin tana kuka a hankali,Daga baya, da sanyin A.C ya ratsa ta…
Barci mai nauyi ya ɗauke ta safa ta taɓe baki.
“Mami, ashe cousin ɗinki typical villager ce.”
Mami ta yi dariya.
She will blend with time.
Marwa ta ce Amma dai gaskiya tana da kyau.”
Mami ta tsaya tana kallon madubi,Ta yi murmushi.
“Eh. A familynmu babu wacce ta kai Tadala kyau. Moussa ma idan kika gan shi, duk da talauci ya ci kyan sa,Mami, Moussa ya yi aure ne?” Safa ta tambaya,Wani kallo ta yi mata,Eh. Amma gobara ta tashi a gidansa yayin da yayi tafiya. Matarsa da yaransa uku duk suka rasu.”
“Subhanallah…” Safa da Marwa suka faɗa a tare.
Mami ta sauke numfashi chan kuma ta yi murmushi.
, idan Tadala ta gama Base University, maybe ta haɗu da ɗan banker ko wani mai kuɗi ya aure ta… at least ta kafa wa familyn su tarihi su fita daga talaucin can.”